← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 118

Sashe 66

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Goben nan idan kun je wajan iyayen Mardiyya kawai a É—aura auren sai na fi samun nutsuwar zuciya ina tausayin Ustaz burina bai shige ya yi aure ba"

"Matar anya ba ki yi gaggawa ba? Ki bari ya dawo" Ta ce "A'a ba wata gaggawa ni ban santa ba, In sha Allah sai dai ya dawo yaga matarsa a É—aki zamansa ya fara dundirata haka"

Hajiya ta kafe Mai ran ƙarfe da wasu mutane suka nufi gidansu Mardiyya nan take kamar auren bazawara aka ɗaura auren Mardiyya Salis da Muhammad-Bilal Tahir Rano a kan sadaki dubu hamsin bisa tsari na Muslunci aka raba alawa da goro. Mardiyya har sujjudul shukri ta yi ta mallaki Ustaz cikin ruwan sanyi miji na kere sa'a ta ce ita ko ba'a gama haɗa kayan ɗaki ba zata bi su Mai ran ƙarfe gidan mijinta ta yi masa kyakkawar tarba gabaɗaya ta mance da cewa ya ce bashi da lafiyar ɗa'namiji.

Kullum Ridayya sai sun yi waya da Sadauki ta cikin wayar yake shaida mata ita ce wacce yake so ta bashi dama. Har yanzu bata ce ta amsa ba, ba kuma ta san mene matsayin Sadaukin a ranta ba kullum sai ya yi kamar zai yi mata kuka kalaman soyayya na musamman ke fita daga bakin Sadauki baya tsoron Ustaz ko kaÉ—an.

Kwana goma kenan da faruwar hakan misalin 11:43 Ustaz ya shigo gidan babu mai cewa shi wata kakkaurar black ɗin jersey ce a jikinsa sai trouser babu ko hirami gabaɗaya a ɗan hargitse yake, babu kowa a main parlour ya nufi bedroom ɗinta ya ɗauki Little ya fita da shi ya kwantar a bayan mota ya dawo cikin ɗakin yaga bacci take sosai ya san baccinta da nauyi, daga ita sai rigar bacci ya sunkuya ya cicciɓeta ya nufi mota da ita yana shiga rufe yana ƙoƙarin yi wa motar key tana farkawa ganinsa ya saka ta buɗe baki za ta yi magana fuskarsa babu walwala ya saka hannu ya riƙe bakin nata tare da murɗe shi da sauri kuma ya ja motar ya fice da wani irin gudu....

🥰🧚🏻‍♀️ Sannun ku Mar'atussaliha na yaba muku wajan comment da sharing Ubangiji ya raya zuri'a. 👉🏼🤙🏼🤙🏼 Zazzafar muhawara team Sadauki da Ustaz Ridayya dai second hand ce.
*MUNAFUKIN MIJI 31*
Mikiya Writers Ass...

Bright pens free batch
Nimcyluv

Hotel ɗin da yake sauka tare da yin rayuwarsa secret and privacy a Kano ɗin nan ya nufa da ita, a jikinsa yake jin idanuwanta na yawo a kansa ya share fuskarsa babu walwala ta yi jajur a haka driving da gudu dukda kasancewarsa Ustaz baya ƙaunar yin tuki a hankali.

Ustaz ya yi parking a harabar hotel ɗin a hankali ya kifa kansa a kan sitiyarin motar yana fid da numfashi wani irin zafi zuciyarsa ke yi masa, ciwon da ya yi na kwana biyu bayan faruwar abun shi ya hana shi dawowa, so yake ya zama mutum mai uzuri baya son nuna zafin zuciyarsa a kan Ridayya akwai tarin abubuwan da idan ya duba ya ke yi wa Ridayya uzuri. Yanzu ma a hargitse ya fito kuma baya son taga fushinsa domin ya fahimci idan ya nuna damuwarsa kamar hakan take so shi ne abinda take buƙata.

Fitowa ya yi daga cikin motar wani ya zo wajansa da sauri ya É—an jingina da motar yana sauraren bayanin mutumin wanda tsayin lokaci ya kasa zama ya ji bayanin sai yanzu.

"Da gaske depression yana neman cin ƙarfinka damuwa ta yi wa zuciyarka yawa baka samun yin bacci cikin dare haka da rana ba yi kake ba, zuciyarka a ƙuntace take sosai hatta yawan ciwon kan da kaɗaitar da kake buƙata duk alamomin depression da rashin son maganar ka yi ƙoƙari ka samu nutsuwa ka ɗan ɓata lokacinka a kan wani abun da zai ɗauke maka kewa gudun kar kwakwalwarka ta samu matsala"

Ustaz ya yatsunsa fuska yana jan gemunsa dake yi masa ƙaiƙayi saboda sauyin yanayi baya son zafi weather ɗin Kano dana Lagos are different. Ya jima kafin ya ce

"Ina jin kamar ana kiran sunana ko ana jana wani wajan idan na rufe"

"Dole za ka ji hakan, amfanin zuwa asibitin kenan idan wasu ne cewa za su yi mutanen ɓoye ne ai cutar damuwa haka take signs and symptoms na depression yake you have to be very careful Sir, symptoms ɗin suna da yawa. Feelings of sadness, tearfulness, emptiness, or hopelessness
Anxiety, agitation, or restlessness
Behavior that looks like extreme laziness, rudeness, or disregard for others. Ɓacin rai da kulawa da lokaci, takaici, jin rashin fahimta da rashin kulawa, jin rashin sha'awa da wasu ayyukan al'ada, janyewa daga jama'a rashin mayar da kira rubutu da saƙon imel. Soke wasu tsare-tsare gajiyawa da rashin kuzari rashin samun wadataccen bacci,Jinkirin tunani, magana, ko motsin jiki. Feelings of worthlessness or guilt
Fixating on past failures or self-blame
Trouble thinking, concentrating, making decisions and remembering things"

Dr É—in ya jinkirta kafin ya ce "Kai namiji ne wanda bai kamata a samu haka daga gare ka ba, i wonder why har ka samu kan ka cikin cutar damuwa dole ka kula kuma.....,"

"Enough!" Ustaz ya furta yana runtse idanunsa ya girgiza kansa kaÉ—an sai kuma kawai ya jinjina wa Dr É—in kai tare da bashi damar tafiya.

Gabaɗaya ji ya yi jiri na neman ɗaukar shi, yana ganin mutane bibbiyu a idanunsa ga wani irin sabon ɓacin rai dake wanzuwa a zuciyarsa me miliyan yake nufi? Mahaukaci zai zama ko me sunan Allah kawai yake ambata har ya ɗan samu sassauci ya buɗe bayan motar ya ɗauki Little da har yanzu bacci yake, a nutse ya nufi ɓangaren ɗaya ƙofar ya saka key ya buɗe ya ganta ta kifa kai tana shassheƙar kuka ga rigar jikinta duk ta manne mata a fata da yatsunsa ya fara mata magana taƙi ɗago kanta shi ba zai iya tashin hankali ba ko buɗe baki ya yi zai yi magana har tsakiyar kansa yake jin wani irin dokawa.

Ta É—ago kai ta kasa kallonsa domin duk abinta bata iya kallon idanunsa, a hankali ta fito daga motar Ustaz ya bita da kallo yaga rigar sam ba ta yi masa ba

"Riƙe shi muga"

Amsar Little ta yi sai cin ɗaci take tana ɓata rai jerseyn jikinsa taga ya cire ya zama sai farar singlet a jikinsa da trouser ya zama ƙato a gabanta ya miƙa mata ta tura baki ta ce

"Ni ka mayar dani"

Ya girgiza kansa bai ce komai ba ya gyara tsaiwarsa tare da marsad ya saka mata jerseyn ta rufe mata kirji ya É—an sauke numfashi maganar ita kanta ba komai take ji ba kamar mai raÉ—a ya ce

"Za ki komai na É—auka, banda nuna tsaraici da sura Sayyada"

Ta tura baki ya kalli lips É—in kansa na juyawa da sauri kuma ya É—auke kai ya amshi Little yana tafe tana binsa domin ya san halinta babu inda ta sani kuma ba zata iya komawa ba.

A ƙofar wani bedroom ya tsaya ya saka key ya buɗe, yanayin wajan na mutum ɗaya ne komai da komai yana shiga ya kwantar da Little har ya je bakin ƙofa ya ce

"Ina zuwa"

Ta bi shi da kallo ya jima kafin ya dawo, yana shigowa taga idanunsa sun rine ba kuma ja sukai ba tsananin azabar ciwon kai ne. Ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito sanye da islamic jallabiyya mai ƙaramin hannu banda ita ba da haka zai kwanta zafi yake ji sosai.

"Abbiey jallabiyya dai wannan jallabiyyar sai na yayyanka su"

Sarai ya jita amma ko kallonta bai yi ba, ya daddafa ya yi sallah ya yi azkar ya miƙe kamar zai nufi gado ta yi saurin tashi bai kalleta ba ya ce

"Ba ki da kai Ustaza, me kike tunani?"

Ta yi shiru, shirun nata kuma damunsa yake ko bai tanka mata ba yana son jin maganarta ya ji kalar tsraiwar data sake

"Sallah zan yi" Ta faɗa kai tsaye ita idan ta yi wa Ustaz ƙarya har cikin zuciyarta bata jin daɗin hakan

"Kwanan wata 15 yau, yaushe al'adar ki ta rikiÉ—e?"

Wata kunya ce ta kama Ridayya komai nata ya sani, da gaske bata sallah tashi kawai ta yi da tunanin kwanciya zai yi a gadon

"Uhmm Ustaza kenan akwai matsala a kwakwalwarki ban miki komai ba a baya sai yanzu? Lokaci dai"

"Ni kawai Abbiey ka mayar dani gida na ce ba zan bika ba, ba zan je gidan matarka ba"

Ya nemi waje ya zauna yana tanƙwashe ƙafafuwansa sosai ya dube ta yana jin ciwon kansa na sauka ya daɗe kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce

"Kina da matsala da matata ne?"

A hassale kamar ba Ridayya ba ta ce "E, ina da ita mene ruwanta da kai zata aureka? Kuma ni ba zan je na dinga ganin yadda kuke rayuwa ba"

Nan da nan idanunta ya cika da hawaye sai yanzu Ustaz ya fahimci da biyu ta yi masa abinda ta yi kwanaki idan ya fahimta daidai ya haÉ—e da fuska sosai kamar ba shi ba a kasashe ya ce

"Oum-Bilal buɗe kunne zuwa gidana da rayuwa dani dole ya zame miki domin ina buƙatar, ina ƙaunar matata kuma ƴar'uwata bisa umarninta na zo gare ki, soyayya da ƙaunarta a zuciyata ya saka nake mata uzuri, idan kika bari ta yi kuka saboda ke za ki ga me zan miki, bana son fushinta kuma rayuwa gidana daban take wacce baki taɓa ganin irinta ba ko a mafarki"

Numfashinta ta ji yana tsayawa ta saka hannu ta ɗan riƙe rigarta bakinta na rawa ta ce "Da gaske wai ka yi aure Abbiey? Waka aura?"

HaÉ—aÉ—É—iyar girarsa ya É—age mata alamar eh don ba zai faÉ—i abinda bashi kenan ba ya juya a hankali ya ce

"Aure lokaci"

Wani irin kuka ta rushe masa da shi tana durƙushe wa a ƙasa "Amma ƙatuwa dani a ga babana ya yi aure? Kuma soyayya kuke kuma ta haihu?"

A ransa ya ce "Babbar magana" a zahiri ya ce

"Laifi ne idan matata ta haihu? Ke dana aurar dake kika haihu laifi ne? A'a ƙiyayya muke kema mu je ki faɗa mini inda kika baro mijinki a daidaita na ba yar dake, matata jinina ce"
Chapter 66 · 0% Book details