← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 118

Sashe 4

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dr ka sani gaba da kallo meke faruwa ne?"Dr ya jinjina kai a hankali ta ce "Ki yi haƙuri ke da Bilal, na yi magana cikin ɓacin rai" Ammi ta girgiza kai ta ce "ƙara faɗar mini da gaba kake, maganarka bata gabana kai da Bilal na san yana sane da ita, Bilal ba mijin Ridayya bane, mijinta ko ƙafarsa bata shigo asibitin nan ba har yanzu" Dr ya dinga kallon Ammi kana ya ce
"Kenan yana sane matarsa ta sha fiya-fiya shi ne ya yi sanadiyar suman da ta yi ya ƙarasa taɓa abin cikinta, banda tana da ƙararren kwana da tuni wata maganar ake ba wannan ba, idan takunka bai ƙare a duniya ba daman sai dai kawai sha wahala, amma maganar gaskiya Hajiya Ridayya tana cikin wani hali, dole a kula da ita"
Tunda ya fara magana take kallon bakinsa kamar ta fahimta kamar bata gane ba, kalmar fiya-fiya ta tsaya mata a maƙoshi, Ridayya da shan fiya-fiya? Ko kuma Zameer ya bata?
Dr ya katse shirun ta hanyar faÉ—in "Za mu yi mata wankin ciki, violence ya yi yawa a zaman aurenta"
Miƙewa Ammi ta yi ba zata iya cewa ga sanda ta shigo room ɗin ba, gani kawai ta yi Junaid ya riƙeta yana faɗin
"Ammi lafiya? Gaggauta faÉ—a mana abinda ke faruwa" Girgiza kai ta yi idanunta cike da hawaye ko gabanta bata gani ta yi waje, sam bata lura da Zameer ba wanda ya shigo ba jimawa hakan kuma ya yi daidai da farkawar Ridayya.
Zameer ya matsa dab da Ridayya yana daidaita nutsuwarsa, a hankali take binsa da kallo kamar mai son gano gaskiyar da yake ɓoye a zuciyarsa? Ta runtse Idanunta lokacin data tuna maganar Mardiyya, ko a mafarki ba zata taɓa yarda Zameer zai ci amanar so da ƙauna, haɗi da yardar da take masa ba. Magana take son yi ta gagara sai wani hawaye mai zafi daya shiga fito mata.
Zameer ya kama hannunta duka biyun ya ɗora a saitin zuciyarsa daidai inda take doka masa yana sarƙe numfashi zuciyarsa na tsukewa tare da curewa waje guda, ya rasa inda zai lalubo abinda babu shi ko kaɗan a zuciyarsa wanda zai nunawa Ridayya a hankali ya ce
"Karki nisa dani Mai sona" Ta girgiza masa kai da ƙyar ta ce
"Idan har na yarda ba zaka ci amanata ba meyasa zan yi nisa da kai?" Meer ya sauke numfashin da yake ta riƙe a nutse ya ce
"Zuwana na biyar kenan kina bacci, kin bani tsoro, idan kin barni ke kan ki ba zaki iya rayuwa ba"
Wani sanyi da nutsuwa Ridayya ta ji yana sauke a zuciyarsa, ciwon da ƙirjinta ke mata yana yayewa wani irin yardar Zameer ya ƙara ninkuwa fiye da ƙima a ranta.
"Ka siyar da É—an kunnen?" Ya yi shiru ta saka hannunta mai lafiya ta juyo da fuskarsa zuwa gare ta ta ce "Mene?"
A taƙaice ya ce
"Kunyarki nake Ridha, da kunya na ce miki ɗan kunnen goal ɗin ki ya faɗi" murmushi mai kyau ta yi wanda ke ƙara fiddo ramarta ta ce
"Haba dani da kayana duk mallakina ne Rayuwata, daman kai zan bawa kuÉ—in ka siya mana kayan abinci da iccen wanka sbd haihuwa kuma kaga yadda Allah ya yi" Ya jinjina kai
"Kamar kin san ina buƙatar kuɗi" Ta yi saurin buɗe ido ta ce
"Me zaka yi da kuÉ—in?"
Ya marairaice fuska yana sumbatar hannunta a hankali yake É—an sauya yanayi ya ce "Mai sona kike tambayata me zan da kuÉ—i, sbd kulawa dake matata" Ai Ridayya duk duniya ji ta yi ba macen da tafi ta zarra da samun miji kamar Zameer
"Ka duba ɗakina ƙasan filo akwai kuɗi" Da sauri ya fara girgiza mata kai ya ce "Haba idan na ɗauka ke kuma fa Mai sona?" Ta haɗe fuska ta ce "Ka fini buƙata,kuma ina yin dashi da ribar ƴar tsala na kusa ɗauka"
Ya yi murmushi ya ce
“I love you mai sona”

"Kai" Suka ji an furta
Gabaɗaya suka juya Bilal ne tsaye bakin ƙofa cikin waganbari da ya yi masa kyau hannunsa zube cikin aljihu, idanunsa akan Zameer ya ce
"Zo ka fita" Zameer ya ce
"Matsayinka nawa?"
"Na wan matarka" Zameer ya miƙe tsaye idanunsa akan Ridayya ya ce "Ridayya kina gani, ƴan uwanki baza su taɓa barina dake ba, kullum cikin jure wulaƙancin su nake saboda kawai ina son ki, sau nawa ina zuwa suna hanani shigowa wajanki?" Zameer ya girgiza kai yana ƙoƙarin ganin ya bayyana rauninsa a fili yadda Ridayya zata gazgata maganar shi ya ce "Cewa sukai ni na ɗora miki fiya-fiya wai don na kashe ki, Ridayya na san lokacin da kika sha fiya-fiya, tun safe na fita ina fafutukar ganin na rufa mana asiri na riƙe ki da kyau amma basa gani, ɓaraho suke son na zama? Ko ɗan fashi da makami? Me ya sa Ridayya me na yi ƴan uwanki?"
Ridayya jikinta ya fara rawa, Junaid mamakin munafurcin Zameer ya kashe shi a tsaye kamar wata mace? Bilal ya ce
"Ka fita, ka zo ka fice daga room É—in nan"
"Ba zan fita ba, wajan matata na zo" Bilal yana zuwa ya É—auke Zameer da mari, har ya É—aga hannu zai rama sai kuma ya fasa ganin yadda Ridayya ta runtse Idanunta. Bilal ya ce
"Idan kai baka san darajar rayuwar Ridayya ba kabarwa wanda ya san darajarta" Zameer ya ce "Ok kana nufin na saketa ka aura? Aure zaka kashe mata ashe" Junaid ya san da gayya Zameer yaƙi rama dukan, sbd idanun Ridayya banda hakan sai dai su daki juna. Bilal ya dunƙule hannu ya kaiwa bakin Zameer naushi da ƙarfi ya ce "YES! I do love her, I love her ka saketa idan ka haifo"
“Bilal!!" Ridayya ta kira sunan Yaa Bilal, wanda hakan ya yi daidai shigowar su Bilkisu da Zuhura, Ammi, Mami da Baba ƙarami, sai Khairy da Mama da Karimatu.
Babu wanda bai girgiza da jin sunan Bilal gatsal a bakin Ridayya ba, domin har Baba ƙarami baya iya cewa Bilal sbd darajarsa da suke gani kaf dangin shi ne babba.

"RIDAYYA!" Mami ta kira sunanta, ta nufeta zata daketa Baba ƙarami ya ce "Karki fara Fatima, ba kiga mijinta ake duka ba?" Ammi ta ce
"Babu yadda za a yi Uban masu gida ya daki mijinta ba dalili kasan halinsa ba komai yake damunsa ba, yarinya ta fifita miji akan kowa?"
Bilal ji ya yi idanunsa na neman ɗaukewa, baya son yarda Ridayya ce ta furta wannan sunan daga bakin da yake jinsa har rai da mutuwa, wani baƙin ciki ya wanzu a zuciyarsa ƙirjinsa ya yi masa nauyi.
Cikin rashin sani ya sake dunƙule hannu ya kaiwa Zameer naushi nan take bakinsa ya fashe, wani irin Miskilin Meer ya yi.
A gigice ta fisge ƙarin ruwan, jini ya fara zuba sam bata damu da hakan ba, idanunta cike da wutar son mijinta..
"BILAL!" Ta kira sunan Yaa Bilal ta ce
"Mijina kake duka kamar ɓarawo haka? Da gaske mijina kake duka? Daman kai kake hana shi zuwa gidanmu?"
Da mamaki gabaÉ—aya mutanen wajan ke kallon Ridayya Bilal ya ce
"RIDAYYA! Sunana kike kira haka...,"
"Na faɗa BILAL, ba haka ne sunanka ba? Bana ƙaunarka kamar yadda baka ƙaunar mijina, ba zan kai ka ƙara ba, Allah ya isa dukan mijina da ka yi...," Wani mugun mari Junaid ya kai mata ya ce "Banza, akan wannan mijin? Daman ni na sallamaki duk wata damuwarki is never be my headache"
Ridayya ta fashe da kuka ta ce "Ko namana zaku yayyenka wallahi ina ƙaunar mijina, ina ƙaunar shi fiye daku" Mami kallon ƴarta take tana jin wani takaici na rufeta yanzu abin tsoro yake bata, anya Ridayya lafiya take? Bata haukace ba, Zuhura murmushin ɓacin rai take wacce irin soyayya ce mai hana ganin laifi yaushe Ridayya zata yarda Meer ba ƙaunarta yake ba?
Ammi ta kalli kowa idanunta ya sauka akan Khairy sai kuma ta juya ta kalli Bilal da jiri ke neman kada shi ta kalli Ridayya data riƙe hannun Meer a fili ta ce
"Komai ya zo ƙarshe In sha Allah a yanzu ba sai anjima ko gobe ba Zameer zai saki Ridayya ba saki ɗaya ba saki uku muke buƙatar ya yi mata yanzu!.....

Page 3

Ridayya ji ta yi ciwon da zuciyarta ke yi mata ya dawo sabu fil, cikin wani irin rikitaccen tashin hankali daya gama mamaye ilahirin lungu da saƙo na ƙofofin halittar ƙirjinta, wacce take ƙara kissima mata soyayyar Zameer a kullum.
"Kada ki nemi kashe ni da rai na Amma, kada ki ce zaki hukata ni ta hanyar da zuciya, gangar jikina ba za su É—auka ba"
Ganin amma taƙi yar da ta kalleta, ya saka Ridayya sakinta tare da
juyawa ta kalli Zameer dake tsaye, idanunsa cike da hawayen daya gama ƙirƙirar su a wajan ta ce "Kalamanki kamar fitar dalma haka suke sauka a ƙirjina Amma, rabani da mijina kamar bayyanar ranar mutuwata ce, wallahi duk duniya ba wanda nake so sama da Zameer idan ki ka cire Mami, ina ji a jikina bayan bautar Ubangiji; Allah ya halicce ni domin na rayu da soyayyar Meer, me ya sa kuke ƙoƙarin kashe ni da rai na? Bayan ina numfashi? Kuna kallona na faɗa muku ina son shi mene ribarku idan kun rabani da shi"

Ridayya ta ƙare maganar tana jan numfashi a wahale, komai nata ya yi tsayiyuwar sojojin da suke tsaka da fareti.

Murmushin baƙin ciki da kuma takaicin halin Ridayya Junaid ya yi, duk yadda ya tursasa zuciyarsa wajan ganin bata ɓaci ba, a kan haukan da Ridayya ke yi musu a cikin asibiti abin yaci tura. "Makauniyyar soyayya ko? Ridayya anya ba ki haukace ba? Kin san kalaman da bakinki suke furtawa Amma? Ko giyar wake kika sha kin yi tsararo ki sauke mana ita a nan, ramin da kika haƙa kin yi
kaɗan ki faɗa ciki da mu, sai dai ki kwashi turɓayar data rufe miki ƙofifin zuciyarki ki rufe kan ki da ita wallahi" A hargitse Junaid yake maganar kamar zai kai mata dukan ɓarin makauniyya.
Chapter 4 · 0% Book details