← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 118

Sashe 115

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanaki biyar da dawowarsu Nigeria Ridayya ta shirya zata asibiti a ƙara duba jikinta tana sanye cikin ash ɗin Abaya ta yi rolling kanta sosai ta yi kyau ta ƙara cika da buɗewa, hankalinta ya kwanta ga kulawar da take samu a wajan Mami da Yaya Zuhura da Anty Kaltum, domin sosai Anty Kaltum ta tura Maiduguri aka amso mata tsumin mai jego hakan ya saka Abbiey daƙulewa ya rasa abinda ke yi masa daɗi, har baya so Ridayya ta ƙarasu kusa da shi sosai yake gigicewa, gashi baya da sukuni a gidan yana ta sauri su koma gidansu domin an kammala komai na hadaɗɗan gidan. Dawowarsa kenan daga duba babban boutique ɗin da yake haɗawa da Sunan Ridayya, business yake sosai kuma Ubangiji ya saka masa albarka dukda cewa Fidelity bank suna ta masa requesting ya dawo amma ya nuna bai son aikin bankin yanzu. A hankali ya juya tare nutsa ganinsa a kanta ta yi masa murmushi shi kuma ya kame fuska sai kallon ta yake har ta ƙarasu kusa da shi ta zauna tana sake kyakkyawan murmushi a hankali ta saka hannu ta shafo gemunsa ta ce.

"Barka da hutawa Abbiey"

Ya É—auke kai yana mayar da idanunsa saman laptop ganin hakan ya saka ta marairaice fuska ta ce "Me na yi kuma?" Still ya yi mata shiru wayarsa ce ta fara ringing suka kalli wayar lokaci guda sunan Muwahib ya fito, Ridayya tai shiru tana tunanin ina ta san sunan?. Ustaz ya gyara zama yana matsar da laptop É—in tare da É—aukan kiran a taushashe ya ce.

"Kina lafiya Wahib?"

Ya faɗa bayan amsa sallama ɗin, Ridayya gabanta ya faɗi who is Muwahib? Da har Abbiey ya bata dukkan attention ɗinsa haka? Bata san me take ce masa ba sai gani ta yi ya miƙe yana ɗan jan gemunsa ya ce.

"Ohh, i will come"

Ya kashe kiran kana ya kalli Ridayya da kanta ke ƙasa ta yi nisa cikin tunani sai ganin shi ta yi ya duƙa gabanta tare da tallafo fuskarta a tafin hannunsa taƙi yarda ta kalle shi ya kai baki ya sumbaci lips ɗinta ta yi saurin janye fuskarta

"Ina za ki?"

"Asibiti"

Ya haɗe girar sama data ƙasa yana sake matsar da fuskarsa dab da nata tare da sauke mata nunfashi ƙamshin bakinsa na shigar mata hanci a hankali ya ce "Wa kika tambaya"

Muryarta na rawa ta ce "I toot i told you"

"Ko?" Ta yi sauri ta miƙe ta ce "To na fasa, ka je kiran Wahib ɗin"

Ta juya zuwa bakin ƙofa ta fara ƙoƙarin buɗe ƙofar zata fita hawaye tuni ya fara cika idanunta tana gani dishi-dishi saboda tsabar kishin daya mamaye idanunta tana tsaye ta ji ya zuro hannunsa ta baya ya saƙale ƙugunta tare da haɗe shi a nasa, ya rungume ta ta baya ya ɗan ranƙwafa ya ɗora kansa a kafaɗarta ya ƙi cewa komai sai kawai ta fashe da kuka tana doke hannunsa, ya sake matseta a ƙirjinsa da kyau, he just trying to explain to her, wace Wahib and who is she to him, taƙi yarda ta ji sai kuka take ai kowa ya nuna mata da wayo, ya kinkimeta gabaɗaya ai kowa da sauri ta riƙe shi ta ce

"A'a don Please"

Ya matse ta jikin bango ya ce "Ok listen" ta ce "Oh oh ok"

Ya ƙura mata she just love her, yana tsananin son matarsa bawai tsoron ta yake ji ba ko shakkata ba, baya son damuwa da ɓacin ranta musamman abinda ya san shine da laifi, haka yanzu bai ma san dalilin daya saka zai yi mata explanation ba.

"She is my ex"

A gigice Ridayya ke kallon shi jin abinda ya ce, ya ɗage mata gira idanunta ya sake cika da haway yana shafa mata fuskarsa ya ce. "Ina son aurenta ne beb" kallonsa kawai take babu ko ƙiftawa ƙirjinta na ɗagawa kamar mai Asthma cikin sauri ya ce

"Kee wasa nake miki, É—alibata ce ta ma yi aure mijinta ne ba lafiya take neman taimako"

"Ka aure ta mana"

Ta faɗa zata shige ya ƙara damƙo ƙugunta ya haɗa da nasa idanunsa ya sauya "Da gaske nake miki Allah" nan da nan ta fashe da kuka kamar ranta zai fita tana yarfe hannu

"To ka aureta mana ai ban hanaka ba ban isa kuma na ce a'a, daman na san ba sona kake ba, u just manage kawai daman ban cancanci ka aure ni ba, ƙaddarar su Al'hussan ya saka ka taimake ni ne kawai kamar yadda ake cewa ni dai na son ina son ka amma don baka so ni ba wani abu bane it's all my fault"

Ba iya jijiyoyin kansa ba, hatta gargasar jikinsa ta gama miƙewa gabaɗaya ya jima tashin hankalinsa bai bayyana ba ƙarara irin yanzu ba, so daman auren under age haka yake? Mutum da girmansa da gemunsa da shekarunsa ƙaramar yarinya like Ridayya ta yi ƙoƙarin sukurkuta masa tunani da lissafi domin tashin hankalin daya shiga ya ninka nata. Ya dafe kansa kana ya kamo hannunta har zuwa bakin gado ya zaunar da ita saman cinyarsa ya riƙo tafin hannunta ya sarƙe da nasa ya kasa cewa komai ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tana shassheƙar kuka wanda duk na ƙarya ne kukan banza ne kawai, ya sauke numfashi.

"Ustaza"

"Abbiey"

Ya juyo da fuskarta ya É—ora goshinsa a kan nata ya ce "I am sorry ok?" Ta jinjina masa kai ya haÉ—e rai ya ce "Talk"

"Na bar Al'hussan zazzaɓi yake"

"Ok ki shirya I'll drop you off beb" ta jinjina kai tana miƙewa ya miƙe shima ya rungume ta.

"I love you beb"

"Thank you"

Ya ware idanu "Are you still angry with me? Ni me zan yi da mace bayan ke? Kin isheni kin kuma wadata ni da komai, soyayya, biyayya anything Mimi ai ba wata bayan ke no one but you Mintyna"

"Uhm'uhm" ta ce cikin shagwaɓa tana turo baki wanda ya sha lipstick. Ya girgiza kai "Allah ya yafe miki Mimi"

"Amin"

"I love you "

Kutunsa ta sumbata ta ce "I adore you"

Ita ta yi driving nasu zuwa asibiti ya ce sam ya gaji, yana riƙe da Sadauki Zainura na baya ita da little da Al'hussan a hannunta Al'hassan sai bacci yake a cikin wani ɗan ƙaramin gado. Bayan sun ga likita suna ƙoƙarin fitowa daga emergency Ridayya ta ji ana "Me haƙuri me haƙuri" da wani irin murmushi ta juya domin ba zata taɓa mance muryar ba, Abbiey na jingine da mota yana kallon su "Wa zan gani kamar Zainaba?"

"Ni ce nan mai Æ´artsala ikon Allah rai kan ga rai" Ridayya ta yi murmushi suka gaisa cikin farinciki ta ce "Ina mijin naki, wai da gaske kece haka mai Æ´artsala?"

Ridayya ta yi mata pointing É—in Abbiey ta ce "Ga mijin nawa can da yarana"

Da sauri Abbiey ya ɗauke kansa kamar bai gansu ba, Zainaba ta zare idanu ta ce "Lillahi wadihul ƙahhar Allah alhakamu, wancan ba shine kikaiwa iskanci kala-kala ba? Ina Zameer ɗin?" Ridayya ta haɗe rai ta ce "Kin jiki da wani zance?"

Zainaba ta yi ƙasa da murya ta ce "To kin bashi labarin abinda ya faru da jami'a kafin aurenku da tsinannen nan?" Ta girgiza kai ta ce "A'a, ina so ya san komai amma" Zainaba ta zare idanu ta ce

"A'a sam kar ki soma, idan Allah ya rufa maka asiri sai kace zaka tunawa kanka? Wallahi ki gode Allah Ubangiji ke son ki da Rahama tunda har ya rufa miki asiri ki yi shiru da bankin, ai idan Allah bai so kunyataka a idanun duniya ba babu wanda ya isa ya yi haka, Allah ya duba zuciyarki ribatarki akai bada sunan iskanci kika je ba" Ridayya ta yi murmushi ta ce "Ga numberta idan na tare a gidana sai ki zo" "Ai kowa in sha Allah za ki ganni faka-faka"

"Mai sona"

Da sauri ta juya ganinsa a wannan halin ya saka Ridayya waro idanu ƙirjinta na bugawa, kafin Zainaba ta yi magana ya zube ƙasan qiwwarsa ya ce "Don Allah ki ji tausayina ki yafe mini Mai sona, karki bari na zauce a tunaninki a zuciyata ki tausaya mini"

Moo ya ƙarasu wajan ya ce "Wai Zameer mene haka? Ba zaka ɗauki ƙaddara bane kai? Aurenta zata kashe ta dawo wajanka?"

"Ba wani aure da ta yi kawai an faɗa ne domin a rabani da ita, a hukunta ni akan kuskure da wawta tare da son zuciyar dana tafka" Zainaba ta taɓe baki ta ce "Jama'a yau ga Zameer a lalace? Ina ita shegiyar yarinyar Khairy take kowa?" Moo ya ce "Ai ita muka zo dubawa, ta yi hatsari ne ga matsala data samu har an cire mata mahaifa ba zata kuma haihuwa ba, shine ta buƙaci ganin Zameer ya yafe mata kan sharrin da ta yi masa na kawowa masa yarinya bayan ta san ba shine ubanta ba, ta buƙaci ya bata yarinyar shi kuma ya ce ba zai bayar ba ya dai yafe mata, kema ta roƙi daki yafe mata"

"Ina ruwana da ita? Allah ya yafe mana bakiÉ—aya"

"Ridayya don girman Allah ki dawo gare ni wallahi mutuwa zan yi" daidai nan Ustaz ya ƙarasu wajan hannunsa ɗauke da little Bilal, yana zuwa Zameer ya yi saurin buɗe idanu yadda kasan photocopy akai na Ustaz a fuskar little kamar ya yi kaki ya tofar, Zainura ta ƙarasu wajan hannunta ɗauke da Sadauki da Al'hussan. Zainaba ta gai da Abbiey ya jinjina kai ya kama hannun Ridayya suka bar wajan "Daman taya kake tunanin zata dawo wajanka kamar ita ta zalunce ka? Ai kai da ita sai dan irin wannan ganin daga nesa yasin" Zainura ta ce "Wallahi, wannan yaran nata ne ƴan'uku ta haifar jajur" tana faɗin hakan ta bar wajan itama. Hawaye ya shiga sakkowa a fuskar Zameer Hanne bata ganin girmansa ga yaransa sai addu'a musamman macen, ga babu aiki sai zuwa gona abokai duk sun guje shi Moo kawai ya rage da ace Ridayya na gefensa da komai mai sauƙi ne a gare shi, zaman Kano ya fi ƙarfinsa Ridayya ta fi ƙarfinsa a yanzu duniya ta tabbatar shi ne ya zalunce ta tunda Ubangiji ya yi mata sauyi a rayuwa.
Chapter 115 · 0% Book details