Sashe 90
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ya kasa ƙarasa maganar tsoro ya shiga zuciyar Ridayya ta mance yadda ake ta manta sam kuma bata shirya ba, uwa uba ga ɗinkin da akai mata ga kuma gyaran data sha a Maiguduri. Hankalinta ya tashi ta fara shassheƙar kuka Ustaz bai ma san me take yi ba yana ƙoƙarin maida Ridayya matarsa ta halak kuma ta sunna kamar gilmawar walƙiyya haka photon Zameer da Ridayya ya faɗo masa a cikin idanunsa sanda ya gansu turmi da taɓarya cikin hanzari ya miƙe tsaye yana dafe bango ya fice daga ɗakin bakiɗaya....
Barkanmu da sallah🤓
Ku yi haƙuri na jina shiru, wallahi ayyuka ne suka sake ƙaruwa. Kun san me rai da buruka wani aiki da na yi apply tuntuni shi ne na samu aikin yanzu nake ta jigilar zuwa seminer. Bana son fara typing na tsaya, but yanzu Allahamdulillah da taimakonku da haɗinku za mu kai zuwa gaci a ci-gaba da yin comment da sharing. A kuma yi haƙuri da abinda za a karanta marubuci baya fara labari ba tare daya tsara shi ba komai aka karanta daman a haka yake dole zai kasance.
Comments
Share fisabilillahi.
*MUNAFUKIN MIJI 39*
Mikiya Writers Ass
Bright pens free batch
Nimcyluv
*Masu buÆ™atar Munafikin miji daga farko ku yi following channel É—ina👇ðŸ»*https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T
Muna yin tallah don ƙarfafa kasuwancin jama'a, a saka maka a status mai 1k to above viewers muna sakawa channel mai 2k zuwa sama followers sai kuma a littafi. Idan kayan mata kake shiryawa muna yi mun sanya shi a kayan da tauraruwa ke using dashi, idan bags ne, shoes ne anything... Ku yi magana ta wannan number 08164069385
Ajjiyar zuciya Ridayya ta sauke tana wurƙila idanunta ƙirjinta sai ɗagawa yake ta jima kafin ta dawo daidai ta ce "Na shiga uku Abbiey me kake shirin yi?"
Can ƙasan zuciyarta ta ce "Ke ɗin fa matarsa ce, yana da iko dake Ridayya, idan bake akwai Mardiyya"
Tunawa da ta yi tana da wata wai kishiya hankalinta ya yi masifar tashi, tsoro ya wanzu a zuciyarta yanzu idan ya barta zai iya zuwa wajan Mardiyya yana da wannan ikon, ƙirjinta ya motsa wani abu mai kama da tsoka ya motsa a gefen ƙirjinta hakan ya bata tabbacin bata mace ba, tana da raguwar zuciya a ƙirjinta wacce babu shakka soyayyar Ustaz ce ta mamaye cikin tsokar da wajanta wacce ta haddasa bugawar ƙirjinta da ƙarfi fiye da bugawar agogo.
Sakkowa ta yi jikinta a sanyaye sai yanzu fitarsa ya dame ta, domin har zuciyarta bata da tabbacin abinda ya hana shi idda nufinsa a kanta, tana tsoro da shakka ƙwarai. Jiki a sanyaye ta nufi parlour amma the parlour is empty ba kowa a ciki, sai ɗumin hiter saboda sanyi. Ta bishi?
"A'a Ridayya kar ya yi miki faÉ—a" zuciyarta ta yi saurin faÉ—ar hakan.
Ta marairaice fuska bata sake bada ƙofar wani tunanin ba, kai tsaye ta nufi ƙofar da take da tabbacin yana ciki. Ƙarar saukar ruwan shower da ta ji ya sa ta san yana ciki da alama kuma wanka yake ta yi can ta zauna. Ustaz ya sauke numfashi sai a lokacin ya lura bai kyautawa kansa da zuciyarsa ba, kokawa yake ta yi da zuciyarsa amma wani irin zafi da yaji-yaji yake ji a tsakiyar ƙirjinsa ɗanɗanon bakinsa ya sauya, bai san me ya sa tunanin abub ya faɗo masa ba, tunda ba zina ya rusketa tana aikatawa ba, sunna ce, sunna mai ƙarfi tunda mijinta kuma koba komai Ridayya ba zata taɓa wofintar da tarbiyyarta ba.
Ya buÉ—e idanu wanda suka shige ciki a fili ya ce
"Allah ka yafewa Ustaz, na yi rashin uzuri ka yafe mini bisa tunanina"
Gyara zaman bathrobe ɗin ya yi ta zauna da kyau a jikinsa, ƙamshin shower gel na fita daga jikinsa, a baƙin ƙofar toilet ɗin ya cire bedroom slippers ɗin ya saka normal slipper na ɗaki yana fitowa zuciyarsa ta doka da ƙarfi ganninta zaune idanunta cike da hawaye, idan da akwai abinda ba zai jure ba shi ne zubar hawayenta.
Kasancewar shafa baya cikin ɗabi'arsa ya saka ya ƙarasa bakin gadon ya zauna, kamar zai yi shiru sai kuma ya juya ya kalleta a taushashe cikin lallausan harshe da murya mai nutsar da sabuwar zuciya a shiga soyayya ya ce
"Mene? Are you okay?
Lafiya kike?"
Ta yi shiru ya kama hannunta ya damƙe cikin nasa
"The tears? Hawayen mene? Nine? Laifi na yi?
A nutse yake magana, laɓɓansa na ware wa ɗaya bisa kan ɗaya amma zuciyarsa rawa take, bai san me ya sa bashi da ƙarfin qwiwa ko kaɗan akan Ridayya ba, tsoro ne hakan? Ko kuma tsananin soyayyarta ce ta hadda masa, ko raunin dake tattare da yarinyar ne?
"Abbiey me ya sa ka juya mini baya?"
Ya waro manyan gajiyayyun idanunsa masu cike da bacci da kuma abinda ke kai kawo a jikinsa, ya sake shigar da hannunta cikin nasa yana raba musu É—umin ruwan wankan, ya ware idanu a kanta ya kasa cewa.
"May be i was wrong da nake tunanin zan samu farinciki wajanka Abbiey"
"Shhhh Ridherh"
Ya ɗora yatsarsa a laɓɓanta baya son jin komai, hawayenta ya sake sakkowa bai yi magana ba ya miƙe tsaye ya kashe hasken bedroom ɗin ya dawo ya kwanta tsakiyar gadon, yana daga kwancen ya miƙa mata hannu ta yi saurin cewa
"Ba za ka yi mini komai ba?"
Ta cikin zuciyarsa ya ce "Jaririya ba ki da hankali, ke É—in halaliyyata ce"
A fili kuma ya lumshe idanunsa ya buɗe alamar “Eh"
Gadon ta hau ya ɗora kanta a ƙirjinsa ya rufe ta da hannayensa, babu wanda ya yi magana cikinsu sai shi da hannayensa suke shafa sumar kanta, ya kasa daurewa saboda ƙamshin turarenta wanda bai taɓa jinsa ba ya addabe shi, haɗin turaren amare ne daga (Hajiya Nana).
Misalin 3 daidai ya zame ta daga cikinsa yana ji tana motsi saboda raba jikinsu da ya yi, ya ja mata pillow. Ustaz bacci ya ƙaura ce masa ya yi alwala ya shimfiɗa ladduma Nafila yake ta yi har lokacin yin Assalatu ya yi.
Samun kansa ya yi da yin addu'a tsakaninsa da Ridayyerh, ya ɗora goshinsa a ƙasa yana kallon Alƙibila da murya ta neman taimako da ɗaukin Ubangiji ya ce.
"Ya Ubangiji ga Muhammad-Bilal Tahir na neman taimakon ka, ni ɗin bawa ne gare ka, mai rauni, mai damuwa, na san ka fini sanin damuwata, ban kuma raina ni'imar da ka yi mini ba, ni Ɗan'Adam ne mai buri da sanya abu a zuciya, ni almajiri ne kuma bawanka mai tsananin tsoron haɗuwa da kai saboda rashin tabbas. Ya Mujibudda'awati ka sanya hannu cikin lamarina. Ina tsananin son matata Ridherh, bana son ya kai ni ga halaka, ina tsoran soyayyar zamani, Allah ka tabbatar da dukkan alheri ga rayuwar aurenmu, idan aure na da Ridherh alheri ne kuma akwai rabo, Ubangiji ka cire mini abinda ke mini yawo a zuciyata, ka rage mini kishinta, ka tsayar mini da zuciyata waje guda, idan alheri ne auren nan namu ka bani ikon mayar da ita cikakkiyar matata ta sunna, ka yi mana tsakani da sharrin mutum dana aljan, ka sanya farinciki da walwala a rayuwarmu, ka sanya mana nutsuwa yarda da juna, ka kaɗe mana fitina, ka sanya matata ta soni ko kwatan son da nake mata ne, domin ba zata mini irin soyayyar da nake mata ba. Idan aure na da Ridherh babu alheri Ubangiji ka fini sanin komai ka mayar mini da mafi alheri ya zuljalalu wal ibkar. Allah buƙatar al'ummar jihata akan zamana gwamna idan alheri ne ke kirana ka tabbatar mini dashi,, idan ba alheri ka nisanta ni daga wannan al'amarin, gani gabanka ya Allah ka taimake ni, ka tausaya mini, ka sanya hannu cikin lamarina"
Ya jima yana addu'ar har sai da ya ji damshi a fuskarsa ya gamsu kana ya ɗago ya shafa ya fara azkar idanunsa a kanta. Kamar yadda aka ce dukkan wani musulmi idan har Assalatu ta yi dukkan baccin da yake sai ya motsa hakan ce ta kasance ga Ridayya, bakinta ɗauke addu'a da salati ta shiga motsawa har ta buɗe ido, ta shafa ta ji ta ƙanƙame pillow ta kwaɓe bakinta.
Zamewa ta yi daga cikin duvet ta sakko ƙasa, mamakin ganin kayan bacci ya kamata kullum Abbiey baya gajiya da sauya mata kayan bacci? Kenan yana kalle mata jiki? Innalillahi ta yi saurin rufe ƙirjinta.
Bata san yana ciki ba ta ji ya yi gyaran murya ya ce
"Sai dai ki ɓoye wani abun ba wannan daya zama t.v ɗin Muhammmmd ba"
Ta tura baki "Kai Abbiey ba kyau"
Ya cije laɓɓansa yana duba lokaci "Uhm Ustaza manya, bari na je masallaci"
"To Allah ya tsare mini kai"
Ya yi saurin Juyawa ya kalleta ya ji me ta ce fuskarsa ta faɗaɗa duk da haƙurinsa bai bayyana ba. Ya juya ya nufi masallaci.