Sashe 40
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wanka ta yi tare sauya kaya, bata son ɗan kwali gabaɗaya ta ɗaure kanta har baya ta fito parlour taya Umma yin abin buɗe baki, lokacin ta samu Abbiey suna ɗan magana da Baba ƙarami a hankali kalli ɗaya ya yi mata tare da haɗe fuska da sauri ta juya ɗakko hirami Baba ƙarami yana kallon yadda Ustaz ke zare Idanu da haɗe fuska. Bata sake fitowa ba sai da aka yi buɗa baki ta sha kunun gyaɗa da ƙosai sai fruits komai take tunaninta yana kan Zameer yadda yake lumshe idanunsa sa zubin halittarsa da adon da yake musamman yadda yake murza shadda _Pretty_ sunan ya yi mata wani irin it was so special to her. Ƙarfe 12 Ustaz ya kira ta bitar karatun Alkur'ani sosai yake mamakin baiwar iliminta abu ne mai matuƙar wahala ka ji ta kuskure amma yawan ya mata tilawa har sau biyu gashi tunaninta ya kaɗai ta tabbas akwai abinda yake faruwa a rayuwar shalalensa.
Har aka kammala azumi a B.u.k dai kullum suna tare da Zameer abinda ya bawa Mardiyya mamaki sosai, sai ta ce ta daina kula shi amma fur ta ƙi ita ba taga dalilin barin Zameer shi ne namiji na farko daya bata kulawa bayan Abbiey ya nuna mata itama mutum ce, ya bata lokacinsa ya nuna muninta is nothing tunda ba ita ta yi kanta ba, kuma shi colour ɗinta ya yi masa hundred percent. Aka sallame azumi akai sallah Mami ta dinga mamakin kaya masu tsadar gaske da Ridayya ke sawa domin ko Zainura albarka.
A zaune a parlour Ridayya ta samu Mami tana mai yin ɗari-ɗari ta tsuguna ta ce "Mami Zainura ta ce kina kira na" Mami ta jinjina kai tare da zubawa Ridayya Idanu, da sauri kuma ta share hawayen daya zubo mata har za ta yi magana sai Ammi ta fito ganin haka ya sa Mami miƙewa ta ce
"Zo mana" Abin ya bawa Ammi mamaki yau Fatima ke kiran Ridayya? Aikinta ya lalace kenan ko me? Ridayya ta bi bayan Mami har ɗaki ta tsaya bakin ƙofa. Ganin inda ta tsaya Mami ta ce
"Shigo mana" Ridayya ta ƙarasa ta nuna mata leda ta ce "Ɗauki naki ne" haɗaɗɗan lace mai kyau da tsada blue and white ɗinkin riga da skirt "Gobe akwai taron family, ki saka"
"Na gode Allah ya saka da alheri" Zainura ta ce "Wannan abayar ta yi miki kyau Ridayya" Ta É—an murmusa ta ce "Bari na cire na ba ki, Abbiyena ya siya mini da yawa"
Kan Mami a ƙasa ta ce "Rabu da ita, ki je kar Abbiey ɗin ya jiki shiru ya yi faɗa" Ta ce "Ai baya nan" Fuskar Mami a ɗaure ta ce "Na ce ki je ko?" Jikinta na rawa ta fita domin har ta fara farin cikin jin muryar Mahaifiyarta. Tana murna ta nunawa Ustaz kayan ya dinga kallon kayan ya ce "Mun godewa Mami"
Taron familyn kowa ya bayyan har su Hajiya da mai ran ƙarfe, Zuhura da Balkisu kowa yana nan Alhji Mansur Rano da Baba ƙarami, sai yaran su. Ammi, da Mami. Farin ciki sosai a zuciyar Mami ganin Zainura da Ridayya cikin kaya iri ɗaya. A ka ci aka sha za a fara tattaunawa Baffa ya ce "Ke tashi kibar nan" Tasan bada kowa yake ba sai ita, ta miƙe hakan yasa Ustaz miƙewa Baffa ya ce "Ya zaka tashi?"
"To bari na dawo na zauna, Ustaza jinin jikina ce, nima na yafe" Mami ta miƙe zata bar wajan Ammi ta ce "Fatima lafiya za ki tashi?"
"Lafiyar kenan"
"Ikon ko na yi miki laifi ne Fatima? Kwana biyu kamar gaba kike dani ma wallahi, me na yi miki? Bafa ni na sheganta miki yarinya ba, bani nakar zomon ba rataya aka bani"
"Don Allah kin ishe ni Maryam, na ce miki wani abu? Rayuwa ce fa kowa ya tashi gina ramin mugunta sai ya gina daidai da shi gudun watarana" a zafafe Baffa ya É—auke Mami da mari kafin ya sauke hannunsa ya sauke wa Ammi lafiyayyun maruka guda biyu tunda ba zata iya marin mijinta ba ta ce
"Ki saurara mini, kin hana ni sukuni kin takura ni haba Maryam me na tsare miki ne? Me na yi miki don Allah kishi hauka ne?"
"Ban taɓa ganin inda abin alheri ya zama sharri ba, ni kika mara Fatima duk ƙoƙari na wajan gina rayuwar Ridayya, kin watsar da ita ko kallo bata ishe ki ba" kuka sosai Ammi take na kissa hakan yasa Hajiya ta ji ba daɗi nan suka ɗorawa Mami laifi ba ta yi halacci ba ta riƙe mata jaririya har girma amma duk a banza ashe take gani. "Hajiya ki yi mini uzuri, babu inda uwa zata haifi ɗa kuma ta bar shi ya wulaƙanta, ku ke a gwada Ridayya cikakkiyar ƴar maye ce ƴar srup duk sanadin Maryam idan kuma hakan shine soyayya babu laifi" Tana faɗin ta fice rai ɓace haƙurinta ya je ƙarshe hakan kuma baya rasa nasaba da kukanta da ta kai wajan Ubangiji.
Ustaz ya dinga kallon Ridayya yana jinjina kalmar shaye-shaye sai yanzu ya fara fahimta wasu lokacin da take masa magana ba kai ba kan gado yawan bacci ko idanunta biyu sai ta dinga lumshe Idanu. A fusace ya damƙi hannun Ridayya ta fara kuka Umma za ta yi magana Baba ƙarami ya dakatar da ita "Ba ruwanki bake kike masa tarbiyyarta ba, ki bar shi"
Kuka take sosai tana "I am sorry Abbiey ka yafe mini don Allah.....," Hannu ya watsa mata a fuska a karo na farko a rayuwarsa idanunsa suka firfito waje fuskarsa ta yi jajur, masifar zafin hannu ne da shi hannu ya ɗaga zai ƙara zabga mata wani marin ya ji ta faɗa jikinsa ta ƙanƙame shi a rikice daga nan kuma ta zube a ƙasa jikinta na rawa da ɓari tana cuccure wa waje guda. Ustaz ya lumshe idanunsa yana murza goshinsa sosai da kyau a hankali ya ce "I am sorry Ustaza...!"
"Gayu an sanku ba a san makwantar ku ba, kaga samarin ƙauyen Nahutun Batsari Giɗaɗo ikon Allah" Zameer ya haɗe fuska ya ce "Wanne cin fuska ne haka Mujahid?"
"Gaskiya dai, bani hakƙina" Zameer ya ciro gudar ɗari biyar ya bawa Mujahid ya ce "Mene wannan ai dubu uku zaka bani, kayan da ka yi opay sababbi ne ko mai shi bai saka ba wlh"
"Sune dani" Mujahid ya ce "Tab, sunanka Zameer Mahboon Dollar fa? Kai da zaka bani dollar naga Naira, Naira ɗin ma ɗari biyar ba girman ka bene" tsaki Zameer ya ja ya fice daga wajan ya nufi makarantar allon domin yamma ne yana zuwa malam ya haɗa shi kula da almajirai yana fita ya tashi ya nufi gidan Mama ta dinga murna data gansa ta ce "Ɗana na kai na, kwana biyu na ji ka shiru na ɗauka ka koma ƙauyen naku?"
"A'a" Ta ce "Wai wanne ƙauye ne?" Ya ce "Ni fa ina da wani deal bana son kina nunawa bake kika haifan ba, zan kawo wata gidan nan ki nuna gyara ake mana sabon gida shi ne muka dawo nan ki nuna yadda nake da nutsuwa hankali da dukiya" Ta ce "A nawa?"
"Kin ji matsalarki ai, ana maganar yadda za a samu miliyan goma kuÉ—i zan ba ki sosai"
"To shikenan"
Kyakkawar mu'mala ke wanzuwa tsakanin Meer da Ridayya, ta daina ganin kyan Abbiey ta janye jikinta yanzu ganinsa take koma baya cikin maza bai iya wanka ba, gashi yanzu yana ɗan haɗe mata fuska sai dai tasan Abbiye mutum ne mai tsananin kwarjini, nutsuwa kamala da haiba kyakkawa ne shi mai tarin baiwar ilimin addini dana boko. Ita kam Zameer yana tsananin burgeta gashi a iya magana kullum suna maƙale a waya. Babban kuskure wanda da shi Zameer ya gina tarko yadda Ridayya ta fara furta masa kalmar Soyayya, ya shure kimar da Ubangiji ya yi mata na ɗiya mace ta nuna ƙaunar ta ga namijin da bama ɗigon soyayyar ce a ran shi ba. Sanda ta faɗa masa tana mai cewa "Ka taimaka mini an ce ba zan taɓa samun mijin aure ba, ni kuma hankalina ya kwanta da kai komai naka yana burgeni" Kasa magana ya yi, sai da ya kira Moo ya ce "Done, she said it, she said she love me wow!" Moo ya ce "Kana da sauran aiki"
Ganin kiran ta ya saka ya É—aga "Muna magana ka kashe" Ya ce "Ridayya dole na kashe na jima ina son ki amma sai naga tamkar hakan ba mai faruwa bane, kina da kyan da zamanki mata a gare ni zai an tona"
"A'a wallahi zan aure ka, ka amince mini please, kai ne ma kafi ƙarfina duk gidanmu babu mai so na sai Abbiey da iyayensa Kullum Baffana ai ban tani yake....," Daɗin soyayya da shauƙi ya saka Ridayya kwasar komai na sirrin rayuwarta dana gidansu ta faɗawa Zameer ya ce "Ina son ki ni ma Baby pretty na" Ta ce "Na gode sosai da amsar ta yi na"
A hankali ya tsuke bakinsa ta cikin speaker wayar ya ce "Mu'ahhh take this as my appreciation" Ta yi murmushi kiss É—in har cikin zuciyarta ya ce "Wannan na waya ne kafin gobe ai haka ake soyayyar" WhatsApp suka koma ta ji ya ce
"I love You Mrs Zameer, i so much love you Baby"
"I love you too"
Huci da fusgar wayar da aka yi ya saka Ridayya juyawa a ruɗe jikinsa taga yana rawa kamar ana kaɗa masa ganji gargasar jikinsa duk sun mimmiƙe a karo na farko taga sauyin yanayin idanun Abbiey ya yi jajur ta miƙe zata kwasa da gudu tako ɗaya ya yi ya damƙo ta "Don Allah Abbiey kar ka dake ni i am sorry please...,"
Kai kawai yake girgiza wa ya kasa magana ya damƙe hannayenta duka biyun cikin nasa, yadda jikinta ke ɓari haka nasa ke yi da ƙyar ya fusgi maganar