← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 118

Sashe 65

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ƙaddara ita ce silar faruwar komai, ƙaddara ita ta sanya Ridayya yin aure kuma har ta haihu kuma ƙaddara ita ta saka mijin ya sake ta. Kasancewar littafin da zanen ƙaddararsu ɗaya ne ya saka shima bai yi aure ba har yanzu, kuma ƙaddara ta ɗauki rayuwar iyayensu ta bar su, su kaɗai a duniya, ƙaddara ita ta saka muka buge Ridayya kuma na kawota gidana zuwan Ustaz nawa bai taɓa ganinta ba, kuma ƙaddara ita ta haɗa su yanzu bana son wannan ƙaddarar ta yi silar rayuwarka Hamza You are my young brother kabar maganar iya mu domin ko Ridayya bata so a wannan karan bata da zaɓin daya shige Muhammad-Bilal"

Sadauki ya zame hannun Tajj ya ce "This is serious. Ni kuma na ɗaukar maka alƙawari ƙaddarar aurena ita ta rabata da mijinta, kuma wallahi ba zan taɓa haƙura ba, bana faɗuwa ko a makaranta ba kuma zan faɗi a Soyayya ba, ko zan rayu da Ridayya na kwana ɗaya a matsayin miji da mata wallahi sai na aureta kuma zan tabbatar mata a yanzu soyayya take buƙata ba zaɓin wani ba, dole ta bi abinda zuciyarta yake so"

Tajj ya yi murmushi ya ce "I wish you all the best Romeo"

"What ever; na ji na yar da kuma zaka sha mamaki Commissioner"

"Commissioner? Yayanfa?"

Sadauki ya haɗe rai ya ce "Ba zan faɗa ba, tunda ka kasa taimakona bana ma buƙata kuma duk sanda ka ji an ce alfatiha ni da Shanshan daga ranar ni ne babba"

Ciki ya koma ya samu Ustaz riƙe da Little yana jijjiga shi ya kalli Mahmah ya ce "Mahmah please za mu fita tare da Ridayya"

"To Allah ya tsare ya kiyaye" Sosai mamaki ya cika Ustaz jin furucin Mahmah sai ya share kawai. Yana zaune yaga sun fito tare da Ustaz kafin ta yi magana Ustaz ya miƙe fuskarsa kamar an yi masa wahayi da ranar mutuwarsa ko an ce masa Hajiya ta rasu ba walwala jijiyoyin kansa duk sun fito ya ajjiye Little ya kalli Sadauki dake bisa hanya. Hannun Ridayya ya damƙa tamkar zai ɓalla shi biyu ya yi ciki da ita suna shiga ya ɗauki akwati ya fara zuba kayanta ciki sai kuma ya fasa ya cire mayafin kanta ya jawota gabansa ya saka mata hijabi ya sake damƙo hannunta ya sunkuya ya ɗauki Little.

"Lafiya Ustaz?"

Wayar hannun Ridayya ya amsa ya bawa Tajj ya ce "Tajuddeen Allah ya yi maka albarka mun gode"

Ya juya ya kalli Mahmah ya ce "Mahmah tarbiyar ƴa'mace akwai wahala musamman lokacin ƙuruciya da matakin girma bai cancanci ana barinta fita ba, ban yi zaton haka ba"

"Ayya Ustaz ai naga Sadauki ne shi É—in kuma É—a ne a waje na shi ya sa"

"Muharraminta ne? Ba haka na raini yarinyarta ba, ki yi haƙuri Mahmah amma ban ji daɗi ba Ustaza bata taɓa fita da wani ba sai lokacin da aka yi mata aure, ina son ruɗin samarin da yaran zamani na yanzu kar su lalata mini ita. Dole za ki ji ba daɗi amma gaskiya ce bana barinta, a kiyaye hakan ko dan Nadra maza basu da tabbas haka ɗiya mace bata da tabbas akan soyayyar zamani, ni na yarda da yarinyata. Babu komai na yafe miki Allah ya kankare zunubanki"

Tajj ya girgiza kai abin dariya abin takaici.

"Ni ba zan taɓa lalata Shanshan ba, ka bani dama a matsayinka na uba mu fita tare da ita zan dawo maka da yarinyarka cikin salama kawai Restaurant za mu, mu yi abu very important.....,"

Wani irin mari Ustaz ya saukewa Sadauki a fuska yana nuna shi da yatsa zuciya ta ɗauki Sadauki ya dunƙule hannu zai naushi Ustaz Ridayya ta yi saurin dakawa Sadauki tsawa

"Mene haka? Dukansa za ka yi?" Ya sauke hannun ƙasa idanunsa jajur jikinsa na rawa ƙwayar idanun Ridayya yake kallo kuma ya fahimci komai ba.

"Shanshan ya zan yi? What do you want me to do? Kin mini alƙawari Shanshan" Juyawa ta yi zata shige ɗaki Ustaz ya riƙe ta ya ce

"Mu je"

Da wani irin expression Ridayya ke kallon Ustaz hawaye ya cika idanunta ta ce "Ba zan bika ba, ba zan taɓa binka ba" sai kuma ta fashe da kuka sosai. Ustaz kallonta yake yana ɓoye tashin hankalinsa.
"Ustaza gidana zan kai ki mu zauna tare"

"Bana son zama da kai bana son ganinka Abbiey baka damu dani ba, baka damu da halin da nake ciki ba, kalle ka ka yi kyau ka ƙara fari ka yi ƙiba kana zaune cikin kwanciyar hankali ka kwanta ka yi bacci, babu mai hattararka babu mai saka abu ya ƙona ka babu mai hanaka abinci babu mai zagin halittarka babu mai ce maka maye, baka taɓa nema na ba ko sau ɗaya babu inda ban shiga ba akan nemanka Abbiey ban ganka ba, bana da kowa bana da dangi babu mai kulawa da maraicina babu wanda zai faɗawa damuwata. Sai yanzu sama taka ka zo ka ce na bika? Ka barni ka rabu dani na ƙare rayuwarta a rashin gata da ƴanci kamar yadda na fara ka bari na mutu ka zo ka ɗauki gawata"

Ba zai ce ƙiyayya ya hangu a idanun Ridayya ba amma ya hangi rashin yarda damuwa tsoro ransa abu, haushi, takaici uwa uba kewa. Fargaba ta kama Ustaz ya rasa me zai ce. Ridayya na kuka ta ce

"Ka kai ni gidanka? Abbiey kenan aure ka yi ban sani ba? Shikenan ka je ka zauna da matarka bana son ƙara ganinka wallahi wallahi Allah ba zan bika ba"

Tajj ya ce "Ridayya You misunderstanding babu..."

"No Tajj" Ustaz ya faɗa a hankali yana miƙa mata Little ta amsa ya juya ya fita daga gidan bakiɗaya. Ikon Allah ne kawai ya kai shi masaukinsa wani irin kuka Ridayya take wanda ita kanta bata san dalili ba. Mamakin wawta da rashin hankalin Ridayya ya gigita Tajj taya tunaninta ya bata Ustaz bai neme ta ba? Har ta kafa hujja a kan haka, ko Ustaz zai yi fushi dole ya faɗawa Ridayya halin da ya shiga. Ganin abinda ke faruwa ya saka Sadauki fita hankali tashe ya nufi gida.

Sama da kwana uku duka wayoyin Ustaz a rufe suke kuma Tajj bai san inda ya sauka ba domin Ustaz mutum ne mai sirri da son rayuwar sirri da keɓewa waje guda.

NAHUTU/BATSARI
Kallon yaron yake cike da damuwa da takaici ganin babu wanda yake ɗaukan shi saboda tsananin muni da ƙazanta, ya ƙara yin wani irin baƙi idanunsa daƙwa-daƙwa ga wani rafkeken hanci gashi gashi ko ɗaya babu a kansa kamar an yi masa ƙwal kwabo tamkar ɗan'ruwa. Ga masifar kashi a wando kuma babu mai ɗaukar shi shi fa duk inda Ridayya take dole ta zo ta amshi ɗan'ta ta bashi nata yana da tabbacin Little shi ne yaron da suka haifa da Khairiyya Harazimi kuma Ridayya ta haife shi, saboda babu yadda za a yi baƙa mummuna kamar Ridayya ta haifi yaro kamar Balarabe.

Ya sauke ajjiyar zuciya saboda masifar yunwar dake cinsa Iya ta ce

"Ka yi hamma ta yi dubu har wannan kar ka cinye ni idan iya ɗan'ka za ka ci da sauƙi, ai muddin ba zaka shiga gona ka taya babanka aikin gona ba ko kayo ita ce kana cikin garari wallahi tallahi yunwa yanzu ka fara zama da ita. Abin tausayi ka saba da cin lemo zubu da biredi da jar miya"

"GiÉ—aÉ—o magana nake"

"Haba Iya sau nawa na ce miki Zameer sunana ko Meer? Yunwa nake ji sosai"

"Sai dai kaci kanka ƙandas wallahi dan ko ƙwayar gero babu balle mu yi gero da wake" Ta faɗa tana ƙarasa watsar garin hannunta zuwa baki. Wani irin yanayi ya ji saboda tunanin Ridayya, ko ta ci ko bata ci ba haka zata ɗauki abinci ta bashi ya ci ya sha ruwa, amma gashi uwar data haife shi ta gaza bashi abinci, Ridayya ta yi masa wanki guga ta dafa masa ruwan wanka haka kuma zata faskara ice a fili ya ce "Da sake"

"Wanne saken? Wai ba zaka nemo yarinyar nan ba? Nifa hankalina yana kan zuwa makka ɗin nan na shiga sararin subuhana na sauka ƙasa mai tsarki, gashi ka ajjiye takardu"

"Iya dole duk inda Mai sona take zata dawo domin bata da wani zaɓi daya shige rayuwa dani, bata da kowa babu kuma wanda zai ce yana son ta domin ta tashi daga aiki ni na fara kuma ni zan ƙarar bata da wata marmora ai na faɗa miki tun kafin na aureta ta bani a kanta, tana masifar so na ba zata iya rayuwa babu ni ba dukda abinda na yi mata, balle yanzu da bata da wani gata duk iyayenta sun mutu har mariƙin nata ko tana da gatan ma ai basa son ta, kinga dole mu mayar da aurenmu a lokacin ma idan ta zo sai na ja ajina"

"Sakinta ka yi ne GiÉ—aÉ—o?"

"A'a ba wani saki guduwa ta yi na san Khairiyya ba zata dawo gare ni ba zan lallaɓa na je wajan Hanne kafin Ridayya ta dawo, kuma zan ɗauki takardun kadarorin nata a satin nan na shiga Kano na fara siyar da fili ko guda uku ne"

Ya miƙe da ƙyar ya fita yana jin Harazimi na kuka. Iyanti ta ce "A yi dai mu gani idan tusa zata hura wuta"

Iya ya leƙo ta ce "Zata hura mana sai dai ba daga Babban ɗuwawu ta fito ba"

Zameer na fita gona ya nufa Moo ya kira shi ya É—aga ya ce "Haba Zameer tafiya shiru shiru har yanzu daga Germany É—in?" Zameer ya fara hura iska ta cikin wayar ya ce "Daddy É—ina abubuwa sun masa yawa yanzu ma muna airport daga Germany za mu shige England a duba lafiyarsa nan da sati za mu dawo"

Moo ta cikin wayar ya ce "Ayya Allah ya bawa Daddy lafiya Gaskiya ne ajeebo kana saurarawa"

Kafin Zameer ya yi magana Moo ya ji ta cikin wayar an fasa ihu ana faÉ—in "GiÉ—aÉ—o wai ka zo maciji ya sari Baffa"

Ganin an haura sati ya saka Hajiya zuwa Rano ta siyar da gona ta saka aka haÉ—a kayan lefe ta ware kuÉ—in sadaki da komai da komai.
Chapter 65 · 0% Book details