← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 118

Sashe 64

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonta kawai yake yana nufar inda take tsaye bai san me yake ba shi dai ya tsinci kansa a gabanta ne hawayen fuskarta sun jiƙa masa tafin hannu kuka ta fashe da shi tana yin baya gani take har yanzu mafarki ne

"Daman nasan mafarki ne ba Abbiey bane me ya sa kasan ba kai bane zaka kora ni ka hanani bin Sadauki?"

Sai a lokacin ta girgiza kai yana jin kalamar Sadauki a kansa a fili ya ce "Ba ki da kai Ustaza"

"Innalillahi wai mafarki nake ko Idanu biyu muryar Abbiey nake ji Abbiey..m.," bata ƙarasa maganar ba ta ji ya cafko hannunta tare da haɗe ta da jikinsa ya riƙe ta gam a ƙirjinsa ba daidai kunnenta yana sauke numfashi ya ce "Ustaza Oum-Bilal" ya faɗa yana yi mata wata kyakkawar rungumar da shi kansa bai san ya yi ba.

Karanta ki yi comment ki danna share to all your groups
*MUNAFUKIN MIJI 30*
Mikiya Writers Ass...

Bright pens free batch
Nimcyluv sarauta

Zazzare Idanu ta yi sai ta ji wani iri ta kasa kallonsa sunan Oum-Bilal ya yi mata wani iri. Sakin ta Ustaz ya yi bayan ya gama zuge mata zip É—in data mance bata rufe ba, wanda shi ne dalilin biyo bayanta da kuma kusancin da suka samu wanda a tunaninta rungumeta zai yi.

Ya ja baya tamkar bashi ya yi magana ba ya ce

"long time Sayyada, irin zuba kyau haka?"

Ridayya ta kasa ɗago kanta dake ƙasa tsoro da kunyar Abbiey ɗin ya mamaye mata zuciya, tunanin hukuncin da zai yi mata a kan Sadauki kawai take yi, daman yasan tana nan amma ya kasa nemanta cikin shekarun nan ko watanni?

"Zo mana"

Ustaz ya furta a taushashe bayan ya gama daidaita zaman shi a saman gefen gadon ɗakin nata idanunsa a kan wayarta dake ringing an rubuta “Sahibi”

Ta ƙarasa tare da zubewa a gabansa ƙasan ƙafafuwansa ko zama ta kasa bakinta na rawa ta ce

"Ina yini Abbiey?"

"Allah ya yafe miki Ustaza ba haka muka saba ba kin ji ko"

Hannunsa na dama ya miƙa mata a hankali ta ɗago kanta tare da cira hannunta na dama ta miƙa masa sukai musabaha ya riƙe ɗan mitsitsin hannu idanunsa zube a fuskarta ya ce

"Assalamu'alaiki"

"Wasallamu'aika Abbiey"

"Sannu Oum-Bilal kina lafiya dai? Komai ƙalau?"

Ta jinjina masa kai ya zame hannunsa yana yin baya ya jingina da jikin frame wasu sakanni ya É—auka kafin ya ce

"Masha Allah. Rabbi ya yi miki albarka"

"Amin"
Ta yi shiru na rashin abin faɗa banda harbawa da ƙarfi babu abinda zuciyarta ke yi mata, a kullum Ustaz na yi mata kwarjini amma na yau na musamman ne ya sauya mata gabaɗaya babban abin ba wani sauyin kamanni a fuskarsa banda shekaru da ƙasumba daya ƙara da yawan sumar kai, sa nutsuwarsa da tarin kamalar daya sake mamaye gangar jikinsa ga wata Ilham ta musamman. Haka kawai ta ji ranta ya ɓaci da ransa da lafiyarsa hankalinsa kwance yake gudanar da mu'malarsa babu damuwa da tunanin yarinyarsa bata tare da shi bai san hali da ƙuncin data shiga ba.

Baya kallonta a zahiri sai sai dai da idanun zuciya yake kallon yanayinta shi bai ma san yaushe ya riƙe ta taɓa ɗazo kawai yasan ba zai zuba Idanu ta fita riga a buɗe ba. Duk suka yi shiru kowa ya kasa magana sai bugun zuciyarsu dake aiki so yake ya tambayeta ina mijin nata? Ya akai ya neme ta ya rasa.

Mahmah ce ta shigo É—auke da Little dake kuka sosai tana faÉ—in "Mimi gashi ya addabi jama'a da kuka kin san halinsa idan ya fara kuka sai kin bashi ya sha hankalinsa yake kwanciya"

Ridayya ta kasa amsar Little ita kunyar Abbiey take yaga wai wannan ita ta haife shi kenan ya san me ta yi ta samu É—an?

"Ina magana kina jin yaro zai fasa kunnen mutane?"

A marairaice ta ce "Mahmah ki riƙe shi zai yi shiru fa"

Daƙuwa ta yi mata ta ce "ungu wannan dan gidanku idan ke ba ki sha nonon uwa ba sai aka ce shi kar ki bashi? Saboda wa Allah ya hallici nonon banda yaranki? Bafa don a do aka mallaka miki su ba. Naga kullum kina bashi yanzu iyayi ne ko san a sani? Karɓe shi ni"

Idanunta tuni ya yi raurau hawaye ya cika su wacce kalar mafisa ce Mahmah ke shirin janyo mata don abin kunya?
"Don Allah Mahmah wallahi....,"

Ustaz dai da kunne yake ji ko É—aga kai bai yi, he just pretend kamar bai san mene faruwa ba.

Ajjiye mata shi ta yi a cinya Mahmah na fita da halin yaran yanzu ta yi waje abinta don ita har zuciyarta bata É—auka ta yi wani laifi ba.
Little ya dinga kuka yana zura hannunsa cikin rigar Ridayya alamar dai a matse take har da haura ƙafa kukan ya yi wa Ustaz wani iri a ka domin har ƙasan zuciyarsa yake jin kukan na Little ya ɗago kai yana haɗe fuska ya ce

"Ba haka na yi miki ba Ustaza da gaske ban raineki haka ba, ko sau ɗaya a ta dalilina ba ki taɓa kuka ba" Ya faɗa yana gyara zama tare da kafe ta da Idanu babu kuma wasa a fuskarsa don shi bai ga wannan dalilin ɗaukan alhaki da zunubin ba.

Ta tura baki taƙi cewa komai ita haka kurum haushinsa ya kamata me ya sa bai taɓa nemanta ba ta kuma yi alƙawarin ba zata yi magana ba amma tuni hawaye sun fara sauka daga idanunta saboda zallar sangarta da ganin kuma Ustaz ɗin a gabanta.

"Ko dai ki bashi abinda ya kewa ko kuma ni na zo na bashi, ko kuma dai ki cire su tunda basu da wani amfani"

Ganin ya miƙe ya saka ta yi saurin riƙe Little ta fara ƙoƙarin fito da shi cikin sauri kuma mai kama da nutsuwa Ustaz ya yi hanyar ƙofa yana jin kansa na sarawa.

Sanda ya fito daga bedroom ɗin Ridayya ya samu Tajj zaune shi da Sadauki daya gama rikicewa ya daddafe kansa da yake masa wani irin ciwo. Shi fa dole yau sai ya fita da Shanshan duk wahala yadda ya nuna masa iko shi ma dole ya nuna masa ya fisa dabara kuma ɗan'yau ne shi. Ya miƙe tsaye ya ce

"Please i want to talk to you Brother"

Tajj ya nuna kansa ya ce "Ni?" Ya jinjina kansa tare da ficewa ya yi waje. Tajj ya miƙe ya bi bayan Sadauki.

"Wannan kiran fa Hamza?" Sadauki ya riƙe hannun Tajj tare da ɗorawa a zuciyarsa ya ce

"Ka ji ko? Ka ji yadda zuciyata take yi to wallahi gab take da bugawa kuma na san ba za ka so na mutu yanzu ban yi achieving komai ba, ban yi aure na haifi kamar Nadra ba, ban san mene daÉ—in aure da daÉ—in zama da macen da kake tsananin so ba, ina so aure sosai"

"Duk ɗan sunna ai ba zai ƙi sunna ba Sadauki"

Sadauki ya jinjina kai yana ƙasa da murya har ɗagawar ƙirjinsa ana gani ya kama hannun Tajj ya damƙe cikin roƙo da neman iri ya ce
"Kai ne tsanin da zan hau na cimma gaci, gina soyayya a tubalin zuciyar daya dace da Hamza Sadauki wannan ba matsala ba, magance abinda zai iya kawo shamaki a rayuwar Sadauki da matar da yake da burin rayuwa da ita shi ne matsalar, Yaya help me please allow me to go with her"

"Ita wa?"

Sadauki ya hargitsa kansa kamar ya make Tajj haka yake ji ya ce "Haba Yaya haba Baban Nadra ya kake haka ne ka fahimta mana"

Tajj ya girgiza kai ya ce "Ban fahimta ba Sadauki"

"Ka fahimta mana da Hausa nake magana bada yaran Jamus ba, balle ka ce don na rayuwa a canne. Ka bani izini na fita da Ridayya akwai magana mai muhimmanci da zamu tattauna da ita ka tausaya mini"

"Wacce magana bisa wanne dalili kake son fita da ita?"

"Saboda ina son ta, ina son ta, ina son Ridayya Yaya kuma aurenta nake son yi" Tajj ji ya yi jiri na neman yar da shi zuwa ƙasa ya yi saurin jingina da motar Sadauki yana karanto Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! A zuciyarsa ga Amini da ɗan'uwa ga kuma shi shi bai tsaya ya nutsu a kan qualities ɗin Ridayya ba kawai ya ji yana son rayuwa da ita ko dan yadda Nadra ta samu farin ciki, yana tsananin tsoron macen da zai aura wacce zata riƙe masa yarinya saboda Allah..

"Ka yi shiru, akwai matsala ne?" Tajj ya girgiza kai ya ce

"Gare ni babu, amma wanda ya ce ta koma cikin nan shi ne problem ɗin. Shi ne komai nata shi ne yake da ikon baka ita da amincewa da kai, idan ka ji ance Ridayya Muhammad-Bilal Rano to ita ce sunansa ne maƙale a nata. Idan na faɗa maka halin da Ustaz ya shiga da babu ita zaka ƙaryata domin tamkar ƴa haka take wajansa"

"Da sauƙi ai ka ce kamar ƴa ina tunanin problem kaɗan ne"

Murmushi Tajj ya yi yana taɓa kafaɗar Sadauki ya ce "Soyayya gaskiya ce Hamza, kuma dukkan inda soyayya ta gaskiya take tana nuna kan ta duk yadda mutum ya kai ga zurfin cikinsa, wani irin abu ne da yake fitar da kansa ba tare da mutum ya shirya ba. Akwai bambanci tsakanin _i have a feelings for you ko you're my crush da i have falls in love with you_. Sadauki ba kasancewar Muhammmmd uba a wajan Ridayya ne matsala ba, Ridayya ita kanta ita ce rayuwar Ustaz wallahi Allah ba zan yi san zuciya ba, ko dan kasancewarka jinina. Ustaz yana tsananin so da ƙaunarta bai taɓa faɗa mini amma halin daya shiga ya nuna, yanayin daya samu kansa daya ganta ya fallasa sirrin zuciyarsa ina tunani ka yi haƙuri ka nemi wata ko a family ne"

Wata kalar dariya Sadauki ya yi yana fesar da iska daga bakinsa yana dinga tafiya yana dawowa sai kuma ya girgiza kai ya ce

"Idan shi yana son ta ita tana son shi ne? Idan yana son ta mene yasa ya barta ta auri waninsa? This is unbelievable"
Chapter 64 · 0% Book details