← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 118

Sashe 6

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A karo na biyu Ridayya ta kalli inda Bilal yake, cikin sa a suka haɗa Idanu. Wata tsinkewar gaba ce ta gitta ta zuciyarta, kaifin idanunsa ya sanya ta ji zuciyarta na bugawa, jikinta ya ɗauki ɓari na abubuwan da take ji a duk sanda ta kalli idanun Bilal, dukkan wata halitta dake jikinta sai data amsa yanayin da Ridayya ke ciki, wanda kallon Bilal ya haifar mata.
Yana mata wani irin kwarjini ko motsinsa ta ji gabanta faɗuwa yake ba tare da sanin dalilin hakan ba, tsigar jikinta duk sun mimmiƙe suna amsa yanayin maikama da ji da motsin buƙatar abu daga gare shi.
Cikin sauri ta ce "Asstagafirullah!"
A nutse Bilal ya juya tare da ficewa, sai a lokacin Junaid ya ce "Wace kuma waccan?" Meer ya kasa É—ago kansa kai tsaye ya fahimci Khairy Junaid ke magana wacce ta bi Bilal da kallo da zai shige. "Tare muke"
Kai tsaye Meer ya furta hakan ba tsoro, duk basu kawo komai ba, ganin ƴan'uwan Meer ɗin suna wajan sai hakan ya shaida musu Khairy wata ce a familyn nasu. Fita sukai daga cikin room ɗin aka bar Zameer da Ridayya wacce take cikin tsananin ciwo, tun bayan fitarsu yake chatting da ƴan mata. Saƙon Khairy ne ya shigo.

"Ka gaggauta fitowa,ina buƙatar ganinka" Ya cilla wayar cikin aljihu tare da miƙewa tsaye. Ridayya ta ce "Ba dai tafiya zaka yi ba?" Ya dubeta ransa na ɓaci ya ce.
"To bari na tsaya na goyaki" Ta saki baki, yanzu akan idanunsa kowa na danginta ya saka ƙafa ya fice ya barsu tunda shi ta zaɓa.
"Idan ka tafi wa zai kula dani? Kana ganin babu kowa?" Ya saki tsaki cikin É—aga murya ya ce
"Karki takura ni...," Ko me ya tuna sai ya yi shiru a hankali a taushashe ya ce "Mai sona idan na zauna a nan Æ´an uwanki zasu É—auka da gaske zaman banza nake, dole na fita na kawo miki abincin dare da kuÉ—in siyan magani"
Nutsuwa ce ta saukar mata, ta yi imani kafin samun miji irin Zameer abu ne mai wahala ta ce
"Na fahimta RAYUWATA, Allah ya kiyaye ka dawo mu kwana tare"

Ya mutsa fuska Zameer ya yi yana juyawa Ridayya ta ce "I love you Rayuwata"
Ko a kwalar rigarsa haka kalaman nata ya jisu, har ya je bakin ƙofa ya tsaya ya ce "A inama kuɗin suke?" Ta maimaita ya fice abinsa..
Har ƙarfe biyu na dare babu labarin Zameer, Ridayya ta ci kuka sosai ganin tana shirin mutuwa babu wanda ya dawo a gidansu hakan bai dameta ba, addu'a take Allah ya sanya Zameer lafiya yake shirun ya yi yawa. A karo na takwas ta sake kiran number shi cikin sa a aka ɗauka a hankali ta ce.
"Rayuwata!" Wani irin tsalle da bugun casar gero cikin turmi haka zuciyarta ta yi, ihu da surutan Zameer ne ya cika kunnenta, da wani irin sauti can ƙasa wanda kai tsaye ba zata iya fahimtar kalar shi ba.
"Rayuwata! Meer!".
Maimakon ya bata amsa sai saukar wata murya ta ji a kunnenta ana cewa.
"Ka yi a hankali, kar a jiyo muryarka, ban saba ba wannan shi ne yi na na farko...

Page 4

Ridayya ta ɗauka kunnenta ne ya sa mu matsala, cikin sauri ta zame wayar daga jikinta tare da saka hannu ta shiga bubbuga kunnen a fili ta ce "Babu mamaki ruwa ne ya shiga ciki, ya toshe ƴar ƙofar ɗaukan sautin har take naɗo mini masifa da bala'i"
Ta mayar da wayar a hankali duk da ƙirjinta dake bugawa da muryarta ke rawa bai hana ta tattaro jarumta kamar jinin Iliya ɗan mai-ƙarfi ba ta ce "Rayuwata, ni ce matarka Ridayya ka na ji na?" Ta yi maganar cike da ƙarfafawa kanta qiwwa, da share gurɓataccen zaton da zuciyarta ta yi mata akan Zameer. Shiru babu amsa sai wayar data fara shuuuu!! Kamar kammalawa shirin gidan rediyo ya yin rufewa, da yin ban kwana da masu sauraro.

"Asstagafirullah! Allah na tuba ka yafe mini, daman nasan sharrin shaiÉ—anne kawai yake son kissima mini wani mummunan zato akan Meer" Ta yi shiru; tana sauraran bugun zuciyarta da take mata, kamar luguden gidan biki.

Duk yadda idanunta ya su runtsawa da samawa kanta nutsuwa al'amarin ya gagara, bacci ya ƙaurace wa idanunta. "Allah ya gani ina so da ƙaunar mijina, Yaa B ka yi haƙuri ba yin kai na ba ne, bana jin zan iya rayuwa ba tare da Zameer kusa dani ba"

Hawaye ya shiga zuba daga kwarmin idanunta, zuciyarta na tsananta bugawa ki manin daƙiƙar gudun lokaci.
Da ƙyar bacci ya ɗauketa gab da asuba, ba wani na kirki ta yi ba ta ji ƙarar wayarta alamar shigowar saƙon karta kwana, cikin ganɗoki ta ɗauka zuciyarta na faɗa mata Meer ganin wanda ba ta yi zato ba ya saka ta ƙura wa saƙon Idanu.

Alert ɗin kuɗi ne, sai gajeren saƙo daya biyo bayan alert ɗin. Ridayya ta rufe idanunta, da gaske tana buƙatar taimako, daga na kuɗi har na kulawa, tana buƙatar sharing damuwarta da wanda zai fuskance ta, wanda zai kyautata mata zato akan soyayyar Zameer ba wanda zai dinga ganin laifinta ba.

Ta zubawa sunan Bilal idanu, wanne irin abu za ta yi masa wanda zai tsane ta? Tsana mai muni ya dinga ganin baƙin ta kamar yar da a yanzu take ganin nasa?

Kuɗi ne kimanin dubu hamsin ya tura mata zuwa asusun bakinta, yasan da gaske tana buƙatar su.

"Yaa Bilal why? Me ya sa? Bana ƙaunar ka, na tsane ka gwargwadon tsanar da ka yi wa mijina, ba kai ba duk wanda zai wulaƙanta Zameer a duniyar nan ko waye zai i ya wulaƙan ta shi..."

Ta yi maganar a fili kuma a raunace, sunan Yaa Bilal data ambata yana mata amsa kuwwa! A cikin kunnenta, bugun zuciyarta na ƙaru wa duk a dalilin jin sunan Bilal ɗin ya fita a bakinta.

Har aka gama sallah tana nan a zaune, da ƙyar ta yunƙura zuwa banɗakin dake cikin ɗakin asibitin. Shiru ba kowa sai ita, ga aikin da akai mata, ga gubar fiya-fiya data sha, ga damuwar zuciya wacce take tunanin babu wanda ya haddasa mata irin danginta. Mijinta bai rage ta da komai ba.

Nas ce ta buɗe ƙofa hannunta ɗauke da kayan duba mara lafiya, ta tsaya gaban Ridayya tana mata tambayoyi da ƙyar take buɗe baki wajan amsa mata har ta kammala.

"Can i ask you dear?"

Ridayya ta kalli Nas sai ta jinjina mata kai alamar "Why not?"

"Thank you"
A hankali ta sauke ajjiyar zuciya tana kallon Ridayya dake matar da shekarunta a haife zata haifi Ridayya a nutsu ta ce.

"Tunda nutsatstan magidancin nan ya kawo ki asibiti na fahimta a kwai damuwa a tattare dake, na ji tamkar Æ´ata Safiya ce a cikin condition É—in da kike ciki, Æ´a Æ´a na kowa ne bawa sai mai shi. Zan so ki buÉ—e zuciyarki ki aminta dani ba zan cutar dake ba, ki faÉ—a mini mene damuwarki please, i just feel your pain"

Kan Ridayya a ƙasa ta kasa cewa komai saboda yar da ba ta jin daɗin al'amarin da yake riskar ta a yanzu.

"Ki yar da dani, mene dalilin shan fiya-fiyan da kikai? Ba rashin sani bane yunƙurin kashe kai da kai kikai ɗiyata, na karanci damuwar dake shimfiɗe a fuskarki what's going on? Waye shi? Su kuma su waye? Kyakkawan namijin nan waye?"

"Shawara kika zo bani, ko kin shirya faÉ—a mini mugun abu game da lafiyata? Ko kina son sanar dani mijina na cutata kema"
Ridayya ta faÉ—a tana mai kallon Nas É—in da raunatacciyar muryarta.

Nas ta kama hannun Ridayya ta ce "Ta ya ya zan aibata miki miji ba tare da sanin ya zamanku yake ba? Ai mai É—aki shi ya san inda yake masa yoyo, rumfar kara ragayar mai shi"
Ridayya ta jinjina kai a ranta ta samu nutsuwa da nurse É—in a taushashe ta ce "Wanda ya kawo ni asibitin nan zan iya ce miki ubana ne...,"

"Uba kuma?" Nas ta dakatar da Ridayya da faÉ—in haka. Ridayya ta ce

"E, Abbiey na ne" Nas Hajjara kallon Ridayya take da mamaki kuma ta kasa fahimtar abinda take faɗa ko dai bata gane wanda take nufi ba ne? "Mamaki ko? Bana ƙarya, ban san yadda ake yinta ba, mutum ɗaya ne ya taɓa sani yin ƙarya a duniya, yanzu kuma na zama shaharriyar maƙaryaciyya"

"Ba mamaki bane, abu ne mai kama da almara kin gane wanda nake magana akan shi Æ´ar nan?"

Murmushin takaici Ridayya ta yi da kanta ta san ba ta yi wa Yaa Bilal adalci da halacci ba, ta yi ƙasa da kanta saboda harbar da gefen kanta ya yi a hankali cikin raunatacciyar muryarta ta ce "Uhm"

"Wani fari zubin buzaye? Mai girman jiki, wani mara fara'a da rashin son magana sosai, wani mai yawan dafe kai? Wani mai tsayi da kuma faÉ—i...,"

Da sauri Nas Hajjara ta ce "Lallai ba shakka shi nake nufi, waye shi a wajanki? Domin na ɗauka shi ne mijinki sanda ya kawo ki asibitin hankalinsa a tashe ko takalmi babu a ƙafar shi, waye wannan ɗin?"

"Babana, Abbiey na"
"Ikon Allah, bai yi kama da babanki ba, amma mene yake faruwa tsakaninki da shi da kuma sauran?"

"Long story, _labari mai tsayi_* Ridayya ta faɗa a taƙaice domin ta fara jin hirar na hawar mata ka, yunwa take ji ga damuwa da ta yi mata ƙatutu a zuciya ki numfashi da ƙyar take haɗiya.
"Ƴar nan zan so jin labarinki da yar da akai kika auri wannan mijin naki wanda ke shirin salwantar da rayuwarki"
A gigice Ridayya ta ɗago rinannun idanunta da suka gama jirkicewa sai kuma ta saki dariya kamar mai taɓin hankali, ta girgiza kai ta ce
Chapter 6 · 0% Book details