Sashe 7
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ko a mugwayen mafarkan da nake yi a kullum, bana fata da gaske bana fata na yi mafarkin rayuwata ta baya, babu komai cikinta babu kowa a wancan rayuwar sai Abbiey ba kowa cikinta, da rayuwar baya data yanzu maja ce, mizaninsu É—aya, rayuwata a jirkice take a baibai take na shiga uku ni Ridayya....,"
Kukan da bata samu damar yinsa lokacin da idanunta ya yi mata mummunan gani a É—akin Zameer shi ne take yinsa a yanzu, shi kansa kuka rahama ne rashin yi tauye zuciya da abinda ke cikinta yake.
Bata son tuna komai, amma abun kamar an yi masa wahayi sai gilmawa ta idanunta yake tamkar majigi.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ubangijn ka tausaya mini ka sa na farka naga bacci nake, wacce irin rayuwa nake ciki ne? Shin daman haka aure yake? Ko wacce mace kalar baƙin cikin da take ɗanɗana kenan ko ni ɗaya ce, daman da ake cewa aure ɗan haƙuri ne hakan shi ne haƙurin?" Sosai Ridayya ke kuka tana buga kanta da ƙarfen gadon jikinta na karkarwa, duk wanda ya ganta dole ya tausaya mata ita kaɗai tasan abinda take haɗiya, damuwar aure na son haukatar da ita shekarunta sun yi kaɗan, ƙwaƙwalwarta ta gaza ɗauka.
"Mene laifina don zuciyata ta so wanda take ganin shi daidai da ita? Mene laifina don gangar jikina ta so rayuwa da wanda take ganin shi ne mahaɗin rayuwarta, bangon da zan jinkina na ji daɗi? Me ya sa bangon ke shirin yar dani ƙasa ya ruftu mini aka? Me ya sa na kasa yar da ko gasgata abubuwa da yake mini? Idan ko wanne bawa da ƙaddarar shi tabbas tawa ƙaddarar ta _SO!_ ce, lissafin ƙaddarata _ZAMEER_ ne, Allah kar ka hukunta ni da zunubaina baya na tuba Allah na tuba kar ka hukuntani na yi ladama"
Nas Hajjara ta rirriƙe Ridayya da jini ke zuba a saman goshinta ta ce. "Babu ƙarya a lafuzzanki da gaske So jarabta ne kuma ƙaddara ne, da so kawai Ubangiji yaga dama sai ya hukunta bawansa da shi, aure ibada ne, kuma ko wacce mace a duniya haƙuri take a gidan mijinta, duk wacce zata fito ta ce miki zama lafiya ne wani abun ba a ɗauke kai a yi haƙuri ki ce mata na ce ƙarya take, domin ko tsakanin harshe da haƙori ana saɓa wa"
Nas ta kwantar da Ridayya wacce ta gama fita hayyacinta ta ce "Wallahi tallahi da na ganki na ɗauka tsohuwa ce, kin wani ranƙwafa idanu ƙwala-ƙwala ga baki da ya yi tsayi ƙashi kamar zan ajjiye jarkar ruwa, babbar matsalar yaran yanzu basa bambance SO da BIRGEWA, ƙuruciya da tashan balaga ne kawai ke ɗibansu da tsinanniyar zumar soyayyar nan ta samarin yanzu da take hurewa yaranmu kunne, yarinya ta na ce akan yaro bayan bata da tabbaci idan son gaskiya take masa"
Faɗa sosai Nas Hajjara take yi kamar zata ari baki, burinta a yanzu bai shige ta ji labarin Ridayya ba da yar da akai ta auri Zameer mene alaƙarta da Yaa Bilal wanda ta bawa sunan Abbiey?
"Who knows the truth? _Only God knows!_" Ta tambayata ta bawa kanta amsa.
_Waye ya san gaskiya? Ubangiji ne kaÉ—ai ya sani_. Kasancewar a file É—in Ridayya akwai information nata da number wayar Bilal data Zameer. A kusan lokaci guda aka kira su.
Zameer na zaune bayan ya kammala karyawa lafiyayyar Indomie ya ci da ta ji kifin gwangwani ya haɗa shayi mai kauri shi da Khairy. Duk a cikin kuɗin da Ridayya ta ce ya ɗauka. Khairy dake kwance kanta a cinyarsa wandon ball ɗinsa na jikinta ba ko riga ta kifa cikinta ta ce "Baby ba kiranka ake ba?" Zameer ya yi jim ganin sabuwar number sai kawai ya share, aka ƙara kira rai ɓace ya ɗaga.
"Muna kira daga nan asibiti, muna magana da Zameer ne mijin Ridayya Bilal Mansur Rano?"
"Nine ya akai?" Daga cikin wayar aka ce "Muna buƙatar ganinka a emergency sashin gaggawa, matarka na cikin halin suma an kasa shawo kan lamarin....,"
Ƙit! Zameer ya kashe wayar can ya ja tsaki ya ce "To ina ruwana? Nina na ɗora mata ciwon ne mace sai laulayi komai ciwo kamar ni zan bata lafiya, mayya kamar dangin tattabara ko soyayyar Layler da majnun ba wata nasara mutuwa ce kema haka za ki yi ni kam ba haukacewar da zan yi"
Shi kansa Zameer bai san mene ya same shi a yanzu ba, haka kurum ya samu kansa da yin faÉ—a can Khairy ta ce "Ka tashi ka je mana matarka ce fa" a fusace ya ce
"Nikam bana so da gaske bana so ki daina yi mini shisshigi Khairy" Khairiyya ta juya baya tana gwalo sai kuma ta dawo ta marairaice fuskarta fara tas farin da Zameer ke mugun ƙauna ta ce "Matarka ce hakƙinta na kanta...,"
"Zan yafa miki yatsu a fuska Khairy da gaske zan sauke mini hannuna" A hargitse yake gabaɗaya, ya ture kanta ya miƙe domin ko wanka bai samu damar yi ba balle ya tsarkake najasar yana zuwa baƙin ƙofa ya ce.
"Why Khairy me ya sa?" Da rashin fahimta ta ce "Mekenan kake magana?" A hankali ya ce "You, both of you are different, difference sweetness and tasty" kafin Khairy ta yi magana Meer ya fice daga cikin ɗakin. Tunani ta shiga yi mene bambancin me kuma ita da wa, Khairy ta kasa fahimta domin bai bata wata ƙofa da zata hasko abinda yake nufi ba, a hankali ta gyara zamanta jikinta duk ciwo yake mata wannan shi ne karonta na farko.
Zameer na fita ɗakin Ridayya ya shiga ya zauna tare da yin shiru, tunani fal zuciyarsa wanda tunda yake bai taɓa zama ya yi akan Ridayya ba, kenan mata sun bambanta, kamar yar da a kamanni suka kowa da nashi? Me ya sa bai samu yar da yake so a wajan Khairiyya ba? Duk irin jiran rana da lokacin da kuma shirin da ya yi wa ranar, baya ƙaunar baƙar fuskar Ridayya ko kaɗan baƙar mace bata tsarin rayuwarsa hasalima idan yaga baƙar mace zuciyarsa tashi take, shi ya sa bai damu da zama kusa da Ridayya ba ko kallon fuskarta ba, but he lost his mind idan ya raɓeta, sai ya ji shi Allhamdulillah! Ba yar da ya zaci baƙar mace ba. Babban damuwar Zameer a yanzu ko rabin matakin Ridayya Khairiyya bata ɗauka ba a wannan ɓangaren, ya zacci yadda fuskarta ke da haske kamar hasken farin wata ɗan goma sha biyar haka sai samu nutsuwa a wajanta. A hankali ya miƙe tsaye ya shiga safa da marwa can ya ce "Me hakan ke nufi?"
Kyan fuskar na banza ne? Munin shi ne abin so ganin ya gaza sanya ko wanne a mizani ya fice daga cikin gidan a ransa yana ayyana Allah ya sa ya samu nasara a caca ya ciwo miliyan biyun nan.
Duk suna zaune a madaidaicin parlon gidan suna jiran shigowar Baba ƙarami tunda Abban sama baya nan ya je can Rano. Balkisu ta ce "Yanzu babu mai zuwa duba Ridayya a asibiti?" Zuhura ta ja siririn tsaki da zuwanta gidan kenan ta ce "Uwar me za a yi mata? Akan Idanunki ta ci mutuncinmu ta zaɓi mijinta fiye da dangi"
"Yaya Zuhura hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar, naka shi ne naka jininka wuya za shi, gobarar data kunno a gidan Ridayya muke da ruwan kashe mata ita, dole ace ita jininmu ce dole a ce ita ƙanwarmu ce, ko babu komai akwai hakƙinta akanmu na zumunci....,"
A fusace Amma ta ce "To uwar Æ´an farsafa da tsara zance kamar wata marubuciya, daman da É—an jarida da marubuci gindin É—aya suke, muddin Ridayya bata ji tausayin kanta ba babu mai jin tausayinta, ni kai na ba kuga me ta yi mini ba?"
A hankali Balkisu ta ce "Ki yi haƙuri Amma, Allah ya kiyaye"
"Na gaba, domin wannan ya riga daya faru Balkisu ki raba kan ki da shiga shara ba shanu, yau ko yayyanka namanta wancan É—an iskan marainin yaron zai yi ba mai hanawa"
Bakinsu ta ce "Allah ya rufa asiri, Allah ya sauƙaƙa mata daman bakina kun riga kun yi wa aurenta tun kafin a yi ai" Balkisu na faɗin haka ta ja bakinta ta rufe ta fara danna wayarta.
Duk abinda ake Mami na zaune ita da Zainura ba wanda ya tanka ƙasan zuciyarta ba abinda yake banda zafi. A hankali kowa ya dinga shigowa ɗaya bayan ɗaya, Junaid, Aliyu, Usman, Umar sai Abubakar. Amma da Mami da Yaya Zuhura, Balkisu da Zainura sai Baba ƙarami mahaifin Bilal, baban Ridayya mijin su Amma daman baya gari ya je can asalinsu Rano.
A hankali Baba ƙarami ya kalli kowa can ya ce "Bilal fa?" Aliyu dake zaune ya ce "Banga Ustaz ba yau gabaɗaya" Baba ƙarami ya juya da nufin tambayar Junaid don shi yake ɗan samun kusanci da Bilal kafin ya yi magana Junaid ya ce
"Banga Ustaz ba Baba ƙarami, ni kam tun jiya idan har akan maganar Ridayya ne ai ina tunanin ba wani meeting ta zaɓi abinda ya kamata da ita ne"
"Yaya Junaid Ridayya yarinya ce gabaɗaya bata rufe sha bakwai ba girma ne ba hankali da ruɗun ƙuruciya, idan mutum na matakin adolescence babu abinda ba zai iya ba, ko wanne bawa da kalar nashi ƙaddarar...,"