← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 118

Sashe 85

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi wallahi idan kika ce za ki ja-in-ja da wannan ƙaddarar to ranki zata ɗauka, ki sani Babban mutum ya yi nisan da ba zai ji kiran ki ba yanzu a shirye yake ya yi faɗa a kan abinda yake so, kuma ganinsa zai miki wahala zai miki abinda za ki yi kuka da kan ki I'm telling you ba a yi wa ɗan yau haka musamman akan soyayya a wannan gaɓar kurame suke zama"

"Yanzu dai saki nawa ya yi mata Allah ya sa ukunne kawai"

"Ba matsalarki bane wannan tunda kin saka ya yi sakin ya kuma bar miki gidan shikenan"

Ransa ɓace ya bar parlourn ya rasa meke damun matar tasa bai santa haka ba bai kuma san yaushe ta lalace ba. Sashin baya ya nufa inda bai fiya zuwa ba, daga nan kuma akwai ƙofar dake kai mutum kai tsaye zuwa bedroom ɗin Ustaz ba tare da kowa ya sani ba, tun kafin ya ƙarasa ya kira Tajj ya ce yana buƙatar ganinsa Allah ya sa kuma yana gari.

Tsaye ya samu Ustaz ya yi shiru idanunsa buɗe kansa kuma a ƙasa ya kalle shi na wani lokaci kana ya nemi waje ya zauna ya ce

"Muhammad-Bilal Tahir Rano dawo nan"

Kamar baya son ɗaga ƙafarsa haka ya jata ya zauna ƙasa wajan ƙafafuwan Baba ƙarami wani hucin zafi ke fita ta cikin bakinsa da hanci.

"Babban mutum me ya sa ka yi haka? Kar ka bani kunya har ka sare da wur wuri ashe daman soyayyar tatsuniya kake ma shalalen ko?"

"I have no idea father, bana shiga shiga fushin uwa"

"Kuma saki ba kyau, halak ne amma Allah baya son shi. Babu zunubi ko kaÉ—an a aurenku babu abinda Æ´ar'uwarka ta yi maka, a zahirance ma bata san matsayinka wajanta ba"

Ustaz ya yi shiru Baba ƙarami ya ce "Do something Abokina ɗaya tal, ka yi abinda zai bawa kowa mamaki ni dai ba zan ce ka rabu da Mardiyya ba domin tana da hakƙi akan ka, haka ba zan lamunci abinda ka yi ba"

A hankali ya jinjina kai don baya jin zai iya magana rauninsa gab yake da gama bayyana.

"Ina zaka?"

"Bana son zaman nan, zan je wani waje daban idan akwai alheri tsakanina da Ustaz tabbatas Ubangiji ya ba zai bar mu haka ba"

"In sha Allah. Ka je ka É—auki abinda ya dace Tajj yana waje zai yi dropping naka, nasan ba zaka iya driving ba"

Part ɗinsa ya shiga ta bayan ya ɗauki atms ɗinsa files ducoments da abubuwan da zai iya buƙata ya haɗa kaya cikin luxury trolley ya nufi waje. A tsaye ya samu Tajj shi da Zainu yana ta tsokanarta tana tura baki.

"Tab Yaya Ridayya É—in ce ta fini kyau, ana ta cewa ni kyakkawa ce"

Tajj ya buÉ—e ido ya ce

"Subuhanallahi amma masu faɗa tsoran Zainura suke, ai colour ɗinku sun yi yawa gari da society namu yanzu baƙar kala ake ya yi"

"TamÉ—ijam! Kawai ka fi son Yaya Ridayya kai da Yaya Ustaz"

"Yes we love her, saboda she is a durlin.....,"

Wani irin kallo Ustaz ya yi wa Tajj fuskarsa ta haÉ—e ta yi jajur Zainura ta ce

"Ina yini Yaya Ustaz"

Wata tsawa ya daka mata ita da Little dake hannunta suka firgita nan da nan Ustaz ya rikiÉ—e kamar ba shi ne fara'ar sisi babu a fuskarsa kamar an yi masa mutuwa. "Mu je na sauke ka"

Ya yi masa banza ya buɗe bayan mota ya saka kayansa ciki ya nufi ƙofar motar. "Ya ina ta magana ka yi shiru, ka bani key ɗin ko ka shiga motata ban fito da securities ba"

"Ka tsahirta mini kafin na watsa maka yatsu"

"Ikon Allah me na yi kuma ni ka zo ka yi wa yarinyar tsawa har yaro yana ihu ka zo kana mini faÉ—a? Daga zuwa aikin lada"

Tajj ya ƙwace key ɗin ya juya yana buɗewa MB USTAZ motar, kamar ba zai shiga sai kuma ya shiga ya yi wa motar key. Tajj shi kaɗai yake maganarsa Ustaz ji yake kamar ya yi bindiga a haka suka ƙarasa airport sai a lokacin ya juya ya kalli Tajj shi kuma ya ɗaga masa gira ya ce "Dole haka za a yi fa"

Hankalin Umma kwance tunda ta san aure dai babu shi ta zaunar da Mardiyya ta yi mata bita da zarar Ustaz ya sauka daga fushi ya dawo ta yi duk iyakar yinta wajan ganin sun samu daidaito kafin Æ´ar mayun ta dawo. Har sama da sati kuma babu alamar BM USTAZ numbers É—insa duka a kashe suke. Umma ta share tasan dole duk inda yake zai dawo ya sameta ne for sure.

Mami na zaune da yammacin ranar ita da Yaya A'isha da suke magana ta ce "Ina jin tsoro Yaya A'isha Ridayya har yanzu babu kulawar uwa a tare da ita, bata san ya kamata ba, ta rasa abubuwa da dama"

"Me kike tsoro ne Fatima?". "Aurenta da Ustaz bata san komai akai ba yana da kyau ta sani, gashi Umma bata ƙaunar Ridayya ko kaɗan ga Mardiyya ta fi Ridayya buɗewar ido wayo da ilimi da sanin kan duniya ina tsoro Ustaz ya rabu da Ridayya ina tsoran wannan ranar"

Yaya A'isha ta yi murmushi irin na manya ta ce "Bari na fara da magana mai muhimmanci ki daina mafarkin Ustaz zai rabu da Ridayya, su ɗin tamkar ruwa da iska ne, kamar Inuwa haka suke, haka kamar rayuwa da mutuwa haka su duka biyun suke, ƙaddararka zane suke dana juna. Ridayya matar so ce, Mardiyya haɗin Hajiya ne a kuma rashin Ridayya aka bashi Mardiyya, auren Mardiyya da Ustaz kamar auren cin amana ne ta yi shi wa kika taɓa gani ya ci amana kuma ya zauna lafiya? Ilimi kuma Ridayya za ta yi shi, za kuma ta waye ke kan ki zata ba ki mamaki musamman ta zama her Excellency"

"Her Excellency kuma?"

"Uhm ai abin duniya baya ɓuya tuni zance ya zaga ana son tsayar da BM USTAZ takarar gwamna"

Mami ta ce "Ikon Allah"

Yaya A'isha ta ɗauki waya tana buɗe furnitures ɗin da dukai order na gidan Ridayya ta ce "Ai da ruwan ciki ake jan na rijiya, abinda ya taɓa hanci dole ido ya yi kuka idan ta yi yunƙurin raba Ustaz da Ridayya to ɗanta zata rasa, ƙoƙari ɗaya za mu yi mu fahimtar da Ridayya Ustaz fa ba ubanta bane mijinta ne, idan har tana masa kallon uba to kunya ce zata shiga tsakani ta zama hijabi namiji kuma baya son kunya a zaman aure, balle kuma wannan Babban mutum ɗin daka gani ɗan Soyayya ne kuma za ku ce na faɗa"

"Kai Anuty shi da yake Ustazu malami"

"Zainura get out, sai nawa zan ce idan manya na magana ki daina saka baki ne?" Miƙewa ta yi ta fice. Yaya A'isha ta ce "Wannan ƴar autar taki ta cika kanzagi, da alama kuma kamar kin haɗiyi wake"

"Rufa mini asiri Yaya, Ridayya na haihuwa ni na haihu ai da kunya"

"To za mu gani ai É—an duma ne dole zai bayyana kansa, wannan karan maga haukan da kishiyarki za ta yi"

Murmushi kawai Mami ta yi suka ci-gaba da duba furnitures ɗin da sauran kayan da za su yi Ridayya da kayan sawa komai da komai daga ɓangaren dangin uwa. Bayan sun gama ta fito raka Yaya A'isha suka tarar da yaya Zuhura zaune tana rusar kuka kamar ranta zai fita Ammi sai masifa take mata ganin su Mami ya saka ta yi shiru cikin sakin fuska da yaƙe ta ce

"Hajiya A'isha kin fito ashe sannu da zaman É—aki"

"Yawwa sannunki da zaman gadi ana shan A.c" Yaya A'isha ta faÉ—a tana dariya tare da mayar wa da Ammi raddin maganarta.
Murmushi ta yi ta ce
"Ke kuma tashi wai fa surukar ta ce babu lafiya shi ne take wannan kukan kamar ni na mutu, ke kam an yi sakarar wofi"

"Allah sarki idan da kima uwar miji ai uwa ce" Yaya A'isha na faɗin hakan ta shige abinta Mami daman bata ce ƙala ba wayarta kawai take dannawa gabaɗaya nutsuwar Mami Ridayya ta ɗauke ta ciff ba abinda ta manta bata ɗauka ba a wannan ɓangaren.

Suna barin wajan Ammi ta ce "Wallahi tallahi sai kin koma gidan mijinki magana ɗaya ki dako ya ji ki dawo gida so kike a samu abin magana a kai na kenan ko? Ko Ridayya data auri miji mara kirki bata taɓa yin yaki ba sai ke da kikai auren soyayya miji na gaban kwatance, to Allah kar ya nuna mini ranar da zanga ƴata na zawarci"

"Haba Ammi ni kaɗai nasan wahalar da nake sha ba, tun yana waya da ƴan mata a ɓoye har ya zamana baya jin tsorona, baya bani abinci yanzu haka dukana ya yi a gaban ƴaƴana kuma ya ce na bar masa gidansa ni kuma kamar mayya sai na zauna don Allah?"

"Ai wallahi sai kin koma tun kafin kowa ya ji ni zan zo na samu mijin naki gantalalle shi ma"

Bata bar Yaya Zuhura ta zauna ba ta mayar da ita da masifa da komai. Koda Ammi ta ce gidan Yaya Zuhura ta iske mijin ya zage yana nanawa Yaya Zuhura wuƙa a wuya gabaɗaya ya ƙona mata wuya da wuƙa nan take abinda ta yi wa Ridayya ta faɗo mata ta hau masifa da bala'i.

Ya kalli Ammi ya juya mata baya tare da cewa "Na ki rududu wannan faɗan ba zai mini ba, ƴarki ce bana so bana ƙauna a yanzu"

"Ashe baka da mutunci É—an wahala ne kai gayyar tsiya? Ashe É—an kwalta ne kai?" Ya ce

"Yanzu zan yanka miki rashin mutunci wallahi ki ɗauki yarƙi ku bar mini gida immediately"

A gigice Ammi ta riƙe hannun Yaya Zuhura ta ce "Ɗan'tadda ne ashe mijin naki na san maganinsa da Burhan zan haɗa shi wallahi" banda kuka babu abinda Yaya Zuhura take kuma ya hana ta ɗauki yaro ko ɗaya har wacce take shan nono ya kwance ta.

Sadauki ya samu relief daga nauyin da zuciyarsu ke yi masa dalilin wayar da suke yi da Ridayya ta tabbatar tana dawowa z a yi maganar komai a shige wajan.
Chapter 85 · 0% Book details