Sashe 47
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na gode" Zuciyarta babu daɗi ta nufi hanyar waje yau ita ce ta shigo gidan ubanta amma bata da iko da shi,duk yadda take ƙoƙarin goge hawayen sai kallon gidan take rayuwarta ta baya na dawowa fes cikin tunaninta rayuwar gidan da a yanzu ita take buƙata fiye data gidan miji.
Yana ganin ta fito ya kashe wayar da yake ya diro daga kan motar hannunsa ɗaya riƙe da ball yana juyata tare da binta da kallo can ya girgiza kai ya ce
"Who are you? Wace ke?" Ridayya ta yi shiru kan ta a ƙasa ya matsa yana ja da baya tare da leƙar fuskar ya ce
"Sai fa kin faÉ—a mini mene ya kawo ki bedroom É—ina fi not"
"If not zaka dake ta ne?" Ya kame fuska ya ce "Kar ki shiga faÉ—an nan Mother ki bar ta mini bayanin kan ta da wannan bakin nata"
"Sadauki wallahi baka ɗauki halin mai sunanka ba, kasan daraja da kimar sunan da a sanya maka" Ya turɓune fuska ya ce
"Na sani" Ta ce
"Bari na tuna maka Hamza sahabin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, cikakken sunan shi Hamza Ibn Abdul mutallib,ya kasance sahabin Manzon Allah (SAW) ne kuma kawu ne na Manzon Allah Muhammad (S.A.W), jarumi, mai farautar zaki"
"E to tunda ni ban samu zakin ba ga zakanya nan a bar ni na farauce ta, sai fa ta faɗa mini wacece ita" Gabaɗaya ya Sadauki ya tare hanyar tare da babbake ta, ba ruwansa da yadda yake acting shi bai ƙi ya cire a daku ba, daman ɗan rigima ne kuma shi ne ɗaya tilo ɗan fari kuma ɗan auta abin ya haɗe masa gashi ƙato da shi saboda ɗaga ƙarfe.
Sai yanzu ta ɗago ta kalle shi, shi ma ya kalleta da sauri ta zame idanunta sanda ta tuna akwai igiyar aure a kan ta. Sadauki bai damu da yadda take ba kawai yana mamakin ashe duk baƙinsa akwai wacce ta ci ubansa a baƙi.
"Ka bani hanya please" Sadauki ya muryar Ridayya ta amsa a kunnensa ya runtse ido ya buÉ—e yana girgiza kai tare da tattara hannu ya ce "Kin ji ba mother? Muryarta kamar kamar ana busa irin jita ta amma kalle ta tsohuwa? Yasin da akwai abinda ke tattare da ita"
"Yi tafiyar ki kin ji" Sadauki ya yi sauri zai bita Hajja Azizat ta riƙe shi tana murɗe kunnen shi. Ya juya ganin Ridayya ta ɗan fara nisa ta kusa gate ya ɗaga murya ya ce
"Kuma sai na rama ko ba yanzu ba, sai na shigo miki É—aki ki ji idan daÉ—i, ki saka a ranki zan sake ganinka Sadauki baya mantuwa"
Da sauri ta fice don ba zata iya da masifar wanda aka kira da Sadaukin ba.
Bata taɓa zuwa gidan Dada ba, balle gidan Yaya A'isha Anuty Kaltum daman ba mazauniyya ba ce. Ta rasa inda zata saka ranta ta ji daɗi a rayuwarta, zuciyarta wani irin zafi da raɗaɗi take mata ga wani irin ciwon kai dake damunta tana jin abinda ke cikinta na juyawa yana sanar mata shi ma yunwar yake ji. Mardiyya ce ta faɗo mata ta mance ma da abinda ta yi mata tana zuwan gidan ta ruski sun yi tafiya zuwa biki sai wata wacce take haya a gidan da alama bata jima da tarewa ba ganin bata da mafita wacce ta shige komawa gidan Zameer ta ji ta bakinsa ya saka ta nufi gida.
Tana ƙoƙarin shiga layin aka ce "Ridayya" Gabanta ya faɗi ta yi saurin juyawa wani matashi ta gani tsaye a gabanta jikinta na ɓari ya ce
"Kar ki ji tsoro, matar Zameer ko?" Nan da nan ranta ya ɓaci jin sunan Zameer take kamar saukar dalma a zuciyarta ya gyara tsaiwa ya ce
"Zan faɗa miki wani abu da ba ki sani ba game da mijinki Zameer. Ya yi auren caca dake da niyyar idan kikai soyayya da shi kuma ya samu budurcinki yana da Naira miliyan goma, sai ya ci sa a kece kika fara furta cewa yana son ki, ya dinga amfani da soyayyarki da kuma rauninki na cewa kar ya barki saboda ba za ki samu mijin aure ba. Zameer bai taɓa son ki ba koda da rana ɗaya ne. Ya yi ƙoƙarin barin ki bayan ya cimma burinsa sai ya ga wata sabuwar damar, kin faɗa masa an mallaka miki kadarori wannan dalilin yasa yake zaune dake saboda su zama mallakinsa one day"
Ƙoƙarin faɗuwa take ta riƙe jikinta sosai ta shiga girgiza kan ta. Gaza ya ce "Ba iya wannan ba ai, gidan daya fara kai ki ara ya yi ba nasa bane, plan ne da ƴan kai amarya sun tafi zai kai ki asalin gidan daya tanada domin ki, lefan da aka sace naki shima haya ya yi da niyyar kai musu bayan biki shi ne akai plan a zo a ɗauke kamar ɓarayi duk shi ya shirya. Uhm! Sai furnitures ɗinki daya siyar ya ce kasuwanci zai yi ko? To caca ya shiga da kuɗin wanda ya ci yana da miliyan kusan 30 ya yi hakan ne idan ya samu ya auri budurwarsa da yake mugun so, ya sace atamfofinki ya shiga caca, ya sace wayarki ya shiga caca maganar da ake yanzu hatta gidan da kuke ciki ya shiga caca da shi kuma an ciye yanzu ba mallakinsa bane shi ne ya ce ma za ku tashi right?" Jin Ridayya bata ce komai ba ya sanya Gaza ɗorawa da faɗin.
"Zameer bai taɓa so da ƙaunar baƙar mace ba, ki yi tunani tunda kuke sumbata ta taɓa haɗa ki da shi? Saboda yana tsantsamin wai dugun bakinki, yana sane ya daƙile miki karatunki saboda kar ki zama wata idan har kikai ilimin mai zurfi za ki hana shi samun abinda yake kwaɗayi wata dukiyarki, ki nazari akwai baƙar macijiyar da kike rayuwa da ita ki gaggauta yin maganinta dukda kin ɗakko hanya"
"Ya isa zuciyata dab take da fashewa don Allah ka ce mini ba gaskiya bane, ka ce mini mijina yana so na wallahi zuciyata zata buga" Gaza ya ce
"Bai kamata ta buga tun yanzu ba, ai kina da rayuwa mai tsayi da muradan daya kamata ki cimma ki yi achieving nasu tas. Wannan kenan abi na gaba shi ne iyayenki"
A gigice Ridayya ta damƙe hannun Gaza ya ce "Su nake nema sune suka rage mini a yanzu ina gama ka da girman Allah ka kai ni wajan su"
"Abu ne mai wahala gawar dake cikin kabari ki ga ta tashi, kamar yadda yake abu ne mai wahala buduwar da bata da mijin kiga ta samu ciki sai dai idan ƴar'iska ce. Ridayya ki yi haƙuri da abinda zan faɗa iyayenki su duka basa raye sun mutu daga ciki kuwa har wannan Manajan Bankin....," Wata shaƙa Ridayya ta yi masa idanunta ya firfito waje kamar mahaukaciya ta ce "Ƙarya ne Abbiey ya mutu ya barni, ƙarya ne na rasa kowa nawa suna nan a raye ka ce mini suna nan basu mutu ba"
Cak kuma numfashinta ya tsaya ta sulale tare da yanke jiki ta faÉ—i a sume.
____
Kuka take sosai kamar ranta zai fita ya kifa kanta a kafaɗar shi tare da damƙe hannunsa dake cikin nata, yadda take kukan zaka ɗauka ƙaramar yarinya ce tsananin damuwa ne ya yi mata yawa a zuciya.
A hankali yake shafa bayanta tare da ɗan bubbuga wa alamar rarrashi amma kamar yana zuga ta ganin kukan ba mai ƙare bane ya sanya ya jawota ya rungume ta a jikinsa, da sauri ta ƙanƙame shi domin da gaske tana buƙatar wajan da za ta yi kuka, kuka mai yawa ko hakan zai sassauta damuwar zuciyarta.
A hankali ya ce "Shhh ya isa haka, daina haka nan ni ma za ki sani kuka" Ta É—aga masa kai kawai tana sauke ajjiyar zuciya
Ɗago kai ta yi ta kalle shi idanunsa sun yi jajur shima ta buɗe ba ki za ta yi magana ya saurin rufe mata bakin ya ce "Yi shiru, na san me za ki ce yau dai ki kwanta ki huta ki kuma samawa kan ki nutsuwa kin ji?" Ta ɗaga kai a hankali ta kwanta ya ɗora kanta a cinyarsa har lokacin hannunsa na cikin nata ta riƙe da ƙarfi a haka ya shiga shafa kanta shi ma yana sauke ajjiyar zuciya.
Kasancewar azumi dab yake da shigowa domin bai fi saura kwana ashirin da wani abuba ya saka ya nutsa tunaninsa ga mutanen da ya dace a bawa zakka wannan shekarar. Kodayaushe tunanin inda zai sameta shi ne burinsa dukda yana son ya samu zuciyarsa ta kaɗaita da tunaninta al'amarin ya girmame shi ita ɗin kula da ita hakƙinsa ne kuma wasiyya ce a gare shi, babu wanda ya rage masa a duniya sai ita ɗin INA ZAI GANTA?
Bai ji ƙarar buɗe ƙofa ba sai sautin murya ya ji a bayansa a hankali ya juya da kyau a kan ƙafafuwansa walwalarsa ta ragu faɗan shi ya ƙaro fiye da kima. Ya rame ya faɗa amma kamar ana ƙara masa kyau da hasken fata ne.
"by now it is appropriate that you stop thinking" Ya faÉ—a yana jan kujera ya yi wa kansa mazauni har lokacin wanda yake magana da shi É—in bai kalle shi ba, bai kuma tanka maganar shi ba
"Na yi magana da Hajiya akan dawowar su Legas"
"Why?" Baita ya watsa hannu ya ce "Haka na yi niyya, have a seat"
Zama ya yi saman haɗaɗɗiyar kujerar shi idanunsa a lumshe sosai ga wani irin ciwon kai daya kasa barinsa Baita ya ce "Yau ka yi niyyar shigowa office kenan?" Bai yi magana ba sai hannunsa da yake kaɗawa yana matse yatsun alamar yana azabtar da kansa ta haka ne duk miskilancin Baita amma Ustaz ya ce shi babansa ne a wannan ɓangaren
"Kwana biyu na shigo na baka labari friend na sameka cikin wannan yanayin, naga kuma bai dace ba koda na je gidanka da ƙyar ka saurare ni kuma ka ji rarrashi na"
"Baka gajiya da magana Tajj?" Baita ya É—aga gira ya ce "Saboda Ubangiji ya bani bakin, kuma kai dai baka isa ina maka magana ka yi mini shiru ba, serious magana nake da ita"