← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 118

Sashe 2

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙit! Ta ji an kashe wayar ba tare da anjira ta kammala magana ba, ta daɗe tsaye tana sake kiran number amma ba'a ɗauka, bata san lokacin data shafe tsaye akan Ridayya ba, idanunta akan screen ɗin wayar, kamar daga sama ta ji an banko ƙofar ɗakin, Zainaba ta yi saurin yin baya bata iya gane fuskar wanda ya shigo ba, saboda ba kowa ta sani a familyn Ridayya ba, tana iya cewa this is the first time ta Idanunta yaga wannan halittar.

BILAL ya tsaya fuska haɗe ganin inuwar mutum, can kuma ya saka gabaɗaya ƙarfinsa ya kinkimi Ridayya da ita, da cikin jikinta kai tsaye waje ya nufa ya sata a bayan motarsa, har zai shiga sai kuma ya tsaya ba tare daya kalli Zainaba dake tsaye ƙofar gidanta ba ya ce "Mi.. mijin nata?" Ya furta da ƙyar yana saka hannu wajan gyara lins ɗin hannunsa, sai a lokacin Zainaba ta kula da jinin dake kwance a goshinsa ta ce
"Ko dana shigo gidan ban tarar da shi ba, ban san yaushe ta kasance a haka ba nima Allah ne ya nufa na zo siyan ƴar tsala a wajanta zan bawa yarinya, jin shiru na shiga ɗakinta na tarar da ita a haka, na yi ƙoƙarin kiran mijinta baya gidan sai wata dana gani a daƙinsa.." hannu Bilal ya ɗaga mata tare da shiga mota da sauri yabar unguwar, Zainaba ta riƙe haɓa ta ce "Ji ƙaddara maganar ma wahala take masa, da shi da Zameer ɗin halinsu ɗaya"
Juyawa ta yi ta shiga gidanta a ranta tana jinjinawa haƙuri da irin makauniyyar soyayyar da Ridayya kewa Meer take.

Bilal tuki kawai yake ba tare daya san inda yake cilla kan motar ba, yasan akan titi yake ya kuma san asibiti yake son zuwa mafi kusa da shi, maganganun Zainaba ke masa yawo a kunnensa, babu abinda ya tsaya masa irin wai ƴar tsala Ridayya take yi? Me Ridayya ta rasa? A kan soyayyar miji ta wulaƙanta kanta har haka? Ta zama abar surutu a dangi da unguwa!

Yana tsaye a reception kansa a ƙasa tun ɗazu da aka shigar da ita Emergency yake kai kawo a wajan daga ƙarshe ya nemi waje ya zauna, inuwar daya gani a kansa ya sanya shi ɗaga idanuwansa akan Mami ya sauke Ammi ya sauke ganinsa ya ɗan rage numfashi Ammi ta ce "Uban masu gidan ya jikin na Auta? Meke faruwa ne?"
Bilal couldn't speak, ya kasa magana ta sake cewa "Na cewa Abdullahi ya biyoni muje shi da Khalifa amma sun ce sun jima da cire hannunsu akan lamarin Ridayya mene ya faru da sassafe? Hajiya Fatima taƙi cewa komai"
Kafin Bilal ya yi magana Dr ya fito yana share zufa, ganinsa ya sanya Bilal miƙewa Likitan ya ce "Kai ne mijinta?"
"Lafiya Dr? Karka ce mana Auta Ridayya ta mutu karka faɗa zaka tarwatsa zuƙata da yawa" Dr ya sake kallon Bilal ya ce "Mijinta ne kai?" Bilal dai kamar an sanya allura tare da ɗinke bakinsa, ya kasa cewa komai banda dokawa a ko wacce daƙiƙa babu abinda zuciyarsa ke yi, sunan Ridayya kaɗai na iya tarwatsa zuciyarsa, jin sunan yake kamar saukar dalma a ƙahon zuciyarsa, ya kasa sabawa da jinsa har yanzu, kalmar mutuwa ita ce ba zai taɓa lamunta ba, ba zai yarda akwai ta idan har akan Ridayya ne.
"Shi ne, mijinta ne"
Ammi ta bawa Dr amsa, Dr ya yarda domin zufar dake goshin Bilal ta gama bayyana masa amsar tambayar shi
"Follow me, _Ku biyoni_"
Ya juyawa zuwa office ɗin Dr ɗin. "Mai suna mu shiga mana" Ya riƙe numfashi da sauri yana girgiza kai bata jira me zai ce ta kama hannunsa zuwa office ɗin.
Dr ya kalli Bilal bayan cike cike a hankali ya ce
"Kai ne mijinta da gaske?" Bilal ya sake shiru Likita ya É—ora da
"Baka da Imani, baka da tausayi, baka cancanci zama mijinta ba, da gaske kai mugun miji ne"
A hargitse Ammi ta ce
"Saurara! Aibatawar ta mece? Kake ƙoƙarin tsine masa bayan bakai cikinsa ba balle haihuwar shi?" Dr ya ce
"Bana da shakka ko tsoro, ya halatta tsinuwa ta tabbata a kan shi, matarka na ɗauke da ciki amma baka taɓa bata ƙwayar magani ba? Sai takura mata ake wajan tarayya? Sexual violence? Gashi abinda ke cikinta ya ruɓe yanzu haka"
Cikin tashin hankali Ammi ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ɗa ya ruɓe a cikin Ridayya? Bamu da labarin bata taɓa zuwa asibiti ba"
Dr ya yi murmushin takaici ya ce "Amma ke uwar miji ce ko Hajiya? Ƙiriƙiri kina ƙoƙarin danne laifin ɗanki? Wallahi da ina da iko maka shi zan a court ni kaɗai nasan halin da yarinyar ke ciki, ga ciwon yunwa daya kamata"
Miƙewa Bilal ya yi yana ganin duhu a idanunsa jiri na neman yar da shi, Ammi ta ce "Bilal!" Bai tsaya ba ta sake cewa "Bilal karka kuskura naga ƙafar a cikin mota balle kayi gigin yin driving"
Sai a lokacin ya juya ya kalleta kafin ya ce
"Ki daina mini ihu Ammi ki daina na roƙe ƙi"
Ficewa ya yi ta kalli Dr ta ce "Yanzu ya ake ciki?"
Ya ce "An yi aikin an cire babyn, Allah ne ya yi da rayuwarta a gaba muna jiran tashin ta ne"
Miƙewa ta yi ta bi bayan Bilal tana zuwa parking space na harabar asibitin motarsa na ficewa, wayarta ta ɗauka ta kira Junaid yana ɗauka ta ce
"Maza duk abinda kake ka baro kasuwa kabi Bilal yana driving hankalinsa a tashe yake kuma"
Junaid ya yi jim kafin ya ce "Ammi ina zanga Bilal yanzu?" A tsawace ta ce
"Da kyau, ya maka kyau ina faÉ—a kana faÉ—a Junaid duk abinda ya samu Bilal zaka sha mamaki"
Wani mahaukacin driving yake kamar zai bar gari, yana jin yau ko zai dauwama a gidan yari a cikin biyu sai dai a yi É—aya, ko Zameer ya kashe shi ko kuma shi Bilal ya kashe Zameer har lahira, idan ya so hukuma ta kashe shi shima.

Page 2

Har wani jan hawaye ne ke kwanciya a idanun Bilal, wanda yake ƙara tabbatarwa da mai kallonsa halin da zuciyarsa ke ciki a bayyane, duk da haɗiye abubuwa daya zama ɗaya daga cikin ɗabi'arsa. Babu abinda yake ɗaga masa hankali irin kalmar sana'ar “Ƴar tsala" da Ridayya take
Meta rasa a duniya? Ta zaɓi miji sama da komai.
Ƙiitttt! Sautin ƙarar haɗuwar motoci biyun ya bayar, cikin saurin driven ɗaya motar ya riƙe nashi kan motar, da hanzari ya ɗago da nufin sauke bala'in dake cin ransa tun a hanya, wanda ya gani cikin ɗaya motar ya sanya bakinsa tsayawa a hangame sai kuma ya buɗe ya ce. "Bilal" A fili kuma da ƙarfi Junaid ya furta hakan saboda ta'ajjujin ganin Bilal gashi a tsakiyar titi amma tunaninsa da hankalinsa ya rabauta.
Junaid ya zuro kansa ta gilashin motar ya ce "Bilal! Bilal!" A gigice Bilal ya dawo tunaninsa yana take motar a fili ya ce
"Su.. Subuhanallahi"
Ya faɗa da ƙyar, sarai; ya gane mamallakin muryar kawai ya zo masa a bazata ne, baya so, da gaske sam baya son kutse cikin lamarin shi, ya daidaita nutsuwarsa har lau bai kalli Junaid ba. "Bilal ina magana ka manshe ni banza"

“Junaid zanci Ubanka, wallahi zanci Ubanka ka sake kiran ko kalmar B balle Bilal ka tsahirta mini" Tun da ya ji Bilal ya yi zagi ya san ba sauƙi, a hankali ya ce
"Girman naka ne idan ka yi zagin ma babu laifi, ka sassauta ka yi parking da motar taka mu yi magana" Junaid ya ware idanunsa akan Bilal.
Bilal ya yi shiru, domin danja ke riƙe da shi dama da tuni ya san inda dare ya yi masa
"Karka ce mini akan Ridayya kake haka, ban yi zaton haka daka gareka ba, ko da kowa a mafarki ne, Ridayya dai? Uhmm!"
Kammala maganar ya yi daidai da bada damar shigewa Bilal ya take giyar motarsa, da sauri Junaid ya mara masa baya, ganin da gaske ba zai daina binsa ba ya sanya Bilal juyawa ya ɗauki hanyar gida kai tsaye. Bilal na zuwa ya fita daga cikin motarsa, daidai nan Junaid ya fito yana faɗin "Don Allah ka saurare ni, Ammi ta turo ni, kai ba a iya gane halin da kake ciki balle hukuncin da zaka ɗauka" Bilal ya tsaya yana ware idanunsa akan Junaid, wata kalar dokawa zuciyarsa ke masa baya ƙaunar jin maganar da duk ta shafi Ridayya. A fili ya ce

"Junaid ka haife ni ne? Shayar dani kake? To; tun kafin na fasa maka baki ka saurara mini"
Ya shige bayan kammala maganar, sashin Baba ƙarami ya nufa, Junaid kuma ya shige sashin su Ammi. Tunani fal a ransa na abubuwan da suke faruwa a rayuwar Ridayya.

Zameer tun sassafe bayan dawowa daga masallaci ya shirya tsaf cikin yadi mai laushi ya yi kyau sosai, kwarjinin da nutsuwarsa ta bayyana a fili, asalin kyansa wanda yake ƙara narkar da zuciyar Ridayya ya fiddo kansa da kansa, wani sahihin kyau ne da shi wanda sai ka nutsa zaka gani, baya da hayaniya a kame fuskarsa take koda yaushe. Yana ɗaura lins ɗin rigar Khairy ta dube shi sosai sai kuma ta ce
"Meer fita zaka yi ne?"
Ta furta a kasalance, wanda hakan ya yi tasirin wajan Meer, duk yadda yake kokawa da kansa wajan ganin ya gujewa kallonta haƙarsa bata cimma ruwa ba, zuciyarsa ta sanya ƙafa tare da shure gargaɗin na Meer, yana riƙe kansa ba tare da zato gabaɗaya yaga idanunsa kwance akan kyakkawar fuskarta fara tas da ita, irin farin da yake so.
"Kina zalunta ta Khary,
Karki sa na sake aikata abinda ban shirya ba"
Khairy ta juya idanunta, fuzga numfashin Meer ya fara a gaggauce, ya juya mata baya.
"Idan ka fita dame zan yi breakfast?" A taƙaice ya ce "Ina raguwar Indomie dana kawo miki katan guda?" Ta ce
"Saura biyu, ƙwan ma haka" Yana ƙanƙance ido a wannan karan duk nacin zuciyarsa ya yi alƙawarin bazai taɓa juyawa ya kalli Khary ba
"Indomie biyu Khairy bai isa ba? Bai isa ba Khairy?" Ta miƙe tsaye, daga ita sai kayan bacci.
Chapter 2 · 0% Book details