Sashe 113
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma ta saki baki Baba ƙarami girgiza kai kawai ya yi ya san daman za a yi hakan ya ce "Mardiyya an yi yarinyar huɗuba?"
Ta girgiza kai tana ta kuka fargaba ta cika mata zuciya tana fatan komai zai je ya dawo ta kasance da Ustaz har abada ta kuma raba shi da Ridayya da ta ci amanarta. Baba ƙarami ya amshi yarinyar bayan ya yi mata huɗuba ya ce "Wanne suna kike so?"
"Sunan Umma na ce a a saka Hadiza Umma na yi wa takwara"
"To ma sha Allah, Allah ya yara Hadizatul-kubra"
Umma ta yi saurin cewa "Wacce Hadizan? Wallahi bana so a ƴar shegen za a saka sunana wallahi na yafe a saka sunan tata uwar ko wannan" Ta nuna Inna. Inna ta zare idanu ta ce "Ni Mero ina ruwana? Bake kikai ta ɗawainiyya da cikin ba" Baba ƙarami ya danne dariyar dake cinsa ya ce
"Kina da gaskiya Inna, Umma ta yi ƙoƙari a cikin nan har fili ta mallaka masa fa? Ai dole a saka Hadiza" Yana faɗin haka ya sawa yarinya Hadiza Umma ta fashe da kuka ta ce "Allah ya isa wallahi, kuma ba ni Hadizan aka saka ba ki je ki fito mini da takardun filayena"
"Wallahi Umma ƴarsa ce sharri yake mini, wa aka aura mini idan bashi ba yawo nake yi ne?" Sai kuka take Umma ta ce "Ke rufa mini baki a nan, Ustaz kalma ɗaya yake idan ƙarya ne kai tsaye zai faɗa haka idan gaskiya ne"
Takaici ya haÉ—ewa Mardiyya Inna dai na tsaye sai zare idanu take suna haÉ—a idanu da Mardiyya ta ce "Ashe tantiriyar Æ´ar iska ce ke?"
Duk suna zaune kamar daga sama Ridayya taga mace a gabanta ta ɗaga idanu ta kalli Mardiyya da take cewa "Shegiya munafuka Allah ya tuni asirinki mai ƙwacen miji wallahi ba ki isa ba sai kin bar mini mijina domin nawa ne ɗaya har abada"
Miƙewa Ridayya ta yi zata shige part ɗin Mami Mardiyya ta riƙo wuyanta, daman tun ɗazo zuciyarta ke yi mata zafi sosai bata tsaya jiran komai ba ta ɗaga hannu ta zabgawa Mardiyya mari ta ƙara sauke mata wani ta nuna ta da yatsa ta ce
"Kul karki kuma, ki haukan ki kan wanda ya ajjiye ki ba ni ba, wahainiyyarki ta kiyayi ramata, ke har ni za ki buɗe baki ki cewa mai ƙwacen miji? How dare you? Ni kikaiwa ƙwace ko ni na yi miki?"
"Idan kin manta na tuna miki, kin tuna sanda kika ce Abbiey ba tsarinki bane jallabiya za ki aura ko shi? Kuma kika ce idan ina da ra'ayi na je na aure shi? Ai tun daga wannan na sakawa raina sai na aure shi kuma ya zama nawa har abada, kin yar ni na É—auka don haka dole ki bar mini mijina"
Maganganun da Mardiyya ta tunawa Ridayya sun mata zafi ta dake ta ce "Ohho dani dake za a ga mai fitar da wani, zama da mijina yanzu na fara kuma yanzu na shirya zan cika gidansa da tarin yara masu kyau irin albarka, zan ci gaba da son mijina don haka kowa ya iya allonsa ya wanke, ina son Abbiey yana sona" sosai suke faɗa ba zaka taɓa cewa sun taɓa zama aminai ba, Mami na ji ta yi shiru shi kansa Ustaz yana tsaye Umma ta ƙarasu ta ce "To wallahi sai kin barwa Ridayya mijinta, domin ita ce irin albarka" kalaman Umma sunwa kowa daɗi kuma sun bawa kowa mamaki ganin jinin Ridayya ya fara rawa idanunta yana wani kala ya saka Ustaz yin murmushi ya ƙarasu tare da kama hannunta ya ce
"No please Mimi" hannu ta saka ta doke hannunsa tana zabga masa harara ta suka ci-gaba da cacar baki "Banza wacce ubanta ya ce ba shi ya haifeta ba, wacce babarta ta gudu ta barta wajan kishiya uwar Æ´ar shaye-shaye kawai wacce ta auri É—an caca.....,"
Caraf Zainura ta ce "E an ji ɗan caca ke kuma da kike yawan ta zubar fa? Mai shafe shafe kuma ita bata zalunci mijinta ba shi ne ya tauye mata hakƙi shi ya sa yanzu take ta ganin sauyi kala-kala, da kike maganar muni kuma ai ga ƙarshen muni nan kin haifa bayan ke ɗin fara ce kyakkyawa ita data kasance baƙa ki dubi nata kalar irin kiga? Ai babban goro sai magogin ƙarfe kuma da tsohuwar zuma ake maganin hakan kuma don tuwan gobe ake wanke tukunya" Burhan sai murmushi yake that's why she always love Zainura yana son mace mai tsiwa da baki wacce yana cewa ke zata ce kai ƴar drama like Zainura. Ustaz ya sunkuya ya sunkuci matarsa ya nufi part ɗinsa da ita sai rawar jiki take, Mardiyya ta juya fuuu bayan taci kuka ta ƙoshi addu'a take Allah yasa jaririyar ta mutu ma, ta dinga kiran number ƙawarta domin ita kaɗai tasan gaskiyar komai amma bata samu ta tuna gift ɗin da Ustaz ya bata hakan yana nufin yana son ta bai kuma yi fushi ba. Ta buɗe kuɗi ne ƴan 1k bandir uku sai ƙaramar takarda tana buɗe taga ya rubuta.
_Wannan kuɗin kyauta ne daga ni a matsayin mijinki, da gaske na so zama dake tunda ni bana buƙatar saki a cikin lamarina aurena dake ƙaddara ne, amma zunubin da kika aikata ya saka na janye nawa ƙudirin ba zan iya zama da macen dake bin maza ba.... Mardiyya na sake ki saki uku kuma ki nemi uban yarinyar da kika haifa_
Wani ihu ta saka tare da sulalewa a wajan babu numfashi. Waya yake yi yana cewa "Na ji ya dawo gari, ba zan taɓa haƙura da cin mutuncin da Zameer Giɗaɗo ya yi mini ba dole ne na baza bidiyon da sukai a jam'i kafin su yi aure, kowa ya gansu tsirara babu abinda ya shafe ni ba'a cin bashina na yi haƙuri wallahi, so zan jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya kenan, daman akwai wani ya bani kwangila ɓata shi Muhammad Bilal Tahir Rano ɗin domin jama'a suka baƙin shi, kaga yarinyar da sukai zina tare da Zameer ai matarsa Bilal ɗin ce da yake neman takarar Gwamna, kuma shi da kansa bai san cewa ta aikata abinda ta yi ba, so babu mamaki ganin bidiyon ya saka zuciyarsa bugawa ya mutu nan take" Khalid ya yi ɗan jim sai kuma ya ce "Ok bari na tura maka bidiyon yanzu da iPhone aka ɗauka ya yi clear sosai a fara posting a tiktok sai ya fi zama trending going in to viral ka yi hash tag sai a koma facebook da X da Instagram sai a turawa bloggers yawwa gashi nan zan tura bidiyon yanzu......
A yi haƙuri gobe zamu kammala
08164069385
*MUNAFUKIN MIJI*
Nimcyluv
48
Mikiya writers Association
Fitowa sukai daga ɓangaren emergency ɗin kana ganinsa zaka san yana cikin damuwa ya ce "Dr yanzu ya za mu yi da gawar? Kuma ba a samu labarin wanda sukai masa wannan rashin ɗa'ar ba?" Dr ya kalli Shaba da Moo ya ce "Ambulance za a kira sukai muku gawar, and wanda suka aikata hakan i think that is not part of my work, an dai samu labarin cewa ƴan daba ne suka same shi a bakin hanya, sukai ƙoƙarin amshe wayarsa ya hana su, garin haka suka soka masa wuƙa a ciki sai data ɓullo ta bayan shi, bayan wayar har motarsa suka gudu da ita shi kuma suka yasar da shi a ƙasa, kafin ma a zo asibiti ya cika" Moo ya sauke numfashi shikenan sun rasa Khalid? Yaushe za a daina ƙwacen waya? Yaushe ne za a daina shaye-shaye? Yaushe ne za a daina daɓa? Abin kullum ƙara girmama yake kamar cin ƙwan makauniyya? Faɗan sai ƙara yawa yake ba mai cewa komai babu mai ɗaukan mataki? Meke haddasa shaye-shaye da kuma daba? (Find out on MUTALLAB).
"Allah sarki Khalid Allah ya jiƙan shi bai so ya rasu bamu daidaita tsakaninsu da Zameer ba" cewar Moo kallon shi kawai Shaba ya yi without saying a single words. In few minutes rasuwar Khalid yaɗu cikin jama'a da kuma yadda ake Allah wadai da masu ƙwacen waya. Ambulance na zuwa aka saka gawarsa suka nufi gida, hankalin duka ƴan'uwa a tashe yake.
Zagaye yake cikin parlon nashi zufa sai yanko masa take ya juya ya kalli wanda ke tsaye a gabansa a hankali ya nisa ya ce "Kuma da gaske bai tura maka bidiyon ba kafin rasuwar shi? Bidiyon nan shine confidence ɗina kuma shinr hope nawa na ɓata farinjinin Muhammad Bilal, da kuma kawo naƙa su a takarar shi"
Guy ɗin ya girgiza kai ya ce "Oga bai tura mini ba, daman na baka shawara wannan aikin da mutum ɗaya kawai ya dace, baya tsoro, baya shakka baya damuwa da duk abinda zai biyo baya shi ɗin tamkar walƙiya haka yake, hagayi sa gabanka inda kake so, shi ɗin murucin kan dutse ne bai fito ba sai daya shirya, ɗan malam yaƙi halin malam, faɗa taka cikawa tashi kuɗi kawai shi ne a gabansa kaci amanar shi uwarka ta haifi wani, jan biro maganin daƙiƙin yaro..... Huhuhu kutumar uban nan wani aikin sai maza da an ganshi fitsari ake a wando, ya gagara matacce ne amma kullum firgita su yake mutum me aikin aljanu, mata maza wajan ƙin mata da sabgoginsu"
Nan da nan jiginsa ya fara rawa ganin haka ya saka Sakataren jam'iyar su Muhammad Bilal Ustaz mai suna Dr Ghali Uba ya ce "to waye wannan É—in da kake ta yi wa kirari haka?" Shazali ya kalli Sakataren jam'iya ya ce
"MUTALLAB"
"MUTALLAB?"
Dr Ghali Uba ya maimaita sai kuma ta ce "Yanzu bamu da wani lokaci, amma idan ina raye ba zan bar Ustaz ya hau wannan kujerar ba, ni na nemi takarar kujerar wajan Uban jam'iyya amma saboda ya wulaƙantani ya ce ban dace da ita ba, ya je ya ɗakko wanda bai san darajar siyasa ba ya bashi? Na ci alwashin lalata jam'iyyar idan ya so na yi anti fati kawai"
"Oga kenan zagon ƙasa kake musu, sun yarda da kai fa? Shi ne kake ɓallo musu ruwa ta ƙasa? Ka daga oga"