← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 118

Sashe 45

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu ya saka ya figo gefen hijabinta ya kafe ta da Idanu hasken fatar jikinta yana damun idanunsa ta masa haske da yawa da yatsa ya saita mata hanyar waje ta yi saurin ficewa daga cikin gidan. Ustaz ji ya yi ciwo na neman kwantar da shi domin ko tsaiwa ya gagare shi hakan ya sa zai bar Kanon bakiÉ—aya.

Ana saura kwana ɗaya ɗaurin auren Anuty Kaltum ta diro gidan ita da Yaya A'isha faɗa suke kamar za su daki Mami sai kuka take ranar an yi tashin hankali a gidan Alhji Mansur Rano ya ce idan har yarinya ta shi ce babu abinda zai hana a ɗaura mata aure gobe. Ya shiga ɗaki ya fito da tulin files ya damƙawa Ridayya ya ce

"Riƙe nan wannan kyautar da na yi miki ce" Yana faɗin hakan ya juya gaban Ammi ya faɗin ganin takardun abubuwan daya mallaka ya saka hannu tare da mallakawa Ridayya su ta bisa da sauri ta ce "Baffa ban gane ba, kasan me ka yi kowa?"

"Kina da tarihin ban taɓa yin hauka ba ko Maryam? Abubuwan dana mallaka na raba gida uku na bawa Ridayya biyu ya riƙe ɗaya shi ne mana"

"Ita kaɗai ce ƴa?" Ya ce "A'a, kawai haka nan na ji ita zan bawa" Za ta yi magana ya daka mata tsawa ya ce "Maryam fice mini a ɗaki kar ki ƙara mini ciwon kan da ban san dalilinsa na addabata ba shekara da shekaru" Ta fice a zuciya. Anuty Kaltum da Yaya A'isha har Mami suka dinga mamakin abinda Baffa ɗin ya yi a yanzu.

Washegari aka ɗaura auren Ridayya Muhammad-Bilal Rano da Zameer Mahboon Dollar auren da babu gata a cikinsa tunda babu Ustaz. Anuty Kaltum ta yi mata furnitures ƴan waje masu tsada haka Baffa da kayan kitchen an narka dukiya gashi kayan lefen ba abinda aka taɓa Ustaz ya bawa Umma komai da komai wanda Ridayya ɗin zata saka har kuɗin furnitures ma ya bata Baffa ne ya ce Umma ta bar shi duk abinda uba ya dace ya yi Ustaz ya ma Ridayya kafin ya tafi ta wajan Umma.

Aka kai kaya cikin wani dakakken gida tare da amarya sai santin gidan ake gwanin sha'awa iyakar haɗuwa ya haɗu. Mardiyya tare da amaryar sai Zainura a haka Zameer ya shigo shi ɗaya bayan sun gaisa ya ce "Ikon Allah har jere akai na manta ban faɗa musu ƙasar zamu bari ba yanzu haka"

"Ƙasar kuma?" Ya ce "E, a can zamu raya daren farko haka na tsara wa rayuwarmu ni da Mai sona" Mardiyya ta jinjina kalmar _Mai sona_

"Zan saka a kwashe kayan a kai ajjiya wani gidan idan mun dawo sai a dawo dasu yanzu haka a airport zaman jiranmu" Mardiyya ta miƙe tsaye ta ce "Za mu yi rakiya kenan?"

"No please hakan ma mun gode sosai" Ta kama hannun Zainura suka bar gidan Zameer ya sa aka kwashe kayan zuwa can wata unguwa wani ɗan ƙaramin gida aka jera kayan kitchen ɗin aka ƙulle. Ita da aka ce za a tafi airport sai ta gansu a wani gida ta dinga kallon gidan tana kallon Zameer ya haɗe fuska ya ce "Zan fara jarraba imaninki za ki iya rayuwa dani a duk yadda nake ko a'a shi ya sa na kawo ki nan idan kin cinye jarrabawa sai mu bar ƙasar"

"Idan har kana tare dani ai bani da wata matsala" Ta faɗa murmushi tana shiga gidan ta tarar da wata budurwa fara tas da ita sai danna waya take ya ce "Yawwa ƙanwata ce sunanta Khairiyya ana ce mata Khairy zata ɗan zauna damu"

"Sannu?" Cewar Ridayya Khairy ta ce "Sannu amarya zance ko bazawara ko budurbazar" Ridayya ta kalli Zameer ya kashe mata ido É—aya ya ce "Tana da wasa sosai don mind her"

Cikin dare Zameer ya matsa gefe É—aya yana tsaki sosai ta ce "Lafiya?" Ya É—aga kafaÉ—a ya ce "Amma dai bakya kula wasu samarin don tsoro ya kamani yadda kika bani budurcinki suma za ki iya basu" Ta dinga kallonsa nan da nan idanunta ya cika da hawaye ta ce "Shiyasa ka matsa daga kusa dani?"

"To uban me zan yi idan ban matsa tunda ba wani É—okin ki nake ba, abu ne ya yadda jiki an bani tun a waje yanzu bani da ra'ayi na riga na san shi, ai ba wani saura kin bani budurci tun waje"

"Me kake nufi?" A É—an fusace ya ce "Ina nufin na gode mana, Allah ya sa ya tsaya iya ni kuma"

Bata ce komai ba, a daren ta yi kuka mai isarta ya ce kuma ya na da vedion abinda sukai ta yi a hankali. Cikin dare aka hauro tare da kwashe kayan lefen tas abu ɗaya ba a bari ba Ridayya ta dinga kuka, Zameer ya jata a jiki ya ce "Suna wahalallu ai talaka haka yake al'amarin shi akwai mugunta, zan mu je ƙasar waje ki zaɓi komai ta ɗauka ƙaddara ce" bayan ta kwanta ya ɗauki waya ana ɗagawa ya ce "Na gode da aron kayan lefe na gode sosai ka duba da kyau babu abinda aka taɓa" Ya kashe wayar. Gari na wayewa babu abinci ya baza wanka tare da yin waje daman ta zo da kuɗi ta yi cefa ne ta aza wuta idanunta sai hawaye yake sosai.

A cikin watanni biyu bayan auren Ridayya aka dawo da Ustaz gida rai a hannun Allah ciwon yau daban na gobe daban ya yi jinya zuciya data jiki kamar zai mutu hankalin family ya tashi aka faɗawa Ridayya Zameer ya ce ai basa ƙasar sai dai idan sun dawo. Ya yi haka ne domin baya so ya san halin da Ridayya ke ciki da gidan da take. Ta kira Ustaz a waya a ɓoye ta yi masa sannu bai iya magana ba kawai ya kashe wayar nan take ya tura mata kuɗi a Account ɗinta naira dubu ɗari. Bishasha ta samu Zameer sai da yaga bayan kuɗin.

Komai ta samu Zameer gani take tana kuskurewa zai saki vedion ta ga al'umma ya ɓata career ta. Ya kwashe kayanta ya siyar wai sabbin zai kawo mata ashe caca ya shiga da su bata sani ba, ganin hakan wahala ya yi mata yawa ta kira Mardiyya ta ce sun dawo sanda Mardiyya taga Ridayya hankalinta ya tashi amma basu ƙare lafiya, Mardiyya ta kwashe ta faɗawa su Ammi akai faɗa sosai Ridayya ta murje idanu ta ce babu abinda mijinta ke mata kuma. Ustaz bai ce komai ba domin ya jima da sanin inda Ridayya take rayuwa kawai ya zuba Idanu kuma shi ne dalilin daya saka yake tura mata kuɗi duk wata. A haka ta fara yin ƴar'tsala suka saba da Zainaba kullum ta yi zata bawa Zameer da Khairy. Lokaci ɗaya ta rame duk ƙibar nan ta zabge saboda wanki da gugar Zameer har ciwon baya ta fara, ba ci ba sha babu suttura sai dai idan buƙatar shi idan ta tashi ya neme ce a haukace haka zai faɗa mata tamkar dabba, bayan ya gama ya magance ta da kalamai masu daɗin gaske da nuna ita ce mace ɗaya tamkar da dubu duk wannan abun bai taɓa haɗa baki da ita a cewar shi wannan zuntumemen leɓen babu uwar da zai tsinana dai wari. Kwanci tashi ta samu ciki a lokacin kuma duk abinda ƴan'uwanta suka faɗa dangane da Zameer zai ta kwashe ta faɗa masa, hakan yasa Zameer ya haba uban kowa zuwa gidansa hatta Yaya Balkisu zuwanta biyu Zuhura sau ɗaya a lokacin Ridayya ta hana su shiga cikin uwar ɗakinta. Takaici ya saka Anuty Kaltum da Yaya A'isha ƙin waiwayar Ridayya kefe ɗaya kuma Ammi bata da burin daya shige taga auren Ridayya ta mutu ta haɗa ta da Burhan saboda kadarorin da suke wajanta. Zameer na ya san da kadarorin amma bai taɓa sanin inda ta ajjiye ba idan ya tambaya sai ta ce suna nan. A lokacin Baffa baya zama sosai kullum cikin tunani Ridayya yake kuma ya sakko akan Mami ita ko kallo bai ishe ta. Huɗuba sosai Zameer ya yi mata a kan ƴan'uwanta ya ce ko gidan basa barinsa shiga wai shi talaka bayan karayar arziƙi iyayensa suka samu. Har cikinta ya tsofa bata taɓa zuwa asibiti ga rashin abinci ta kwana da yunwa ta yini da ita ko abincin ta samu sai ta bawa Zameer wani lokacin kuma tana kallon sai su kwana ɗaki ɗaya da Khairy ta yi magana ya ce ai ƙanwarsa bai zarge ta ba sai shi zata zarga? Ta kira Mardiyya a waya a lokacin shi ne suka faɗa kaca-kaca a kan ta ce namiji ba ɗan goyo bane musamman Zameer kuma Khairy ba ƙanwarsa bace farkar shi ce ta ce babu ita ba Mardiyya har abada, a ranar ne kuma da daddare ta samu Zameer a ɗaki shi da Ridayya turmi da taɓarya har ta nemi kashe kanta da fiya-fiya

WANNAN KENAN.

BACK TO STORY
Kuka sosai Zainaba ke yi haka Ridayya, Usman mijin Zainaba ya rushe da kuka har da face majina aka rasa wanda zai rarrashi wani da ƙyar Ridayya ta ce "Duk abinda kuke faɗa na sani bani da wani option wanda ya shige watsar da maganganunku na riga na bawa Zameer mutuncina, kuma a duk sanda na yi yunƙurin rabuwa da shi ya ce zai saki vedion a duniya"

"Tsinanne matsiyaci ce *MUNAFUKIN MIJI* wutar Allah ta ci shi" Ridayya ta goge idanunta ta ce "Amma wallahi tallahi sai ya sake ni na koma wajan Abbieyna, ko da zai saki vedion zinar da mukai ne.......

Share and share please
Ina godiya da comment da goyan baya masu zagen Ridayya ku yi mata uzuri please Allah ya yafe mata.

Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
08164069385
*✿ MUNAFUKIN MIJI 23 ✿*
Mikiya Writers Ass....

BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
Nimcyluv

"Yanzu kina nufin Ustaz bai san kin watsar da tarbiyar da ya yi miki ba, ba shi da labarin kin bawa saurayi budurci tun a waje saboda soyayya da ganin idan ba ki ba shi ba zai aure ki ba?"
Chapter 45 · 0% Book details