Sashe 69
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Idan kowa baya son ki ai ni ina son ki ko?" Ta yi shiru ya ce "Idan Allah da kansa daya halicce ki ya samar dake a duniya yana son ki kuma ya amince da ke to babu damuwa kowa ma yaƙi ki, mutanen ƙwarai Ubangiji yafi jarraba imaninsu Ustaza ki kasance mai haƙuri da gode Allah da ni'imar da ya yi miki. Mutane da yawa sun lalace da yi wa mutum ba'a na daga halittar da Ubangiji ya yi masa, amma tunda kike kin taɓa ganin mutum ya yi halitta?"
Ta girgiza kai ya kalleta ta madubin ta yi saurin cewa "A'a"
"To bai kamata ki yi fushi ba, yin hakan kamar kina nuna rainuwa ga Allah da nuna masa bai iya halitta ba, ki saka a ranki ke mutum ce kamar kowa mai tarin marudai wanda kike shirin cimma, ki yi ƙoƙarin bawa masu faɗar hakan kunya, ki zama mai ƙwatarwa kan ki ƴanci a ko'ina kar ki bari a wulaƙantaki kuma kar ki wulaƙanta kowa, Allah da kansa ya ce wáakaramna bânii adama"
"To idan mutane sun guje ni me ya sa su Baffa za su yi mini haka?"
"Ki manta da abinda ya shige, mutanen kuma da basa raye wanne ƙorafi Ustaza? Ki yi addu'a ki yafe musu ki zama mai uzuri"
A sanyaye idanunta na cika da sabbin hawaye ta ce "Allah ya jiƙansu da rahma na so ko sau ɗaya Baffa ya kira ni da sunan ƴa, ya saka mini albarka kamar su Zainura su Yaya Khaliperh"
Ustaz bai sake kallonta ba ya fara shirin barin wajan ta ce
"To baka faÉ—a mini me ya sa kai kake so na?"
"Ban sani ba"
"Ina son sani Abbiey
Dole ya kai Ridayya a duba lafiyar tunaninta da kyau domin yana kokwanto ta marairaice sosai "Ka faÉ—a mini"
"Saboda you're lovely ke bar so ce"
"To ni da matarka wa ka fi so? Kuma me ya sa ka aureta maimakon wata? Abbiey ka taɓa ce mini aure ba dole bane daka haƙura"
"To ni dai ina son matata"
Sai kawai yaga ta fashe da kuka sosai tana cewa "Amma ba zata haihu ba ko?"
"Ke za ki haifa mini idan ita bata haihu ba? Idan kin yarda duk shekara za ki bani baƙaƙen yara kamar ki to"
"Ga Little na baka kyauta, kuma me ya sa Little yake fari kyakkawa kamarka?"
"Saboda abin cikin ƙwan ya fi ƙwan daɗi, Little ya mini kaɗan zuri'a nake so mai yawa kinga da gani sai ke muka rage sai ki yi ta haihuwa, idan kuma ba zaki haifa ba nan da wata tara za ki ga Mardiyya ta haifa mini"
Wani abu ta ji ya tukare mata zuciya kanta a ƙasa ƙirjinta na ɗagawa, shi ɗin babanta ne taya zata iya haifa masa yaro wannan ai iskanci ne kawai. "Ustaza ban yi zaton zan sake ganinki ba, bana faɗar abinda ya shige a baya amma kaɗuwar ganinki gidan Mahmah ya kasa barin tunanina, gani nake kamar a mafarki na fita daga gidan saboda tashin hankali da mamaki kuma zan iya abinda bai dace ba, yanzu haka ina ganin kamar idan na rufe idanu na buɗe ba zan sake ganinki ba, ke ɗin ƙaddarata ce tamkar inuwata haka kike ban iya guje miki, ba zan iya zama hankali kwance ban san ya rayuwarki take ke ɗin amana ce. Ban taɓa nunawa Tajuddeen photonki ba balle na ce yana sane ya ajjiyeki a gidansu, a labari dai ya sanki banda kamanni ya akai kika je? Ina mijinki?"
Wani irin miki ne ya taso mata bata ƙaunar tuna Giɗaɗo gabanta faɗuwa yake tana yawan manta abubuwa amma ba zata manta rayuwarta gidan Zameer ba.
"Abbiey shi ɗin MUNAFUKIN MIJI ne, ba don Allah ya aure ni ba, ashe ba ɗan kano bane a Katsina yake ya zo Kano Almajiranci sunansa Giɗaɗo. Baya bani abinci, baya yi mini ɗinki babu magani ba sabulun wanka babu man shafawa, ya kwashe kayana ya siyar ya ce aiki ya samu da yake buƙatar kuɗi, ashe caca yake yi komai nawa ya siyar ya sace wayata ya siyar ya sace atamfofina ya siyar, na yini na kwana banci abinci ba baya barin kowa zuwa gidana baya barina fita, lefen da ya yi mini ashe na haya ne ranar da aka kai ni ya saka aka sace su, na fara yin ƴar'tsala mutane suna siya da kuɗin nake cin abinci na siyi omo na kwanka da kuɗin kuma shima yake amfani, duk kuɗin da kake tura mini tura mini shi yake amfani da su. Na yi faskare na dafa masa ruwan wanka na yi masa wanki da guga ya ƙona mini fuska da iron ya karya mini hannu, kuma ya dinga shaƙe ni a wuya idan zai....,"
Ta kasa faɗa haka kurum ta ji nauyin faɗawa Ustaz abinda Zameer yake mata a gado, kuma ta kasa faɗa masa zaman Khairy a gidan tana ganin kamar sirrin aurenta ne wannan ko dan ɗanta Little ba zata tunawa ubansa asiri a wannan ɓangaren ba.
Ustaz ya kasa cewa komai kallonta yake yana jiran jin me zata ce kuma?? Yadda zufa ke yanko masa da yadda jijiyoyin kansa suka tashi kaɗai zai saka mutum yasan ran Ustaz ya ɓaci zafin zuciyarsa ya motsa.
"Abbiey ka yafe mini don Allah kar ka ce na koma gidan Giɗaɗo kashe ni zai yi kuma ya ƙwace takardun da Baffa ya bani please forgive me Abbiey"
Ustaz ya taka zuwa gabanta yana riƙe numfashi ya jima sosai sai kuma ya ce "Ya zama kukanki na ƙarshe, ban taɓa fushi dake ba ya isa haka nan, fatan za ki nutsu ki gane kuskurenki ki buɗe zuciyarki kin san wanda ya dace dake a rayuwa a matsayin miji....,"
"Sadauki Abbiey"
A sama Ustaz ya ji sunan Sadauki shi har ya mance ma, da wani irin expression na mamaki yake binta da kallo gabaÉ—aya naman jikinsa rawa yake ya kasa cewa komai ya juya tare da ficewa tabi bayansa to me ya sa ya yi shiru kuma?
Fasa fita ya yi ya koma bedroom É—insa ya kwanta yana kallon sama tunaninsa ya tsaya cak bakiÉ—aya ma ya rasa wanne Irin tunani ya kamata ya yi wanne kuma irin tunani ne da Ridayya? Har akai zhur yana kwance Hajiya ta shigo ta ganshi zaune saman ladduma ta ce
"Wai daman kana gidan nan? Babban mutum sallah a ɗaki ban taɓa gani ba"
Ya kalleta bai ce komai ba ta zauna kusa da shi ta ce "Lafiya dai? Meke damunka Babban mutum?"
"Hajiya bani da Nagarta da za a so ni ne? Ko ni ba mijin ƙwarai bane ko ba zan iya kula da mace bane?"
Ta sauke numfashi jikinta a sanyaye ta ce "Injiwa? Wane ya faɗa maka hakan Muhammmmd wallahi kwaɗayin halinka ya saka na karfafa aurenka da Mardiyya, kai ɗin mutum ne mai ƙoƙarin kyautatawa mutane da neman na kansa kuma hakal da zuciyar neman addini riƙon amana da gaskiya, na saba cancanta gaka kyakkawa son kowa ƙin wanda ya rasa ma macen da zaka tunkara ta yi fatali da soyayyarka ka bawa Mardiyya dama ban sani ba ko akwai wacce kake so ka yi haƙuri ka yafe mini na yi kutse a rayuwarka da tunanin na isa na yi hakan ba dan na baƙan ta maka rai ba, tausayin halin da kake ciki nake, ka rungumi Mardiyya hannu bibbiyu"
Daidai nan Mai ran ƙarfe ya shigo.
Ustaz ya riƙe hannun Hajiya da kyau ya ce "I was depressed, ƙofar da kuka saka a ɗakina bai wa ɗakin kyau ba, ba haka na tsara ba kada ku saka na zama mai karya alƙawarin zuciya"
Hajiya da Mai ran ƙarfe suka saka Ustaz tsakiya domin suma ɗin shi suke kallo matsayin mataimaki. "Muhammad ka faɗa mini wacce kalar ƙofa kake so, wacce zata haska ɗakinka ko a ina take zan yi iya ƙoƙarina wajan ganin ka mallake ta, ko bata son ka zan saka ta soka" Ya yi shiru kansa na harbawa, baya son yi wa Ridayya dole ko kuma amfani da damar shi.
"Babban mutum ka yi magana shiru baya magani" Mai ran ƙarfe ya faɗa yana riƙe kan Ustaz shi kansa ya firgita da yadda jijiyoyin suke harbawa. "Zurfin ciki ba shi ne mafita ba, wacece? Ka faɗa, yi magana"
"Oum....," Sai kawai ya girgiza kai ya miƙe yana shigewa toilet. Hajiya ta fashe da kuka ta ce
"Mun shiga uku wanne irin hali ne wannan? Miskilanci da riƙe damuwa kar zuciyar yaron nan ta buga"
"Ba zata buga ba in sha Allah. Ƴar rainonsa yake so na jima da fahimta musamman a dawowarsu na so ya furta ya ce Ridayya yake so da wallahi tallahi a yau Ridayya ba zata kwanta ba sai da igiyar auren Muhammmmd a kanta". "Babbar magana wannan shirgegen ai ya mata girma, kuma duk shekarun daya kwashe sai ya auri bazawara kuma mai haihuwa? Ina masa kwaɗayin samun budurwa"
Mai ran ƙarfe ya ce "Mata mata ku dai tunaninku na musamman ne, shi so na gaskiya ba ruwansa da wannan idan kuma don wannan yake sonta ai daya haƙura yanzu. Ko a baya dan dole ya aurar da ita" Hajiya ta ce
"To yanzu mene mafita? Kawai tunda mu mun fahimta a aura masa ita mana ai É—an'uwanta"
"Bana son Ridayya ta fahimci alfarma ta yi wa Babban mutum, ita a yanzu bazawara ce tana da ikon zaɓawa kan ta wanda take so ne, kuma ina son Muhammmmd ya san ba a komai zurfin ciki yake da amfani ba, mutum kan iya rasa abubuwa da dama idan har ba zai buɗe zuciyarsa ba, ki bari sai ranar daya furta da bakinsa ni kuma a ranar zan nuna masa gata kuma ya je ya gina soyayyarsa a zuciyarta, ya fara nuna mata akwai halarcin aure a tsakaninsu ya kuma nuna mata bashi ya haifeta ba"