← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 118

Sashe 54

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tajj ya haÉ—e fuska shima ya ce "Lallai Babban mutum kana ciki na shigo amma ba magana?" Ustaz bai É—ago kansa ba balle ya kalli Tajj ko ya kula shi a nutse kawai yake danna wayarsa shi bai ma san me yake dannawa ba kawai rashin sabo da yin maganar ne ya saka ya fara danna wayar.

"Lallai ya yi maka kyau, ina yini ka zo lafiya zuwa yaushe?" A hankali ya ɗago idanunsa ya kalli Tajj sau ɗaya sai ya zame ganinsa ya yi shiru wasu daƙiƙo a shirun nasa can ya numfasa ya ce

"Kana lafiya Tajuddeen?" Tajj ya watsa hannunsa ya ce "Lafiya lou nake Babban mutum ya leges kuma? Ban yi tsammanin ganinka a Kano ba, ka ci sa a ni ma yau na shigo gari" Ustaz bai yi magana ba don zancen na Tajj ya masa yawa "Mahmah a kawo mana abincin nan ki kawo man shanu daban ni ban so Friend dai yana so"

"Ai da yake kai ne maybe ya ci, amma daman shi idan an ce abinci sai ya ce I'm full" Tajj ya yi dariya sosai ya ce

"He is always full daman amma banda yau" bayan tashin Mahmah Nadra ta bi bayanta tana tsalle Daddy ya dawo, ta ƙasan idanu Ustaz ya bi Nadra da kallo yana so da ƙaunar yara a hankali ya lumshe idanunsa yana tunanin yaushe zai samu nasa ne? Me ya sa ƙaddara ta yi masa kutse tare da yi masa tabo a zuciya me ya sa a kullum ƙaddara ke bibiyar rayuwarsa ne? Ya san hakan tabbatacce ne kuma al'amarin Ubangiji ne, tarihinsa ba zai taɓa cika daidai ba dole sai da sunanta rayuwa da ƙaddara abu ɗaya ne kamar yadda karatun littafin yake abu ne mai wahala na rashin sanin meke ƙunshe a cikinsa, idan ka karanta wannan shafin ba zaka san mene a shafin gaba ba dole sai ka buɗe to lissafi haka ne yaƙini da wanzuwar karatun littafin ƙaddararsa dole idan anga sunansa a gaba kaɗan za a ga nata bashi da tabbacin da numfashi da tunaninta wani ya fi yawa a ƙirjinsa. Ya ɗan sauke ajjiyar zuciya a sauƙaƙe yana riƙe yanayin da yake ji wanda ganin Nadra ya dawo masa da shi.

"Ga abincin fa ina ta magana". "Azumi"

Ustaz ya furta a taƙaice yana ɗauke ƙafafuwanta ya tanƙwashe saman kujerar parlourn Mahmah da shi wani ɗan gata ne tausa yake buƙata a gajiye yake sosai, ba uwa ba uwa ba ƴan'uwa ba mata ba ƴaƴa Maybe bashi da wani rabo ne. Tajj ya ce "Me ya sa kullum cikin azumi kake ne Ustaz? Ba a gane azumin lada dana kai da kai? Kalli yadda ka rame ka saurara da yin azumin nan"

"Kana da matsala da azumi na ne Baita?" Da sauri ya ce "Of course ina da shi ko dan lafiyarka" Ustaz bai sake magana ba sai da Tajj ya yi surutunsa shi kaÉ—ai ya ga ji ko tari ya ji Ustaz bai yi ba kamar daga sama ya ji ya ce

"Labarin yarinyar na zo ka bani, ka sameta? Wace ita?" Ya yi maganar É—aya bayan É—aya yana mai jan gemunsa Tajj ya ce "A'a, nama manta da ita wannan ne dalilin zuwan naka?" Kafin ya yi magana an kira Tajj an sanar da shi jininsa bai yi daidai dana Ridayya ba. "Shikenan zan zo"

"Wai wanne labari kake da shi a kan Ridayya ne? Nifa bulayi nake bara a kofai ko ganinta na yi i can't recognize her saboda ko a picture baka taɓa nuna mini ita ba, kasa na fara tunanin ko dai son ƴar rainon taka kake yi labarin rainonta kawai na sani ba ita ba please ka nuna mini ita maybe ma na taɓa ganinta rashin sani ne" Ustaz ya miƙe ganin yana ƙoƙarin fita ya sa Tajj miƙewa ya ce "Ɗan jirani"

Ustaz ya fita zuwa waje ya shiga motarsa mai kyau blue black ce mai baƙin glasses ya ɗan jima kansa kife a jikin hannun motar kafin Tajj ya shigo ya ce "Muje" a hankali Ustaz ya yi bismillah ya yi wa motar key suka fita daga babban gate kai tsaye Tajj ya ce "Aminu Kano hospital please" Ya sauya direction mamakin shirun Ustaz da miskilancin shi yake bawa Tajj mamaki. Suna ta ce ya ce "Mun yi magana da Hajiya ai ta ce lallai nasa ka nemo matar aure ko kuma duk wacce ta yi mata wallahi ta aura mata cikin watan nan, kuma ni na yarda ta maganarta wallahi ka nemo matar aure ko na ce ka bata zaɓi"

"Ina ta magana ka yi shiru" Gabaɗaya Ustaz ya saki kan motar ganin yana neman kashe su jikin Tajj na rawa ya riƙe motar ya ce "Babban mutum mene haka kashe mu za ka yi saboda ka ga ji da rayuwarka?"

"Wallahi zaka fita daga motar nan da gaske zaka fita mtwsss"

"Commissioner guda kake wa haka? Tsawa fa yau guda yafiyar da kake nema wa jama'a bari na nemaka Allah ka yafewa Ustaz kar na kama shi na kai bayan kanta" har suka ƙarasa asibitin kamar an ɗinke bakin Ustaz yana kallo aka ɗauki jininsa leda biyu amma bai tambayi dalili ba, tambayar ma wahala take masa. Jiri na ɗan ɗaukar shi ya kifa kansa tsakanin cinyoyinsa. Mintina wajan goma ya ji muryar wani na mita..

"Tab gaskiya Yaya ka yi haƙuri i can't, jinina fa? Daman shi ne kiran da kake ta mini kamar zaka fasa mini dodon kunne"

"Ni kake cewa zan fasa maka dodon kunne? Zauna a ɗauki leda biyu ai aikin lada za ka yi banda rigima da rikici mai ka ajjiye har cewa na yi ina nemanka ka ƙi zuwa wai kar na juya ka?"

Ya haÉ—e fuska sosai "Da tausayi É—aukan jini har leda biyu a wannan zamani salon ka saka wacce zan aura hasara, ni a faÉ—i nawa ne kuÉ—in na biya a siya kuma taimako ba sai mutum ya yi niyya ba"

Tajj ya juya ya kalli dr ɗin dake ta dariya yana mamakin ƙarfin halin mai maganar commissioner guda yake faɗawa haka shi kuma Tajj ya san matsalar baya son allura ne duk wannan hanya-hanya ɗin

"Lallai yaron nan au matarka? Oya zauna a ɗauki before i shoot your legs" ya ƙara yin kicin-kicin da fuska kamar ya ce ya shiga uku shi ya ɗauka ma bashi da lafiya ne da har ya kira shi zuwa asibiti ya zo

"A'a kafa daina ce mini yaro shekara 30 ba kwana uku bane ni kaga ma bana jin daɗi na ci maiƙo yau Olser ta mini mugun kamu"

Tajj ya dake ya ce "Dr É—auki jinin please kar ka saurari maganarsa"

Ya girgiza kai tuni ya rikice ya ce "A'a dole a ji reason É—ina idan ba gado kake so a bani a nan ba, kuma a bari na shirya"

Kamar an tsikari Ustaz ya miƙe tsaye yana daddafe kansa yana jin kamar kansa zai rabe har tsakiyar kansa ya ke jin musayar yawun nasu ga wani jiri dake ɗaukarsa da ƙyar ya riƙe jikinsa ya fice. Da ƙyar ya bari aka ja jinin yana ta mita tunda aka soka allurar ya yi tsit fuskarsa ta sauya ana gamawa ya miƙe ya yi luuuu zai faɗi Tajj ya riƙe shi ya ce

"Be careful" a ƙasan maƙoshi ya ce "Cika ni" muryarsa ba wasa ya haɗe rai tamau kai ka ce shi ne gaba da Tajj Baita ɗin ya nufi ƙofa sai da ya je ƙofa ya tsaya ya ce

"Kuma wallahi sai ka biya ni ko na kwasa a kuɗinka" Yana faɗin hakan ya fice mamakin ƙarfin jininsa ya cika Tajj domin kamar bashi ne aka ɗauki jini har leda biyu a jikinsa ba. Nan da nan aka ɗaurawa Ridayya jinin Ustaz ya fara shiga jikinta bayan sun keɓe Tajj ya ce

"Dr matsalar fuskarta da kuma fatar jikinta fa?"

"Ina tunanin sai dai ku je asibitin Bela nan za ku samu likita mai kyau" godiya ya yi masa kafinwya fito daga Ustaz har mai mitar kowa ya shiga mota ya fice da ra'ayi iri É—aya a zuciyoyinsu.

Sanda Tajj ya ga Little Bilal mamaki ne ya cika shi banda yasan waye Ustaz babu shakka da ya ce wannan jininsa ne ko kuma É—ansa ya É—auki yaron ya koma gida Mahmah ta yi masa wanka ta sauya masa kaya nan da nan Tajj ya shiga yi masa pictures da video yaron sai dariya yake yana lumshe idanunsa ya É—ora shi a status da caption É—in _My lovely son_

Zirga zirga take yi hankalinta yaƙi kwanciya ta juya ta kalli Zuhura ta ce "To yanzu da kika dawo gida da zuƙar yara uwar me zan yi miki? Kina nufin kashe aurenki za ki yi ki zo ki tare mini a gaba ko mekike nufi"

"To Ammi ni ya zan yi ne baya bamu abinci kullum cikin wahala nake gashi ni bani karatu na yi ba balle na samu aiki haka kurum yunwa ta kashe mu" Ammi ta ce
"To ba kece ba tun ina lallama ki ko ƴar diploma ki haɗa amma karatu baya gabanki yanzu wa gari ya waya ki barni da abinda yake damuna mana" Zuhura ta fashe da kuka ta ce "Wallahi don ba ki san wulaƙancin da Nura yake mini bane a cikin gidan nan kamar wanda ya fara neman mata. Kwata-kwata bana jin daɗin zaman gidan mijina"

"To dan ubanki ni daɗin zama nake a gidan uban naki, kina kallo yadda komai yake neman fin ƙarfina sai na yi kwana biyar a cikin gidan nan ban saka Alhji a Idanuna ba, sisi ta daina haɗa da shi ya tattara komai ya liƙe a gindin wancan shu'umar matar wacce ta gama a sirrice shi, ki duba ki gani wai don duk ya daidaita abubuwan da suka faru tsakanin Babban mutum da mummunan wannan yarinyar ya liƙa mana hatsarin ƙarya"
Chapter 54 · 0% Book details