← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 118

Sashe 53

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah ya amsa. Commissioner ya shigo Nigeria kasan watansa biyu baya nan, mun yi waya ya ce yana nemanka" Nan da nan Sadauki ya haÉ—e fuska ya ce "Gaskiya ba zani ba, Æ´arsa masifar surutu ne da ita kuma ni bana son ka nemi juya ni"

A can ƙauyen Batsari yamma sakaliyya wasu mutane a babura sukaiwa ƙauyen tsinke kamar yadda suka saba hankalin jama'ar ƙauyen ya tashi domin sun san ƴan kidnaping ne ko masu kwashe musu shanu. Gida bayan gida suka dinga shiga suna kwaso yara da mata duk wanda ya yi yunƙurin hana su nan take suke kashe shi. Cikin rashin sa'a suna tsaka da al'amarin da kwashe jama'a manyan motocin jami'an tsaro sukaiwa ƙauyen tsinke suma daman sun zo bincike ne da kuma kawo musu taimako wanda kuma Commissioner da kansa ya buƙaci zuwa da jagorancin tawagarsa. Musayar wuta aka fara dukda ƴan sandan sun yi nasarar kashe wasu da kama wasu amma kidnappers ɗin suma sun yi nasarar tafiya da wasu.

Daga can kuma Zameer ne ke cewa "To ai sakin wasa ne bada gaske nake ba, BAN SAKE KI BA" kallon baka da hankali kawai Ridayya ke yi masa Allah ya bata iko ya riƙe Little Bilal a hannunta dukda jirin dake kwasarta saboda rashin jini ba ta yi ƙasa a qiwwa wajan barin inda Zameer yake ba da gudu.

Ya mara mata baya "Wallahi ban sake ki ba duk inda kika je za ki dawo ne sakin wasa ne ba" Kasancewar bata gani yasa gudu kawai take ta ƙanƙame ɗan ta duk yadda suke mata horn bata ji ba. Driven ya yi ƙoƙarin kauce mata amma ina bai ankara ba sai ihu da ƙarar faɗuwarta suka ji. Ya ajjiye wayarsa da yake tura information na gaggawa ya ce "Ya akai?"

"I am sorry DCP TAJJ MUJID BAITA mun kaÉ—e wata mata ne...

Nimcyluv sarauta
*MUNAFUKIN MIJI 26*
Mikiya Writers Ass

Bright pens free batch
Nimcyluv

*Masu wattpad a dinga following ɗin Account ɗina (profile) a kai ni 5k follower🌚 kunga ai kwana biyu ina ƙoƙarin posting*

https://www.wattpad.com/1425391962?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=nimcyluv

"Accident? Mace da yaro?" Tajj dake bayan mota ya furta hakan, haka kurum gabansa ya faÉ—i bai tsaya an buÉ—e masa motar ba.

Ya ajjiye wayar hannunsa ya fito da sauri yana gyara zama suit É—in jikinsa ya ce

"Subuhanallahi garin yaya aka bugeta? Is she alive?"

"Sir mun yi ƙoƙarin kauce mata amma mun kasa, da gudu ta shigo gabanmu kamar mahaukaciya ce ma ga baby a hannunta"

Tajj ya dinga kallon wacce ke kwance dukda abin bigeta amma tana ƙanƙame da yaronta wanda ya haska baƙar fatar jikinta. Ya ɗan juya kafin ya kalli sergeant Tukur ya ce

"Katsina to Kano awa ne zai É—auke mu ne?"

"3 hr (176.0 km) Sir"

Ya yi jim sai kuma ya ce "Zata wahala har tsayin awa uku, ina tunanin za a yi booking Flight ni da ita da babyn kafin ku ƙarasa mun je asibiti" Cikin girmamawa Sergeant Tukur ya ce

"Yes sir"

Tajj bai tsaya tunanin wani abu ba ya É—auki Ridayya ya sanya ta abayan mota, har lokacin bai ga fuskarta ba kawai ya samu kansa cikin mummunan faÉ—uwar gaba ne. Little Bilal kuma yana wajan sergeant a haka suka nufi masaukinsu kafin a samu booking Flight É—in ya zama ready.

Cikin sa a suka samu jirgin da yake shirye da tashi har airport suka kai su a kan idanunsu suka shiga jirgin kuma basu bar wajan ba har jirgin ya tashi da D.c.p Tajj Mujid Baita da Ridayya da kuma babynta, sai sergeant da aka sanya shi cikin tafiyar saboda yaron, lokaci zuwa lokaci Tajj Baita ke kallon Ridayya da fuskarta take a rufe mamakin hakan ya cika sergeant domin ya fi kowa sanin waye Dcp É—in baya shiga lamarin mace da sai dai idan harkar taimako ne yadda ya nuna tausayi da attention É—insa lokaci guda a kan Ridayya shi ne ya fi bashi mamaki sosai.

Aminu Kano Teaching hospital a nan aka kwantar da Ridayya nan da aka sanya mata ruwa tare da yi mata gwaje-gwaje bayan kammala komai Dr ya kalli Tajj ya ce "Office please" "Ok" Tajj ya faÉ—a yana rufawa Dr É—in baya jikinsa a sanyaye ya shiga ya zauna sosai kafin Dr ya kalli Tajj ya ce

"Allahamdulillah mun kammala bincikenmu a kan wannan yarinyar?"

"Yarinya Dr?" Dr ya jinjina kai ya ce "E, yarinya zai wahala idan ta cika 17yrs daidai ma. Akwai abubuwan da take buƙata sosai" Tajj ya yi shiru jin hakan ya saka Dr gyara zama yana zame gilashin idanunsa ya fuskanci Tajj sosai ya ce

"Sir da farko tana buƙatar jini a ƙalla leda huɗu kenan,abu na biyu ta samu ƙari a wajan haihuwar da ta yi amma ba a kula ba domin wajan ya ɗan fara kamar ruwa zamu wanke kuma a yi mata ɗinki, a ɗinke wajan tas. Tana buƙatar hutu domin samun nutsuwar zuciya data kwakwalwa idan ba haka ba tunaninta na iya gurɓata ainun ko Depression ya kamata saboda bincike ya nuna mana tana cikin damuwa da ƙuncin zuciya duk wasu alamomin cutar damuwa sun gama bayyana tattare da ita"

"Dr na ji ba damuwa, a yi komai kawai" dr ya girgiza kai ya ce "A'a sir maybe da kwai wani abu ka fara shiga wajan yarinyar ka ganta ko?"

Ya ɗan ɓata fuska yana jan kujerar baya domin duk a gajiye yake ga wani irin bacci dake damunsa a kasalance ya ce "Ba sai na je ba ina tunanin ka tattara baya nan kuɗin ka bawa sergeant"

"Ka dai shiga"
Ganin yadda dr ya takura ya miƙe ya nufi ɗakin da aka ajjiyeta na musamman. Tunda ya ɗora idanunsa a kan fuskarta jikinsa ya yi sanyi ya ƙura mata idanu a hankali kuma ya ci-gaba da takawa zuwa gaban gadon zuciyarta na harbawa da ƙarfin gaske "You?" Ya furta daidai da kunnensa a zuciyarsa yake cewa

"Finally i got you" Wani irin tausayinta nan take ya mamaye zuciyarsa baya son mace cikin wahala da rashin kwanciyar hankali, hankalinsa tashi yake sosai musamman irin yarinyar da a shekarunta ba zai shige ace tana makaranta tana karatu ko gaban iyayenta ba, yana buƙatar sanin wacece wannan yarinyar, daga ina ta fito ina zata, last time ya ganta a Kano yanzu kuma ya ganta a Katsina meke faruwa? Dole akwai wani ɓoyayyen al'amari a cikin rayuwarta wacce ita kawai tasan hakan. Ya ɗan haɗe rai a fili ya ce

"Ba na ce miki ki kira ni ba when you need my help? Shi ne kika ƙi ko gashi nan na same ki ba zan ƙara barinki ba sai na taimaka miki" daidai da kunnensa yake maganar kafin ya juya ya kalli dr ɗin cikin nutsuwa yake masa wani bayanin yana mai ɗan matsa hannunsa

"Zan je gida na dawo kafin nan ka gwada jinina idan zai yi daidai da nata sai a É—auka ga fuskarta ma kafin wani abinne ya sameta ko?"

"Ƙona ce" Laboratory suka shige aka ɗauki jinin Tajj Baita domin a gwada ko zai yi daidai dana Ridayya daga nan sukai sallama ya nufi reception na asibitin kai tsaye ya samu driver na jiran shi ya shiga bayan mota aka nufi da shi gida. Kasancewar a gajiye yake ya saka ana parking ya fito yana zame ƴar saman rigar tashi a hankali yake tafiya kamar baya so har ya nufi ƙofar farko ya buɗe ya shiga ya sake tura ta biyu ya shiga babban parlourn gidan. Da gudu wata ƙaramar yarinya kyakkawa da ita ta tashi tana faɗin

"Daddy daddy" Ya sunkuya ya É—auketa yana cewa "Iyee Æ´ar Daddy kullum tana zaman jiran daddynta" Murna ta kama yarinyar ta ce

"I miss You Daddy jiya na dinga kuka a kai ni wajanka amma Mahmah taƙi ya" Mahmah dake fitowa daga ɗaya parlourn ta ce

"To farfesa komai a kai kamar kina kira ubanki ya dawo ki wassafa masa ko gulmarsa mukai a banza mukai" Yarinyar dai ta yi shiru ta lafe jikin babanta. Mahmah ta nemi waje ta zauna, shi ma Tajj ya zauna kusa da Mahmah ya ce "Barka da rana Mahmah mun same ku lafiya?"

"Allahamdulillah Tajuddeen ya aiki? Ka zo lafiya" ya É—an gyara fuska ya ce "Aiki sai addu'a kawai Mahmah ko jiya an kai hari Katsina fa sun kwashe Æ´an mata wallahi"

"Wannan ƙasata mu ko yaushe komai zai zama daidai? A dinga sace jama'a musamman ƴan'mata ga kashe al'umma ba gaira ba dalili idan zaɓe ya ƙaratu an dinga abubuwan da basa tafiya daidai" rufe idanunsa yana shafa kansa sosai. Jin ya yi shiru ya sa Nadra cewa

"Daddy Uncle ya zo yana nan" Idan ta ce Uncle ya san wa take nufi kuma bai yarda da maganar ta Nadra ba, yasan halin surutunta Uncle ba zai taɓa shigowa Kano ba saboda ya tsani kano a yanzu ɗin kuma daman rabon Uncle ɗin da gidan su Tajj har ya manta. Don haka ya share maganar ta Nadra ya rufe Idanu yana ji tana jan samarsa. Mahmah dake zaune ta ajjiye remote ɗin hannunta ta ce "Ustaz bari a ƙarasa kammala maka tuwon ko?"

Shiru kamar ba zai yi magana a hannun Tajj ya ji saukar muryarsa a nutse cikin kunnensa ya ce "No" Ya buɗe idanu sai kuma ya juya kallonsa ya sauka kan Muhammad-Bilal Ustaz dake zaune a saman kujera ya kishingiɗa a gefe kamar mai yin bacci fuskarsa a haɗe sosai tamkar bashi ne ya yi magana yanzu ba, dukda maganar bata arziƙi ba ce. Sosai Tajj ke kallo Ustaz ganin yau gwarjininsa ya fito ga wani irin kyau da ya yi ko dan bai taɓa ganinsa cikin wagambari ba? Getzner wagambari brocade ce a jikinsa sai ɗaukan Idanu take kana gani kasan an kashe kuɗi wajan siyan shaddar. Blue green ce ta yi wa farar fatarsa masifar kyau gashi saje da ƙasumba sun ƙara cika fuskanta ya gyara sosai sukai ma fuskar kyau nutsuwa da haibarsa ta sake bayyana ƙwarai a fili. Ya ɗan ɓoye shekarunsa ta hanayar tsare gira kodayaushe baya ƙaunar raini.
Chapter 53 · 0% Book details