← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 118

Sashe 42

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu bana ƙasar Daddy ya aike ni zuwa Switzerland a nan zan haɗo miki lefe ma, kuma gidanmu ana ta gyara ne" Kai tsaye ya ce Switzerland ɗin ba tare da ya san wacce ƙasa ce ba, kawai da ya yi searching na best country in the world sai suka nuna masa Switzerland ɗin matsayin ƙasar da ta fi ko wacce shi ya sa ya faɗa mata.

"Oh Allah ya dawo da kai lafiya" Ya ce "Cewa za ki Allah ya dawo mini da mijina lafiya, ki daina jin kunyata fa" Ta yi murmushi kan ta a ƙasa ta ce "To na ce"

"Ridayya"
"Na'am" Ya yi jim sai ya ce "Me ya sa mutane basu da uzuri ne? Suna manta Ubangiji ke yin halittar bawa a yadda ya so, bana jin daɗin yadda friends ɗina ke nuna mini wai bai dace na aure ki ba" A rikice ta ce "To saboda me?" Ya ce "Saboda yanayin halittarki wai muninki ya yi yawa, nikam cin uban shegu nake ai basu san daraja da alfanun baƙar mace ba wlh, kuma ina ce musu you're the first person da kika nuna kina so na kuma na yi supporting tare da accepted naki a yadda kike"

Jikinta ya yi sanyi kar a raba ta da wanda take ganin tuni ya zama miji gare ta, tana tabbacin idan ta rasa Zameer to babu wani namiji da zai ƙara ce mata hello ko da wasa balle maganar soyayya tabbas ita ta fara cewa tana son Zameer kuma ya amince ba tare da san aibun hakan ba, ta shure duk wanda girma, daraja, baiwa, ni'ima da Ubangiji ya yi mata. A sanyaye ta ce

"Don Allah ka riƙe ni amana ka zauna dani tsakani da Allah nasan ba zan taɓa yi maka laifi ba, kar ka ce ka fasa aure na, kar ka ce zaka rabu dani kar ka ce zaka sake ni bana son zaman gidanmu ko kaɗan wallahi.....," Sai ta fashe masa da kuka a ransa wani farin ciki ya ji ya samu weakness nata available a fili ya ce.

"If you are never fallen madly in love, understand that God has done you a huge favour. Wallahi na masu na tabbatar dake matsayin matata kuma wannan Abbiey É—in naki yana neman yi mana shamaki amma idan muka bi hanya É—aya ba shi ba ko Baffa ba zai hana ba" Ridayya ta ce

"Shi Baffa da mai damu dani ba ya ce ni ba Æ´arsa ba ce kaga ai ba zai hana ba" Zameer ya ce "To kice ba ki da wani gata ma kar ki damu zan maye miki gurbin kowa da kowa kin ji? Za ki yi farin ciki sosai Mrs Zameer Mahboon Dollar" Ta yi murmushi ta ce "Na gode" Ya kashe murya ya ce "I love you so so much my wife matata, ki zo makaranta gobe da wuri ina son ganinki"

"Ka ce baka ƙasar?" Ya yi saurin zare ido jin ya kwafsa ya ce "Ai soyayyarki ta motsa ta yi bake-bake a zuciya zan dawo da sassafe" Sallama sukai Ridayya na ji wata nutsuwa a ranta.

Sama da sati Ridayya bata saka Ustaz a idanunta, hankalinta duk ya tashi gashi Zameer yana ta tambayar yaushe zai ga Abbiey É—in a lokacin sai ta ji bata damu da wayar Meer É—in ba tunda tana da tabbacin zai aure ta É—in. Nufar part É—in iyayenta ta yi ta kuma ci sa a duk suna nan dake weekend ne har da su Zahura suka dinga kallonta haka Mami Zainura ta ce "Yaya Ridayya" Ta juya ta kalli Zainura a tsawa ce Baffa ya ce "Lafiya kika faÉ—o mana gida?"

"Aure nake so a yi mini Baffa" Maganar ta gigita kowa musamman Mami amma ta yi shiru hankalin Ammi ya tashi ganin plan É—inta na aurawa Burhan Ridayya zai lalace "Aure wanne iri? Idan aure ne ki je ki yi magana da Babban mutum mana" In ji Balkisu domin ta jima da fahimtar tsananin son da Ustaz ke yi wa Ridayya É—in ta ce "Na faÉ—a bai yarda ba, ni kuma aure za a mini bana son zaman gidan nan"

"Tab amma wannan yarinyar ba ki da hankali, yaushe kika san soyayyar wanne mara hankalin ne zai aure ki kuma? Ya taɓa ganin fuskarki?" Ridayya ta ƙi kula Zuhura domin ta san ba ƙaunarta take ba. Junaid ya ce "Kuma kika kasa yi wa Yaa Bilal ɗin biyayya ki jira yi uzurin shi?" Ridayya ta ce "Bashi da wani uzuri fa, kamar yadda Yaya Zuhura ta ce babu mai iya aure na to yanzu na samu aure nake so"

Baffa ya miƙe tsaye ya ce "Allahamdulillah ni na ji daɗi gwara na aurar dake na huta wallahi" Da sauri Ammi ta ce "Wannan ɗin zaka aurar? Me ta sani dangane da soyayya balle zaman aure wallahi ba za a aurar da ita ba ban shirya ba, ba kuma haka na tsara ba" Baffa ya ce "Zan aurar da ita sai dai idan yaron ne ya ce baya so ban kuma damu da dukkan wanda zata aura ba koda zai dinga taka ta a turmi ne"

"Kar ka yi wa aurar baki Baffa ka sanya albarka" Baffa ya ce "Ki rawo mini yaron" Da sauri Ridayya ta kira number Zameer ya ce gashi nan zuwa. GabaÉ—aya wanda suke wajan sai la'antar auren suke musamman Baffa da Ammi da Zuhura Mami bata cewa komai tunani take wanda ya sha bambam da nasu.

A lokacin har Baba ƙarami yana wajan da Umma kowa ya hallara Zameer na zaune ya ci uwar shadda ta babbar riga ga ɗan makulin mota ga iphone a hannunsa. Balkisu sai kallonsa take ita da Mami haka kurum suka ji bai kwanta musu ba. "Kai ya sunanka? Waye ubanka a garin nan? Mene matakin karatunka?"

Sai kuma Baffa ya sake cewa kodayake ban damu ba idan zaka aure ta ɗin dukda na yi mamaki. Zameer mamakin yadda ake ta wulaƙanta Ridayya a kan idanunsa a cikin gidansu ya kama shi ya ce

"Sunana Zameer Mahboon Dollar, ina GRA dake Nassarawa da zama Daddyna bai fiya zaman ƙasar nan ba, na yi degree a Bayero University a nan na haɗu da Ridayya ƴarka, kuma ta kwanta mini kuna iya yin bincike domin ku tabbatar" Baffa ya ce "Ba wani bincike da za a yi, kawai ka turo a magabatanka sai a ɗaura aure ka ɗauki matarka" Zameer ya yi hamdala Baba ƙarami kallon Zameer ɗin yake shi da Mami da Balkisu harda Junaid.

"Yanzu kenan ka yi degree aikin me kake?" A ransa ya ce "Zaman banza mana" A fili kuma ya ce "Ina Business a wajan ƙasar nan ina tafiyar da harkokin mahaifina" Da gaske ya yi degree domin ya dage yaga ya yi karatu domin ƙarya da shiga sabgar manya sai da ilimi kawai ya yi alƙawarin idan ba aikin Gwamnati bane da zai dinga ganin kansa a office mai A.c yana juyawa yana saka hannu a manyan files na harkar maƙudan kuɗaɗe to zai taɓa wani aiki saɓanin wannan ba.

"Na baka ita"
"Ban amince ba, sai mun yi bincike a kan ka" Da sauri Baffa ya kalli Baba ƙarami Ammi ma ta ce "Ban amince nima" Haka Balkisu. Nan da nan Ridayya ta fara kuka hankalinta ya tashi "Ka je zan kira ka ko?" Cewar Baba ƙarami.

Kwana biyu tsakani Ridayya ta dinga neman Abbiey ɗin nata baya nan ta san shi kaɗai ne kawai zai ji tausayinta,number shi a kashe bedroom ɗinsa a rufe. Baba ƙarami ya dinga neman Ustaz shima domin abin ya zo saɓanin tunaninsa shin daman ba son Ridayya yake ba all this time?. Abinda basu sani ba Ustaz na gidan ya rufe kansa a ɗaki shi kaɗai sai rubutu yake a cikin diary ɗinsa cikin kwana biyu ya faɗa ga wani ciwon ƙirji komai ya dai na yi masa daɗi ya ƙara zama shiru-shiru Ridayya ta bashi mamaki ta gigita shi da kalamanta.

Yau tunda ta je makarantar ba taga Zameer ba yanzu ne kuma suka shiga second semester. Mardiyya ta ce "Dole na kalle ki ban É—auka haka kike ba, wallahi za ki yi ladama idan kika auri Zameer I'm telling you Ridayya"

"Ki samun albarka kawai Mardiyya" Diyya ta ce "Ba kya tausayin Abbiey wallahi yana son ki duniya ma ta san haka"

"Ki aure shi mana Mardiyya, ai ke kina jin tausayin shi ko?" Da mamaki Mardiyya ta ce "Haka kika ce? Ni fa aminiyarki ce idan ban faɗa miki gaskiya ba waye zai faɗa miki? Ki nutsu sosai ki gane dalilin daya saka kike son auren Zameer na tabbatar ba soyayya ba ce, kamar yadda shima ba son ki yake ba, soyayyar gaskiya tana wajan Abbiey" Ridayya ta miƙe ta ce

"Mardiyya me kike nufi? Jallabiyya zan aura ko hirami ko carbi, ki auri Abbiey mana wallahi zan fi kowa murna idan na gan ku tare as husband and wife ni bana son shi ke kuma ya yi miki sai a haÉ—a bikinmu rana É—aya ki zauna kullum ya dinga faÉ—a miki Asstagafirullah subuhanallahi ko kuma ya yafe miki" kalaman Ridayya kamar ka yi musu dariya amma gaskiya take faÉ—a. "So kina so ki ce he's not romantic? Jallabiyya baya burge ki ko? Kin san wani abu baki san su waye ustazai ba Ridayya lokaci ko na ce rana É—aya idan ki kai soyayya da su wallahi sai kin hauka ce, su É—in daban suke ba a banza ake kiran su da Ustazai ba sun karanta sun gani sun san mene soyayya da aure, ki rubuta ki ajjiye wallahi tallahi sai kin yi kuka akan Abbiey"
Chapter 42 · 0% Book details