Sashe 77
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sadauki ya kalli mother yaga duk ta sauya ya san akwai damuwa a ranta, mother tana buƙatar mijinta a kusa da ita kewarsa take sosai ta manta yaushe rabonta da shi matsayin miji da mata Sadauki zai yi magana ta ce "Wanne gida ka ce ka zaɓa ne? Kuma zan tura a fara haɗa lefe"
"Mother nrml fili nake so gidan da zan ginawa Shanshan na musamman ne" Ta yi murmushi ta ce "Oh Allah ya nuna mini wannan rana"
"Wallahi mother ina tsananin son Shanshan Allah ne shaidata i love her with all my heart I so much loves her"
"Allah ya baka ita" da sauri ya ce "Yama bani"
Duk suna zaune a parlour banda Ridayya wacce kullum kuka take sun rasa gane kanta rabonta da Ustaz tun ranar da Sadauki ya zo. Idan ta fara tunanin Sadauki sai tunanin Abbiey ya danne na Sadaukin tunanin yadda zata zama fara shi ne kawai a ranta.
Baba ƙarami ya ce "Allahamdulillah komai ya yi farko yana da ƙarshe kuma in sha Allah zamu tattara mu koma Kano da zama a Babban gidan da aka sauya. Kuma zamu tara mutane a yi addu'ar ɗaurin auren Ustaz da Ridayya kana a yi walima dole jama'a su shaida kuma aurenta ya zama mai ƴanci ba kamar wancan ba. Babban mutum zai gina gidansa da zai zauna da iyalinsa zamu bayyana ga wanda suke zaton mun mutu. Aure rai ne fa shi duk wanda yake ƙoƙarin ganin bayansa idan akwai rabo mai tsanani sai Ubangiji ya raba shi da duniyar bakiɗaya, auren Ustaz da Mardiya nufin Allah ne haka auren Ustaz da Ridayya rubutacciyar ƙaddara ce wacce ta jima a zane, kuma a bayanin Hajiya na fahimci Ridayya ita ce uwargida an riga ɗaura aurenta akan na Mardiyya domin mun jima da hakan mun su rufewa sai kuma aka yanke hukuncin rabawa dangi alawa da goro su saka albarka, ba wani wa'azi da zan yi sai ranar da aka yi biki Ridayya zata tare zan haɗa na yi musu wa'azi"
Hajiya ta ce "Hakan ya yi Allah ya saka Albarka a wannan auren ya tsole idon maƙiya. Oh ashe zanga wannan ranar jikokaina aka haɗa aure Allahu Akbar"
Ustaz ya watsa mata harara Junaid na kallonsa ya yi murmushi kawai. Baba ƙarami ya zaro kuɗi ya ce "Zainu kira mini Yaya Ridayya na bata sadakinta"
Sai a lokacin Ustaz ya ce "Sadakin baƙar mace daban yake Abba ka bari zan bayar"
"Gaskiya ne yanzu samun baƙar mace sai an bincka bincike mai tsanani" Mardiyya ta zo wuya.
"To In sha Allah gobe zamu koma tunda jikin da sauƙi sai ku zaba cikin shiri"
Ustaz ya gyara murya ya ce "Don Allah kar a sanar da Ustaza maganar auren nan zan faÉ—a mata da kaina"
Duk suka yi na'am Mardiyya ta tashi fuu ta nufi ɗaki zuciyarta sai wasiwasi take mata babu mamaki ciwon Ustaz ƙarya ne kamar yadda Umma ta faɗa mata plan ne don a raba auren a bashi Ridayya. Ta fara tunanin mafita dole a yau ta saka Ustaz ya kusanceta but how? A fili ta ce "Maganin saka feelings" da sauri ta ɗauki jaka da mayafi ta fice ba tare data tambaya ba.
Mami ta shigo ta samu Ridayya tsaye tana kallon madubi ta yi murmushi tare da kama hannunta suka zauna bakin gado ta ce "Bakya gajiya da kallon madubi? Ko kina shirya wani abu ne, Ridayya ke ta musamman ce ba za ki gane ba sai nan gaba" Ridayya dai ta yi shiru domin bata saba da Mami É—in ba.
"Mene matsayin Ustaz a wajanki ne?" A hankali ta ce "Abbieyna"
"Baffa kuma fa?"
"Babana" Mami ta ce "To waye uban na gaskiya kenan Ridayya ga Ustaz ga Baffa kowa kuma uba dole akwai wanda yake amsa sunan daba nashi ba. Baffa shi wanda ya yafe miki kuma biological father naki, Ustaz kuma yayanki ne wanda ya raine ki"
"Kuma me ya sa ake kira na da sunansa?"
"Saboda shi ya buƙaci haka. Ridayya buɗe kunnenki Ustaz ba mahaifinki bane a rashin uba a kan yi ubanɗaki a rashin gata da uba kika samu Ustaz. Kamar yadda Junaid yake haka Ustaz yake a wajanki bambancin shi ne Ustaz nada ikon aurenki ki zama matarsa domin ɗan gidan Abba ne ke kuma ƴar Baffa ce akwai aure a tsakaninku"
Ridayya ta zare idanu tana rufe baki tana jin maganar wata kala ba tsari taya Abbiey zai zama mijinta? Wannan shafi abin kunya ne "Yanzu kika fara rufe baki na yi tunanin za ki fahimci cewa Ustaz yana son ki?"
"Mami na sani fa, i knew everything ina jin wani lokacin ai matsayin uba ne wani lokacin kuma sai na manta abubuwa ban taɓa kawo shi a matsayin miji ba. Mami Abbiey bai cancanta dani ba na yi zunubin da ba zai taɓa yafe mini ba idan ya ji, wallahi ba zan iya kallon Abbiey matsayin miji Mami ban dace da shi ba"
"Ya taɓa faɗa miki yana son ki?" Ta yi shiru koda ta nutsa tunani sai kanta ya fara ciwo Mami ta miƙe ta ce "It's okay. Mimi babu abinda yafi rayuwa da wanda yake sonka daɗi, ki tuna wanda ke zuciyarki wanda kike jin kishinsa idan kin ganshi da wata macen wacce kike jin dake kawai kike son ya rayu"
"Abbiey ne Mami bana son ganinsa da Mardiyya" Mami ta yi murmushi ta ce "Sai ki ƙoƙarin maye gurbin Mardiyya a zuciyarsa ki zama kamar ita da matsayinta a wajansa"
"To ki bani shawara, amma Sadauki fa?"
"Shawara kike irin ta uwa ko kuma irin ta Aminiyya? Sadauki ban ce ki daina tunaninsa ba nima"
"Aminai mugwaye ne, abokina ɗaya Abbiey ki bani irin ta uwa" ta faɗa tana kwaɓe fuska
"Da farko dole ne kina hira da Ustaz, ki kula da shi daga abincinsa har ruwan wanka kayan sawa ki dinga nunawa kina son shi hakan zai saka Mardiyya ki shi, kinga dai kin girma amma a wajansa ki nuna ke da Little ɗaya kuke idan kun yi faɗa kar ki bari Mardiyya ta gane, duk abinda zai ɓata ran Ustaz kar ki yi kina kwaliyya kina zuwa kuna hira amma kar ki kwana wajansa" Ta yi saurin cewa "Ai ba zan iya bama tunda kika ce zai iya aure na nake jin kunyarsa"
Mami ta miƙe tsaye ta ce "Sannu Mimi ke kam ko Zainura ta fiki wayo ki je yanzu ki yi masa sannu"
Fita Mami ta yi Ridayya ta miƙe daman ta yi wanka ta gyara sumarta ta ɗaure dake dare ya fara ta saka riga body short ta saka slippers ba zaka ce ita ta haifi Little ba domin jikinta har ya fi na Zainura kyau balle kuma na Mardiyya. Burhan na zaune a parlour ta zo ta shige ya bita da kallo yana hura hayaƙin tabar shi a parlourn.
Shiga ta yi bedroom ɗin a hankali bakinta ɗauke da sallama shiru babu kowa bedroom ɗin sai ƙamshi yake komai a gyare ta dinga kallon ko'ina ta nufi gaban madubi ta tsaya idanunta ya sauka a kan diary ɗin Ustaz ta buɗe ta ɗauka ta dinga dubawa ta buɗe shafin Farko idan aka saka _FIRST LOVE_ da mayan baƙi. Tana ƙoƙarin karantawa ta ji an ziro hannu ta saman kafaɗarta an ƙwace an dafa kafaɗarta da ɗaya hannun.
Ta cikin madubin ta gan shi yanzu ma dai jallabiyya ce a jikinsa mai ɗan faɗi ya faɗa ya ƙara fari ya cika mata Idanu ya mata kwarjini sosai sai duk kunya ta kama ta ta fara ƙoƙarin matsawa ya ƙara faɗi bakinta na rawa ta ce
"Abbiey ya jikinka? An ce ka ji ciwo a mara ko?"
"Injiwa?" Ta tura baki ta ce "Haka na ji wai ƙafarka nata jini yanzu ya daina ko? Da zafi wajan ciwon da yawa ne? Mu gani nuna mini wayyo Abbiey"
Ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaga jallabiyyarsa zuwa sama ya yi saurin durƙusawa ya riƙe hannunta yana rufe Idanu saboda zafi ya kame hannayenta duka ya haɗe waje guda ya ce "Ustaza ba ki da kai sam, kin san me za ki gano?"
"Mararka zan gani mana wajan ciwon sai na yi maka addu'a" bashi da wani ƙwari gashi neman fin ƙarfinnsa take a dole sai taga wajan ciwon sai ƙoƙarin ɗaga jallabiyyarsa zuwa sama take. Cikin dabara ya janyeta yana tsayar da ita gaban madubi idanunsa a ɗan lumshe yake kallona yau Ridayya ce a gabansa take amsa sunan matarsa? Taya zai fara godewa Allah? A hankali ya ware hannunsa ya ce "Zo ki ji wani sirri" Ta ƙarasa har tsakiyarsa taƙi kallonsa a hankali ya zagaye hannunsu ya yi covering ɗinta tare da yi mata halal hug ya rungumeta a tsakiyar ƙirjinsa tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa kamar na rashin sabo ya sauke ajjiyar zuciya mai nauyi ya ce "Allahamdulillah ya rabbil alamin" Za ta yi magana ya damƙe hannunta tare da sumbatar tsakiyar goshinta irin na larabawa idanunsa a lumshe ta ji abu mai zafi na zuba a fuskarta kafin ta ɗaga kanta ya juyar da ita yana zama saman gado ya nuna mata lemon da Mardiyya ta kawo masa ya ce "Miƙo mini" jikinta a sanyaye ta ɗakko lemon ta ji san yi sosai ta ce "Abbiey na ɗan sha mu ji?"
Ya kalleta da kyau tana yin komai kamar yarinya shi bai ba san ame ta É—auke shi ba. Mijin ko aboki ko kuma uba? "Na sha kar ka mini rowa"
"Sha" kawai ya ce kurɓa ɗaya ta yi ta ji daɗi sai ta zuƙe duka daga ƙarshe ta ji wani ɗanɗano nada ban ya ware Idanu ta kalli kofin shi ma kallon kofin yake kishin giɗa. "To wallahi daɗi ya yi"
"Allah ya yi miki Albarka Ustaza ya ba ki lafiya daga miƙo mini lemo sai shanyewa?" Da sauri ta ƙarasa ganin ya lumshe idanunsa ta yi saurin kame ƙafarsa ta ce "Yawwa ai wallahi sai naga wajan ciwon inda ka yi maka aikin.....
Karanta ka yi share
08164069385
*YI DOMIN ALLAH*
*SARAUTA CHARITY FOUNDATION*
Ciyar da marasa ƙarfi da almajirai lokacin azumi. Ta hanyar yin abinci, kunu, ƙosai da ruwan sha tun daga kan 200 zuwa sama na abinda Allah Ya a hure maka.