← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 118

Sashe 80

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai duk jikin Anuty Kaltum ya yi sanyi domin an faɗa mata matsalar Ustaz da halin da yake ciki, kawai Ridayya za ta yi sacrifice farincikinta da ƙuruciyarta just to be with him da kuma abinda ya yi mata na alheri, kinga an saka alheri da alheri a inda ya dace ga matsalar uwar miji sai gorin baƙar fata take mata da muni wai kuma ita bazawara ce"

Yamara ta saki dariya sosai ta ce "Kan uba ji wani zunubi za ta yi wa kanta domin wallahi soon zai fara bijire mata, wake tsayawa tunani idan zai faɗa soyayya ita take ganinta a bazawara amma shi kallon yarinya budurwa yake ba, so na gaskiya baya buƙatar dalili ko hujjar yinsa, idan don haka yake son ta to tabbas kawo yanzu daya daina amma ya fasa? Wallahi ta kiyaye zuciyar data kamo da matsananciyar soyayyar mace domin ta fi komai illa kuma bazawara za taga aikin zawarawa"

Anuty Kaltum ta sauke ajjiyar zuciya Mami ta yi kamar bata san me ake cewa ba, domin daman ita magana bai wani dame ta ba Yaya A'isha ce take ta dariya ita kaÉ—ai.

"Ke dai Allah ya kyau don ma na bugi cikin yarinyar data haifi Little an yi mata ɗinki ita fa empty head ce a ɓangaren soyayya da zama da miji karatu na musamman nake so ki yi mata idan mun zo Barno"

Sun jima suna tattaunawa sukai sallama Yaya A'isha ta ce "Wallahi ina jin tausayin Ustaz wannan a corner zaku saka shi"

"Bari uwarsa ta ja masa wallahi kwana nan zai zama Munafukin miji akan Ridayya don wallahi zai ta share masa wannan tuzuruntakar tashi zai yi alfahari da ita"

Kafin su tafi Anuty Kaltum ta je ta samu MB USTAZ a part É—insa na gidan domin tuni ya tsara yadda yake so a yi masa ginin gidansa Mardiyya tana nan tare da shi Ridayya kuma ta gudu wajan Mami yana zaune saman kujera ya kame nutsuwarsa da ilhmarsa ta bayyana bayan ya gaishe ta, ta numfasa ta ce "Alfarma nake nema za mu ke je a nuna matarka a dangi tunda ba a santa ba"

"Ina?" Ya ce a taƙaice ta ce "Nan cikin garin Kano mana" Ya dinga mamaki bayan su daya sani Mami na da wasu dangin kenan

Jin ya yi shiru ta ce "A bamu permission ba riƙe maka mata za mu yi ba"

Ya duba agogo ya ce "Ok kar ta yi dare"

"Wanne dare kuma ai kwana za ta yi wata guda ma za ta yi ai dangin da yawa wasu basu taɓa ganinta ba, to kafin ayi bikin muke buƙatar su ganta basai an kai musu katin bikin ƴar wajan Fatima ba su ga ba a kyauta musu ba"

Ya miƙe tsaye yana gyara zama babbar rigarsa idan ka kalli Ustaz zaka ɗauka yana da tarin zuri'a saboda tunaninsa da kamalarsa da kuma tsare gira banda tsantsar kishin tafiyar babu abinda take gani a idanunsa.

"Wannan cutarwa ne ai haramun kuke son aikatawa"

"Subuhanallahi haramun kuma?"

"A'a kifa daina salati kamar ba ki gane ba, yanzu don Allah ya General zai ji ki tafi ki barshi har wata guda?"

Anuty Kaltum bata taɓa tunanin ya san sunan mijin nata ba sai yanzu furr ya sakawa idanunsa toka yaƙi yarda.

"Wannan mijin na Ridayya akwai taurin kai da miskilancin tsiya kinga yadda yake mitsi-mitsi da Idanu wai idan ni ce zan tafi wata guda ya General zai ji kamar wanda ya san daÉ—in mace"

Murmushi kawai Mami ta yi ta ce "Babban mutum kenan zai aikata"

Washegari ya shirya tsaf cikin wagambari mai tsadar gaske zai je meeting ɗin da aka yi inviting nasa na Madugu daga nan sai ƙarasa police station. Fuskarsa fau tana wani yellow saje da ƙasumbarsa sai kyalli suke da sheƙi suke ya yi wani irin kyau ya rusuna ya ce "Abba Umma barka da safiya"

"Barka Babban mutum an fito?" Ya jinjina kai Umma taƙi amsawa "Sai ina?"

"Zan É—auki Ustaza za mu É—an je wani waje"

"Bada yawo na ba, idan har nono na kasha wallahi babu inda zaka fita da ita"

Ustaz ya kalleta ya ce "Asibiti za mu ga? Hakƙina ne kula da matata idan ba Ubangiji kike so ya yi fushi dani ba, wallahi Umma ba kyau shiga tsakanin ma'aurata"

"Ni kake faɗawa haka? Ina faɗa kana mini bita tare da ɗora mini hadda? To wallahi sai ka sake ta a yanzu maza ka sauwaƙe mata"

Baba ƙarami ya tashi ya ce "Hadiza ban hanaki kar ki tursasa Babban mutum wajan sakin matarsa ba, amma ki sani sai dai ku yi zawarci tare da Ridayya yana sakinta zan ɗora miki naki saki ukun, kuma zan buɗe idanu na zaɓo kyakkawa budurwa dal na aure ki daina ganina da furfura kyakkawa ne ni domin a waje na Muhammmmd ya kwashi rabin kyau, wallahi da gudu za a fara rububina zan auri budurwa mu sha soyayya, idan wacce zata ƙwace ni har abada ne sai na nemo ƴar Maiguduri, idan ilimi nake so na nemo ƴar Abuja idan wayewa ne na ɗauki ƴar kaduna, idan soyayyar ce ƴar Kano,idan biyayya ne Zamfara idan kishi ne Sokoto ko Katsina don haka ki bi a hankali, wallahi wallahi Allah kika saka ya saki Ridayya sai na sake ki kuma na auri budurwa sai ki zaɓa zawarci tare da surukarki ko haƙura da ƙaddarar Ubangiji"

Baki Umma ta saka Baba ƙarami ya ce "Jeka Allah ya tsare Babban mutum"

MB USTAZ ya sauke numfashi ya nufi ɓangaren Mami lokacin suna zaune a parlour Zainura sai ƙoƙarin haɗa breakfast take ya shigo ta ce "Yaya Bilal good morning?"

Bai kalleta ba bai amsa ya nufi wajan Mami yana durƙusawa ya ce "Barka da safiya Mami"

"Barka Babban mutum ka wayi gari lafiya?"

"Cikin aminci Mami" kunyar surukai duk ta kamata shi kam ko a jikinsa ya juya yana miƙewa ya ce "Ustaza bata shirya ba?"

"Tab ai dai ka je ka taso, da alama ka sangartata da baccin safe tun ɗazo nake abu ɗaya" MB USTAZ ya zaro idanu yana duba agogo ta nuna masa direction ɗin bedroom ɗin ya tura yana yin sallama underneath his breath. A kanta idanunsa ya sauka tana tsaye gaban wardrobe tana ƙoƙarin maƙale bra ɗinta bata ji sallamar ba balle ta ji zuwan shi, sai saukar lips ɗinsa ta ji a tsakiyar bayanta da laɓɓansa masu sanyi ta yi saurin sakin rigar tana juyawa a tsorace bakinta na rawa ta ce "Abbiey" ya yi saurin ɗora yatsarsa a bakin "Why Ustaza? Ni kike gudu" ta yi narai narai da Idanu ya sunkuya ya ɗauki rigar ya juyar da ita ya saka mata yana ɓalle ɓallin ta ce "Ba kyau fa Abbiey" idanunsa duk wani ya kala ya ce "Mene babu kyau?" Ta ce "Ganin jikina da gaske ba kyau haramun ne"

A taƙaice ya ce "Bari na yi abinda yake mai kyau kuma halal" zillawa ta yi ya girgiza kai ya nufi waje ya zauna yana danna wayarsa shiryawa ta yi cikin brown colour ɗin Abaya mai ɗan faɗi ta saka igiya ta ɗaure ta yi rolling kanta ta saka pech ɗin lipstick ta yi fresh da kyau a hankali ta dawo ta tsuguna ƙasa ta miƙa masa hannu ya ajjiye wayar ya miƙa mata nasa hannun sukai musabaha ta ce "Good morning Abbiey"

"Kin tashi lafiya?" Ta ce "Lafiya lou, ya jiki?"

"Uhm bakin ki ne jikin zan gwada miki ƙalau nake"

Ta kasa kallonsa ya ɗagota ya ce "Zo mu yi special gaisuwa" a kan ciyarsa ya ɗora ta ya juyo da ita ya sunbaci goshinta da kumatunta a hankali ya ce "Allah ya yi miki Albarka Ridherh" Ta yi ƙasa da kanta ya ce "Ki faɗawa wannan masifaffiyar Anutyn taki ta zo ta ɗauke ki ku je unguwar za ki bani address wata ɗaya ya yi yawa, daga nan zamu je asibiti idan mun dawo za a yi bikina da matata"

"Wanne asibitin?"

"Za ki gani ne, sati biyu za mu a asibitin bana son a sani fa appointment nake jira na asibitin"

"To wa za a kai?" Da yatsa ya danna ƙirjinta tsakiya ya ce "Mijin Ustaza"

"To bikin naka Mardiyya ce matarka?" Ya ɗage mata kira sai ta shagwaɓe fuska ta fara kuka wiwi "Wallahi ka nemo wata matar ni bana son ta ka zauna kawai babu aure" Ta dinga kuka tana yarfe hannu tana diddire ƙafa ƙugunta sai rawa ya zubawa ƙugun idanu sai kawai ya miƙe.

Da ƙyar ta yi shiru a parlour ya ɗauki Little Bilal daman tuni ta daina bashi nono police station suka fara zuwa Ustaz ya cike komai. Ridayya na zaune ɗauke da Little taga mutum tsaye ta yi baƙi da duhu ta ji an ce "Mai sona?" A razane ta ɗago kai jin muryar da ba zata taɓa mantawa da ita ba a rayuwarta sukai Idanu huɗu da Zameer a gigice yake kallonta ganin kamar ba ita ba, ya ji duk wahalar daya sha a rufe ta kau ya ji wani abu da bai taɓa ji ba yana motsa masa a zuciya wani abu mai kama da zahirin so sadidan na gaskiya ya tsirga masa Ridayyan daya ce ta tashi daga aiki yaga kamar yau ya fara ganinta babu alamar ta yi aure ba balle a san da zaman Little ta yi ƙiba ta zama ƴar lukuta ya dinga kallonta zuciyarsa kamar zata ratso ta ƙirjinsa. Ridayya ta yi saurin ɗauke kai da sauri ya nufe ta BM USTAZ ya tare shi "Yawwa matata mai sona ke nake ta jira lovely mu koma gidanmu ga ɗanmu ya yi wayo" gabanta ya faɗi kar dai Abbiey mayar da ita zai yi? Officer ya ce "Hajiya kin shi? Wannan mijinki ne?" Ridayya ta haɗe rai ta ce "Gaskiya ban taɓa ganinsa ba sai yau bani da haɗi da shi" Gaban Zameer ya faɗi muryarta na rawa ya zube gaban Ridayya kamar zai yi mata sujjada bai taɓa jin abinda ya taɓa jin irinsa ba "Wallahi ke matata ta ce ga ɗana nan wajanta, ni ba ruwana da filayen ma matata kawai nake so" Officer ya ce "Hajiya kin ji?"
Chapter 80 · 0% Book details