Sashe 11
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Duk lalacewa GIDAN AURENA NE" Zainaba ji ta yi kamar ta yi wa Ridayya mugun duka, sai dai tausayinta ya danne haushin da take ƙunsa mata ta ce "Kira wannan kamilin ko shi ne ya kai ki asibiti" Ridayya ta yi shiru yanzu ta kira Abbiey ta ce masa me? Ustaz ina son ganinka?.
"Kira shi mana Ridayya ba lokaci idan ba haka ba kina kallo za ki ruɓe" Ridayya bata da zaɓin daya shige kiran Abbiey ɗin nata, idan kowa zai guje ta babu shi. Abin mamaki wayar baya tafiya tunda take bata taɓa kiran layinsa ya dawo mata ba sai yanzu. "Kiran baya tafiya" Zainaba ta yi shiru ta ce "Gashi babu kuɗi wajena, amma ina dubu biyar ɗin dana ba ki?" A hankali ta ce "Ya amsa?"
"Waye?" Cewar Zainaba duk da ta gane ta ce "Rayuwata" wata lailayayyiyar ashar Zainaba ta ƙunduma ta ce "Lahirar ki dai makashinki shege da munafukan idanunsa, dake ke makira ce uwar son miji shi ne kika kwashe kuɗin kika bashi? Ohhho ni Zainabu Abu ina ganin rayuwa a wannan gidan Munafukin mijin, Allah ka nuna mini sanda Ubangiji zai jarabci wannan mugun ya nuna mini ranar da zai ga amfanin matarsa"
Ridayya jin Zainaba take, ba don ta yar da ba ta ce
"Akwai wata Atamfa valisco da super was a akwatina idan za a samu masu siya, ki siyar mu je asibitin" Zainaba ta miƙe.
Neman duniya babu atamfofin nan sun yi ɓatan dabo hankalin Ridayya ya tashi domin sune kawai kadarar daya rage mata sai katifar da take kwana akai. Duk atamfa ɗaya ta kusa dubu hamsin haka Abbiey ke bata baya mata ƙaramar suttura. Waye zai ɗakko har ɗakinta. Zainaba ta ce
"Uhm, lokaci"
Fita ta yi babu jimawa ta dawo da kuɗi a wajanta ta dafawa Ridayya ruwa ko zani baya zama jikinta haka ta rufe wajan ɗinkin dauɗa na taso mata ta yafa ruwan. Ruwan shayi mai kauri Zainaba ta bata ta kasa sha ganinta take kamar kayan cikinta zai fita, ta dinga kiran Zameer a waya shiru baya ɗauka Maman Hajjo ta kwace wayar ta ce "Uwar me zai mana banda ƙaryar da zai shirya miki, napep na waje mu je" da ƙyar ta shiga napep suka rufe gidan tare da nufar asibiti,suka samu Nas Hajjara cikin sauri aka yi wa Ridayya komai a account ɗin Nas Hajjara aka cire kuɗi, a nan kuma Ridayya ta kwana washegari da dare aka sallame su da zummar nas Hajjara zata dinga zuwa duba ta, har sannan Zameer bai kira waya ba.
Gama shan shayinta kenan bayan sun yi sallama da Zainaba Zameer ya shigo a gigice yana zuwa ya saka hannu ya É—auke Ridayya da mari za ta yi magana ya sake É—auketa da mafi ya ce "Ni kika mayar mahaukaci a unguwa? Kika rufe gida kika ta fi yawon duniya abinki? Har ki kwana ki yini bin maza kika fara?"
Ta kasa magana balle kuka bakinta ya kumbura tare da ƙara tsine ya sauya mata kama abinka da baƙar mace mai rangwamen kyan halitta muninta ya fiddo fili.
Ganin yar da take jan numfashi jikinta ya fara rawa kamar mai jijjiga ya saka Zameer yin ƙasa da murya ya ce.
"My love, ban yi da niyya ba, na gigice na zama mahaukaci a wajan nemanki da gudun kar na rasa ki, tsananin farin ciki ya saka na mare ki ba tare dana tuna ba ki da lafiya" Rana ta farko da ya ce "My love, masoyiyata" sai ta nemi duka zafin marin ta rasa ta kasa cewa komai.
Ya tausasa murya ya ce
"Haba mana, ki rama idan ba ki haƙura ba" Ridayya ta ce "So kake Allah da mala'ikunsa su yi fushi dani?" Ya kashe mata ido ya ce "Well is allowed"
"Baka tambayi ina na je ba, baka kuma ka neme ni a waya ba ai kasan tana wajena" Ya shafa kai ya yi mitsi mitsi da ido kafin ya ce "Ohh ina kika je?" Ta ce "Asibiti, daka gamar biyan buƙatar rai ka fita ka bar ni yashe a sume" Kamar bai sani ba ya zare ido ya ce "Suma kikai? Ayya"
Kafin ta yi magana sun ji an ce "Sweetheart" da sauri Ridayya ta ɗaga kanta taga Khairy tsaye daga ita sai three qauter na Zameer da kuma half vest iya ƙirji.
"Me kika ce Khairiyya?"
"Sweetheart na ce"
"Yayan naki ne sweetheart? Wandonsa ne a jikinki fa? Kalli rigar da kika saka ai da haka kika fito zai fi"
Khairy ta fara yunƙurin cire vest ɗin tana faɗin "Ok bari na cire idan hakan zai fi" Zameer dai na zaune yan ta son ya juya ya kalli Khairy kaifin idanun matar tasa ya hana "Fitar mini daga ɗaki" Khairy ta ce
"Su ɗaki manya, kar fa ki manta gidan miji ne wannan ba gidan uba ba, a yanzu zai iya tafa miki rasit ki yi gaba ni kuma zama daram mai naƙuda ta samu katifa don haka ki saurara mini kar ki nemi ɗaga mini hankali"
Ridayya ta kalli Zameer ta ce "Kana jin mai ƙanwarka ke faɗa mini?" Ya juya ya kalli Khairy daidai lokacin data kammala cire vest ɗin "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Wanne irin tashin hankali ne "Na shiga uku Khairiyya kina da hankali? Kalli ƙirjinki a bayyane kalli yar da yayanki ke binsu da ido"
Kasa magana ya yi ya miƙe tare da ficewa daga cikin ɗakin, wani irin kishi ya turnuƙe Ridayya ta fashe da kuka, sai da ta yi mai isarta ta haƙura har lokacin bacci ya yi bai shigo ba, ga sauro kamar ya cinye Mutum.
Ganin ba a kawo nepa ba ya saka ta kunna hasken wayarta domin rage sauro. Cikin bacci kamar kuma ido biyu taga an zuro hannu tare da ɗauke wayar kafin ta motsa an yi waje da gudu ta laluba bata ji Zameer ba ta saki ihu tana faɗin "Wayyo jama'a ɓarawo.....
*Ku yi haƙuri da jina shiru bana jin daɗi ne, wannan ma da ƙyar na yi ya ɗan yi short da yawa.A ci-gaba da bibiyar labarin RIDAYYA na MUNAFUKIN MIJI😢😠Bright pens na godiya da karɓar su hannu bibbiyu da kukai*
08164069385
*✿ MUNAFUKIN MIJI ✿*
Nimcyluv@Arewabooks
Page 7
BRIGHT PENS🤙🼠free batch
A kiɗime ta ƙara cewa "ɓarawo, Innalillahi wa'inna ilahir raji'un ɓarawo a ɗakina, Meer rayuwata ɓarawo ya shigo mana" Babu wanda ya amsa Ridayya balle kawo mata ɗauki ta tashi zaune tare jingina da jikin bango, abu goma da ashirin ya haɗe mata. Ƴar raguwar wayar da ta yi mata saura a kadara itama an rabata da ita wai meke shirin faruwa ne. Daidai ɗaga labulen ɗakinta sa'arda nepa suka kawo wuta, hasken wutar ya haska fuskar Zameer da yake ɗan mustsike Idanu alamar bacci cikin kulawa ya ce
"Sama-sama ina bacci na ji ihunki lafiya?" Ya tambaya yana daga tsaye, domin baya jin zai iya zama a É—akin.
Ridayya ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Kana gidan ashe?" Ya ware Idanu kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru kawai.
"Ina bacci ne ɓarawo ya shigo, ya ɗauke wayata" Zameer fuskarsa shimfiɗe da damuwar daya ƙirƙira a lokacin ya ce "Waya kawai aka ɗauka?" ta jinjina kai alamar "E" Ya ja tsaki a fili ya ce "Shi ne abin ihu a kan ɗaukar waya? Ke dai Ridayya ba ki da tawakkali Kwata-kwata, kece raki idan babu lafiya, kece surutun yunwa kamar za ki yanki naman jikina ki gasa kici, duk abinda na yi miki baya birgeka bana miki gwaninta daman kece kika zubar mini da ƙima da girmana a idanun ƴan'uwanki, ni kam na auri matar ƙaddara!"
"Matar ƙaddara!?"
Ta maimaita a fili idanunta tsaye cur cikin na Zameer domin a ko wanne yanayin a duk halin da zata tsinci kanta bata shayin sanya idanunta a cikin nasa. Muryarta na rawa laɓɓanta na karkarwa saboda ciwon ciki ta ce
"Ni kake kira da matar ƙaddara Rayuwata? Ni Ridayyanka?"
Ya ɗaga kafaɗusa duka biyun yana ƙanƙantar da idanu murya ƙasa ya ce
"Kar ki mini gurguwar fahimta, kar ki mini, ai ba kece ƙaddarar ba, ƴan'uwanki da auren sune, tunda na aureki ban hutawa raina ba, Allah ya ƙara mini haƙuri, shi ya sa magabata suke cewa Allah ya saɓa halayya"
Ikon Allah kawai Ridayya ke kallo ko dai mijin nata wani abu ya sha yau? Bai taɓa mata furuci makamancin wannan ba a hankali ta ce "Don na bar ƴan'uwana baya nufin bana son su ai" Ya riƙe ƙugu ya ce "Ba shakka, idan tururuwa ta so lalacewa, daman fiffike take yi ta tashi ai"
Idanunta suka cika da hawaye fal idan da sabo ta saba da kuka tun a daren amarcinta ta ce
"Meke damunka na rayuwata? Me na yi da zafi har haka? Don Allah ka yi haƙuri ka yafe mini"
Ya ja tsaki yana juyawa. Kasancewar a waje ya yi shimfiɗe tunda ya kammala buƙatarsa da Khairy. Juyi ya dinga yi akan tabarma shi sam ba haka ya tsara gani a auren Ridayya ba, duk abinda yake buri bai samu ba sai masifa kala-kala da auren ya jefa shi. Ridayya ta share hawayen da yaƙi tsaya mata, tana nan jingine da jikin bango, da tana da ikon tariyo rayuwarta ta baya babu shakka da ta yi hakan domin gyara ƙazantar data aikata wacce babu mamaki warinta ke bibiyarta a yanzu.