← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 118

Sashe 13

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Baffa ne ke kaiwa yana dawowa sai sura masifa yake Mami kan ta a ƙasa Amma ke bashi haƙuri Junaid dai bai tanka ba. Ya ce "A zuri'a ta jinina har na haifi ƴar da zata nuna tafi ƙarfinmu? Wallahi ba a haifeta ba idan har ni uban Ridayya ne kuma ta haifu wallahi tallahi sai na raba aurensu da yaron nan gwara ta zauna a gabana har ta mutu babu aure" ya juya kan Mami ya ce "Babu shasha wacce bata san darajar ƴarta ba irinki Mami, ni ba haka na tashi naga ko wacce uwa na yi ba, amma kin zuba idanu ba ki da wata asara ko gawarta za a kawo miki sbd ba ki san wahalar rainonta ba" Mami kanta a ƙasa Zainura sai kuka take ganin yar da ake wa babarta faɗa kamar za a dake ta. Baba ƙarami ya ce "Saurara Bawan Allah Fatima bata da wani laifi, a haka kuka ɗora ta tun zuwan Ridayya duniya,kuma da kake hayaƙin baki a kan taƙi ɗaukan mataki daman hakƙinka ne kwatarwa Auta ƴanci"
Baffa ya ce "To wallahi idan har ina raye sai na kashe auren Ridayya" Ya É—auki waya ya shiga kiran layin Ridayya ba jimawa aka É—auka Zameer ya ce "Barka da yamma Baffa"

"Ina ƴata? Ka ce ina buƙatar ganinta yanzu yanzu a gida" Zameer ya ce bari na bata wayar ya cire wayar daga kunnensa ya fara cewa "Wife... Wife sweetheart Baffa yana kira" ya ɗauki seconds kafin ya mayar da wayar kunne ya ce
"Baffa wai bata buƙatar magana daku, ta haƙura daku kuma ta yi nisa daku kamar yar da ta yi muku alƙawari" Wani tari ya turnuƙe Baffa da sauri Mami ta ɗauki ruwa ta bashi ya girgiza kai yana ture hannunta ya ce
"Ni mahaifinta? Ni Ridayya take faɗawa haka ashe girman haukanta ya kai haka?" Idanuna ya sauya Baba ƙarami ya ce "A kul ka zubar da hawaye saboda ita, idan ka yi hakan to ka bata lasisin ƙara lalacewa ka yi addu'a sharrin soyayyar zamani ne kawai" Ya jinjina kai ya ce "Ku shirya gabaɗaya a yau ɗin nan zamu tafi Rano duba Hajiya Junaid harku gabaɗaya ku shirya a faɗawa Balkisu, Zuhura Ustaz ya ce zai bimu daga can Lagos ɗin zamu bar wa Ridayya garin na wasu lokaci. Nan da suka fara shirin tafiya Rano a gaggauce gabaɗaya familyn banda Ridayya da Ustaz.
Mami kuka take sosai ta cikin waya ta ce "Haba Yaya A'isha ya ake so na yi, ni da Ridayya bamu da wata shaƙuwa ina buƙatar ƴata ina buƙatar tattaunawa da ita"

"Ki je gidan nata kafin ku shige Ranon" Tana kuka ta ce "Baffa ba zai barni ba, ya É—auki zafi ban san me mijin Ridayya ya faÉ—awa masa ba"
Yaya A'isha ta ce "Fatima tun farko kin yi sake a yanzu kuma kafin ki gyara kuskurenki abu ne mai wahala raina ɓaci yake idan na zo gidanki amma ni zani gidan Ridayya ɗin ki kwantar da hankalinki" Mami ta ce
"Idan har ban mutu saboda baƙin ciki ɗa namiji ba, to tabbas Ridayya ba zata mutu ba, hakƙina akan ubanta ke bibiyar tata rayuwar ina mata fatan alheri a rayuwarta Ubangiji ya kawo mata sassauci"

Ridayya kamar an tsikare ta haka ta miƙe tana saka hijabi Zameer ya kalleta ya ce "Ina za ki"
Kai tsaye ta ce "Wajan Mami ina buƙatar ƙarin haske ina son ta fahimtar dani abinda na gaza fahimta"
Ya dinga kallonta mamaki ya cika shi jin yau ta ce Mami ba Amma ba, ya ce "Tab, Baffa ya dawo na je gaishe shi ba, amma ba kiga korar karen da ya yi mini ba, cin mutunci ta uwa ta uba kuma ya ce ko da wasa ya ganki a gidansa wallahi sai ya tsine miki" Zaman ƴan'bori Ridayya ta yi kanta ya kulle ta rasa wanne irin hali take ciki ne? Tana buƙatar zama a fayyace mata ma'anar so da ƙauna, so da birgewa da kuma soyayya ta gaskiya tana buƙatar ta fahimci mene take na kuskure. Kuka ta rushe da shi kamar ta yi hauka "Na shiga uku Baffa don Allah kar ka tsine mini zan dawo gare ku wayyo Allah na" Ficewa ya yi. Zainaba ta shigo da kwanon abinci ta ce "Ridayya don Allah don girma ki bani tarihinki wacece ke? Ki bani labarin rayuwarki da aurenki da Zameer don Allah kullum da kwaɗayin jin hakan nake kwana" Cikin kuka Ridayya ta ce "Babu komai a rayuwata sai tarin baƙin ciki da takaici sai baƙin cikin labarina ya haddasa miki ciwon zuciya ku yi mini uzuri a duk abinda na aikata wallahi ina cikin hankalina ko a mafarki bana ƙaunar tuna rayuwata ta baya" Kuka itama Zainaba take sosai ta ce "Wallahi ina tausaya miki ina jin tausayinki kayan haushinki da takaicinki ke mini yawa yana danne tausayin ji nake kamar na jaki na lakaɗa miki mugun duka wallahi, don Allah ki bani labarinki" Ridayya ta ce "Zan ba ki amma gobe da alƙawarin za ki riƙe mini sirrina" Zainaba cike da gulma da son jin zance ta ce "Kin yi alƙawari? Gobe da yaushe kuma kyan alkawari cikawa" Ridayya ta jinjina kai, a yanzu burinta bai shige ganin Mami da Baffa tana jin ko za a kasheta gobe sai ta je gida sun gana da Mami...

Tunda suka ɗauki hanyar Rano babu mai magana a babbar mota suke ciki gabaɗaya family guda ɗin, daga Kano zuwa Rano tafiyar 1 hr 18 min (68.7 km) ce kuma cikin dare suka tashi, a karo na farko Baffa ya ji wani matsanancin tausayin ƴarsa zuciyarsa ta shiga zullumi da zarar ya dawo zai dawo mata da duk abinda ta rasa a rayuwa. Junaid dake driving ya ce "Ustaz fa ba za shi wata Rano ba Baffa dabara kawai ya yi maka" Yaya Zuhura ta ce "Kai kam Junaid ka sakawa Ustaz idanu kamar wani sa'anka" Gabaɗaya cikin motar suka saka dariya banda Mami da Baffa Zainura na jikin Mami idanunta, Junaid ya shiga duba lokaci a wayarsa ɗaguwar da zai yi yaga wata ƙatuwar tirela tayo kan motarsu gadan-gadan tirelar na ƙoƙarin kaucewa motar su Baffa na ƙoƙarin kaucewa a ƙoƙarin Junaid na tsayar da motar a tsakiyar titi, gabaɗaya ya danne giyar motar kai tsaye ta yi ƙarƙashin tirelar Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Gabaɗaya tirelar ta bi ta kan motar ta danne jama'ar ciki baka jin komai sai salatin da jama'ar motar ke yi wasu na ihu a hankali aka daina jin motsin kowa sanda tirelar ta mirgina ta ƙarasa danne kan motar su Baffa....

Don Allah idan kun karanta a yi sharing please saboda masu nema a kuma yi comment kar ku manta free book ne.

08164069385
Na'ima Sulaiman Sarauta

*✿ MUNAFUKIN MIJI ✿*
Nimcyluv@Arewabooks

Page 8
BRIGHT PENS🤙🏼 free batch

Yau duk wanda ya karanta ina son ya shiga Tiktok ya yi mini comment ta can👇🏼👯🏻‍♀️
https://vm.tiktok.com/ZM6Q2SoAj/

Hatsari ne wanda duk wanda ya gani sai ya girgiza, wasu su kuka da faruwa mummunan al'amarina na yiyuwar rasa rayuka da dama, masu matsanancin tsoro ta iya yiwuwa su yi mafarkin yar da babbar motar ta bi ta kan, ta su Baffa. Titin ya cika da jama'a aka dinga parking da abeben hawa, da ƙoƙarin ceto wanda Allah ya nufa suke raye.
Da ƙyar aka samu damar zare motar jini na zuba sosai daidai ambulance suka danno kan motarsu, basu tsaya tantance akwai masu rai ko duk sun mace ba duka aka kwashe su zuwa mota aka nufi asibiti mafi kusa da wajan da hatsarin ya afku. Tsoran Allah ya ƙara shigar wasu.

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, yanzu haka ahhali guda ne irin tafiyar da ba'a so, duk wanda ya yi saura a dangin ji zai yi kamar shi ma ya mutu ya huta, sun fito lafiya babu wanda ya taɓa tunanin lokacin mutuwarsa ya yi, kana tafe ne baka san kwana ya ƙare ba, Allahu Akbar wayyo Allah!"
Wata mata dake gefen mota ta dinga faɗa kuka yaƙi tsaya mata hankalinta ya tashi ainun. Mijinta ya riƙe ta ya ce "Ki kwantar da hankalinki Madam, kar ciwonki ya tashi kuma, shi ya sa a kullum a kodayaushe ake son bawa ya dinga aikata abin arziƙi domin mutuwa bata sallama balle kasan ranar tafiyarka lahira.
"Allah sarki ni fa sai naga hannun wata kamar ya cire ga kan wani ya yi daga-daga wallahi zai wahala idan duk basu mutu ba" Nan da nan hankalinta ya ƙara tashi ta rushe wa mijinta da kuka da ƙyar ya lallaɓa suka shiga mota. Ana ta rai da neman taimako, a gefe guda kuma wasu sun taro sun sace kayan mamatan babu tsoran Allah da tunanin suma za su je inda sauran suka je.

Emergency ɓangaren ƴan hatsari aka nufa da su, aka shiga duba wa ko akwai sauran masu rai, aka bar likitoci su yi aikinsu, ƴan'sandan kuma suka shiga fafutukar inda za su gano ƴan wanne gari ne mamatan, da inda za su samu wani nasu amma har gari ya waye babu wani Information da zai tabbatar da su waye su, har lokacin ba'a samu cikakken bayani na kasancewar wasu a raye ba, ko duk babu.
Chapter 13 · 0% Book details