Sashe 55
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zuhura ta ce "Ammi ai ba hatsarin ƙarya bane kawai dai Allah ya kiyaye muna da raguwar numfashi da motar da akai hatsarin da ta mu iri ɗaya ce muna baya ɗaya motar na gaba ta mu ta shiga cikin jeji ki duba yatsan Khaliperh kusan cirewa ya yi, kuma ni ina maganar gidan mijina mene nawa da nan gidan fisabilillahi"
A harzuƙe Ammi ta ce "To ba dole sai ina da kuɗi zan ji da matsalarka ba, addu'a nake Allah ya rusa farin ciki da daidaito ɗin dake tsakanin Baffa da Fatima, kuma muddin ina raye wallahi tallahi ko Ridayya na duniya ba zata taɓa zama wata a duniya ba kuma dole ne mu mallaki wannan kadarorin da aka bata gabaɗaya haihuwarsa yarinyar nan masifa ta zame mini"
Zuhura ta cika ta yi fam ta ce "wannan mayyar mijin kike tunanin zata iya rabuwa da shi? Kila ta tattara ta mallaka masa dukiyar" "da kowa na yi ɗaiɗai da rayuwarta wallahi Ridayya ba zata taɓa zama wata a duniya ba, ai daman sai dai shi Zameer ɗin duk yadda naso kashe auren Burhan ya aureta abu ya gagara ni addu'a nake ma plan ɗin Alhji ya yi daidai dukda yaƙi faɗa mini komai ta dawo ta auri Burhan ai daman shi ne ya zama dole a yadda take uban wanne namijin ne zai aure ta ko shela akai matsayin kyauta babu mai amsar ta yin"
Miƙewa Zuhura ta yi ta ja hannun yaranta a ƙalla ta yi ya ji sama da biyar gashi igiyar auren nata saura ɗaya tal da take lilo.
"Kee Zuhura" Baffa ya kira sunanta ta tsaya ta ce "Na'am Baffa ina yini?"
Bai amsa ba ya ce "Me ya kawo ki gidan nan? Asiri kike son tuna mana? Bana gaya miki bana son a san wani daga cikin ahlinmu na raye ba? Shi ne kike ta mini zurga zurga?"
"Baffa ka yi haƙuri wallahi daman Nura.......," Caraf Ammi ta ce
"Nuran ne baya gari ya ce ta zo gida kafin ya dawo"
Baffa ya juya ko Ammi bai kalla ba ya ce "To ki kiyaye zan yi magana ta Nuran idan ba zai iya haƙuri har mu kammala ba kawai ya barki a gidan nan har zuwa sanda komai zai zo daidai" Yana faɗa ya yi sashin Mami.
Ammi ta cije bakinta ta ce "Kin gani ko Zuhura ko inuwata Baffa baya son gani? Na zama mujiya to ni me na yi masa duk yadda na riƙe yarinyar nan tsakani da Allah?"
"Ammi kin fiya mita shi Baffa kin taɓa ji ya miki maganar Ridayya ne? Duk kin damu kan ki"
Miƙewa ta yi ta nufi ɗaki number Biba ta kira tana ɗagawa ta ce "Biba ko ba za ki dawo ƙasar nan ba ki turo mini kuɗina na wajanki ko miliyan biyar ne" daga cikin wayar Biba ta ce
"Maryam babu kuɗin nan fa wallahi an sace" Wata uwar ashar Ammi ta ja ta ce "Kan uba ni za ki cewa ba kuɗi last kuɗin dana tura miki a ƙalla ya yi miliyan huɗu da rabi kuɗina a wajanki ban san adadi ba shi ne ki ce mini an sace na bi sata da gudu ba wando....,"
Ƙittt! Biba ta kashe wayar nan take kuma ta saka number Ammi a Black list.
Satin Ridayya biyu cikin asibitin ta warke sosai aka sallame ta Tajj ya dawo da ita gidansu saboda ita yaƙi komawa wajan aiki dukda yana son zuwa wajan Ustaz can leges ɗin rabonsa da shi tunda aka ɗauki jininsa ko wayarsa ya kira a kashe yake jinta. Kulawa sosai yake bawa Ridayya Mahmah da kanta ta saka aka kawowa Ridayya sabbin abayas masu kyau da tsari wando da riga su english wears mayuka wanda aka rubuta mata a asibitin Bela bana saka fari bane amma nan da nan fatarta ta yi fresh daga tattarewar da ta yi ƙashin wuyan ya fara cikowa ta fara miƙewa sosai a kan ƙafafuwanta daga ɗan ranƙwafawar da ta yi hips ɗinta ya fara buɗewa zuwa asalin yadda yake. Tajj yana ƙoƙarin janta a jiki da son jin muryarta amma ko daga bedroom bata fitowa gaisuwa ce kawai ke haɗata da shi kullum cikin tunani take ko ta shagala da kallon Little Bilal. Gashi abinci mai kyau da gina jiki ake bata bisa tsarin likitoci ba a bata mai ya ji saboda bata son ya ji Kwata-kwata.
Wajan watanta guda kenan sati biyu da tafiyar Tajj tana zaune a gaban madubi Little Bilal ya maƙale bayanta sai rigima yake mata ya hanata sakat kamar mai zazzaɓi dai kokawa take da gashinta da take son ɗaurewa take gashi wata ƴar ƙaramar riga ce a jikinta sai wani wando iya qwiwa tunda tasan daga ita sai Mahma ta saki gashin ta kalli kanta a madubi gabaɗaya babu tabon ƙonar fuskarta ta yi fresh asalin baƙinta mai kama da chocolate ya bayyana ashe duk wahala ce ta dafar da ita da rashin kula gashi yanzu data samu hutu da abinci mai kyau ga gado da a.c ga mayuka bisa yardar likita sai baƙin wahalar ya kai fatar sai glowing take baƙin gwanin sha'awa ga gargasar a saman fatar da sukai kwance luff gashin girarta kamar su haɗa dana juna, laɓɓanta yirrr jajur da su idanunta farare tas kamar tana ɗiga musu wani abu. Idan ka kalli fatar ta a time ɗin ba za ka yi sha'awar farar fata ba domin irin skin ɗinsu ke wahala a wannan zamanin. Sumarta har gaban goshi ta langwaɓe kai cikin siririyar muryarta ta ce
"Abbiey me kake so ne?" Ta faɗa tana ɗaukar shi ta ɗora saman mirror sai ya fashe da kuka ta taɓa jikinsa ta ji zafi nan da nan idanunta ya cika da hawaye
"Ka daina kuka please" Idan duk bata san me za ta yi wa yaron ba daman Tajj ke rarrashinsa idan yana rigima sai kawai ta fashe da kuka tana kifa kanta. Mamaki ya hana Tajj dake tsaye bakin ƙofa magana mene na kuka ita sam shagwaɓa baya yi mata wahala ne? Kodayake ai yarinya ce babu mai cewa ta haifi Little Bilal jikinta ya dawo ɗanye shi kansa ya san yana kashe kuɗi a kan ta. Ya ƙarasa kusa da madubin ya ce
"Like mother like son, mrs crying"
Ta kasa É—ago kan ta saboda kunyar kayan jikinta Tajj ya É—auki Little ya rungume shi ya zauna bakin gado ya ce
"Ka saka Mimi kuka ko? Mimi a taimaka a yi haƙuri kar a saka Daddyn Bilal kuka" Kamar ya ce ta ƙara sautin kukan nata ta sake fashewa da kuka Tajj ya miƙe ya nufi inda take ya zauna saman mirror ya ce "Mimi wannan kukan fa" ta yi shiru ya ce
"ÆŠago kan ki muga" Kasancewar ta É—auke shi matsayin yayan data rasa a baya ya saka ta É—ago kanta ta kalle shi fuskarta jage jage da hawaye ya ce
"Tsakani da Allah Mimi wannan kukan na shagwaɓa ne wannan ai ni za ki illata" Ta marairaice fuska a hankali cikin sanyin murya ta ce
"Abbiey ke ta kuka shine na yi nima" Tajj ya yi saurin ɗauke abinda ke zuciyarsa a taushashe ya ce "Saboda ke ƙaramar yarinya ce ko? Waye zai rarrashi wani?" Ta yi shiru
Ya sake rage murya ya ce "Ki daina ban so kukan nan, akwai sanda za ki yi na shagwaɓar ba yanzu ba" Ya ɗago wani magani ya bata ya ce
"Kullum da daddare kina shafawa a lips ɗinki na ƙasa, wannan kuma Dynewell safe da rana za kina sha saboda na lura baki son cin abinci"
"Na gode Yaya" Ya ta zaune ya yi yi wa Little Bilal pictures wani mai masifar kyau ya É—ora a status tare da emojin na love. Tun kafin ya fita yaga Ustaz ya yi viewing can yaga ya yi masa reply da.
"ÆŠan waye?"
"ÆŠa na ne mana, bani kaga na saka shi a status ba?"
A taƙaice Ustaz ya ce
"Bana son wasa É—an waye wannan? Ka cire shi a status"
Tajj ya ce "Me ya sa kake son jin É—an waye?"
"I just seen my photocopy, we look alike" Ustaz ya bashi amsa Tajj a fili ya ce "Ikon Allah"
Kiran wayar Ustaz ya shigo wayar Tajj ya ɗauka ya ce "Wai ya naga duk ka damu ne tunda ka buɗe WhatsApp baka taɓa mini magana ba, sai yanzu? Abinda baka sani ba takwaranka ne wallahi sunansa Bilal"
Tsit Ustaz ya yi can ya ce "His mother please? Kirani vedio call ka bani yaron mu gaisa" Tajj ya ce "Ba zan nuna maka É—an mutane ba kuma.....,"
"Yaya Yaya Yaya" Ya ji ana kwaɗa masa kira ya ajjiye wayar saman mirror ɗin ya fita tsaye ya ganshi hannunsa riƙe da jita ya ce "Wannan kiran fa?"
"To ka je ka wani shige ɗaki tun ɗazo na zo ni bana son jiran gaskiya ka sani ni sai naga me kake a ɗakin" kafin Tajj ya yi magana Sadauki ya shige cikin bedroom ɗin lokacin Ridayya na tsaye tana ta kallon wayar Tajj da ake kira a jiki an rubuta friend haka kurum ta ji tana son ɗaga kiran hannunta na rawa ta ɗaga tana kai kunnenta tare da yin shiru tana jiran a yi magana. A hankali Sadauki da yake tsaye riƙe da ƙugu ya ce "You?"
"Sadauki zo ka fita" cewar Tajj ya faɗa idanunsa sun yi jajur Sadauki ya juya ya kalli Tajj fuskarsa a haɗe shima baya son Ridayya ta san yana ɗakin don sai ya rama yadda ta yi masa ya damƙi hannun Tajj kamar za su fita tare yana zuwa baƙin ƙofa ta tura Tajj waje ya rufe ƙofar tare da sanya mata key ya cilla makullin cikin Aljihu ya nufi inda take tsaye tana jin sautin bugun zuciyar Ustaz ta cikin wayar.....
Share and share and share as so much as you can! Saboda masu tambaya
[email protected]
08164069385
*MUNAFIKIN MIJI 27*
Mikiya Writers Ass
Bright pens free batch
Nimcyluv