← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 118

Sashe 35

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda a rayuwa baka san mene zai faru da goben ka tunda al'amarin na kasancewa kamar karatun littafi, abinda ka karanta a wannan shafi ba shi ne zaka ruska a shafin gaba ba, haka kuma bangon littafi bashi zai fasalta yadda labarin ya gunsa ba. Yau fari ne gobe baƙi, yau dariya gobe kuka, yau zuma gobe maɗaci. Rana ta juya zuwa kwanaki, sannu a hankali kwanaki ke mirgina wa suna rikiɗe wa zuwa satutttuka, sati ya zama watanni daga sai a yi maganar cikar shekara. Tafiyar Ustaz zuwa Lagos ya dawo da rayuwar Ridayya sabuwar fil, ta koma ruwa. Damuwa da ƙunci sune abokan hirar ta, bata jin daɗin zaman gidan domin hatta Umma bata wani damu da ita ba, hakan baya rasa na saba da sabon Malamin da Ammi ta sauya, asiri gaskiya ne sai dai ya zo maka da sauƙi idan kana da kariyar Ubangiji.

Bayan rubuta Jam ta samu maki na ban mamaki wanda ya yi daidai da kalar makarantar da Ustaz yake muradin sanya ta ciki wato B.U.K _Bayero University Kano_ A baya basa ɗaukan under 18 amma dake abu na manya ne an shiga an fita aka samar mata da Admission ta samu gurbin shiga a shekarunta daya kasance 16 amma jikinta ya ƙaryata ƙanƙantar shekarun.

"Ridayya tun ɗazo kikai shiru, wai a hakan bama ki fara attending lectures ba?" Ridayya ta yi shiru zuciyarta na bugawa da abinda zata ruska yau a gida, Baba ƙarami baya garin ya je Rano gashi Hajiya Grandmother ɗinta ta je Umra tunda suna cikin watan Ramadan ne. Tsaki wacce suke tare ta yi ta ce "Matsala ta dake wulaƙanci da raini"

"Haba mana Mardiyya"
Ridayya ta furta a sanyaye idanunta na cikowa da hawaye. Mardiyya ta ce "Mtwsss mene na kuka to? You looks so doll mene?"

"Nothing, babu" Ta faɗa tana share hawayen idanunta daya kasa tsaya mata. Diyya ta ce "Ni bana son irin haka, sai na faɗa miki damuwata amma ni kiƙi faɗa mini meke damunki ko Abbiey ne?" Jin sunan Abbiey ya saka Ridayya ɗan lumshe idanunta tana kokawa da numfashinta daya gama tsaya mata a maƙo shi

"A'a" A fusace Diyya ta ce
"To banga amfanin zama ƙawa a wajanki ba, daman nike tuttura kai na ina miki shisshigi a rayuwa, na yi hakan ne saboda conditions ɗinki"
Ridayya ta marairaice ta ce "Kema na ishe ki?" Sai kawai ta fashe da kuka har da shassheƙa ta ce
"Don Allah na dawo gidanku da zama kafin Abbiey ya dawo Mardiyya?" Tausayin Ridayya ya ƙara kama Diyya ta ce

"Komai ya zafi maganinsa Allah, ita ƙaddara tana da nata lokacin ki rubuta ki ajjiye watarana zai zama tarihi" Ridayya tunani take a zuciyarta yaushe za ta yi murmushi irin na Zainura? Irin na su Junaid yaushe zata zama cikakkiyar ƴa kamar kowa a gidansu? Ita da gidan ubanta amma ya fi ƙarfinta? _How long_ zata kasance haka? Sai yaushe komai zai zama daidai a rayuwarta? "Don Allah na tambaye ki Mar"

"Allah ya bani iko" Ridayya ta ce "Da gaske ba zan taɓa yin aure ba wai? Ba zan taɓa samun wanda zai ce yana so na ba? Wai zan ƙare a gidanmu har abada kamar baiwa" Diyya ta ce
"Ki daina faɗar haka, shi aure ai lokaci ne da shi da mutuwa ba a saka musu rana, da shi da haihuwa ba a yin gorin su babu maki ki yi auren ki bar ni, ki manta ki saka karatu a gaba ki yi achieving abubuwan da kike da buri" Ridayya ta yi shiru tana sauke ajjiyar zuciya hawaye yaƙi tsaya mata gashi idan tana kuka leɓen ƙasa ya yi sharɓeɓe ya sakko ƙasa hancinta ya bubbuɗe. Ganin tana sauri ya saka Diyya riƙe ta sosai

"Wannan saurin fa? Kar ki faÉ—i fa" GabaÉ—aya ta tsangwami kan ta ji take ko'ina a makarantar gulmarta ake gashi ta hango wasu matasa tsaye a jikin mota sai kallonta suke kamar ta kurma ihu ita kam idan haka ne bata jin zata iya karatun. A haka suka gilma ta gaban samarin suka shige wani ya yi saurin toshe hanci ya ce

"Smell wannan kill me oh gosh!" Wani matashin saurayi ya faɗa yana rufe hanci da hanky. Moo Ya ce "Ban son sharri kana nufin mun yi tusa ne?" Khalil ya ce "No, I don't mean that, that black girl data shige ita ke yin warin" Duk suka juya suna kallon bayan Ridayya abaya ce a jikinta mai ɗan faɗi ta ɗaure igiya a ƙugunta, yadda abayar take baƙa ƙirin haka jikin Ridayya suka yi anko haƙonta ne kawai da idanunta masu haske a jikinta. Haɗa baki sukai wajan furta
"Rabbi ya yi halitta, halitta, halitta...," Shaba ya ce "Asnanic ya yi basira wajan yin waƙar nan, wlh ban taɓa cin karo da baƙar mace irin wannan ba, tab kwalta"

"Ga leɓe ina ruwan Dandamali" Moo ya ce "But she's arrogant, i like the way she's act"

Tunda suke surutun su, bai ɗago ba bai ma san a kan wa suke magana ba, saboda ba kowa ya sani a school ɗin ba. Sai baza ƙamshi yake mai ɗaukan hankali kaf cikin haɗaɗɗun matasan babu wanda ya kama yatsarsa a kyau da haɗuwa Ubangiji ya yi halitta, fari tas har ɗan yellow yake ga sajensa daya gewaye fuskarsa ya yi daidai da gemunsa mai kyau. Wagambari ne a jikinsa brown colour ya ɗora hula zanna bukar ya bluetooth a kunnensa ya riƙe waya iphone a hannunsa yana dannawa. Kan shi ya ɗaga ya kalleta idanunsa a sauka a faffaɗan ƙugunta dake juyawa ta cikin abayar, ya jima kana ya ɗan taɓe baki ya juya. Khalil ya ce
"Meer ka san ta ne?"
Ya É—aga shoulder duka biyun alamar "No"
"Bama zata kula ka ba, ba hannunka ba ce?"

"A saboda bani da qualities da zata kula ni? Mu ai sai dai mu saka mace kuka mu ɗora mata hawan jini, har yanzu banga kala ta ba" Moo ya ce "Na santa fa" Duk suka juya suna kallonsa da alamar ƙarin bayani ya ce "Ridayya Muhammad-Bilal Rano is her name, babanta a yanzu mai arziƙi ne sosai da sosai yana da kantuna a katin kwari da sabon gari, gashi yana kwangila kala-kala business yake na ban mamaki, sai babban yayenta mai suna Muhammad-Bilal Tahir Rano ana ce masa Ustaz shi ne Md a fidelity bank dake Lagos yana mugun son ta, hatta aikin da ya ke yi domin ita ne. Babban mutum ake ce masa a familyn saboda ya girmi kowa kasancewar basu da wani yawan ƙwarai duk abinda ya mallaka sunan Ridayya ne a jiki, sai dai ita kuma kaf dangin basa son ta hatta babanta wai ya ce ba ƴarsa ba ce shi ne shi kuma Ustaz ya raineta tun tana ƙarama, yarinyar nan da kake gani ba hannun kowa ba ce dukka da muninta kamar a yanka a ɓoye wuƙar ko a haɗata da su Dila a kejin zoo road"

Meer ya ce "Wow interesting, kawai ka ce kadara ce" Moo ya ce "Meer kai me za ka yi da ita ai Daddynka ba zai bari ka auri ugly ba" Meer ya jinjina kai ya ce "Zai bari mana, matsalar na tsani abu mai muni gaskiya bana ƙaunar baƙar mace yadda nake fari na samu fara mu dinga haifar farare"

"Ba zata taɓa sauraran ka ba" Cewar Moo. Da sauri Meer ya ce "Hujja?"
Kai tsaye ya ce "Ta yi sati tana shigowa School fa, kuma ina bibiyarta duk wasu gulma na Æ´an mata ni nake kawo muku, to ko mata bata magana da su balle namiji, kullum cikin kuka take sai dai tana da diri fa idan ka nutsu ka kalleta wallahi"

"Ko soyayyar minti ce sai na rinjaye ta mun yi, na ci moriyar ganga na yar da ƙwallon mangoro na huta da ƙuda kuma" Khalil da babansa ya fi na kowa kuɗi a wajan ya ce
"Caca" Gabaɗaya sukai shiru Meer ya ce "Ina ciki" Khalil ya ce "Idan ka nemi soyayyar yarinyar nan, kuma ka sami abinda kake so kana da 5 Million kassh" "Are you sure?" Khalil ya ce "Ai idan maganar caca ne ba a wasa, idan kuma bata amince maka ba zaka bani wani abu dana jima ina buƙata a wajanka, na baka nan da wata biyu" Duk sukai ihu Meer ya dinga tunanin miliyan biyar ko dubu ɗari ta kansa bai taɓa riƙe wa ba, hatta yadin jikinsa wajan Mujahid mai guga ya yi opay ɗin su, wayar ma ta Mujahid ce amma kaf cikin abokan nasa babu wanda ya san asalin Meer ganinsu yake kamar duka masu kuɗi shi ne kawai ɗan gidan Malam Ɗan'lami ya ji a ransa dole ya bi salo mai kyau na burge Ridayya kafin furta soyayyar.

Ridayya na komawa gida ganin Umma bata nan ita kuma ba zata iya yin girki ba saboda ciwon cikin dake damunta, gashi ko azumin ma bata yi, ya saka ta cire hijab ɗin kanta daga ita sai duguwar rigar da ta bi jikinta ta yi luf ita na maiƙo rigar na maiƙo. Ita ko powder bata taɓa shafawa ba bata kwalliya bata san yadda ake ba karatu kawai ta saka a gaba don tana da buri mai girma da take son cimma, dake ɓangaren Mefa take son karanta Medicine, daga ta zama Medical Doctor sai ta nufi Gynea. Bachelor of Medicine (MB) of Surgery (BCh) and of Obstetrics (BAO).

Idanunta rufe take son buɗe cooler ɗin ta ji an ce "Wallahi kina taɓa wa zan faɗawa Mami" Ridayya ta kalli Zainura tunu idanunta ya sauya ta ce "Yunwa nake ji"
"To cinye ni, ko me kika taɓa a gidan nan najasa ce wallahi" Ridayya ta kalli Zainura bata kula ta ba ta fara ƙoƙarin ɗora tukunya zata dafa Indomie "Wannan kuma ki ɗauki mai kama dake Allah ya sauwaƙe ki zama yayata kila ke fa shegiya ce zina aka yi aka haife ki"
Chapter 35 · 0% Book details