← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 118

Sashe 34

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ustaz ya bi Ridayya dake kwance a ƙasa tana juyi da mummurɗewa zuciyarsa na ƙoƙarin tsinkewa ganin kumfa na fita daga cikin bakinta ta abu kamar bugun jinnu "Ustaz ya haka ka zubawa yarinya ido cikin wannan hali, haba babban mutum" Umma ta furta tana ƙoƙarin kai hannunta jikin Ridayya. Ya furzar da iskar bakinsa ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya kafin ya ce "Karki taɓa ta"

"Kamar ya?" Ya É—an marairaice fuska kamar an yi masa dole ba tare daya kalli Umma ba ya ce "Hausa fa na yi, da gaske Hausa ce Umma" Ta girgiza kai ya juya a hankali tare da É—akko hiraminsa ya rufe jikin Ridayya da shi, bakinsa na motsa wa a hankali yana mai yin addu'a tare da tofa mata.

Can ta saki fitsari a saman carpet yana bin cibiyoyinta. Ustaz dai na tsaye haka Umma na kallon abin al'ajabi domin ba'a taɓa yin farfaɗiyya a gabanta ba sai yau. "Ikon Allah, Allah ya sauwake daman haka take yi kenan? Baiwar Allah" Tausayin Ridayya duk ya mamaye mata zuciya bayan matsalar gidan uba gata zubin halitta, gata gorin kalar munin da ake mata, ga makarantar babu daɗi. Uwar data haifeta ma sam bata damu da ita ba, balle kuma uba, wata sabuwar ƙaddarar na lalura ita kanta ba ko wanne namiji ne yake ƙaunar mace mai farfaɗiyya ba, ga shi ƙanwarta Zainura kamar ba jini ɗaya ciki ɗaya suka fito da Ridayya ba haka take nuna mata.

Da ƙyar ta buɗe idanu saboda tsananin kunyar Umma da Abbiey wanda yake tsaye har yanzu, ita bata san lokacin data faɗi ba gashi duk sanda ta yi hakan sai ta yi fitsari a kwance. Basu san ta dawo hayyacinta ba sai sautin kukanta suka ji wani irin raunataccen kuka bai taɓa zuciya. Ustaz ya runtse idanunsa saboda wani irin dokawa da zuciyarsa ke masa, a hankali komai na jikinsa yake sage wa kansa ya fara sara masa da wani irin ciwo. Ya saka hannu yana dafe kan tare da furza goshinsa.
Can ya juya a ɗan fusace kamar zai yi faɗa sai kuma ya tausasa murya, daga ƙarshe ma ya rufe bakin ya fasa faɗar abinda ya yi niyya.

Yatsu ya kaɗa mata yana gyaran murya ta miƙe da sauri tana bin bayansa da sanyin jikin daya zame mata jiki komai nata a sanyaye yake yadda take tafiya kamar bata so haka take yi ko gudu bata iya ba, muryarta kodayaushe a ƙasa ba hargagi so silent, innocent gril. Ta yi jim tana leƙen bedroom ɗin can kuma ta shiga tana furta "Assalamu alayka"

Babu tabbacin ya amsa kawai tana da yaƙi nin dole zai amsa idan har ba ta yi sallama ba baya kula ta duk kalar zancen da za ta yi masa. Ganin yadda ya yi tsaye a bakin wardrobe bai kula ta ya saka Ridayya ƙara fashewa da kuka tana yarfe hannunta
"I am sorry Abbiey, ban san na faÉ—i ba, ban san na yi fitsari ba Allah"

Ustaz ya juya ya kalleta idanunsa duk ya shige ciki sai ya girgiza kai a hankali ya ce "Yaushe Ustaza za ta girma?" Da sauri ta ce "Yau Abbiey" Sai kuma ta girgiza kai ta ce "A'a ai ba zan girma ba, ai dabbobi basa hankali ni ma ba zan yi ba" A rikice Ustaz yana riƙe jarumarsa ya juya ya kalleta da kyau kana ya yi baya a taushashe ya ce

"You said that?"
"Zainura ce Abbiey" Ya yi shiru tana shassheƙar kuka sosai ta kama hannun Ustaz ta ce "Abbiey da gaske wai tsinto ni a kai ba nan ne gidanmu ba? Abbiey you're my father ko? Ammi ce Ya haife ni ko?" Ustaz ya rasa wacce amsa zai bawa Ridayya wacce za ta yi daidai da tunaninta ya fahimtar da ita ƙaddarar ta ce ta zo a haka? Ya nuna mata babu wanda ya isa ya ja girman ƙaddara, komai lokaci akwai sanda za ta shige. Bai dawo daga tunanin da yake ba ya ji ta saki ajjiyar zuciya.

"Abbiey mene kwaila kuma? Yau da muna yin final exam ina murna wata ce mini wai na daina murna jss 1 a dawo dani saboda ni kwaila ce kuma Kangaroo basa zuwa University. Abbiey mene kwaila kuma mene Kangaroo?" Ustaz ya yi shiru yana son Ridayya ta fahimci abubuwa da dama amma babu mai faÉ—a mata, babu mai nusar da ita shi ya sa wani lokacin idan ta yi magana yake girmama wawtar ta, da tunanin har yanzu ita É—in yarinya ce gata Æ´ar'fari ga lalura abin ya yi mata yawa. Jin ya yi shiru ta sake marairaice fuska ta ce

"Abbiey mana, please"
Ya kama hannunta tare da janta saman kujera bayan ya zauna ta, zauna a ƙasa wajan ƙafafuwansa kan ta a ƙasa shi kuma ya zuba mata ido, yana jin yadda zuciyarsa ke dokawa da ƙarfin gaske abubuwa da yawa na farmakar shi. "Ustaza" A sanyaye ta ce "Abbiey"

Ya yi shiru ya ce
"Kina bari ana raina ki ta hanyar nuna ƙuruciya Ustaza, da gaske ba za ki girma ba har yaushe zan kasance dake haka?"

"Kasancewa kuma Abbiey?" Ta tambayata cikin rashin fahimta. Ya fasar ya ce "Wai suna nufin ba ki fara irgan su Zainu su Junaidu su Abdullah ba" Ta yi ƙuri ya ce "Wai fa nono suke nufi Ustaz idan mace nada shi ta girma if not kuma she's still a baby, kwaila ce ita" Ridayya ta zare ido sai kuma ta yi ƙasa da kanta. Ustaz ya tallafo haɓarta yana zubawa fuskarta Idanu ya nutsu yana nutsa ganinsa da kyau wai ko zai yi dace ya hango ta inda Ridayya ta samu tawaya amma ya kasa. Yasan idan ana neman asalin baƙar fata ta ƴan arewa to Ridayya ce a fusge kuma yanajinta kamar haihuwar ƙasar Ethiopia ko Mali. "Kin fahimta?" Cike da rashin sanin me take cewa ta ce

"Ni ina ruwana da wani nono Abbiey? Ai ɗan Iska ake gani da shi nikam bana so" Ya ɓata fuska ya ce "Saboda me bakya so?" Ta ce "Ai yarinya ce ni shiyasa" A ransa ya ce
"Allah ya sa motsin gado ce ke Ustaza" A fili ya ce

"Allah ya shirya mini Ustaza" Ta yi murmushi tana lumshe idanunta a hankali ya ce "Congratulations an gama school sai University daga nan kuma sai.....," Ya yi shiru ta miƙe ta ce "Sai auren Abbiey in ji Umma" Bai kalleta ba sai girgiza kai da ya yi kawai yana sauke numfashi domin tun ɗazo a takure yake jinsa ya kasa nutsuwa da zuciyarsa bai bama ga dalilin dawowarsa Kano ba a daidai wannan lokacin.

Da sauri ya shiga shagon yana duba lokaci can dai ya tsaki yana gyara sajensa daya zaune a fuskarta ya yi masa kyau, ga farar fatar nan ta shi gwanin sha'awa kyakkawa ne ajin farko, san kowa ƙin wanda ya rasa ga aji da masifar ɗaukan wanka. Ya sake yin tsaki a karo na biyu yana cije laɓɓansa.
"Ni da wajan sana'a ta ba za ka zo kana mini tsaki ba a gaskiya, kuma yau ko asirinka zai tuno ba zan baka aron kayan kowa ba. Haka kurum kaja mini jarfa jiya fa da zaka je dinner ɗin Farouk wallahi saura kaɗan mai kayan dana ɗauka na baka ya ci ubana, to neman halak ɗina nake wanda zan rufawa kai na asiri da iyayena ban ja magana ba, to ka yi kaɗan ka yi tsararo ka ja mini ita wallahi" Rai ɓace ya kai ƙarshen maganar yana ɗauko wata dakakkiyar shadda gezner blue black ta ji ɗinki sai ɗaukan idanu take ga ƙamshin turare na tashi a jikinta. Ya shimfiɗa rigar shaddar yana yayyafa ruwa zai goge domin mai ita ɗan bala'i ne. Ganin yana ta tsaye ya saka shi kada baki ya ce

"Zai fi maka kyau kasan inda dare ya yi maka, tunda ka ɗauki rayuwar da Allah bai baka ita ba ka ɗorawa kan ka, banda ƙarya da yaudarar yaran jama'a babu abinda ka iya, ba fus ba ass sai zaman kashe wando idan mota Benz ta shigo shigewa a ɗora buri da lissafin duniya a kanta, bayan ana fama da dattin aljihu" Sai a lokacin wanda ya shigo shagon ya ce

"Kasan dai zan yi arziƙi kuma zan zama millionaires?" Mai gugar ya saki dariya ya ce "Ina fa? Nasan dai watarana zaka ci ubanka ka kuma koma Nahutun Batsari"

"Shikenan daga na faɗa maka sirrina sai ya zama abin gori Mujahid? Mene ya kawo maganar Batsari kuma?" Mujahid ya ce "Babu laifi a tunawa mutum asalinsa, ai arziƙi ne ka yi baƙo ya kashe ka" Mujahid ya sake yin dariya ya ce "Wallahi ka ji tsoron Allah ka daina rayuwar ƙarya"

"Idan ban ji tsoron Allah ba, Mujahid kai zan ji tsoro duk abinda nake yi bashi ne zan biya ka dana amsa sunan mijin Hajiya" Mujahid ya riƙe guntun gemunsa ya ce
"Ba shakka, wannan shi ake kira da kunne ya girmi kaka, duniyar rawar Æ´an'mata na gaba ya koma baya, kai a É—an iska ba labar farko ne"
"Ka rufa mini asiri"
Mujahid ya ce "Allah ya rufa mana, ai duk duniya babu mai jin wannan zancen ka huta ka sarara" Ya yi murmushi yana ƙanƙance idanunsa cike da iskanci wanda suke fusgar ƴan'mata ya ce "To ya Opay na zo yi, ka bani wannan shaddar awa ɗaya zan yi kawai ka haɗa mini da hula zanna bukar ka bani aron air-pies ɗinka na Iphone or bluetooth ake ce masa ko? Sai kuma takalmi"

"Duk a nawa? Domin masu kayan anjima za su zo amsa karka bar ni a ruwa don ubanka zan ci" Yana jingina da jikin bango hannunsa É—aya a cikin aljihu É—aya yana shafa sajensa ya ce

"1hour ya yi yawa zan dawo, wani get-together zani ne a group ɗinmu na Kano celebrities". "Yaushe Bakatsine ya dawo Bakano? A gaskiya idan ajeboters suka ji abin ba zai yi kyau ba" Tattara harɗaɗɗiyar shaddar ya yi, ya ba shi yana karta masa warning sosai ya ce "Dubu biyu za ka bani" Ya ce "Na ƙara maka da ɗari ɗaya"
Mujahid ya girgiza kai ya ce "ÆŠan iskan Almajiri"
Chapter 34 · 0% Book details