← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 118

Sashe 22

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka dai na yi mini tsawa, nikam ka daina bana so, a gaban yara Baffa kalli yara kake mini tsawa a gabansu?" Babban ɓacin ran Bilal har da mutanen da bai taɓa ganin su ba sai yau, amma Baffa zai masa tsawa a kan idanunsu salon su raina shi? Bayan kowa ya san da shekarunsa a ka. Baffa ya ce "Sannu gyanbo, Bilal ka basu shegiyar ƴar su na ce"
Idanun Bilal ya shige ciki saboda ɓacin rai, suka yi jajur jijiyoyin kansa duk suka fito, ba matsalar ƴar ce gabansa ba, damuwarsa faɗan rainin wayo da rashin tubalin yinsa, shi ba wanda ya yi masa faɗa sai shi za a yi wa? For God sake!

"Bilal ni Baffanka ka ke yi wa haka? Ni?" Bilal ya ƙara nutsa idanunsa a cikin na Baffa ya ce "A kan idanuna kake musayar yawo da Hajiya, Hajiya fa, ashe ba daɗi?"

"Me kake nufi da ɗaukan yarinyar nan?" Kai tsaye ya ce "Rainonta zan yi, zan kula da ita, kyautar da ubangiji ya baka ka wofintar ni ina so, zan kula da ita da izinin Ubangiji zan kuma aurar da ita da ƙudirar Allah" Murmushin takaici Baffa ya yi ya ce "Ok, bada kuɗina ba, ba kuma da abinda na mallaka ba zaka ciyar da ita ba, kuma ka tattara kayanka ka bar part ɗina" Bilal ya jinjina kai don baya jin zai iya magana har yanzu idanunsa cikin na Baffa, ganin yana shirin juyawa ya saka Baffa cewa
"Ka basu Æ´ar nan na ce, Muhammad-Bilal"

"Baffa?" Bilal ya faɗa a rikice yana jin tsawar har tsakiyar kansa, ya taka har inda Baffa yake ya kama hannunsa ɗaya ya damƙe sosai ya ce
"Na roƙe ƙa da ka tsahirta haka nan, ban so da gaske ban so, nikam ban son tsawa, ka bar daga ni sai kai ka yi mini" Baffa ya ce "Sannu ubana" Bilal ya sake runtse idanunsa gam kamar ya nutse a wajan ganin yadda Baffa yake shirin zubar masa da girma "Kashe ni kawai Baffa zai fi wannan" sanin Bilal da masifar taurin kai da son girma ya saka Baba ƙarami cewa "Babban mutum jeka, Allah raya maka ɗiyarka ya sanya mata albarka" Bilal ya lumshe jiƙaƙƙun idanunsa da sukai laushi ya jima kamar ba zai magana ba ya ce "Amin Ya Allah, na gode ƙwarai Baba ƙarami"

"Wanne suna ka saka mata?" Ya yi sak domin bai yi mata huɗu ba sam, yana buƙatar tantance sunan da zai saka mata a hankali ya ce "Zuwa gobe zan saka mata suna" Baba ƙarami ya jinjina kai ya ce
"Allah ya kaimu" Yaya A'isha ta ce "Babba mutum kawo ta, zuwa anjima sai ka amsheta" Bai kalli Yaya A'isha ba, ya ɗan kalli fuskar jaririyar yana sake ƙanƙameta a ƙirjinsa ya jima sai kuma ya miƙa mata ita da ƙyar yana bata yabar cikin asibitin. Yaya A'isha ta juya zuwa cikin room ɗin da Mami take kwance tana hutawa hannunta ɗauke da baby. Anuty Kaltum kuma ta kalli Baffa ta ce
"Muna jiran takardar sakin Fatima, domin gida zamu shige da Ita"
"Ban niyya ba, ban shirya rabuwa da matata ba, kuma kar a kuskura a tafi da ita idan har nine mijinta" Yana faɗin haka ya fita, Anuty Kaltum za ta yi magana Dada ta hana. Kuka sosai Hajiya ke yi Baba ƙarami na bata haƙuri, kana suka dinga bawa su Dada dangin Mami haƙuri akan komai zai shige. Zuhura da sauran yaran suka tafi gida. Zuciyar Baba ƙarami babu daɗi takaicin abinda ɗan'uwansa ya yi, ya masa tsaye a zuciya.

Har kwana biyu jikin Mami bai yi daidai ba saboda jijjigar da ta yi, sai a kwana na uku ta dawo hayyacinta bayan ta buɗe idanu ganinta ya sauka a kan Dada dake zaune hannunta riƙe da azkar, motsin da Mami ta yi ya saka Dada juyawa cikin farin ciki ta ce
"Ma sha Allah autata ta farka" Ƙuri Mami ta mata kafin ta ce "Me na haifa?" Kai tsaye ta ce "Ɗiya mace Allah ya ba ki Batool ɗina" Mami ta yi ajjiyar zuciya ta ce
"Ki yafe mini Dada haihuwa akwai wahala, Allah ya saka miki da alheri da kika haife mu kika kula da mu, bamu da abin saka miki wallahi na ɗauka mutuwa zan yi haihuwa da wahala Dada" Dariya Dada ta dinga yi ta ce "Su Autana an girma an son zafin haihuwa da ciwon uwa, ba ki mini komai ba Allah ya raya mini ke da jikata cikin aminci da kwanciyar hankali" Mami ta yi murmushi, sai rarraba Idanu take taga ta ina za a bata babynta? Ta faɗa mata azabar data sha kafin samuwar ta. Ta kasa haƙuri ta ce

"Ina babyn?" Daga bayanta aka ce "Kima cire ranki daga ita Fatima" a rikice ta kalli Anuty Kaltum ta ce "Saboda me Anuty Kaltum?" A fusace ta ce"A saboda ubanta ya ce shegiya ce ita, bashi ne mahaifinta ba, ki nema mata uba wani wajan" Mami ta dinga kallon bakin Anuty Kaltum kamar zautacciyya, hawaye na zuba daga cikin idanunta ga wani azabar ciwo da nononta ke mata ya cicciko alamar babyn na buƙatar abincinta "Ban gane ba ƴarsa ba ce? Wallahi tallahi tunda nake a duniya babu namijin daya taɓa riƙe hannuna, Baffa ne wanda ya raya daren aurenmu, me na yi masa da zai haɗani da wannan masifar? Anya Baffa ne?" Kuka take kamar ranta zai fita ga ɗinkin dake cikinta nan da nan jikinta ya nemi rikicewa, Dr ne ya shigo yana yi wa su Anuty Kaltum faɗa da ƙyar akai mata allura bacci ya ɗauke ta.
Faɗa Dada ta shiga yi wa Anuty Kaltum a kan a matsayinta na babba don ranta ya ɓaci ba haka ya dace ta yi ba, idan bata kwantar wa da Mami hankali ba waye zai taushe ta?

Bilal na zaune idanunsa ƙuri a kan yarinyar fuskarsa baka tantance yanayin da take ciki. Mahaifiyarsa kallonsa kawai take yi har yanzu bata ce masa komai a kan al'amarin daya faru ba, domin ya tattara ya dawo shashin iyayensa da zama. Ya ɗago idanunsa wanda kullum suke a ƙasa a nan yaga kallon da Baba ƙarami da babarsa suke masa, ya yi kicin-kicin da fuska
"Baban baby har yanzu baka faɗi sunan ƴar taka ba" Bilal ya zubawa yarinyar ido can ƙasa ya ce "RIDAYYA"

"Ridayya" Baba ƙarami ya maimaita kana ya ce "Ma'ana?" Bilal ya miƙe tsaye ya ce "Zuciya, shi ne ma'anar sunan" Ɗakina ya koma ya dawo da wasu ledoji manya manyan guda biyu ya ce "Kayan dana siya nata, gobe za a kawo rago" Baba ƙarami ya ce "Kai, Ma sha Allah har da Ragon yanka? Lallai uban Ridayya mai zuciya ne, ina ka samu kuɗi?"

"Aiki na yi, zan nemi aiki saboda ita tunda na kammala karatuna" Baba ƙarami ya jinjina kai. Ya miƙe tsaye zai shige ɗaki sai a lokacin mahaifiyarsa ta ce "Ina zaka da ita? Ko kana da nonon shayar da ita, ka kaiwa A'isha ita" Sak Bilal ya yi domin ya manta da batun shayarwa ya dinga tunanin wanne nono kuma? "Zan siyo a kanti"
"Shi nonon kenan? Riƙon yarinya na neman sawa ka zauce Babana? Daman nonon a kanti yake ko a jikin uwarta? Bilal ya gwalo ido ai shi ya mance da wani abu a jikin mace kuma a ce da shi ake shayarwa? Juyawa ya yi ya fita kawai tare da barin parlon don yau da yarinyarsa yake son kwana ta ji ɗomin uba kamar ko wacce jaririya.

Washegari da safe Ammi na zaune sai kuka ta ke a kan Baffa ya ji tsoron Allah ya amshi Ridayya, ko ita ce ta amince zata riƙe ta da amana zata kula da ita kamar su Zuhura da Junaid. Tausayin Ammi ya kama Hajiya wacce take shirin tafiya Rano, bata taɓa ganin kishiya mai tausayi kamar Ammi ba, har tattara kayanta ta yi ta ce zata bar masa gidan tunda haka ne. A haukace Mami ta shigo gidan kai tsaye ta yi wajan Baffa ya ce "Baffa ina soyayyar? Ina tattalin ina yardar? Ka tausaya mini kada ka aibata ƴata, bayan ita halastacciya ce, ka da ka yi mata baƙin tabon da zai dinga bibiyar rayuwarta, kada ka yi abinda za ka yi ladama, wallahi ban taɓa kusanta kai na da zina ba, ban taɓa ganin wani namiji bayan kai ba, shin Ubangiji ba shi ke halittar bawa a yadda ya su ba? Baka halitta bana halitta balle mu zaɓi kalar yaran da muke so mu haifa, kalar halittar Ridayya har ya kai ka nisantaka da jininka? Har ya kai ka laƙaba mata kalmar shegiya? Kada ka gurɓata rayuwar ƴarka tun ƙuruciya Baffa ba roƙe ka" Tana kuka Ammi na yi kuka, Anuty Kaltum ta cika ta yi fam ganin kukan Ammi take tamkar na munafurci.
"Fatima wallahi tallahi na rantse da Allah ba zan amshi yarinyar nan ba, bana buƙatar sanin uban nata ki shige cikin ɗakinki ki zauna"

"Ɗakin ya ci uwarsa da ubansa, wallahi wallahi Fatima ba zata zauna da kai ba, ka sauwaƙe mata" Baffa ya jinjina kai ya ce "Na sauwaƙe miki?"
Mami ta ce "Muddin ba zaka amshi yarinyar da Ubangiji ya halatta maka ita matsayin jininka ba, ni kam ka sauwaƙe mini zan raini yarinyata in sha Allah, Ubangiji zai mini sakayya" Baffa ya jinjina kai ya kalli Ridayya dake hannun Bilal kana ya kalli Mami ya ce "Tunda haka kika zaɓa shikenan, na sake ki saki ɗaya Fatima na sauwaƙe miki"
Saki babu daɗi musamman idan da soyayya, ta dinga kallon Baffa sai ta ji komai na yayewa na soyayyar da take masa daga ƙirjinta, wani abu ya tsaya mata sai kuma ta miƙe tsaye ta ce "Babban mutum bani Ridayya" Kafin ta amsheta Baffa ya yi caraf ya amshi Ridayya daga hannun Bilal ya juya ya damƙawa Ammi ya ce "Riƙe ta na bar miki ita halak malak Maryama, na bar miki ita Ammi"
Chapter 22 · 0% Book details