← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 118

Sashe 37

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsakiyar gado ya hango ta, ta cure waje guda alamar sanyi take ji, bargo daban ita daban, haka rigar baccin daban ya jima tsaye yana tasbihi a ransa a fili ya ce "Mugun gani Ustaza" Ya furta yana zama a gefen gado, a hankali ya kai duban shi ga fuskarta duk ta marairaice saman idanunta ya kumbura sai ajjiyar zuciya take saukewa na wahala da ƙyar ta yi bacci saboda ciwon ciki ita kaɗai a ɗaki kamar mayya.

"Allah ya yafe miki Ustaza, bani da laifi" Ya faɗa yana ja mata rigar ta rufe mata cinyoyinta ya ja mata saman ƙirjinta yana mai neman ya fiyar Ubangiji. Caraf ya ji ta riƙe hannunsa tana fashewa da kuka. "Abbieyna ka dawo zan mutu bafii cikina Abbiyena" Ya ɗauka mafarki take ganin yadda jikinta ke rawa ya sa shi fahimtar zahiri ya sauke numfashi yana mai lalubo kalamar

"Shalale... Ustaza"
Da sauri ta buɗe ido wanda ya kumbura ganinsa ya saka ta sauke wata ajjiyar zuciya tare da mirgina wa ta ɗora kanta a cinyarsa tana marairaice fuska "Abbiyena cikina zan mutu wayyo Allahna" Addu'a ya fara yi mata yan shafa sumar kanta, da ƙyar yake motsa hannunsa saboda yadda gargasar jikinsa ke mimmiƙe wa tana zubewa, zuciyarsa na doka masa da tsananin ƙarfi tunaninsa na neman gurɓata, kokawa yake da zuciyarsa yana ambaton sunan Allah zufa sai yanko masa take kyakkawan bugun da zuciyarsa ke yi masa ya tsananta, ya yi saurin matse hannun Ridayya. Da ƙyar ya iya tattaro jarumta ya aza bisa gangar jikinsa. Kuka Ridayya ke yi sosai tana jin kamar zata mutu gashi ta bi ta shige masa jiki kamar anan zata samu sauƙi, jikinsa mahaifi daɗi gare shi kuma an ce mutuwa na jin kunyar idon mahaifi wannan dalilin yasa Ridayya riƙe Ustaz da kyau tana kuka "Abbiey zan mutu cikina" Da ƙyar ya ce "Ba za ki mutu ba Ustaz, sorry" Bashi da wani zaɓi haka ya rungume ta a jikinsa yana yi mata addu'a hannunsa ɗaya na shafa sumar kanta. Iddar da sallar ƙiyamul laili ya yi daidai da lafawar ciwon bacci ya ɗauke ta a jikinsa tana sauke numfashi mai zafi ya ƙura mata Idanu a fili yana girgiza kai ya ce _"When?_ Sai yaushe ne?" Kwantar da ita ya yi yana rufe ta da bargo ya miƙe tare da nufar waje.

A parlour ya same su suna shur Umma ta ce "Babban mutum saukar yaushe?" Ya nemi waje ya zauna Baba ƙarami ya ce "Jiya ko?_

"Na rasa sunturin da yake bashi Kano bashi Lagos shi kuma ba auren ba" Nan da nan ya kame fuska a nutse ya ce "Abba, Umma ya ibada?". "Allhamdulillah!" Suka amsa lokaci É—aya Umma ta kalle shi ta ce "Rashin lafiya ka yi a can ne naga duk ka rame idanunka zuru-zuru?" Ya É—an gyara fuska ya ce "Haba mana Umma haba, kin ce rama kin ce sunturi kamar mota, haba mana"

"To Ubana na yi shiru" Baba ƙarami ya yi murmushi ya ce "Kowa lafiya ta yi wa daɗi ba kamar mai ita ba, sannu sannu ai bata hana zuwa sai dai a jima ba a je ba, ki daina gaigaye za ki ci tumu ne" Umma ta ce "Gwara na yi shiru yanzu sai ya ce bana son tsawa da gaske ban son tsawa Umma" A ɗan fakaice Ustaz ya yi murmushi yana shafa kansa zuwa gemunsa "Tea please"

"Shur da tea?" Ustaz ya ce "With lemon" ya ƙare yana lumshe idanunsa Umma ta miƙe ta nufi kitchen. Baba ƙarami ya kalli Ustaz ya ce "Muhammad-Bilal" Ustaz ya runtse idanunsa sosai jin sunan ya yi har tsakiyar kansa ya juya ya kalli Baba ƙarami dake cewa "Yaushe za ka yi aure? Tun ƴan'matan na marmarinka sai ka tsofa a idanun nasu? Kasan shekara nawa kake a yanzu, me kake nufi Muhammad-Bilal"

"Ina nufin lokacin Abba, sai na fara aurar da Ustaza" Ya runtse idanu sam maganar ba ta yi masa daɗi a zuciya da kuma baki ba, gudun kar Baba ƙarami ya sake magana ya miƙe yana bin Umma kitchen.

Ta farka jikin da sauƙi ta yi wanka ta shirya cikin milk ɗin abaya ta ɗora mayafi fuskar ta faɗa sai maiƙon da take idanun sun ƙara girma laɓɓan sun yi jajur saboda kuka. Bisa umarnin Ustaz ta nufi part ɗin Baffa lokacin 12 na rana ta samu Baffa a parlour shi da Ammi suna maganar kayan sallah ta durƙusa ta ce "Ina yini Baffa, Ammi?" Ko inda take Baffa bai kalla ba Ammi na yin murmushi ta ce "Lafiya lou ƴar University, ya karatu?" Cikin cool voice ɗinta ta ce "Yau ne zan fara attending lectures"

"Oh i see" Ta kalli Baffa sai kuma ta ce "Yanzu nake cewa Baffanku ya bada kuɗin kayan sallarki amma fur ya ƙi ya bawa kowa, Zainura kala kusan goma ya yi mata" Ridayya bata ce komai ba ganin yadda take ta kallon Ammi ya sa ta ce "Saƙon ki yana kan mirror" Ta miƙe ta nufi best ɗin Ammi. Baffa ya ce "Maryam ki daina haɗa ni da wannan yarinyar zan miki abinda ba ki yi za to ba"

"Jinka wuya za shi. Kuma ai duk lalacewar goma ta fi biyar albarka dole a kira Ridayya da Æ´arka, idan baka so kawai ka kure ta a gidan gabaÉ—aya ko kuma ka tsine mata" Kalmar ta daki Baffa haka kurum a ransa yana jinjina kalmar tsinuwa. "Kuma ka tura mini kuÉ—in kayan sallar nata yanzu umarni nake baka" A sanyaye ya ce

"Nawa?" Ta ce "Kala sha biyar zan mata, ka bada 250k" Bai yi magana ba a nan take ya tura mata kuɗin ita kuma ta turawa Biba ta ce ta haɗa mata a kan sauran. Ridayya sam bata lura da wanda yake zaune a ɗakin Ammi ba tana ƙoƙarin ɗaukar kwalbar ta ji an ce "Wow irin wannan diri haka?" A firgice ta juya idanunta ya sauka a kan garjejen dake kwance saman gado. Ƙanin Ammi ne don ta gane shi ya miƙe ya ce "Kin yi mini da harka ƴan'mata" Ridayya jikinta ya fara rawa sosai ko maganin bata sha ba ta nufi hanyar waje ya yi saurin tare mata hanya ya ce "Ke cika yane, ki gane mana ki zo mu sarara kafin na sata" Bakinta na rawa ta ce "Ka yi haƙuri"

"Hahaha ji gaja, mu saya za mu yi, na baki gishiri ki ban manda kin ji ƴar baka ƴar duma duma jin ki ya fi ganinki" A tsorace ta ja da baya ganin yana ƙoƙarin kamo ta "Ka bari bana so, wannan iskanci ne" Burhan ya ce "Ai daman Iskancin zan miki, ki bani dama ki ware ki ci duniyarki da tsinke, domin idan kina tunanin aure ki daina. Wallahi babu mijin da zai ɗaukar wa kansa jaraba da bala'i da ƙaddara, duk matan duniya sai ke? No no Animals" Kalmar Animals ya daki zuciyar Ridayya ko dai babu wanda zai aure ta ɗin kenan? Ba namijin dake son ta sai Abbiey?

"Thinking? Kar ki wahalar da kan ki sai ki mace a tunkuɗaki kabari a narka gasa, aure sai dai a mafarki wanda za ki yi sai kuma ki yi wanka, amma har gaban abada ba za ki taɓa samun mijin aure ba, ki rubuta ki ajjiye idan ma an yi dace sai dai wulaƙantacce amma ko shela a ka yi ba za ki samu ba, gwara ki zo mu shaƙata ita Maryam ɗin ce ta bani dama ta ce mu yi awa biyu ba wanda zai sani zata ɓoye mu ki zo na dandali roman daɗi na farke wannan rufin kafin wani ya ruga ni don tabbas ƙarshen budurcinki a waje ne ba dai gidan aure ba, kar ki mini asara" Hawaye ya ɓalle a fuskar Ridayya domin yanzu tana fahimtar komai albarkacin karatun littafan Hausa da zama da Mardiyya.

Burhan ya ce "wallahi na kwaɗaita zan sarara dake zan rufa miki asiri ba wanda zai san na yi tarayya dake, mu maza duk mai mukai ado ne kune zai zame muku gori, gashi kin nuna sosai kaya iya kaya" Fita za ta yi ya damƙo ta ta daddage ta gartsa masa cizo ya sake ta yana ƙara ta fice a guje. Ammi na zaune a parlour bayan ta damfari kuɗaɗe tana jiran taga fitowar Ridayya tana jirga ƙafa jini na bin ƙafarta haka shi ne zai bata tabbacin plan ɗinta ya yi. Ta miƙe da sauri ganin Ridayya ta fito ta ce "Ke lafiya lafiya?" Daidai nan Mami ta fito zata kasuwa ita da Zainura kai tsaye Ridayya wajan Mami ta nufa tana zuwa ta faɗa jikinta ta fashe da kuka, wani irin kuka take wiwi kamar wacce aka ce Ustaz ya mutu a hankali kuma ta ji wani sanyi na ratsa zuciyarta, jikin uwa daban ne wani irin abu wanda bata taɓa ji ba shi ne yake ratsa ta. Mami ta yi shiru ta kasa taɓa Ridayya daman ita ta san Mami ba zata taɓa jan ta a jiki ba, itama kwaɗayin uwa ne da kuma neman inda zata zubar da hawayenta. Da sauri ta saki Mami ta nufi part ɗin Baba ƙarami kai tsaye bedroom ɗin Ustaz ta nufa. Mami ta tsaye da sauri kuma ta ɗauke kanta tana goge hawayen idanunta babu shakka addu'a daban take tasan kusancin ta da Ridayya yau addu'ar data jima ta na yi ce cikin watan mai falala.

"Fatima bani kuÉ—in dana baki na kayan sallar ki na fasa ban niyya ba" Baffa ya faÉ—a yana haÉ—e fuska. Mami ba ta yi magana ba ta ciro cash É—in kuÉ—i dubu hamsin ta bashi. Ya ce "Fitar ma bana da ra'ayi" Ta yi sak ta ce
"Nan kuma ɗaya, kuɗinka na baka daman ban damu da su ba domin ba a wulaƙance ka ganni ba, fita kuma babu fashi" Zainura ta ce "Siyaya za ta yi mini fa Baffa" Bai kula Zainura ba ya ce
"Wallahi kika fita a bakin auren ki" Mami ta ce
"Ka ji tsoron Allah Alhji Mansur, ka tuna Ubangiji yana kallon ka"
Chapter 37 · 0% Book details