Sashe 24
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya yi gaba cikin kamilalliyar nutsuwarsa yana bada faɗi har ya je bakin ƙofa ya tsaya ya ce "Ita ma ta dinga ce mini Yaya Bilal, idan ba zata iya ba ta kalle ni ta shige" Hajiya ta rafka salati ta ce "Uwar taka ce zata dinga ce maka Yaya?" Har ya buɗe ƙofa ya dawo da baya yana riƙe kansa dake juya masa sosai da sosai ya ce "Ta faɗi sanda ta yi cikina ta haifa, nikam bana son haka raini ne da gaske raini ne Granny"
Ya fice yana banko ƙofar, Ammi ta yi ƙwafa a ranta ta ce "Zan ci ubanka ne, shegen yaro me uban son girma ma rainin kowa da taurin kan tsiya" A fili ta ce "Ai kar ki damu Hajiya haka halinsa yake sai mu dinga cewa Yaya Bilal ɗin muna bashi girma kamar yadda yake so" Sallama sukai Hajiya ta fita zuwa harabar gidan, ta nemi Bilal ta rasa domin ya ji haushin yadda ta ce Ammi babarsa ce.
Wani irin shu'umin murmushi Ammi ta yi tana girgiza ƙafa wacce ta harɗe su ɗaya kan ɗaya kafin ta miƙe tsaye ta ce "Ni za a bawa rainon ƴar kishiya? Ni Maryam ko a gidanmu ba kishiya, na zo nan na yi zaman bora sannan a haɗani da rainon ƴar kishiya?" Dariya ta kece da ita sai da ta yi mai isarta kafin ta juya ta ƙura wa fuskar Ridayya kallo kana ta ce
"Barka da zuwa hannun kishiyar uwa, barka da zuwa uƙubar kishiyar uwa, zan fanshe duka haushin da ubanki ya gana mini da cikinki, zan fanshe fifikon soyayyar da ubanki ya nuna a kan majaifyarki, na rantse da Allah duk abinda na haɗiya na ɓacin rai da kishi a yanzu zan amayo da shi a kan ki, zan tabbatar muguwar azabar da zan miki sai ta ƙarasa rayuwarki, kamar yadda Mansur yake mugun sonki tun kina ciki, gashi yanzu a ranar da kika zo duniya tsana mai tsanani ta maye gurbin soyayyar, ai ɗan halak shi ya san idan an yi masa ya rama, tuwon girma, miyarsa nama"
Ammi ta girgiza kai tare da kaÉ—a hannu ta ce
"Ɗan kishiya ba zai taɓa zama ɗa ba, kamar yadda kishiya ba zata taɓa zama ƴar'uwa ba"
Hannu ta saka ta ɗauki Ridayya sai kuma ta saka zaftara-zaftaran faratanta ta gantsarawa Ridayya mintsini a cinya har sai da fatar wajan ta sutale, tunda a ka haifi yarinyar ba wanda zai ce ya ji kukanta banda wanda likitoci suka saka ta yi, sai kawai ta dinga zabura ita kaɗai. Tsananin azaba da yadda mintsinin ya ratsa jaririyar ƴar kwana biyar zuwa shida a duniya wacce bata san meke faruwa ba ya saka Ridayya sakin wata ƙatuwar shaƙuwa ita kaɗai gumi zai yanko mata yake, ta dinga zabura kamar wacce ake kaɗa mata gangi, dukda irin azabar da Ammi ta yi mata bai daka Ridayya yin kuka ba. Ammi ta duba taga fatar wajan ta sutale jini na zuba ta ƙarasa kitchen ta kwashi gishiri ta manna a wajan, ta kwashi ya ji shi ma ta manna, yarinyar ta dinga sakin ajjiyar zuciya fuskarta ta yi sharkaf da gumi. Ganin har yanzu ba ta yi kuma ba ya saka Ammi cewa "Tsinanniya gayyar tsiya, yadda ban taɓa ƙaunar uwarki ba wallahi ba zan ƙaunace ki ba" fuuu ta yi part ɗinta a tsakiyar parlo ta shimfiɗe Ridayya bayan ta cire mata kayan da Bilal ya saka mata ta ƙure a.cn dake cikin parlon kana ta yi cikin bedroom ɗinta. Wata number ta kira ana ɗagawa ta ce "Ki tura masa raguwar kuɗin, ki zo ina buƙatar ganinki" Tana faɗin haka ta kashe wayar.
Muhammad-Bilal na fita ya nufi ɓangaren iyayensa ya samu Umma zaune tana kallo, yanayin yadda ya shigo ya sa bata kula shi ba, duk da mutum ne shi mai zurfin ciki bai fiya shiga sabgar da babu ruwansa ba, sai a yi abu sau naya bai tanka ba ta rasa dalilin daya sanya ya damu da lamarin Ridayya? Ta girgiza kai tare da ci-gaba da kallonta. Wanka ya yi ya shirya cikin wata blue black ɗin jallabiyya mai kyau da taushi sai zabga ƙamshi yake komai na ɗakinsa a tsaftace yake, drawer ɗin littafansa daban tari guda duk na addini ne, Alkur'ani, hadisi, tafsir, azkar, ƙawa'idi, Dala'ilu, umdatul ahkam, zajidul zauj, hakƙun mubin littafai na addini kala-kala. Yana tsaye hannunsa ɗaya goye a bayansa takardun kammala karatunsa yake gani, bai taɓa sha'awar neman aiki ba sai yanzu. Kasancewar ɓangaren Accounting ya karanta fannin business, finance, and accounting ya sanya ya fita da sakamako mai kyau, baya wasa da duk abinda zuciyarsa ke so da muradi yana da naci, da ƙwallafa rai ga taurin kai ga duk abinda zuciyarsa ta kwaɗaitu a kai, ya dinga kallon takardun yana tunanin ta ina zai samu aiki? Ko bai samu ba, ta wacce hanya sai dinga neman kuɗi? Wayarsa ya ɗauka da takardun ya fita bakinsa ɗauke da addu'a ya haɗe rai sosai a dole baya son raini gani yake yawan magana da sakin fuska shike kawo raini.
Makarantar islamiyyar da yake koyarwa ya fara zuwa, É—alibai na ganinsa suka shiga hankalinsu ya nufi aji shida ajin Æ´an sauka gabaÉ—aya Æ´an'mata da samari ne a ciki waje ya nema ya zauna suka gaishe shi, É—aya bayan É—aya suke bashi haddar Alkur'ani har aka zo kan Muwahif, duk sanda zata bawa Bilal karatu sai ta samu matsala gabanta ya dinga faÉ—uwa saboda tsananin kwarjininsa, haiba da mazantaka ta cikakken namiji.
A hankali ya tsaya da danna wayarsa ya yi mata kallo ɗaya jin haukan data rafka masa kowa ya yi nisa amma har yanzu a izu biyar take bata jima da zuwa Ali'imran ba. Kallon da ya yi mata da nufin ta gyara sai ya ga ta ƙura wa fuskarsa Idanu da kuma tsayayyen gemunsa mai kyau da sheƙi. "Keee" Ya kira sunanta amma ta shagala wata ta zungureta ta ce "Wahif Ustaz yana magana, Wahif" Firgigit ta dawo hayyacinta tun kafin ya yi magana ta fashe da kuka tana ƙoƙarin cewa "Ustaz ka taimaka mini wallahi ina...."
"Out" Ya faɗa a tsawa ce da gudu ta miƙe tare da yin waje tana rushewa da kuka, bayan gama karatun ya fita ya nemi aiki ko na hannu ne bai samu ba da ƙyar ya samu aikin jiran wani babban shago na wani Alhaji. Sai magriba ya dawo gidan.
Dr ne tsaye yana ƙare wa Dada kallo kafin ya ce "Mu je office" bayansa ta bi ita da Yaya A'isha ya ja kujera ya zauna idanunsa a kan Dada kana ya sauke ajjiyar zuciya yana zare glasses ɗin idanunsa a hankali ya ce
"Mun sauya mata É—aki zuwa ICU" Yaya A'isha ta zare ido ta ce "ICU Dr? But why?"
"Eclampsia, dalilin jijjigar da ta yi kafin a yi mata Cs, binciken da mukai ya tabbatar tana da hawan jini kuma ta ɗauki lokaci tana naƙuda wacce ya haifar mata da zazzafan zazzaɓi da ciwon kai, sanda ta fara jijjigar mun su yi mata Loading dose mgso4 amma babu hali hakan yasa mukai aiki aka cire babyn" Likitan ya yi shiru can ya ce
"Ta farfasa bakinta sosai sanda ta yi jijjigar, babbar damuwar ta yi saurin farkawa daga coma da wuri kuma hakan hatsari ana iya samun rasa rayuwa ko hankali gabaÉ—aya"
Yaya A'isha ta fashe da kuka sosai ta ce "Amma dukda wannan baƙar azabar da Fatima Batool ta sha wajan haihu aka iya ɗauke jaririyar a bawa kishiya? Ko zafin haihuwar da wahalarta bai gama sakinta ba, ga saki ga ƙwacen dole da raba soyayya ina Alhaji Mansur zai kai wannan hakin don Allah?"
Likitan ya ce "Pardon, bangane ba an karɓi baby ba, kuna nufin babyn baya cikin asibiti under special care na likitoci? Ba kusan cewa Eclampsia na iya taɓa jariri ba?" Hajiya ta yi jigum saboda wannan tashin hankalin ta kuri Anuty Kaltum ta ce "Jijjiga na taɓa jariri ne Dr?" Ya jinjina kai ya ce
"Sosai ma, suna samun Cerebral palsy irin yaran nan Abnormal dolaye irin galahanga ɗin nan, babyn ma na iya rasa ransa, ko a haife shi yaƙi kuka kamar yadda itama babyn taƙi yi, idan baby ya samu Cerebral palsy akwai matsala, wasu suna kurmancewa ne, wasu basa gani sosai, ko kuma kaga gabaɗaya yaro baya gane karatu"
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Shi ne abinda Dada take faÉ—a Yaya A'isha kuka kawai take ta ce "Don Allah don girman Allah Dada a dawo da Ridayya wajanmu, yarinyar ba cikakkiyar lafiya ta cika ba" Godiya Dada ta yi wa Likitan tunda ba za su samu damar shiga wajan Mami ba sai zuwa safiya tana addu'a a ranta Ubangiji ya sa kada sanadin haihuwa Mami ta rasa tunaninta ko ta haukace.
Wajan ƙarfe goma Ammi ta ruski Baffa a ɗakinsa yana ganinta ya ɗan saki murmushi ya ce "Uwar gida ran gida, idan ba ke ba gida" Ammi ta juya idanunta ta ce "Yau kuma kirarin na uwar gida ne, ina na amarya Fatima?" Nan da nan annurin fuskar Baffa ya ɗauke domin baya ƙaunar jin sunan Fatima ko da wasa.
Ya riƙe kafaɗun Ammi idanunsa cikin nata wanda suke ƙara rikita shi ya ce "Maryama kar ki kashe ni da raina don Allah" Ta ware idanunta kafin ta ce "Rufa mini asiri na kashe mijin Fatima baban Ridayya Uncle ɗin Bilal" ai gabaɗaya Baffa ya ji ɗakin na juya masa yana jin kamar ta caka masa wuƙa a zuciya ne ya riƙe ta da ƙarfi ya ce
"Ki tausaya mini Maryam, sunan Fatima azaba ne a gare ni ban so koda wasa,na tuba; na bi Allah na biki matata Maryam" Ta yi murmushi tana kashe mata ido ta ce "An gama ranka ya daɗe, angon ƙarni" Juice ta bashi ya kalli ruwan lemon jajur da shi kamar an kaɗa jini, bisa umarnin zuciya da abubuwa dake fusgarsa ya damƙi hannunta gabaɗaya mai ɗauke da kofin ya shanye lemon. Bayan ya shanye yana tsaye ta ce "Zauna mana Baffa?" Ya kalleta sai ya ce "Na zauna Maryam?"