← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 118

Sashe 105

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba ƙaramin gigicewa Ridayya ta yi ba ganin gawar Sadauki a gabanta, a ƙasar da babu kowa nasa ba uwa ba uba, ba ƴan'uwa hatta ita kanta bata da kowa wanda ya shige Ustaz gashi kuma yabar ƙasar ya koma Naija? Ta rasa mafita sai kuka take tana girgiza shi ta fita hayyacinta sosai gani take tamkar ita ce silar mutuwar Sadauki "Don Allah ka tashi karka zama ragu a soyayya shin ba ka ji sunanka bane Sadauki? Ya zan yi dakai a ƙasar da bamu da kowa ka farka don Allah na san suma ka yi soyayyata ba zata taɓa zama ajalinka ba..." Sosai take kuka ga wani abu daya tukare mata a ƙirji. A kusan tare wasu manyan motoci guda biyu sukai parking a gefen Ridayya da kuma Sadauki dake kwance baya ko motsi, ta cire idanunta gabanta ya faɗi ganin bata gane mota ko ɗaya ba, a hankali aka buɗe motar farko wacce ta kasance ash wani matashi ne wanda zai iya girman Sadauki ya fito daga motar, fuskarsa sosai ta nuna tashin hankali ya ƙarasu wajan yana kallon Ridayya da Sadauki kafin ya ce

"Me ya sa ya kwanta a ƙasa what happened to him?" Ridayya ta kasa cewa komai idanunta duk ya jime saboda fargaba Riyad ya nisa ya ce "Kece Ridayya? Naga lafiya ya fito ya ce wajanki zai zo, daman hankalina bai kwanta ba tunda kwana ya yi jiya bai runtsa ba, ya kira number Mother sun yi magana, ya kira mahaifinsa kuma more than 30 miss calls bai ɗauka ba, don Allah ki sassauta kukan ki mini bayanin abinda ya faru in briefly" da ƙyar ta ce "Ka fara duba nunfashinsa ka ji ko yana raye" sai a lokacin Riday ya lura da rashin bugawar zuciyar Sadauki ya nufe shi kasancewar shi Dr ya fara duba shi hankali tashe.

Tsaye ya yi a kanta tun bayan fitowar shi daga motar, hankalinsa ya ji yaƙi kwanciya har ya je airport kawai ya saka aka dawo da shi, sai dai bai yi tsammanin ganin abinda yake gani ba, ya shanye damuwar dake ƙoƙarin bayyana a fuskarsa ya ce "Ridha.." jin muryarsa ya saka ta miƙe har tana ƙokarin faɗuwa ya yi saurin taro ta gefensa tana ganinta kusa da shi ta faɗa jikinsa ta fashe da kuka sosai "Abbiey na shiga uku na shiga uku Abbiey na kashe Sadauki" Ustaz ya kasa cewa komai sai bayanta da yake bubbugawa a hankali alamar rashin, deep down na zuciyarsa addu'a yake ta yi ga Ubangiji ya tashi kafaɗun Sadauki sosai al'amarin ya shige shi ya kasa furta komai Dr Riyad ya goge zufa ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, Allah gare ka muke kuma gare ka zamu koma Ubangiji ya sanya can tafi nan sannu da aikin bauta Hamza Allah ya yafe maka" kalaman shi suka daki Ridayya da Abbiey ta ƙara rikicewa ta riƙe Ustaz da kyau shi ma ɗin riƙe ta ya yi gudun kar a yi biyu babu. Abbiey wayarsa ya ciro ya kira number gidansa wacce ta sada shi da Maid Ilhas, magana ya yi a gajarce kana ya kashe kiran. Hannun Ridayya ya kama zuwa mota ya yi wa Dr Riyad alamar ya jira shi a nan wajan, rarrashin Ridayya ya fara cikin kulawa da soyayya dukda kasancewar jinta a jikin Ustaz yana yaye mata abubuwa da yawa amma yanzu ta gagara nutsuwa gani take idan Sadauki ya mutu tamkar ita ta kashe shi. Addu'a ya shiga yi tana maimaitawa suna a haka mota ta sauke Ilhas ya fito ta yi saurin cewa "Good day sir!" Ya jinjina kai yana ɗauke idanunta can ya ce "Ki kula da ita, ku kasance tare ok"

"Yadda ka ce in sha Allah" motar ta shiga driver ya ja su zuwa gida shi kuma kai tsaye ya nufi wajan Dr Riyad ya ce "Me kake son cewa? Who are you?"

"Sadauki's friends" Dr Riyad said yana goge hawaye ya ɗora da "Allah ya yi masa cikawa kuma ina da tabbacin bugawar zuciya ce na farat ɗaya amma zamu je asibiti na ƙara bincikawa" MB USTAZ ya ja numfashi ya fesar "No need, zamu shige Nigeria yanzu" daga nan ya fara neman number wayar Tajj Baita gabaɗaya bai san yadda iyayen Sadauki da shi kansa Tajj za su fahimci wannan al'amarin ba. Kasancewar abu ne na manya ya sanya cikin awa guda suka samu jirgin da zai ɗaga dasu, da BM USTAZ da Dr Riyad sai gawar Sadauki daman tuni ya yi waya da Tajj ya masa bayanin komai kasancewar Abbiey bai iya ƙarya ko ɓoye magana ba, yana da zurfin ciki amma ba a komai ba.

Hajja Azizat na zaune ta yi zuru tana sauraren yayarta mahaifiyar Tajj tace "Yaya ban san meke damuna ba, kawai na ji bari na kira ki ko zan ji sanyi a raina, gabana faɗuwa yake sosai wallahi, gidan ya mini girma idan na kira Professor bana samun shi sama da sati ina son na faɗa masa al'amarin Sadauki" daga can ɓangaren Mahmah ta ce "Hajja Azizat ki yi haƙuri komai zai zama tarihi in sha Allah, yaushe Sadaukin zai dawo I'll talk to him zan masa bayanin yadda zai gane ya fahimta ya kuma yi tawakkali" Mother ta sauke ajjiyar zuciya tare da goge hawayen idanunta ta ce "Nothing goes well Yaya, Sadauki yana da ƙulafuci, kafin ya fita sai da ya bi mahaifinsa office domin ya ji matsalarsa da rashin son zama cikin iyalansa, lafiya ya fita amma daya dawo ban gane kansa ba, ya dinga ce mini na yi haƙuri da rayuwa da amshi ƙaddara a yadda ta zo mini da Prof da babu duk zan iya rayuwa, kuma karna bari wani abu ya sake shiga tsakanina da Prof, Yaya hankalina ya tashi na rasa gane me Sadauki yake nufi ban san kuma mene ya je ya gani wajan mahaifin nasa, main reason ya haɗu Ridayya kuma kin san tana da aure, ina guje masa fushin Ubangiji Yaya kuma ina jin tsoron faɗa masa gaskiyar lamarin na gaji na gaji Sadauki shi ɗaya nake da shi, zaman gidan babu daɗi" Sosai Mahmah ta tausayawa Hajja Azizat ƙanwarta cikin rarrashi take ce mata "Azizat kin yi haƙuri komai zai shige kowa da tasa ƙaddarar mumunin mutum Ubangiji baya barinsa haka nan. Ni da kaina zan fahimtar da Sadauki da zarar ya dawo Prof kuma ki masa uzuri ai kince ayyuka sun masa yawa, ga sabgar siyasa banda an ɗaga Elections ɗin da tuni an yi komai mai rabo ya samu, ba ki rasa komai ba"

"Yaya buƙatun ƴa mace ba iya ci da sha da suttura bane, kawai dai abar tunawa zan ta addu'a shi kuma Hamza Allah ya yaye masa son Matar auren, ai masifa ce wannan kuma jarrabwa babba" Mahmah daga nata ɓangaren da take zaune a saman kujera Nadra na kusa da ita tana bacci, ƙoƙarin magana take kamar daga sama taga Tajj ya shigo yanayinsa ya mata daban ta ce

"Ya zaka faɗo mini a gigice kamar kurarre lafiya? Wani abun ne kuma Deen?" Ya kasa magana sai zufa yake sharewa idanunsa sun yi jajur, dukda rashin jituwa da suke da cousin brother ɗin nasa amma sosai yake jin Sadauki a zuciyarsa, ya sha ɗaukar waya da niyyar kiransa just to find out if he is ok, daya tuna rikicin shi sai ya fasa, babban dalili a maza bashi da ɗan'uwa wanda ya shige Hamza, taya zan iya fuskarta Anty ya ce mata Sadauki ya rasu sanadiyyar bugawar zuciyar farat ɗaya, dalilin mace kuma a ƙasar daba ta shi ba? Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun! "Wai lafiya ina magana zai zufa kake ji idanunka kamar zasu shige don tashin hankali"

"Ƙaddara ce ta same mu wacce daman tana kan kowa Mahmah"

"Ƙaddara? Aikin ka rasa ko asarar dukiya ka yi" a rauna ce ya ce "Gwara na rasa aiki da dukkan abinda na mallaka da na rasa abinda na rasa a yanzu Mahmah, iya faɗan da muke da Sadauki ya wadatar dani yanzu dawa zan dinga yi?...," Mahmah ta ji cikinta ya juya gudawa na neman zubo mata ta yi baya kamar zata kifa ta ce "Mene ya samun Sadauki"

"Allah ya amshi abinsa, a inda bashi da kowa sai wani jinin nada ban, mun rasa Sadauki Mahmah Sadauki ya rasu" Salati kawai Mahmah take idan ta kamo wannan sai ta saki ta gigice ta fita hayyacinta lokaci guda, Tajj ya rasa ya zai yi ya ce "A'a Mahmah wannan bai dace da Sadauki ba, addu'ar da kika fara ita za ki ta yi in sha Allah yana cikin aminci zai kasance É—aya daga cikin samarin Aljanna wanda Ubangiji yake alfahari da su"

Ta share hawayen da yaƙi tsayawa ta ce "Taya zan faɗawa Azizat wannan al'amari? Ya za mu yi?" Tajj ya ce "Faɗa mata ya zama dole, amma nima ba zan iya ba wallahi tsoro kallon idanunta nake na ce Hamza ya rasu" Da ƙyar Mahmah ta iya controlling kanta ta kira Mother tana ɗagawa ta ce "Ki zo gidana yanzu"

"Yaya lafiya?"

"Ki zo na ce"

"Ban tambayi Prof ba Yaya, bari na kira shi idan ya barni sai na zo"

"Ƙarama meke damunki ne? Wacce kalar biyayya ce haka? Kin san girman dalilin daya saka na kira ki? Sai kin tsaya kiran Prof?"
Chapter 105 · 0% Book details