Sashe 46
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ridayya ta kasa magana sai wani irin ajjiyar zuciya da take saukewa, a kawo biyar na damuwa da ƙuncin data wanzu da shi tun haɗuwar ta da Zameer yau babu kaso ɗaya. Zainaba ta girgiza kai kawai har yanzu kuka take ita har yanzu tana ɗorawa Ridayya laifi, dukda cewa rayuwa da ƙaddara suna tafiya daidai ne kamar shaƙar numfashi ne da bugun zuciya.
"Wallahi ji nake kamar na ja ki ka zaune na yi miki mahaukaciya dukan kawo wuƙa, to kar na ƙarasa gawar da bata wa ba, amma Ridayya ba ki wa kan ki da Ustaz adalci, ba ki wa zuciyoyinku halacci ba, ina da tabbacin duk sanda Ustaz ya yi baki babu shakka sai ya biki, ya yi miki abinda uba da uwa ba su yi ba, ya raine ki da tafukan hannunsa, ya ciyar dake daga dukiyarsa, ya ba ki ilimi daga baiwarsa, ya ba ki tarbiyya daga cikin abinda ya sani, ya nemi aiki domin ya kula da rayuwarki. Ya yi miki wanka, ya yi miki tsifa ya gyara wannan sumar kan naki mai kama da bishiya, ya goya ki kin zama tamkar bakwaini amma haka zai yi amfani da ɗumin jikinsa domin ki ji shi tamkar cikin uwa mahaifiya, kin yi babban zunubi Ridayya. Da na san abinda kikai masa kenan wallahi tallahi ba zan barshi ya kai ki asibiti gwara kawai ki mutu ya yi jinyar zuciya da kuma mantawa dake bakiɗaya"
Shassheƙar kukan da sai yau ta samu damar yin mai isarta ta ci-gaba da yi tasan ba kowa zai yi mata uzuri ba, ba kowa zai fahimci dalilinta ba.
Zainaba ta ja tsaki tana zabga mata harara ta ce "Wallahi hannuna rawa yake ki daina wannan kukan banzan ko ka kwasa miki mari mtwsss" Ta girgiza kai ta ce
"Samarin yanzu? Wannan gantalalliyar soyayyar da kalaman da mazan zamani ke amfani da shi haka yake ruɗa ƴan'mata fa, musamman a ga namiji fari tas da shi yana saka suttura a tsayar da gemun da wani mai yake shafawa na bana Allah da Annabi bane, da kalaman ƙarya na bugi da zarar ya samu nasarar a kan mace kuma shikenan fa, wata mara kan gadon ma ki na da saurayi amma ba ki san tuni an yi masa baiko da wata ma. Uhm! Soyayya har haukata ɗiya mace na yi tafi talauci barazana ga rayuwar yara mata......,"
"Ai ita ma a haukace take, ta haukace a lokacin" Usman mijin Zainaba ya katse maganar matarsa ta hanyar É—aga labulen É—akin ya zuro kai yana faÉ—a tare da face majina.
"Kai fa Baban Hajjo ba zan taɓa yi wa Ridayya uzuri ba, Allah ɗaya kawai za ta ce mini na yarda. Ka yi tunani idan har Ustaz ya ji labarin abinda ta aikata na yin iskanci da wani ya sai tsinci kan shi? Tsaf zuciyarsa zata buga kwarankwasa"
Ras! Zuciyar Ridayya ta bada sauti ita koda wasa bata taɓa zama ta yi tunanin abinda hakan zai haifar wa Abbiey ba, bata taɓa tunanin kuskure ta aikata ba domin a lokacin mahaukaciya ce ita, ta samu makantar zuciya data kunne aure, soyayya, da Zameer ɗin sune kawai a idanunta.
"Don Allah mu bar maganar nan Maman Hajjo, ki ɗauka ban taɓa faɗa miki ba, don girman Allah kar ki kalle ni da wannan sigar"
"Wannan zunubi kike faɗa kina wasa ne don ba ki san yadda nake jin zuciyata ba, uwa ce ni fa? Wallahi ina miki kallon wacce ta wofintar da kan ta a waje tamkar tsirara haka kike a idanuna" Wani abu ya caki zuciyar Ridayya ta runtse idanunta zuciyarta na yi mata zafi da raɗaɗi na maganganun Zainaba ta san kuma ba ita kaɗai ba duk wanda ya yi da kalar maganar da zai jefe ta da ita take, ta yi kuka har ta gaji a ranta tana karkarta tubalin ginin ƙaddararta da Ahlinta.
Da ƙyar ta miƙe ta yi sallar asuba domin daman ba bacci ta yi ba. Zainaba ta lallaɓa ta tare da cewa ta yi wanka da ƙyar da ta yi domin ita yanzu tana jin bata wata wani saura banda jiran ranar da mutuwarta zata rusketa. Bata tsaya ta ci abincin da Zainaba ta bata ba ta lallaɓa tare da ficewa daga cikin gidan.
Tunda ta fara take tafiya ta ji faɗuwar gaba na tsananta a ƙirjinta, ta dinga addu'a tana jin komai ya kusa zuwa ƙarshen ta kusa isa gida babu mamaki ma ta tarar da Abbiey yana ciki. Ta faɗaɗa murmushinta ganin gate ɗin gidan abu tare da ƙara tafiyar da take zaton sauri take har ta shiga cikin gate ɗin lokacin Maigadi yana cikin ɗan ƙaramin ɗakinsa. Ridayya ta wanzu tana tunanin ina zata fara zuwa wajan Mami? A hankali ta girgiza kai ta nufi ɓangaren Baba ƙarami kai tsaye bedroom ɗin Ustaz ta nufa da siririyar muryarta tana faɗin.
"Abbiey.... Abbiey.... Abbieyna"
Babu magana sai tashin kiÉ—a dake tashi a hankali, direction É—in da ta ji sautin kiÉ—an ta bi da kallo a tsaye ta gan shi gaban madubi ya zage yana taje gemu da mataji farar fatarsa ta sauya sosai daga yadda ta santa a baya ta sake yin fresh. There is a difference between her previous Abbiey and this Abbiey. Domin wannan riga Armless ce a jikinsa ta kama shi, ga gajeren wandon dake jikinsa, idan ya yi tazar sai ya fara goge tsakiyar goshinta kamar Abbiey.
"Abbiey ina ta magana" Ta faÉ—a tana matsa wa inda yake tsaye amma har lokacin bai juyo ba, da alama bata san yana yi ba ta buÉ—e iyakar muryarta ta ce "ABBIEY!"
A hargitse ya juyo yana gwalo Idanu waje saboda tsoro, ta ƙwalla ƙara saboda razana ta yi baya jikinta sai rawa yake tamkar mazari daman ba wani ƙwari ne ita ba.
Ya riƙe ƙugu daman tun safe ransa a ɓace yake ya kalleta sosai ya ce
"Lallai ji mini wata tsohuwar kilaki da alama kece iyar da aka ce za a kawo Æ´ar'aiki sabuwa ko?" Ridayya ta saki baki
Iya? Ta maimaita kalmar a zuciyarta kenan burin Zameer ya cika bai barta da komai na É—iya mace kuma budurwa ba? Ya tatse komai na albarkar jikinta har ta yi kama da tsohuwar da za a cewa Iya? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!.
"Wait wai mene ya kawo ki bedroom ɗina? Na faɗawa Alhji ban buƙatar maid duk ƙazamai ne kamar ke ɗin nan"
"Ina Abbieyna?" Ridayya ta faɗa muryarta na rawa sosai. Ya sake riƙe ƙugu ya ce "Ji rainin wayo waye kuma Abbiey ki shigo har gidan uban cikin ɗakina ki kuma tsare ni da wani ido kina tambayar wani? How dare you?"
Ridayya dai kallon yadda yake zuba masifa hankali kwance take shi kaɗai duk ya hargitsa kan shi. Da sauri wata ta shigo ɗakin Matashiyar mata mai zubin haƙuri da nagarta ta ce
"Lafiya meke faruwa ne tun daga parlour na jiyo wannan muryar taka kullum cikin faÉ—a baka gajiya kamar Dage?"
Ya É—age gira É—aya cur kuma ta tsaya dake cikakkiya ce ya ce.
"How can i know mother? Kawai ta shigo É—akina wai ina Abbiey nata? Na bi Abbiey da gudu ba wando wai banda lalacewa maid ce zata shigo kai tsaye É—akina without my knowledge?"
Wacce aka kira da mother ɗin ta kalli Ridayya tun daga ƙasa har zuwa sama take kallonta kafin ta girgiza kai ta ce.
"Zafin rai Sadauki? Ka dinga yayyafawa zuciyarka ruwa kana shan ruwan alwalar sallar asar"
Sadauki ya dafe kansa ya ce "Kawai ta faÉ—a miki wace ita duniyar nan babu gaskiya mother"
"Wacece ke wa kuma kike nema Æ´ar nan?" Sadauki ya yi caraf ya ce "Wacce Æ´ar? Tsohuwa ce wannan....,"
"Ya isa ya isa Sadauki kar na ƙara jin bakin ka nan wajan" Ya yi shiru kawai yana jijjigata kan shi
"Ya sunanki?"
"Ridayya" Hajja Azizat ta ce "Ohh wakike nema? Kin shigo har cikin gidanmu kin taho É—akin É—ana kin san shi ne?"
"Wallahi bata sanni ba, kawai ki tambayeta me ta zo yi mini" Hajja Azizat ta girgiza kai daman ta san ba shirun zai yi ba, Æ´ar banzar mita gare shi.
"Ina jin ki baiwar Allah"
"Abbieyna na zo nema ai gidanmu ne nan É—in kuma nan ne É—akin Abbiey"
"Kutumar u....,"
"Kar ka ƙarasa ta a kunnena Sadauki" Idanunsa har hayaƙi yake, ya yi ƙwafa yana ɗauke kan shi zuwa gefe. Hajja Azizat ta ce
"Ikon Allah gidanku? Allah sarki to saɓani aka samu domin mijina ne ya siye wannan gidan gabaɗaya idan kin lura mun yi gyara sosai kafin mu tare, wannan ɗin ɗana ne sunansa....,"
"No please mother"
Ya faÉ—a yana haÉ—e fuska tare da girgiza mata kai alamar baya son a faÉ—i sunansa mene haÉ—insa da ita, wayarsa ta fara ringing ya É—auka da sauri a hankali yana cewa.
"She is already here, yes Nadiya" iya abinda ya faÉ—a kenan a É—akin ya fice.
Kuka sosai Ridayya ke yi tana durƙushe wa a wajan hannunta bibbiyu ta haɗe ta ce "Don Allah don Allah karki kure ni a gidan nan wallahi gidan Baffana ne kuma nan ɗin ɗakin Abbieyna ne, ki ji tausayina ki faɗa mini inda Baffa Mami Abbiey suke don Allah"
Jikin Hajja Azizat ya yi sanyi tausayin Ridayya ya kamata amma tasan halin mijinta baya ƙaunar kowa cikin gidansa idan ba su ba. A sanyaye ta ce
"Babu shakka da ina da hali zan taimaka miki da inuwar da za ki shiga ki samu sanyi, ni ma zama nake a ƙarƙashin wani bisa umarninsa nake komai" Ta tausasa harshe ta ce "Komai ya yi zafi maganinsa Allah, ki ɗauka gobara ce ta tashi a cikin kogi Ubangiji ne kaɗai zai yi maganin al'amarin"
Ridayya ta miƙe idanunta ya kumbura sosai jiri na kwasarta don yunwa. Hajja Azizat ta ce "Amma ke kina ina iyayen naki suka bar gidan? Ki kira number su mana idan suna kusa sai ki je" Ridayya bata ce komai ba can ta ce "A wajan wa kuka siyi gidan?"
"Gaskiya bana ce ba domin mijina ne ya san mutumin. Ki tsaya ki yi ƙarya sai ki tafi"