← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 118

Sashe 89

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya mata shiru sai da ya gama hargitsa wajan ya É—ago ya sake kallonta can ya ce "Wanne mai da turare kike using?"
Da yatsa ta yi masa pointing wani mai na Aloe vera. Ya girgiza kai sai ya matsa ya sake riƙe kafaɗunta ya shafa da sauri ta rufe idanu saboda amsawa da jikinta ya yi, ya sake murza fatar wajan wani irin laushi da santsi haɗe da taushi yake ji, bai taɓa jin abu mai laushi kamar fatar jikinta ba, gata dai baƙa amma fatarta na shirin sa shi abinda bai niyya ba. Ita dai kanta a ƙasa bata san halin da yake ciki ba muryarsa bata fita sosai ya ce "Uhm" har zai juya sihirtaccen ƙamshin na asalin haɗaɗɗiyar kwalaccar Nana da wata shekararriyar humra ta Nana ya shiga hancinsa ya shaƙe shi da kyau ya damƙi hannun Ridayya ya sakko da ita ƙasa cikin sauri a kamalance kuma ya zura hancinsa da kyau a wuyanta ƙamshin ya zauna masa sosai ya yi masa wani irin daɗi, so yake ya tantance ƙamshin wanne turare ne amma sam ya kasa ya ƙara ɗora hancinta saman ƙirjinta ta yi saurin riƙe kansa ta ce

“Abbeee....," Sauran abinda ta ji ya saka ta ja sunan nasa tana riƙe shi, jininta ya ɗauki rawa da kakkarwa bata taɓa zaton haka ba, sai gashi Ustaz ya rikiɗe mata zuwa Simba ta fara shassheƙar kuka tana yarfe hannu ya ɗago kansa ya dube ta, ya dake shi kansa ya ji kunya ganin abinda ya yi wa jaririyar tasa ta dinga yarfe hannu tana ɓoye ƙirjinta ta mayar da rigar.

"Kin bar ni da yunwa" ya yi saurin ficewa da bashi da abin faɗa, ji ya yi ma kamar zai yi zazzaɓi wallahi bai taɓa tunanin hakan al'amarin yake ba.

Yana ta zaune saman kujera can ya miƙe ya nufi bedroom ya shiga bathroom wanka ya yi mai kyau kuma da kyau, ya saka armless da wando iya qwiwa samun kansa ya yi da ƙarewa kansa kallo sai ya ji yana son saka turare ko Ridayya zata shaƙa watarana.

Ya fito fuskarsa wasai kamar bai yi komai ba, ya samu Ridayya zaune ta jera breakfast É—in ya zauna saman kujera.

"Bani abinda ki ka yi?" Ta buɗe plate ƙwai ta soya mai yawa da kuma soyayyen dankali ta haɗa masa green tea ta saka spoon ta miƙa masa da hannu biyu ya amsa ya ɗora a cinyarsa. A hankali ya dinga cin abinci yana ratsa shi sukai shiru can ta ji ya ce

"Zo mu gaisa mana Oum-Bilal" ta miƙe tana ƙoƙarin zama ya jata saman cinyarsa ta ce "Ina kwana?"

"Yana kwano"

Murmushi ta saki domin basa ƴar haka dashi ya ce "Ya baƙunci? Kina cikin aminci?"

"Abbiey wai ina ne nan" yana bata ƙwan a baki ya ce "Japan" ta sake yin murmushi ta ce "Zaka saka ni a jirgin ruwa irin na ƴan India?"

Zuba mata idanu ya yi tana cin abinci tana masa surutu da yaƙi tankawa ta shiga wasa da gemunsa, mamakin ƙuruciyarta da saurin manta abu kawai yake, ɗazo ya yi mata abu har ta kasa haɗa Idanu da shi amma yanzu ta manta. "Iya jirgin ruwan? What about the babies?"

"Ka siya mini teddy babba mai irin tsayin Little" ya yi murmushi yana girgiza kai ta saka cewa "Wai baka da lafiya ko Abbiey?"

Ya ɗage mata duka girarsa biyun ya ce "Haka na ji" ta shiru can ta ce "Abbiey ka amshi kujerar da suke maka magana saboda Allah, da kuma al'ummar Musulmi. Ina da tabbaci da kyakkawar zuciyarka kuma ina da yaƙinin za ka yi nasara, kawai ka saka Allah a ranka ni zan tsaya maka ai kaga na isa yin zaɓe kuma ina da voters card zan zaɓe, I'll be by your side zan yi supporting naka kuma da ina da ƙawaye sai na saka duk su zaɓe ka amma bana da su, nasan za a dace. Ubangiji yana bayan mai gaskiya kuma kana da ita ai kaga zaka zama Gwamna ka yi aiki mai kyau wanda ko bayan baka nan za a yi alfahari da kai, please say yes"

Ta faɗi yes ɗin a shagwaɓe tana narke murya ya juya ya kalleta can ya ce "A matsayinki nawa a wajena kike bani shawara?"

"Matarka"

"To, stop calling me Abbiey"

"Zan daina to ka ce ka yarda" ya shafa kansa yana zamewa tare kwanciya a cinyarta ya ce "I'll think about it...,"

"Yaushe?"

"Idan kika bani baby" shiru ta yi kawai ya sake mata dukkan nauyinsa ya juya fuskarsa zuwa wajan cikinta...

Ya jima sosai tsaye a ƙofar gidan yana jin kamar ya shiga ciki kamar kuma ya tsaya,he can't go without talking to Ridayya, mai son shi da ƙaunar shi bai taɓa jin abinda yake ji game da ita ba a yanzu, bashi da sukuni bashi da wani lokaci sai nata kullum cikin tunanin muryarta yake, bai taɓa zaton Ustaz na raye ba da ba zai yi gangancin da ya yi ba, ya zama dole ungulo ta koma gidanta na ainahi.

Yana tsaye Zainura ta fito kyakkawar yarinya fara tas sai ya ji farin bai wani birgeshi ba ƴar baƙarsa yake son gani. Kallon sama da ƙasa ta yi masa dukda kwarjini irin na Zameer ta ce
"Kai kake neman Yaya Ridayya?"

Hadda murguɗa masa baki ta yi Little yana tsaye kusa da ita hannunsa riƙe da chocolate ya ce "Ba ki gane ni ba ne Zainu?"

"What? Na haÉ—e dangi da kai ne da zan gane ka? Ko kuma ce maka a yi gantalalliya ce ni? Ko da yake ai babu mamaki Bakatsine haka yake" da mamaki Zameer ya ce "Ni kike faÉ—awa haka? I'm older than you..."

"Matse maka ta yi kai da older ɗinka wani guntun turanci irin na fulanin katsina, kuma kar ka sake zuwa ƙofar gidan nan domin bamu da haɗi da kai" Takaici ya kama Zameer ya kalli Little ya ce

"Come my boy" ya maƙale ka faɗa da Zameer ya yi ƙoƙarin ɗaukarsa ya saka ihu yana riƙe Zainura. Suna haka Junaid ya fito cinin shigar yadin voyel ya kalli Zainura ya ce "Shiga ciki"

Har ƙasa Zameer ya durƙusa ya gaida Junaid abinda bai taɓa yi ba, Junaid ya ce "Lafiya Malam?"

Zameer ya shafa kai ya juya ya kalli gidan sai kuma ya kalli Junaid ya ce "Daman matata Ridayya na zo gani"

"Matarka? Daman baka sake ta ba?" Ya zaro ido yana girgiza kai ya ce "Cewa ta yi na sake ta? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ashe ƙiyayyar da Habibty ke mini da gaske muna zama lafiya ta ce dole sai na sake ta, na ce ba zan iya ba domin ina son ta da gaske masifar yau daban ta gobe daban sai wayagari muka yi ta gudu, to; ta mance da takardun filayenta na yi yunƙurin siyarwa da gangan na san dole sai wani nata ya bayyana cikin sa a na samo gidan nan" Mamaki ya cika zuciyar Junaid kenan Ridayya AURE TA YI KAN AURE? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un dole duk inda take ta dawo haka Ustaz.

Yana ƙoƙarin magana yaga an fito da Mardiyya tana kelaya uban amai kamar zata mutu, Umma sai murna take a tunaninta ɗanta Ustaz ne ya saka ƙwallo a raga ganin hakan ya saka Junaid bawa Zameer haƙuri ya bashi uzurin gobe ya dawo.

A can Japan dukda babban gidan da suka sauka a gyare yake kuma gida mai tsari irin na turawa bai hana Ridayya ƙara share ko'ina ba ta yi mopping kana ta ɗora musu dinner domin bata iya cin abincin ƙasar, shi kuma abinda ta ci shi zai ci. Ta gama komai ta yi wanka ta saka riga da wando amma wandon iya qiwwa ne rigar kuma mai faɗi ce tana da kauri ta kunna hiter ta ɗumama gida.
Misalin 8:2 daidai ya shigo cikin main parlour ɗin wanda yake a zagaye ya haɗu sosai, yana shigowa ya lumshe idanunsa yana mai tasbihi a ransa a hankali ya buɗe idon daidai fitowarta da sauri ta ƙarasa tana "Oyoyo Abbiey, na yi ta jiranka ina jin tsolo" riƙe kansa ya yi da kyau ta amshi kayan hannunsa ta dinga mamakin shigarsa wasu jersey ne masu bala'in kyau kuma duka baƙaƙe sai hula daya jata har kunne sumarsa ta sauka, yana yin numfashi hayaƙin snow ke fita daga bakinsa da hancinsa. Ganin bai yi magana ba ta fara ƙoƙarin kama hannunsa ya yi saurin zamewa yana waro mata idanu ya ce "uhm a'a"

"Kar na taɓa ka?" Ya jinjina mata kai kamar yaro da sauri kuma ya shige part ɗin da yake.

Tana zaune shiru shiru bai fito ba, shi kuma yana can saman gado sai juyi yake ya yi nan ya juya nan, bai taɓa jin zafin ƙaddararsa ba sai yau, gani yake jaririyarsa ta yi muguwar ƙanƙanta da ɗauke buƙatunsa bai kuma saba ba, bai san yadda ake ba, wata kunyar ƴar tashi yake jaririyarsa ƴar rainonsa. Daga shi sai boxer amma duk sanyin garin zufa ke tsasstafo masa yana tsananin buƙatar matarsa shekaru wajan arba'in ba wasa bane. Wayarsa ya jawo ya nemi numberta daman ita ce last kira tana ɗaga kiran ya ce

"Come" yana faɗin hakan ya kashe ya kifa cikinsa idanunsa rufe, yana a haka ya ji ta shigo da sallama bai amsa ba ta ƙarasa ta ce "Do you need something?"

Ya yi shiru
"Abinci za ka ci? Ko baka da lafiya ne?"

Duk ya yi mata shiru ta miƙa hannu zuwa wuyansa ta ji zafi sosai kafin ta ɗauke ya damƙota tare da fincikota zuwa saman gadon ta faɗa jikinsa ya riƙe ta gam, idanunsa rufe ya miƙa ya kashe hasken ɗakin magana yake son yi amma ya kasa laɓɓansa sai rawa da ƙyar ya furta. "Yes; i need you, i need to feed on you.....,
Chapter 89 · 0% Book details