← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 118

Sashe 75

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan fitar Mardiyya Baba ƙarami ya kalli Umma ya ce "Kin kyauta kuma kin yi yadda kike so, amma hakan ba zai hanani yin yadda na so ba, kece uwar Muhammad nine ubansa kina son Mardiyya ina son Ridayya domin jinina ce, ko babu aure ta zame wa Babban mutum dole hakƙinsa ne na kulawa da ita. Sai dai kin yi a banza domin sara da sassaƙa baya hana ganji toho, kamar yadda Mardiya take matarsa haka Ridayya take matarsa ta sunna babu mamaki ya zama na ita ce uwar gida domin idan aka bincka nata auren aka riga ɗaurawa"

"Can ta matse muku da kai da masu ɗaurin auren, da munafukar uwarta data goyi baya. Ko a cikin hadisi an ce ka bi uwa har sau uku kana uba, maganata kamar yankan wuƙa haka take a kan Bilal, ba shawara nake bashi ba umarni ne kuma zan ga wanda zai tilasta ya zauna da wata bazawara muguwa butulu wacce bata san halacci ba, balle ban yarda an ɗaura auren ba I'll never accept her as my daughter-in-law"

Tana faɗin hakan ta fice daga room ɗin, Baffa ya bita da kallo yana jin haɗin da sukai na neman sare masa tunda yana ƙoƙarin taɓa zumunci kuma ahli ɗaya. Kasa cewa komai ya yi sai ficewa daga room ɗin ya koma wajan Ridayya yaga halin da take ciki. Junaid ya kalli Ustaz da jikinsa har yanzu rawa yake ga wani irin zafin zazzaɓi dake farmakar shi a hankali ya ce

"A kira Dr Abba"

"Ba Dr Ustaz ke buƙata ba, ka je can wajan Baffa ka kula da ƴar'uwarka Junaid lokaci ne na bata gata da bata dukkan wani support da take buƙata kune yanzu muke buƙatar ku haɗe kan ku, mutuwa bata san inda rai yake ba, bata san inda ciwo yake ko shekaru yake ba, amma mu a kodayaushe ta Allah zata iya kasancewa da mu, kuma Allahamdulillah mun yi wa zumunci hidima dukda bamu da yawa. Jeka Junaidu maza jeka" Junaid ya miƙe yana jin ƙarfin qiwwa a maganar Baba ƙarami bayan fitarsa ya rage daga Baba ƙarami sai Ustaz da har yanzu idanunsa a rufe suke.

Waje ya nema kusa da Ustaz ya zauna, tare da kama hannunsa ya riƙe cikin nasa lokaci mai yawa basu samu kusanci da ɗan nasa haka ba, rauni irin na uba ya mamaye zuciyar Baba ƙarami ya san zurfin cikin Ustaz tun yana ƙarami mamakin yadda zafin zuciyata ya ragu sosai yake.

"Babban mutum buɗe Idanunka" A hankali ya buɗe sun yi wani irin jirkicewa yanayin da Baba ƙarami bai taɓa gani ba, ƙwayar idanunsa tamkar ba tasa ba, wani irin jan abu ya kwanta ciki tun ɗazo yake ƙoƙarin yin magana sai ya ji tamkar hayaƙi ne zai fito maimakon furuci. Baba ƙarami ya sake riƙe hannun Ustaz sosai a taushashe cikin kulawa ya ce

"Duk inda ake neman jarumin mutum kuma sadauki mai bada farincikinsa saboda wani ya yi murmushi to a nemi jarumin ɗana. Muhammad baka buƙatar damuwa a yanzu ƙarfin qiwwa kake buƙata ka yi haƙuri ka daure abinda kake ji karka bari rauninka ya fito, a wannan karan kar ka yi faɗa domin Ridayya ka yi faɗa domin abinda zuciyarka ke so, kuma take son rayuwa da shi. Bani da tabbacin mene a zuciyarki game da ƴar rainonka abu ɗaya zan faɗa maka ka kula ka yi ƙoƙarin ganin ta zama taka ka yi hakan ƙarfin qwiwarka yana ga abinda kake so"

A hankali ya shiga girgiza kansa yana matse hannun Baba ƙarami dake cikin nasa bakinsa na rawa ya cec

"Bana jin zan iya Abba zuciyata a matse take bana fahimtar komai"

"Be strong; ka yi abinda ya fi haka idan abu ya ƙare baya nufin rayuwarka ce ta ƙare, something is over doesn't means yourself is over. Har yaushe zaka zauna haka? Shiru baya maganin matsala ciwo yake haddasawa a zuciya da kuma dana sani mara iyaka ba zan ci-gaba da faɗa da mahaifyarka ba, ba tare dana san kana son Ridayya ko a'a ba?"

Ustaz ya ware idanunsa a lokacin ya kalli mahaifinsa ya kasa furta komai sai zufa da take yanko masa shi gani yake me ya sa dole sai ya furta ba za su gane bane? Me ya sa ake son fallasa masa asirin zuciyarsa "Ka faÉ—a mini ina jiranka, mene matsayin Ridayya?"

"Abba please"

"Please what?" Ya yi ƙasa da idanunsa zuciyarsa kamar ta fito waje.

"Look Muhammmmd the most important thing is to be yourself. Ni mahaifinka ne don ka fiddo mini sirrinka ka buÉ—e sirrinka ba wani abu bane, idan kana son Ridayya i most be by your side, idan baka son ta shikenan I'll let her go ta zama free"

Da sauri ya matse hannu Baba ƙarami hatta tsokar jikinsa rawa take ya shiga girgiza kai laɓɓansa na rawa "Say it Muhammmmd"

"Ni daban Abinda ke zuciyar Ustaza daban Abba"

"Ko hakan yana nufin ita É—in tana amsa sunan matar Muhammad-Bilal Tahir Rano ne?"

"A'a Abba babu kyau kar ka fara wannan zunubi ne na yafe maka kuma"

Baba ƙarami ya ce "Zunubi ko? A wannan lokacin kai Allah zai yafewa bani ba Babana, da gaske nake ina nufin abinda na faɗa. Ridayya Mansur Rano is your halal wife matar sunna"

Ustaz ya kasa tantance halin daya shiga kallon Baba ƙarami kawai yake da wani irin firgitaccen yanayi da shakku dukda a zaune yake amma tun daga kan babban yatsarsa har zuwa saman jikinsa rawa yake fuskarsa ta fara sauyawa zuwa wani launi kamar ba Ustaz ba.

"Allah ya yafe maka Abba Allah ga Abbana"

Baba ƙarami ya yi murmushi ya fahimci Ustaz har yanzu bai yarda ba, ya ciro wayarsa ya kunna video recorded ɗin da aka yi na ɗaurin auren. Play ya danna Ustaz ya zubawa video Idanu ya Baffa ga Baba ƙarami ga Tajj har da Junaid ga Barrister ga kuma General mijin Anuty Kaltum. Sanda ya ji liman ya ce “An ɗaura auren Muhammad-Bilal Tahir Rano da Ridayya Mansur Rano a kan sadaki dubu ɗari biyu”

Tsigar jikinsa ce ta fara mimmiƙewa yana jin wani emotions wanda baya kaiwa ƙasan mararsa a iya zuciyarsa yake tsayawa da gangar jikinsa ƙofofin gargasar jikinsa suka buɗe wani irin sanyi yana shigarsa, zuciyarsa ta buɗe hannunsa ya shiga rawa duk jarumtarsa ta kau ikon Allah kawai yake gani mai yin yadda ya so a lokacin daya ga dama, Hausawa sun yi gaskiya da suke cewa kana iya aurar matar wani amma ba zaka iya haihuwar ɗan wani ba, matar mutum kabarinsa.

"Abba gaske kake?"

"Da gaske nake Babana hukuncin Ubangiji ne ba namu ba, kuma tsarinsa ne Ridayya matarka ce"

Ustaz kasa magana ya yi sai halin ɗan fari dana autar ya bayyana ya ɗora kansa a cinyar Baba ƙarami wata ƙaƙƙarfar ajjiyar zuciya ya sauke a ransa yana yin hamdala ga Ubangiji daya ara masa ganin wannan ranar. Bai taɓa fitar da hawaye a rayuwarsa ba bai suna zuba ba sai da Baba ƙarami ya riƙo fuskarsa yana share masa hawaye ya ce

"Kuka? Al'amarin har ya kai haka Babban mutum baka tunanin ka girma?"

Ya É—an marairaice fuska ya ce "Allahamdulillah!"

"Shi ne abin godiya, zan yi magana da kai idan ka samu nutsuwa"

Ustaz ya kasa tantance wanne kalar farinciki yake ji, tsoron abinda Dr ya faɗa ya wanzu a zuciyarsa anya zai iya? Me ya sa bai samu Ridayya ba sai yanzu da ƙaddara ta faɗa masa ƙaddara mai zafi da munin gaske Ridayya ta saba da rayuwar gidan miji ba zata jure halin da yake ciki ba, domin ba zai amfana mata da komai ba shi ɗin kamar photo haka zai zama. Idan ya ture wannan taya zai fara rayuwar aure da Ridayya? Ƴar cikinsa yarinyar daya raina kuma yana jin ya mata girma, shi da kansa kunyar wannan al'amarin yake yana jin son rayuwa da ita har bayan abada idan akwai amma bai taɓa hango wani nauyi na musamman ba, taya zai iya kwana da ita gida ɗaya ɗaki ɗaya gado ɗaya matsayin matar, su kwana matsayin mata da miji? Ya rufe idanu a hankali yana sauke numfashi nauyin zuciyarsa na raguwa kamar a mafarki haka yake jin batun auren nasu gefen zuciyarsa Ridayya ɗin kawai yake son gani, a wannan karan zai yi mata kallo ne na matarsa kuma halalinsa.

"Tsuguno bata ƙare ba"

Ridayya Sadauki ne a ranta, shi kuma Ridayya ce a ransa Mardiyya kuma Ustaz ne a ranta ga matsalar rashin mazakuta ga matsalar Umma wacce tafi ko wacce illa a zuciyarsa ga matsalar Sadauki ga matsalar ciwon Ridayya ɗin _“What should I do?_”

Allura aka sake yi wa Ridayya mai nauyi ta fara bacci al'amarin ya ƙara hargitsa kwanyarta wacce take a gurɓace har yanzu shocked ɗin ganin Ustaz zube a ƙasa ne bai yar kanta ba.

Kwana biyu a tsakani ta farfaɗo cikin hayyacinta kuma babu abinda ke damunta sai ramar da ta yi ta ƙara yin zuru-zuru ta yi ɗan duhu a kan na baya saboda kwanciyar asibiti. Lokacin da idanunta ya sauka a kan Zainura firgicewa ta yi ta hau salati da addu'a

"Yaya Ridayya ni fa ba fatalwa ba ce ki bar addu'a" Ridayya ta girgiza kanta ta fara yunƙurin guduwa Baffa ya ce

"Fatalan suna da yawa"

Da wani irin sabon tashin hankali take kallon Baffa sai kuma Mami ta dinga nuna su da hannu

"Kun kun mutu an ce kun mutu ko kun zo tafiya dani ne, kar ku bar ni zan biku lahira É—in an ce...,"

Sai kuma ta sulale jikin Mami a sume daman sun zan za a rina an saci zanin mahaukaciya bayan ta farfaɗo ta fasa wani ihu Mami ta riƙe ta gam a jikinta ita kanta kuka take Zainura ma kukan take Baffa ya sunkuyar da kansa.

"Mami da gaske kece? Kece a gabana kike riƙe ni baku mutu ba aka ce kun mutu? Ashe ƙarya ya yi mini mugu azzalumi ba zan taɓa yafewa Giɗaɗo ba ya saka na dinga wahala ashe kuna raye Abbiey ma ya ce kun mutu to babu ruwana da shi tunda ya yi mini ƙarya"

Ita tana kuka Mami na kuka "Shiitttttt ya isa haka kinga ba ki da lafiya ki bar kukan haka"
Chapter 75 · 0% Book details