← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 118

Sashe 104

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A'a guys karku ɓata zumuncinku akan macen, kai Khalid ka yi kuskure kaima Giɗaɗo ka yi " Shaba ya faɗa yana riƙe dariyarsa musamman idan ya juya ya kalli yarinyar wajan Khairy ya dubu Hanne da har yanzu take tsaye. "Ba ruwan ka Shaba karka shiga abinda ba bai shafe ka ba" Khalid na faɗar ya yi gaba zuwa motarsa. Moo dai couldn't speak saboda al'amarin ya fi ƙarfinsa tunanin rayuwa kawai yake.

"Kece matarsa baiwar kenan ke kishiyar Ridayya ce?"

"Sharri! Kwarankwasa ƙarya ne a gabana a kunne na akan idanuna ya saki matarsa Ridiyya, bayan sun yi yarjejeniyar zata bashi takardun da aka bata na filaye shi kuma ya ce zai sake ta, yasan wai dole duk inda ta je ta dawo wajansa sata komo tunda bata da kowa a duniya sai shi iyayenta sun mace tuni, ita kuma ta ce aradu ta yadda ya sake ta, ya ce ya sake ko sako ɗaya ne? Na rantse da Alkur'ani mai girma ya saki Ridiyya ba tare da idda ba domin tana haihuwa hakan ya faru ji munafukin miji?"

Salati kawai Moo yake yana kallon Hanne zuciyarsa na tsinkewa tana wani irin rarrabewa a ƙirjinsa, ya yi saurin cewa "Haba Hanne ki tausaya mini wanne ce kaɗai hanyar da zan dawo da Ridayya zuwa duniyata wallahi ina son ta, ban san har haka son ta ya addabi zuciyata ba sai yanzu, zan iya rasa raina da ita kawai nake samun nutsuwa, ina jin zan rayu da Ridayya ko zata mini iyaka da taɓa yatsanta ne, bana iya bacci kullum sai ta mini gizau ki taimaka mini, karki bari ahhalin Ridayya su ji wannan batun" Kallonsa kawai Hanne take tana girmama son zuciyarsa ta ce "To shikenan mu je ka bamu wajan zama da abinci" da sauri ya ce "Ok jira ni a nan na samu napep ok" ya yi bakin gate ɗin makarantar da sauri. Moo tausayin Zameer ya ji amma ya san shi da Ridayya har abada.
Zainura na tsaye gefen motar driven gidansu watching them ta kalli komai da komai ta yi saurin yin saving VR É—in na wayarta, ta nufi wajan Hanne cikin sauri tana mata magana.

Japan....
Kallonsa ta yi a hankali ta ce "Abbiey sai yaushe zaka dawo ne?" Ya dube ta ya ce "Soon" Ta marairaice sosai ganin yanayinta ya saka ya kama hannuna ya ce "What? Ba mun yi sallma ba daga nan airport zan shige"

"I will go with you"

Ya kalle ta da kyau sai ya nuna mata cikin jikinta ya ce "Sai kin haife mini wannan babin ɗin, na ƙara miki wani cikin ko ki mini" Ta tura baki cikin shagwaɓa ta ce "Tab, ni daga wannan ban kumawa ɗaukan ciki wahala dakon shi haka haihuwa kai duk me ka sani"

"DaÉ—i"

"Me ka ce?"

"Na san daÉ—i mana, kema haka É—aukan ciki dai daÉ—i gare shi Ustaza" Cikin jin kunya ta É—auke kanta gefe ya kai tafin hannunta zuwa bakinsa ya yi kissing so lightly in a romantic style "I need u" ta yi masa gwalo ta ce "Abbiey"

Ya yi ƙasa da murya sosai yana sake damƙe hannuna ya ce "Are You okay with me? Please Mintyna open ur heart ni mijinki ne kuma sirriki muna samun saɓani wannan duka nrml ne ga ko wanne ma'aurata but ban san zaluntarki ta wannan ɓangaren na san akwai alkunya" Ridayya ta sake yin ƙasa da kanta tana murmushin ya ce "Talk Ustaza"

"You are the best Abbiey, na gamsu sosai" ya saka hannu ya dungure mata kai ta ce "Auchhi"

"Allah ya yafe miki Ustaza ba ki taɓa appreciate ƙoƙarina ba, kin san ni ba inji ba, ur words make me feel enough and encourage my energy" Ta yi saurin ɓoye kanta a should ɗinsa tana dukan ƙirjinsa a hankali kuma ta fara shafa sumar da ta yi kwance jikinta ya saki ta ji mijinta kawai take buƙata wani irin son Abbiey take kamar rai kuma har yanzu bata taɓa mayar masa da raddin he loves him ba, tana jin kamar bata cancanci zama matarsa ba still har yanzu kuma hankalinta a tashe yake kullum cikin fargaba yake. Tana jin yana jan hancinta underneath his breath ya ce

"I love you Ya Rouhi"

Ta yi shiru can ta ɗago kanta, ya zuba masa idanu with different emotions dake cin ranta da zuciya, for the first time a rayuwarta ta matsar da fuskarta zuwa gare shi, hakan ya sa ya gyara zuwan al'amarin da kyau..... She just give him a hot and deep kiss on his lips sai kunya ya kamata tunda wannan shi ne karon ta na farko, sosai take jin kunyar Abbiey a wannan ɓangaren tana ƙokarin matsawa ya yi saurin riƙe fuskar nata ya shiga bata sumbata halattacciya ƴar sunna irin wacce aka halatta wacce kuma ya karanta. Sai abin ya zama na su biyun ita ma ta cire kunya aka koma ban gishiri na baka manda da sauri ta yi baya ta ce

"Zan yi test"

Ya yi miskilin murmushi ya kasa cewa komai can dai ya nisa ya ce "Thank you, Allah ya yi miki Albarka Ustaza, ya sauke cikin aminci ya kare ki bisa kariyarsa.... Jazakilla bil khair Nisful hayaat, i love you Miftaahu qalbiy"

Sosai ta ji daɗi ta kama hannunsa ta ce "Wasiymna, Allah ya kare ka da kariyarsa ya kare ka daga sharrin mutum da aljan, ya ƙara baka buɗi da arziƙi mai amfani ya wada taka da kyakkyawar zuciya ta taimako, ya kiyaye ka daga sharrin ƙarfe, Allah ya raba ka da haram ya haɗa ka da halak Allah ya tsare mini Qalbiy" Bashi da wani option wanda ya shige rungume ta sosai zuciyarsu ke bugawa da ƙyar ya cire ta, ya fita ya buɗe mata mota ta fito jingina ya yi da motar yana kame kansa da kyau fuska a kame ta ce "Abbiey zan shiga Allah ya kiyaye"

Kai kawai ya jinjina mata idanunsa na yawo a harabar makarantar kamar mai duban wani abu, har ya juya sai kuma ya tsaya kamar bai son magana ya ce "Ki kula ok?" Ta ɗaga masa kai tana tsaye har ya bar makarantar..... Hankali kwance ta gabatar da karatu da kuma test ɗinta sallah ke tayar da ita jikinta ya mata nauyi sosai ƙafarta ya kumbura ainun, ƙarfe biyar ta fito tana kiran number drive kamar daga sama ta ganshi ta yi saurin ja baya, sosai ta razana ganin kamar ba shi ba ya yi duhu sosai ya rame.

" I couldn't sleep shanshan, don Allah ki tsaya muyi magana idan tsoro kike sbd cikin nan ni ban ɗauki hakan a komai ba sai ƙaddara kuma ke ɗin nake so ba wani abu naki ba" Ta yi shiru Sadauki ya matso gabanta ta yi baya da sauri ya cafko hannunta a gigice ta saka hannu ta zabga masa mari ta ce "Ka dawo hayyacinka Sadauki ba cikin shege na yi ba, ina da aure ina da aure matar aure ce ni, cikin sunna ne a jikina"

Dumm!! Haka Sadauki ya ji a kansa tamkar a duka masa wani abu, ya dinga kallon Ridayya can ya ce "Zan so ki ƙara marina ko zan farko daga mafarkin da nake, wannan kalman naki na banza ne wasa kike mini, day by day haka nake rayuwa da tunaninki, soyayyarki, ƙaunarki a zuciyata ba za ki iya auren wani ki bar ni ba, ba cancanci hakan ba"

Kuka ta fashe da shi sosai tana girgiza kanta ta ce "I am sorry i am sorry Sadauki " da ƙyar ya ce "Is like something wrong with you?"

"Yes seriously I have something to tell you, i want to apologize for my actions. I realize now that i made mistake by prioritizing financial status over our relationship. I deeply regret hurting you and i understand if it's difficult for you to forgive me".

"Me kikai?"

"I choose someone over you "

"After a year? Duka wanna Ridayya da wanna maganar gwara ki ɗauki wuƙa ki caka mini a ƙahon zuciya Ridayya, gwara tun Fil'azal ki ce bani kike so ba da ki dinga wasa da feelings ɗina, me ya sa?..." Wani irin hawaye ne ya fara zuba daga cikin idanunsa wanda bai shirya musu ba, ƙirjinsa ya dinga ɗagawa jijiyoyin kansa suka firfito magana yake son yi amma ya kasa ya riƙe saitin zuciyarsu da ƙyar ya ce

"You broke my heart Ridayya, ki tausaya mini don girman Allah.... I love you Shanshan Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun! Wasbunalallahu wani'imail wakil Ubangiji ka ɗauki raina my heart hurts my chest is burning Ridayya why? Why don Allah why are you doing this to me?..." Cikin kuka tana durƙushewa ƙasa dafe da cikinta ta ce "Sadauki stop all this forgive me don Allah" Ya girgiza kawai tears running down to his face wasu na korar wasu ya ce "I just forgive.... But will never forget"

Kuka gabaɗaya suke da ace zata iya auren maza biyu tabbas data auri Sadauki ta haɗa biyu shi da Abbiey amma bata da wannan ikon. Tari ya fara da ƙarfi jini ya fara zuba hanci da baki yana ƙoƙarin miƙa hannu ya taɓa ta, da ƙyar ya ce "I will die for your love Ridayya Ubangiji shi ne shaida, stay with me please hold my hands ko sau ɗaya" Girgiza kai ta yi ta ce "I can't i can't Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun na shiga uku wai meke damuna mene ya yi coursing problems ɗin nan a rayuwata why all this happens to me, forgive me please Sadauki a gigice ta yunƙuru tana nufar kansa ganin idanunsa ya yi sama zuciyarsa ta daina bugawa ta fasa ihu ta ce "Karka ka mutu Sadauki don Allah karka mutu i love you....." Ta girgiza shi ta taɓa zuciyarsa bata bugawa ta taɓa agogon hannunsa baya harbawa wani irin ihu ta yi ta ta ce "Nooooo karka mini haka Sadauki don't leave me

Daga yau in sha Allah kullum za a dinga yi har a kammala babu jira kuma kafin sallah mu idda ai alamu ya nuna ma...

A yi comments a yi sharing
08164069385
*MUNAFUKIN MIJI*

Nimcyluv......
45

*Masu arewabooks ku yi following account ɗina domin samun duka books ɗin 👇🏻*
https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv
Chapter 104 · 0% Book details