← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 118

Sashe 82

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta girgiza mai hawayenta na sake yawa muryarta na rawa ta ce "What if i don't want you to love me? Abbiey....,"

Yatsarsa ya É—ora a lips É—insa alamar ya isa ya kasa maganar. Kukan Ridayya ya tsananta ta ce

"Kallon mahaukaciya ake mini, na yi mamaki daya kasance har da kai amai yi mini wannan kallon. Wallahi ina da hankali Abbiey ni ba mahaukaciya ba ce, kuma Umma ta yi maka zaɓan da ya fi ni ta baka budurwa fara kyakkawa, bana jin aure Abbiey ko zan yi aure Sadauki ne zaɓina Abbiey ka yi mini uzuri please"

Ta kasa ƙarasa maganar saboda kuka ta ɗora kanta a cinyarsa kuka take mai cin rai, duk wanda ya ce bata fahimtar shirun Ustaz, da kallonsa ko tarinsa ko maganarsa ya yi ƙarya, sam Abbiey bai dace da ita ba yadda ya ƙare rayuwarsa haka yana da kyau ya samu kyakkyawar mata budurwa mai budurci, ba ita data watsar da nata tun a gabansa ba, tun kafin ta yi aure ba, ba ita data aikata zina ba. Wannan dalilin ya sanya take masa fatan samun macen data fita komai na rayuwa, Sadauki ya sota ne a yadda take ya kuma san ta yi aure ta haihuwa ko gaskiya ce ta bayyana ba zai ji zafi da baƙin cikin da Ustaz zai ji ba, shi ne ya bata rayuwa, ya kula da maraicinta dukda tana da Iyaye a raye ya bata tarbiyya daidai gwargwado tsakani da Allah amma ta saka ƙafa ta shure hakan ruɗin shaiɗan da uƙubar gidan uba, da mugun fata na Burhan da tsangwamar jama'ar gari ya sanya ta ji barin gidan shi ne mafita a gare ta, ta yi believing idan Zameer ya bar ta ba zata taɓa samun mijin aure ba ta yanke hukuncin bashi abinda ya buƙata tunda ta yi imani idan ta yi hakan zai zama miji a gare ta, mai share mata hawaye sai dai kash! Aka yi rashin sa a ashe MUNAFUKIN MIJI ta aura.

Ranar data bawa Zameer kanta ya dawo sabo a tunanin a hankali shuÉ—aÉ—É—un abubuwa suka dinga maimaita kansu a idanunta da zuciyarta dama kwakwalwarta suka zama sabbi a gare ta.

"Shhhh ya isa"
Muryarsa bata ma fita har yanzu sunan Sadauki ne a kansa zaune. Ya É—agota yana murmushi ya ce "To maganar ta shige ok? Bana son mu yi irin wannan sallamar"

Ta jinjina masa kai wayarta ta fara ringing ganin sunan Anuty Kaltum ya saka Ustaz É—aga kiran ya yi shiru.

"Wai uwar me kika tsaya yi ne daga zuwa sallama?"

"Hakƙin mijinta ta tsaya saukewa"

Ƙitt Anuty Kaltum ta kashe wayar Ridayya ta zaro Idanu ya haɗe fuskarsa yana goga mata hanci a hankali ya sunbaci goshinta ya ce "Blessing women"

Ya sauka daga kan bed ɗin ta bisa da kallo wallahi ƙato ne shi bata taɓa ganin girmansa ba sai yau, abinda ya fi ɗaukar hankalinta farar fatarsa ga suma luf luf kuma daga shi sai boxer.

"Abbiey ciwon ya warke ne kake saka É—an mitsitsin wandon nan?"

Ya juya ya kalle ta ba yabo ba fassala sai ya É—auke kansa ya share kamar ba zai magana saboda ya ja lokaci ta ji ya ce.

"Maybe ke yake jira, do you like it?"

Ta É—auke kai da sauri sai kuma ta sakko ta fara gyara masa bed É—in bai kulata ba ya buÉ—e drawer ya É—auki wasu abubuwa kana ya rufe.

Yana tsaye har ta gama gyara masa gadon ta saita komai tunda ta saba bayan ta gama ya ce "Jazakhilla bil khair Jaririyata, Allah ya yi miki albarka"

Kanta a ƙasa ta ce "Amin. Abbiey na bar Little a wajanka"

"Shi wai ba a shirya yi masa ƙanne bane?"

Ta yi murmushi kawai ta nufi waje ya bi bayanta suka jera a tare. Zaune suka samu Mardiyya da sauri ta goge hawayenta tas amma idanunta ya yi jajur har ya kumbura domin ta laɓe ta ji komai hankalinta ya tashi sosai wani irin son mijinta da kishinsa ne suka dinga damunta. Ta fara yarda Ustaz bashi da lafiya idan hakan ya tabbata akwai matsala amma dole ta sake gwada shi domin gano gaskiya.

"Kaga Æ´ar Abbiey É—inta kun fito?"

Ridayya ta share ta yi kamar bata ji ba, Ustaz ya san mene hakƙin iyali baya son Ubangiji ya kama shi da wannan laifin ya fahimci Diyya da kyau a kame ya ce

"Lafiya? Akwai damuwa?"

"Babu kawai bacci nake ji ne ina jiran kuma mu yi sallama da Ridayya"

Ridayya yunƙurin tafiya ta yi Ustaz ya yi mata wani kallo da sauri ta tsaya jikinta na rawa. Mardiyya ta fara ƙoƙarin haɗa jikinta dana Ustaz sai suka ji Ridayya ta fasa ihu ta zube tana riƙe ƙafarta hakan yasa da sauri Ustaz ya matsa daga kusa da Mardiyya ya ɗan rikice da tambayar Ridayya lafiya mene meke mata ciwo wani abu ne?

"Abbiey ƙafana ya maƙale ba zan iya tafiya ba ka ɗauke ni"

Kuka take sosai hankali kuma tashe take riƙe ƙafar Mardiyya ta tsaya kamar statue. Ustaz ya ɗauki Ridayya cak ya nufi main parlour da ita. Tun daga nesa Umma ta fara salati tana "me zan gani ni Hadiza wai ɓatan nono a ƙirjin budurwa"
Hankalin Ustaz baya jikinsa balle ya fahimta kukan Ridayya kawai yake ji, Umma ta yi saurin shan gabansa ta ce
"Sauke ta almura munafuka uwar Æ´an iya mitsitsiyya dake kin iya kissa daman zawarawan nan haka suke da nacin miji"

Ustaz ya kalli Umma ta ce "Yanzu zaka fara Allah ya yafe mini ko? Ka zama shanyaye na mace nan gaba ɗan Daudu zaka zama kama maƙale hannu da kashe murya duk a sanadinta sauketa ka juya"

"Bana gane komai Umma ki mini uzuri Ustaza ba lafiya"

"Ta mutu mana? Idan ta mutu ni na mutu"

Da wani tashin hankali ya kalleta ya ce "Gwara ni na mutu Umma"

Yana faɗin hakan ya yi gaba tana kwaɗa masa kira ya share. Baba ƙarami murmushi kawai yake yana mamakin Hajiya Hadiza da bata san mene mayen so ba. Anuty Kaltum ta dariya domin taga komai a ranta ta ce "Za kiga aikin bazawara soon domin ba kiga komai ba sai Ridayya ta ke Maiduguri ta dawo ganin ɗanki sai ya gagare ki tunda kina jayaya da hukuncin Ubangiji"

Suna nufar hanyar harabar gidan Ridayya ta yi saurin cewa "Sauke ni" da mamaki Ustaz ya kalleta ganin ta zame ta sauka tare da tsayawa a kan ƙafafuwanta ya dinga binta da Idanu ya kasa furta komai. Anuty Kaltum ta ƙarasu wajan ta ce "Mu je ko ana ta jiran mu" Ridayya ta ɗan ji ba daɗi ta juya ta kalli Ustaz shi kam ya share ya yi kamar bai gani ba

"Abbiey zan tafi" Ta faɗa idanunta yana cika da hawaye ya juya yana riƙe kansa da yanayinsa da kyau a ɗan kame kamar koyaushe murya a taushashe ya ce

"Mene na kuka?"

"To za ka zo ne? Zaka kira ni a waya?"

"To ki haƙura mana Ustaza" Ta girgiza masa kai ya ɗan matsa kusa da ita ya ce "ki kula da kan ki, ki girmama kowa banda raini banda surutu da maza, be careful" Ta jinjina kai ya shafa kanta ya ce "Allah ya yi miki Albarka, Little fa?"

"Wajan Mami zai zauna" ya sauke numfashi yana ta kallonta taƙi yarda ta kalle shi sai ya sake ta ya ce "Take care of yourself Ustaza"

"To Babban mutum za mu shige mu duk ka cinye mana lokacin" Bai kalli Anuty Kaltum ba ya miƙa mata robar hannunsa ya ce "Duk dare ta sha, ki kula da ita please"

Yana faÉ—in hakan ya juya zuwa cikin gidan su kuma suka shiga mota zuwa wacce zata kai su Maiduguri driver É—in sai mita yake musu.

Ridayya bata saba tafiya haka ba tun tana ware idanunta na kallon hanya har bacci ya ɗauke ta. Anuty Kaltum tana ƙara jinjina girman so da ƙaunar da Ustaz ya kewa Ridayya ta ɗauki niyyar ko komai nata zai ƙare a wannan karan za ta yi zumunci aiki Ridayya zata share masa damuwarsa zata zame masa irin matar da yake so, bazawara zata ɗauke masa dukkan buƙatunsa koma zata saka Umma ta dawo cikin hayyacinsu ta fahimci zawarawa suma mata ne. Balle irin Ridayya sauta ga wawa?

Sanda Ridayya ta farka ta samu Anuty Kaltum na waya da General yadda ta ji ana musayar kalaman soyayya ya bata Maman ƙwarai da gaske, har take ganin wannan rashin kunya ce ta yi zuru tana kallonta. Ridayya ta yi mamakin ganin ƴan'uwan kakarta wacce ta haifi Mami wato Dada kusan ita ce ta ɗauki yalwar suma irin nasu, asalin kanuri cikakkun mazauna garin Maiguduri yawanci sun saka lafaya ga wani irin kitso a kansu gwanin sha'awa kowa ka ganni akwai zanen lalle a ƙafarsa so ma sha Allah. Dangi aka yi ca ana ganin cikar Dada ta wajan Fatima Batula aka sauke su da shatara ta arziƙi tun a lokacin Yamara ta fara fito da kayan gyara tsofaffin ajjiya aka haƙa rami aka fito da wasu itatuwa da tsumammun turarruka aka wanke ramin tsugo tas. Tun a daren data bawa Ridayya wani magani tasha wani irin ruwa ya dinga fita daga jikin Ridayya mai yauƙi yauƙi kwana ta yi ba tai bacci ba sai sauya zani take.

Kwananta biyu tana shan maganin sanda aka zo gyaran fata har kuka ta yi saboda azaba sai ta ji kamar fatar jikinta zata kwailaye kafin ka ce baƙar fata da dawo wani special colour na musamman ita ba za a ce baƙa ba, kuma ba za a ce chocolate ba. Idan ta hau ramin tsugo kowa ba a magana sai jikinta ya gaya mata, ta ji ta matse da kyau kamar ba ita ba, ko sanda aka yi mata wannan ɗinkin na haihuwar Little bata ji ba domin tunani take anya zata iya fitsari? Bayan ta yi turare sai a haɗa ruwa a babban baho mai ɗauke da kaya kala-kala ace ta zauna ciki sai ta yi awa guda, idan dare ya yi sai a bata na shafawa kala biyu dana fata da wanda zata shafa a gabanta.
Chapter 82 · 0% Book details