← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 118

Sashe 94

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu tunda ba Ridayya ga wani sabon plan, Zainura ita ce target ɗina ka san duk yadda ka yi ka samu kusanci da ita, idan har tsarinmu ya yi daidai sai a nan gab da bikinku ka ɗirka mata ciki ka gudu yanzu ba kuɗi ne a gabana ba, kawai rayuwar yaranta nake so na wargtsa kamar yadda komai nawa ya juye na yi nasara akan Ridayya na bata wahala tun tana zanin haihuwa na rabata da iyayenta, na juyar mata da tunani bayan n bata maganin shaye-shaye na ƙona mata harshe da wuƙa, ni ce na dinga assasata akan Zameer wannan shi ne babban abinda ba wanda ya sani, na dinga ƙarfafa mata qiwwa. Daman na ce ba zata taɓa zama wata a duniya ba gashi ba inda ta je ta rabu da mijinta, Bilal ya aureta uwarsa ta saka ya sake ta kaga an fara lissafa mata aure kenan, in sha Allah haka zata dinga aure tana fitowa ko wanne ta je kuma ta haifi ɗa ɗaya, kuma duk ta haifi lalatattun yara"

Ta juya ta kalli Burhan da yake busa sigari ta ce "Wai kana jina ma? Idan kana busa shegiyar abar nan ba komai kake fuskanta ba"

"Na ji, ni ban iya wata soyayya ba"

"To daman ina mashayi ina soyayya ka nutsu ka tambayi abokai"

Ya miƙe bayan ya ɗauki wayarsa ya ce "Bari na doƙa yanzu abinda za a yi ki nemi jauwalarta ki bani shaɗayanta ko?"

"Mene shaÉ—aya kuma?"

"Ke ciki ce fa, ana miki inkiya bakya ehhh, number wayarta nake nufi naka yarinyar mai ƙirice matsalar kawai yama sunanta kika ce ta fita haɗewa"

Ammi ta ja tsaki ta ce "Ji wawa ba maganar yayar muke ba ta ƙanwar muke"

"Ohh sure zahabu zahabu ya sunan beb É—in?"

"Zainura"

Burhan ya lissafa faɗar Zainura ya kasa sunan ya masa wani iye yane. Sai kawai ya ce “Zinu"

Cikin sa a yana fita ya yi karo da ita ta dawo daga makaranta dake weekend ne ana ta kiran sallar magriba tana ganinsa ta haɗe rai bai taɓa tsayawa ya mata kallo sosai sai yanzu ba ya tsaya a hanya ya cake ta haɗe fuska cikin muryarta ta tsiwa ta ce

"Malam ka tsaya mini a hanyar shiga gidan ubana?" Ya yi mata shiru sai warin sigari yake ta yi saurin rufe hanci

Zata shige ya yi saurin kama hannunta tana juyawa ta ɗaga hannu ta kifa masa mari ta ƙara kifa masa wani ta ce "Sakarai shashasha ko an faɗa maka ni irin ƴan iskan da kake bi ne? To ɗabi'ata ta sha bamban da taka jikina mai tsarki ba irin naka ƙazami...."

Hannunta ya fisga da ƙarfi ta yin saurin matsawa kusa da shi saboda yadda ta ya jawo hannunsa idanunsa jajur sai huce yake yatsun hannun Zainura raɗau a fuskarsa ya zaro wuƙa a aljihu nan Zainura ta firgita amma ta dake jiran yadda zai soka mata kawai take. Idanunta rufe ba zato ta ji ya ce

"Ina son ki Zinu ki koyi so na dole" yana faɗin hakan ya sake ta ya fice kamar walƙiyya.

Junaid bai samu faɗawa Baffa uzurin Zameer ba yama manta shaf dake baya yawan zama always yana wajan aiki. A ɓangaren Zameer baya iya bacci ya zama kamar sauna matarsa Ridayya kawai yake muradin gani kusa da shi duk duniya babu wata ƴa mace dake gabansa sai Mai son shi Ridayya kuma zai yi komai saboda ya mallaketa shi kaɗai zai rabata da ko wanne namiji. Ya shirya cikin shadda skyblue ya nufi gidansu Ridayya da addu'ar Allah ya sa ya haɗu da Baffa ko Junaid ko ita kanta Ridayya ƴar Aljanna.

Sadauki ya zama sai addu'a ya kaÉ—aita sosai sai ya yi kwana da yini a É—akinsa sosai suma ta taru a kansa da fuskarsa kamar mahaukaci ya daina walwala ko da Mother ne. Tajj ya zo har gidan shi kansa ya firgita da yanayin Sadauki ya faÉ—awa Hajiya Azizat gaskiyar Ridayya ta yi aure amma kar ta faÉ—awa Sadauki idan lokaci ya yi zai sani.

Takarar BM USTAZ ta kankama ko'ina an sanya poster ɗinsa da inkiyar Fari mai farar aniyya ya samu karɓuwa wajan jama'a dukda ba a ba a bada damar fara yin kamfen ba. Al'amarin daya ƙara gigita Mardiyya soyayyar Ustaz ta dawo sabuwa fil a ranta gefe guda mata suna fara crushing akan shi. Yayinda shi kuma yake ƙasar Japan zaune da matarsa ko wanne meeting ta zoom yake halatta sai ya sauka a Nigeria har ya koma ba wanda ya sani.

Har yanzu Ustaz ya kasa furta komai akan first night ɗinsa da yake cewa Ridayya ta amshi budurcinsa, duk abinda ya lissafa sai ya ga bai dace da Ridayya ba. Bai jima da shiryawa ba suna zaune akan duguwar kujera daga shi sai wata haɗaɗɗiyar rigaw armless amma mai kauri ya zuge zif ɗin gaban rigar saboda yanayin da yake ciki a yanzu ke haifar masa da zafi a ƙofofin gashin jikinsa. Ridayya kuma na kwance a jikinsa ta miƙe ƙafarta a saman tashi tana wasa da wayarsa shi kuma ya yi shiru yana shafa samar kanta data kunce kitson.

Ta ji yana shige gona da iri ta yi masa banza a hankali ta ji ya ce

"I am very lucky"

"Dame?" Ta tambaya hankali ya É—ago ta bayan ya kalli cikin idanunta ya ce "Ko wanne namiji yana amsar budurcin matarsa ni kuma matana ta amshi nawa dole na yi wa Ubangiji godiya"

Ta É—aure fuska ta ce

"Magana kake faÉ—a mini idan na fahimta ka auri bazawara"

Nan da nan fuskar Abbiey ta yi jajur fushinsa wanda bata taɓa gani ba ya bayyana ya dinga kallonta da wani irin firgitaccen yanayi goshinsa ya fara fidda zufa ya kama hannunta duka biyun kamar zai yi faɗa sai ta ji muryarsa a ƙasa ya ce

"Ridha" ya yi shiru ta kasa kallonsa

"Ɗago idanunki ki kalli cikin idanuna" a hankali ta kalle shi abinda ta gani a idanunsa was very different yanayi ne da babu wanda zai iya ganewa amma zuciyarta tuni ta buɗe wani irin son Abbiey ɗinta ya dunga huda mata ƙirji yana shiga zuciyarta

"Na taɓa miki maganar mijinki ko aurenki na baya? Kin taɓa ji na yi magana akan surarki ko wani abu? Balle budurci ko bazawara?"

Ta girgiza kai "BuÉ—e baki ki yi magana" ta yi shiru cikin faÉ—a ya ce

"Zan watsa miki yatsu a fuska Ustaza, gaggauta magana Ustaz na jinki"

Muryarta na rawa ta ce "A'a Abbiey"

Yana riƙe da hannunta ya matse alamar hukunci yake mata can ƙasa daidai yadda za ta ji cikin wata kalar murya ya ce

"Ban taɓa damuwa da wannan ba, ba kuma don shi na aureki ba, ba don shi ya sa nake son ki ba. I'm just love you for the sake of Allah for the sake of love Ustaza, ina ta laluban dalilin daya sa nake son ki tun kina jaririya ina goya ki har kika girma na ji ina son rayuwa dake na kasa, nasan soyayyar gaskiya bata da wani dalili" ya yi shiru ya murza tsakiyar tafin hannunta

"A shekeran jiya na samu amsar tambayata, Ridha bayan son tsakani da Allah da nake miki na ji a raina tarbiyyarki kawai na yarda da ita a cikin ƴan matan duniya, saboda ni na tarbiyantar dake na kare mutuncinki har zuwa gidan aurenki, matan yanzu abin tsoro ne wayewa ta musu yawa wasu soyayya da suke abin tsoro ce, Ridha ba kunya za kiga mace tana bari namiji yana riƙe mata hannu. Innalillahi Allah ka yafe musu Allah ka yafe masu wallahi da na auri Iran matan nan gwara na zauna haka, ke kam ina alfahari dake kin riƙe mini kimarki da mutuncinki na ɗiya mace"

Gaban Ridayya ya yi mummunan faɗuwa ƙirjinta ya duka da ƙarfi, wani tashin hankali ya mamaye ta nan take jikinta ya yi sanyi tausayin Abbiey na yardar da ya yi mata ya kamata idanunta ya cika da hawaye.

Ustaz ya saki murmushi har dimple ɗinsa na shigewa yana riƙe da hannunta a hankali ya kai yatsunta zuwa bakinsa ya tsotsa tare da sumbata ya ce
"A gare ni babu wani abu da nake ɓoye miki, babu shi don Allah idan akwai abinda ya kamata na sani tun yanzu ki faɗa mini na san yadda zan fuskance shi, bana son rayuwar ɓoye abu idan na miki abu kawai ki faɗa mini ok?"

A hankali ta ce "Ba komai" ya tsora mata idanu kamar mai fahimta "Are you sure?"

Ta jinjina kai ya jawota jikinsa ya rungume yana jin yanzu abinda ya yi masa saura gashi ga muradin ransa

"Thanks for the gift, thanks for the virginity, i appreciate it. Ubangiji ya yi miki albarka ya ba ki aljannar firdausi, u make my day kin mai dani cikakken mutum"

Idanunta cike da hawaye ta ce "Ka yafe mini Abbiey, bana jin na cancanta godiya ƙaddara ta zo ba yadda muke tunani ba ban baka.....,"

"Shhhh!!" Ya É—ora yatsarsa a bakinta

"Ni budurci na amsa da gaske Ustaz i feel very comfortable with you ban yi zaton haka ba, ke ta musamman ce Sayyada ki saki jiki Allah yana kallo ina son soyayya ina son romantic love, ba zan ɓoye miki me na ji idan na gamsu baya nufin kema haka karki cuci kanki if u need more, all you have to do is ask I'll be the best husband for you bani da bakin gode miki ba kuma zan yafewa kai na idan zuciyata bata cika da soyayyarki ba"

Kunya duk ta kama Ridayya ta É—aga kai ta kalle shi ya kashe mata ido É—aya yana É—age mata curin girarsa "Na gode"

"Mu je ki kai ni asibiti"

"Baka da lafiya?"

Ya dubeta yana sauya yanayi sosai ya ce "Tun first night É—ina da kika amshi budurci jikina ke ciwo ba ki gasa ni a ruwan zafi ba ban sani ba ko na ji rauni "

"Uhm uhm kai Abbiey "
Chapter 94 · 0% Book details