← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 118

Sashe 98

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Alhaji Mansur zo ka zauna" Baba ƙarami ya kira sunan Baffa yana nuna masa wajan zama domin ya lura gabaɗaya hankalinsa a tashe yake tsoro da firgici sun shige shi sosai ainun da gaske.

Junaid ya kalli Zameer yadda yake ta share hawaye tunda yake ko ada can baya bai taɓa ganin ladabi da tsantsar tsoro a fuskar Zameer ɗin ba sai yau bai kuma taɓa ganin hawaye akan fuskarsa ba, rashin yadda ya gitta a zuciyar Junaid ya ce

"Idan baka saki Ridayya ba, to akwai wani abu a ƙasa tunda da can bata taɓa yunƙurin fitowa daga gidanta ba, ta dawo gida a saboda ka saɓa mata ba, balle a yanzu da take tunanin bata da kowa tunda Ridayya ta dawo ne kafin ta san cewa muna raye. Me ka yi mata? Me kaiwa Ridayya da har ta baro inda kake ta gudu? Me ya sa baka biyo bayanta ba sai yanzu?"
Da wani kalar shock Zameer ke kallon Junaid da kuma sauraren shi, ganin yadda zai rutsa shi ya saka ƙaryar shi ƙarewa Zameer ya ce
"Yaa Junaid ai kasan ba zan yi ƙarya ba, go and ask her ta san komai she knows everything wallahi tallahi"

"Da mamaki wannan lamarin, ba a rabu da Bukar ba an haifi Babu, wacce irin ƙaddarar ke bibiyar rayuwar Ridayya" Cikin fusata Junaid ya ce "Karku yadda da shi, domin tun farko shi ɗin ba abin yadda bane ina da tabbacin Ridayya bata taɓa cutar da kai ba, balle ta aikata wannan babban lamarin"

"Ya isa Junaid please"

Zameer ya sake sauke kansa ƙasa cike da ladabi kamar zai yi sujjada muryarsa a raunace ya ce "Ita ta ce na taɓa cutar da ita? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Lallai a bar mace da kaidinta amma ni ba zan ce komai ba, idan kana ganin ta dinga yawo da aurena a kanta shi ne daidai to babu damuwa I'll let her be tunda kana ɗaurewa ƙanwar gindi"

Junaid ya kalli Zameer cike da ɓacin rai yana tuna abubuwan da suka shiga tsakaninsa da Yaa Bilal musamman a cikin asibiti a kan Zameer Ridayya ta yi wa Ustaz Allah ya isa kuma ta kira shi da sunan da ko a family shakkar kiransa ake da shi. Idan Junaid ya tuna ranar sai ya ƙara jinjinawa Ustaz na irin so da ƙaunar da ya kewa Ridayya.

Baba ƙarami ya yi murmushi irin na manya mutum mai tunani da girmama zumuncin Allah da bawa kowa haƙƙinsa ya ce "Ɗana Zameer kana ina Ridayya ta gudu garin yaya hakan ta kasance ka yi wannan sakacin?"

"Abba muna nan Garin Kano ba sakaci na yi ba cikin dare ta gudu wai ta gaji da zama dani saboda kuskuren dana tafka a rayuwa, na mata laifi ni É—in mai kaifi ne Abba amma girman laifin bai ka ga Ridayya ta gudun daga cikin gidanta na sunna ba kuma tare É—ana. Abba kai mai fahimta nasan zaka fahimce ni"

Zameer sam bai kula da Tajj daya shigo ya zauna ba, yana sanye da black suit irin ta manyan ƴan sanda sai baza ƙamshi yake idanun Tajjudeen Baita zube akan Zameer shi ma yana sauraren shi. Tajj zai magana da hannu Baffa ya yi masa alama da ya yi shiru.

"Karka wani damu ɗana ka ɗauka ni ɗin tamkar uba mahaifine a gare ka zan saurareka kamar yadda zan saurari ɗan dana haifa kuma na maka alƙawarin wallahi wallahi wallahi uku kenan idan har kai ne da gaskiya to zan dawo maka da Ridayya cikin gidanka da yaronka matsayin matarka"

Da sauri Baffa da Junaid da Tajj suka kalli Baba ƙarami da yake ta murmushi, firit Umma t fito daga laɓewar da ta yi ta ce "Kai Allahamdulillahi idan hakan ta faru zan fi kowa murna da samun nutsuwa a zuciya, Babban mutum ya rabu da kwallon mangoro ya huta da ƙuda har abada. Na daɗe ban ji tsanar da na yi wa mutum irin ta matsiyaciyar ƴar nan Ridayya ba, ba zan taɓa ganin farinta ba wallahi mummunan mai baƙar zuciya mai kama da Alade kawai"

Baffa har ƙasan zuciyarsa yake jin zafin maganganun Umma amma babu yadda ya iya matar yayarsa ce dole ya zuba mata idanu. Mami data fito hannunta ɗauke da Junior ta tsaya cak saboda furucin Hajiya Hadiza karamcin Ustaz ya shige ta faɗawa babarsa magana wallahi Anty Kaltum ta ji maganar itama niyyar tafiya ta yi amma kawai ta juya cikin ɗakin Mamai ta yi alwala tare da gabatar da sallar asar.

Baba ƙarami bai kula Umma ya dubi Zameer ya ce "Wanne laifi ka yi wa Ridayya da kake neman yafiya?"

"Abba i was wrong i was totally wrong ban san da wanne harshe zan maka bayani ba komai zan ce komai zan furta ba lallai na ƙara fari a idanun Ridayya ba"

"Tunda you are already knew dat why are wasting your time here? Me ya sa za ka zo nan ne ma?"

Da ƙarfi Baba ƙarami ya ce "Abubakar Sadeeq!"

"I am sorry Abba"

"Ina jinka Zameer"

Zameer ya sassauta murya ya ce "Abba farkon fara haɗuwata da Ridayya a makaranta ne, na sameta tana ƙoƙarin kashe kanta ta hanyar rataya a ƙarƙashin bishiya, Allah ya kawo ni wajan domin na ceci rayuwarta Abba just to save her life. Ban tambayi Ridayya komai ba amma sai ta fashe da kuka ta fara zayyana mini halin da take ciki, ta ce mini mahaifinta ya tsaneta haka mahaifiyarta kowa na gidan baya sonta ƴan unguwa da ƙawaye haka a makaranta kowa na aibata halittar da Ubangiji ya yi mata sannan ta ƙara da cewa...,"

Ya yi shiru kansa a ƙasa yana girgiza kai ya kasa cewa komai. Baba ƙarami ya ce "Go on my dear ina jinka ka faɗa mini komai tsakaninka da Allah"

Hawayen da yake ta rikewa ne ya sake gangaro masa ya ce "Abba ka yi mini uzuri abar maganar domin zata iya rusa wannan zumuncin naku magana ce da zata iya sawa zuciyar kowa ta buga daga ciki kowa har kai Abba ko kuma Abban Ridayya just let bygones be bygones Abba"

Baba ƙarami ya miƙe tsaye ya ce "Ya zama dole ka ƙarasa faɗar abinda ka yi niyya ba a mini haka ba zaka fara mini ba kuma"

"To Abba ya zaka ji idan na shaida maka cewa Ridayya ta faɗa mini saboda ɗan'uwanta Ustaz wanda ya zama kamar uba a gare ta take son kashe kanta? Ya zaka ji idan na faɗa maka cewa sanda Ridayya ta je gidana ta je da shigar cikin da Ustaz ya yi mata? Ta shaida mini tun tana yarinya yake lalata rayuwarta kuma ya yi mata barazana da faɗin muddin ta faɗawa wani sai ya yankata da wuƙa? Me ya sa ba ku taɓa tunanin ƙin auren shi da ta yi a fari ba? Me ya sa ta zaɓe ni ta barsa? Abba da farko bani na fara cewa ina son Ridayya ita ce ta buƙaci hakan ni kuma na tausaya mata a haka har na fara son ta, Abba laifina a nan shi ne na ɓoyewa Ridayya gaskiyar waye ni maimakon Zameer sunana Giɗaɗo ɗan asalin Garin Katsina can ƙauyen Nahutu yankin batsari na zo Kano Almajiranci ne, ban yi haka don na cutar da mai so na Ridayya ba, na yi ne saboda kar na rasa ta na yi ne saboda na rufa mata asirin da ɗan'uwanta yake ƙoƙarin tuna mata na yi kuma da tunanin idan kun ganni talaka zaku hanani auren Ridayya, bayan ta gano gaskiyar dana ɓoye mata shi ne ta ce dole sai na rabu da ita"

Tunda ya fara maganar tasa Baba ƙarami zufa ke yanko masa jikinsa ya ɗauki rawa dukda cewa a zaune yake amma ƙoƙarin faɗuwa yake wani abu mai kama da tashin hankali da fashewar bom ya ji a zuciyarsa da gangar jikinsa kansa ya fara juyawa maganar Ridayya ta yi aure da cikin da Ustaz ya mata ita kaɗai ke gigita masa lissafi da ƙoƙarin saka zuciyarsa bugawa.

Ya kama hannun Zameer ya damƙe idanunsa na fitar da ƙwalla ya ce "Yaro ka ji tsoron Allah ka tuna zaka mutu da gaske ne abinda kake furtawa akan Bilalu ɗana? Babban mutum fa? Ka ji tsoron Allah karka goga masa baƙin fentin da ba zai iya shafewa daga jikinsa ba, ko ka yi ne don matarka ta dawo gare ka?"

"Haba Abba haba Abba ina dalilin wannan furucin naka? Mene ribata idan na wulaƙanta mutum kamar Muhammad Bilal? Gaskiya ɗaya ce kuma ita na faɗa"

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Hasbunallahu wani'imal wakil Muhammad Bilal? Babban mutum Allah ya...."

"A'a yaya don Allah, don't say that karka ce haka"

"Me kake so na ce Alhaji Mansur? Ɗana na cikina ya wulaƙanta ƴarka tun tana ƙanƙanuwa? Ta ina zumuncin Allah zai bar ni? Wannan shi ne dalilin daya saka ya ƙiyin aure? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un" nan da nan Baba ƙarami ya gigice ya riƙe ƙirjinsa hankalin Junaid dana Tajj Baita ya yi mummunan tashi wacce lukutar masifa ce wannan? Anya Muhammad Bilal zai aikata haka? Mene gaskiyar lamari? Only God knows! Likita aka fara ƙoƙarin kira Baba ƙarami yana cewa a bar shi haka nan

"Idan har maganar nan gaskiya ce wacce Zameer ya faÉ—a wallahi Allah sai na É—auki hukunci sai na É—aukarwa Ridayya fansa wallahi sai na É—aure Muhammad Bilal da hannuna"

Da sauri Zameer ya ce "Ai gaskiya ce ma Abba kaɗan kenan daga abubuwan da suka dinga faruwa" wani irin hawayen baƙin ciki dana tsanar Ustaz Baba ƙarami ya dinga zubarwa deep down na zuciyarsa yana ƙoƙarin ƙaryata lamarin. "Kai out of this house before i count 1"

Junaid ya cewa Zameer miƙewa ya yi with confidence ya bar parlorn ya yi waje a zuciyarsa yana jin cewa wannan shi kaɗai damar da yake da ita wajan sawa Ridayya ta dawo inuwar aurensa yana jin wani iri idan ya tuna ta, he feel very comfortable without her, her love,her voice, her.... He miss everything about her more especially her soft skin ga kullum lips ɗinta dake masa barazana ga Black skin ɗinta sai ya ji gabaɗaya baya son farar mace baƙar matarsa kawai yake da interested akan ta wannan shi ake kira da LOVE!
Chapter 98 · 0% Book details