Sashe 103
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ɗauke idanunta domin yana da murya mai sanyi gashi daman rashin kulawar iyaye da masifar talauci ya saka ya shiga halin da yake ciki "Mene gaskiyar lamarin?" Nan take ya warware ko wanne ƙulli da Ammi ta ƙulla bai ɓoye komai ba, domin yana da faɗar gaskiya bashi da tsoro Baffa yana jin komai sai jiri ya fara ɗaukar shi ya saurin riƙe kansa da sauri ya juya zuwa part ɗin Ammi tana zaune ta yi zuru-zuru tun bayan faruwar tunan asirinta Baffa bai ce komai ba, tana tsoron matakin da zai ɗauka da sauri ta miƙe tsaye ta ce "Baffa lafiya?" Wayarsa kawai ya danna yana ta tsaye idanunsa akanta wajan mintuna 15 aka kira shi ya ɗauka ya ce "Su shigo" Polices ne mata guda huɗu ya kalle su ya ce "Arrest her" Ammi ta ce "Baffa police ne fa me na yi matarka ka saka a kama?" Ya juya baya ya ce "Take her out please na sake ki Hajiya Maryam, ta faɗa muku abubuwan data aikata mini nida yarana idan taƙi ku yi ta dukanta" Yana faɗar hakan ya fice Ammi ta zumduma ihu sosai tana kuka ihu da kururuwa kafin ta sulale a ƙasa ba numfashi haka suka ɗauke ta zuwa waje Baba ƙarami bai san meke faruwa ba haka Mami Yaya Zuhura daman ba ruwanta da Ammi Burhan ko a ƙafarsa ta Zainura kawai yake Baffa ya nufi ɗakin Mami tana riƙe da junior Baffa ya shigo kafin ta yi magana ya rungume ta tare da fashewa da kuka mai tsanani. Mardiyya ta dinga tunanin yadda BM USTAZ zai dawo har ta samu kusanci da shi kuma ta dangana masa alhakin zama uban cikin jikinta, dabara ta ƙare mata gashi tana gab da haihuwa ne a ranta kuma take jin yanzu ta fara zama da Muhammad Bilal ba zata ta bari kowacce mace ta raɓe shi ba.
Suna tsaye gabaɗaya a harabar makarantar Zameer na gujewa ganin Tajj burinsa ya sake samun dama ya koma wajan Baba ƙarami ya lafta masa wata ƙaryar da dole zai saka Baba ƙarami ya bawa Ustaz umarnin sakin Ridayya shi kuma ya saka ta dawo gidansa zai lallaɓata da soyayya irin wacce ya saba yi mata a baya. Daga nesa suka ji ana cewa
"Gashi can aradun Allah hene mijina ne Allah ya kawo ni Kano" Ta faÉ—a tana tisu kewar wani yaro wanda suke shekaru É—aya da little Bilal ga wata yarinyar itama a baya ta yi yarkace kace zani na neman faÉ—uwa Moo ya ce "Wancan fa kika ce wancan ai mijin Ridayya ne"
Ta zabga salati tana yagalo yarinyar daidai nan Zameer ya fara ƙoƙarin guduwa ya ji an tare shi ta gaba ya buɗe idanu ganinsa ya sauka akan Khairy itama hannunta riƙe da wata baƙar yarinya ta sha bille taya-taya a fuska ga leɓen yarinyar ya sakko ƙasa suka saka Zameer a tsakiya......
A yi haƙuri a yi haƙuri Please...... A tsitsita haka nan a tausasa zuciya 🤓 ko editing ban ba bear with the errors and spelling mistake.
*_MUNAFUKIN MIJI_*
..... Nimcyluv
44
Ya kalleta ya ce "what brought you here Khairy?" Ta juya idanunta tana nuna shi da hannu ta ce "Lallai so are you questioning me? Ba ka yi expecting ganina ba ko?" Ya haɗe fuska ya ce "I have no reason da zan buƙaci ganin ki balle na yi expecting zuwan naki" Khairy ta yi wani irin ciji baki jin wani rainin wayo na Zameer ta ce "Oh really? Is that so haka ma za ka ce kodayake ban yi mamaki ba mutumin ƙauye kuma bakatsine ɗan Fulani ba tsiyar da ba zai iya tufkawa ba, musamman ta wajan mugunta" Ta juya ta kalli Hanne dake tsaye yarkace kace ta kalli ɗanta Harazimi wanda duk ya fice daga hayyacinsa ba zaka taɓa cewa rana ɗaya aka haife su tare da little Bilal ba. Yarinyar hannunta ta dire masa a gabansa ta ce "Kaga dalilin zuwana, bayan na haifeta ba zan iya ci-gaba da zama da ita ba, domin ko nono bata taɓa shaba ba zan iya dakon wahala ba" da wani irin expression Zameer ya dinga kallon Khairy without saying a single words, sosai kalaman Khairy suka saka masa wani irin gigita ya fara goge zufa domin shi rabon shi da ita tunda ta taka tun daga Kano ta iske shi har garin Katsina ƙauye Nahutu dake Batsari, amma shi ne zata kawo masa wata yaƙunanniyyar yarinyar kamar ƙarshen duniya ta ce ƴar shi ce? Mahaukaci ta mayar da shi kenan. Ya yi murmushi ya ce "Khairiyya Please ki faɗa mini mene ya kawo ki bani da lokaci"
"Hehehe sai ka ce mai aikin gwamnati ko wanda yake rolling babban kamfanin babansa, banda aikin banza da zaman kashe wando babu tsiyar daka iya, sai shegiyar ƙarya kamar me ga fake life kamar jinin ƙaruna, wai Zameer Mahboob Dollar ai kowa naga dollars ganin idanuna a gona, wallahi ka kiyaye ni ba Khairy daka sani bace, kuma ni ba irin Ridayya ba ce for sure don ma ka ji" Zuciyarsa ta buga tana neman tarwatsewa a ƙirjinsa da ƙyar ya iya controlling kansa domin bashi da wata power ga yadda friends ɗinsa suke kallansa ya ce "Ki yi komai ki ce komai amma karki sake sako sunan matata a nan wajan, domin ita ba irin ki bace Khairy kuma kika yi wasa yanzu zan sauke miki yatsun hannuna a fuskarki" Khairy ta ware idanu ta ce "Yau nake ganin ɓatan nono a ƙirjin budurwa wanne dare ne jemage bai gani ba? Wanne kalar cin mutumcin da cin fuska ne ba ka yi wa Ridayya ba saboda ni, ka dake ta, ka ƙona mata fuska, ka karyata a hannu saboda ta gane ina ɗauke da cikin da ka yi mini kuma a cikin gidan aurenta na sunna,har na gama zamana a gidan ta rayu ne da tunanin ni ƙanwarka ce, ranar da na kai maka shegen ɗanka dana haifa a Katsina ta san komai a take ta yanke jiki ta faɗi naƙuda ta kama ka, ina cewa a garin naku ma mayya suke ce mata saboda muninta da baƙar fatarta, wanne mataki ka ɗauka eh? Ai wallahi tallahi masifu yanzu ka fara gani ita kuma mayyar bata san darajar kanta bane shi ya saka ta manne maka har yanzu" Tana faɗin haka ta sake tura masa yarinyar dake kuka tana share majina baki har kusan kunne ga uban leɓe an yi mata wani tsagu a fuska fuskar nan sai naso take tamkar an shafa mata soda ta ce "Ƴarka ce uwarka na yi takwara gata nan ana ce mata Deluwa, and please daga yau babu ni ba kai har gaban abada bana son yaran ciki daman kai ka yi shi ina son na yi free domin ban son ƙaddararka ta shafe ni Giɗaɗo"
Kamar statue haka Zameer ke kallon Khairiyya yama kasa tunanin komai da ƙyar ya ce "Ki ji tsoron Allah Khairy na san cewa namijin ɗana ne amma wallahi tallahi bani ne uban yarinyar nan ba, ki dube ta ki dube ni babu ta inda mukai kama da wannan yarinyar, wallahi ki nemi ubanta tuntuni" Ta juya idanu ta ce "Matse maka ta yi wallahi ina da abinda zai saka ka tafi gidan yari for life har mutuwa, ba wai blackmailing naka zan ba, and this is my final decision bani ba kai" Zufa ce ta dinga yankowa Zameer ganin gininsa na neman rushewa shegu har biyu ya shiga uku ya zai yi dasu? Ya dinga kallon yarinyar da ƙyanƙyami a fuskarsa gashi kamar wacce ta san shi sai manne masa take Harazimi ma ya matsa kusa da shi, ga yarinyar wajan Hanne ya shiga uku! Yara har uku amma babu na zaɓe gashi yana ji yana gani an ƙaƙaba masa yarinyar da bashi da alhakin samar da ita.
"Wai Zameer meke faruwa? Daman abinda kuka aikatawa Ridayya kenan kai da Khairy? Taya Ubangiji ba zai jarabce ka ba, na sha baka shawara akan abubuwa da kake gashi yanzu wankin hula na neman kai ka dare, a cikin gidan aurenka ka yi zina da wata matarka ta sameka turmi da taɓarya har ta rufa maka asiri kuma ka ci-gaba da zaluntar ta? Akan karuwarka ka fifita matarka ta sunna? Yanzu ka dubi yaran da suke gabanka da sunan naka? Wacce kake ganin matsayin mujiya bora a cikin mata mummunan ita ta haifa maka kyakkyawan yaro, wanda kake ganin sun fita kuma ka abinda ka shuka nan ka girma, ba a kushe halittar Ubangiji wannan ya zama izina gare ka" Khalid ya ce "Wannan shi ake kira da baƙar tukunya mai fidda farin tuwo, ƴar baƙa mummunan da haifar kyakkyawa, sai na ji ni baƙar macen wallahi ta fiye mini fararen nan sosai" idanun Zameer ya sauya ya rini maganganu Shaba sun masa zafi kamar ya watsa wuta a ƙirji ya ce "Khalid karka sake aibata mini mata wallahi zanci uban daya kawo ka duniya yanzu"... "Ni kake zagi akan gaskiya? Ina cewa kai ka fara aibatata a gabanmu eh? Da sanda ta fara cewa tana sonka wanne kalar zagi ne baka yi mata ba? Kuma...," bai ƙarasa sauran maganar ba Zameer ya kai masa naushi a baki tuni bakin ya fashe jini ya fara zufa ya ƙara kai masa duka
"I love my wife, ina son matata Ridayya har gaban abada yanzu na fara son ta, ina jin kuma son ta ne zai zama ajalina wallahi akan ta sai na iya kashe ka muddin zaka ci-gaba da abinda kake faÉ—a a kan ta"
"Ni ka daka?"
Zameer ya ɗaga shoulder ya ce "Na daka ɗin ka ƙara cewa uffan akan mai sona" Khalid ya wani irin murmushi yana tare jinin dake zuba ya ce
"Ka yi kuskure baka san waye ni ba, you have no idea na abinda zan maka amma wallahi tallahi sai na yi bugu, bugun da zai taɓa zuciyarka ta fashe nan take ka mutu zaka san waye Khalid"