← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 118

Sashe 68

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farin cikin da Hajiya ta yi na ganin Ridayya ya ɓaci ta rasa inda zata saka kanta don farinciki ashe zata sake ganin wani nata? Jikinta kai Allahamdulillah komai ta ce jikata Mai ran ƙarfe ya dinga murna. Ridayya ta yi farin ciki sosai bayan ta huta ta ce "Granny ɗan bani aron wayarki"

"Riƙe ƴar'nan na baki ita duka ma" number Sadauki ta kira yana ɗagawa ta miki a hankali ta ce

"Sahibi"

Ya sauke ajjiyar zuciya ya ce "Na azabtu Shanshan don Allah kar ki sake mini haka karki hukuntani ta wannan hanyar"

"Ka yi haƙuri"

"Uhm kina ina?" Ta faÉ—a masa sosai ya yi mamaki "ki tura mini address via email, zan zo gobe"

"A'a mu yi waya ba sai ka zo ba" cikin zafin rai ya ce "Yakike so na yi? Har yanzu ba ki amsa mini ba, kina so na ko a'a kin guje mini kuma yanzu ki ce kar na zo what do you mean by that eh?"

"Shikenan zan tura maka" Ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya a hankali ya ce "I'll call you later"

"To" cikin wata kalar murya yana sauke mata numfashi ya ce "I love you Shanshan, i love You till the end of my life, i love You to square of infinity mu'aaah"

Da sauri ta kashe wayar jikinta na amsawa tana rufe Idanu.

Duk suna zaune a parlour tun bayan dawowarsa bai fito ba sai yini cikin bedroom da ƙyar ya samu ya fito ya zauna saman kujera ya rufe Idanu abubuwa sun masa yawa Hajiya ta ce

"Ango ango kaga ango mijin amarya" Ya yi saurin buɗe idanu. Kafin ya yi magana Mardiyya ta fito daga wani part sanye da lemon ɗin lace sai baza ƙamshi take ta kafa ɗauri tana taku ɗaiɗai. Lokaci guda Ustaz ya haɗe rai ƙasa-ƙasa kuma yake kallon Mardiyya ɗin

"Barka da gida Hajiya"

"Yawwa Mardiyya kin fito ya gajiyar hanya?" Ta yi murmushi kawai ta nemi waje kusa da Ustaz ta zauna cikin iyayi ta ce

"Na shiga dubaka kana baccin gajiya, ya hanya Yallaɓai?"

Ganin wani irin kallo da Ridayya ke yi masa shi da Mardiyya ya saka shi daurewa ya ce

"Lou"

Wata irin zufa ke yanko masa ta ciki tashin hankali ya bayyana daga ta cikin zuciyarsa me Hajiya ke nufi? Me ya kawo Mardiyya gidan nan?. Ridayya kuma cike da mamaki take kallon Mardiyya daman ita Abbiey ya aura ya rasa wacce zai aura sai aminiyarta? Ita Mardiyya za ta ci amana kenan don ta ce ta je ta auri Abbiey É—in shi ne ta aure shi? Wani irin É—aci ta ji a ranta har wani duhu take gani a idanunta.

"Barka da hanya ƙawata aminiyyata kuma ƴata ya rayuwarki kuma?"

Miƙewa Ridayya ta yi daidai nan suka haɗa Idanu da Ustaz ta auna masa wata harara idanunta cike da ƙwalla ta yi cikin ɗaki. Tana barin wajan ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa, Hajiya ta bishi ta wassafa masa komai da yake faruwa.

"Ba ki kyauta mini ba, kin haÉ—a ni da aiki duk abinda na yi wallahi zunubi a kan ki"

Ta riƙe baki ta ce naga kana ƙifta Idanu kana girgiza kai "Ohho maka aure dai an ɗaura nan da wata tara na ji kukan jariri ai nasan ƙarya kake lafiya lou kake"

"Sai ki je ki yi mata cikin ai"

Ya shige toilet abinsa. Washegari da safe Hajiya ta ce Ridayya ta je ta kira Ustaz ya yi breakfast. Gudun faɗa yasa ta miƙe ta nufi ɓangarensa tana shiga ta ganshi tsaye a gaban madubi ga Mardiyya a gefe. Ganin Ridayya ya saka Mardiyya saurin rungume Ustaz ta ce "Abbiey ka bari na zaɓa maka kayan sawa"

Ai gabaɗaya maganar Ridayya ta maƙale jikinta ya ɗauki rawa ta yi saurin juyawa Ustaz ya kalli Mardiyya ta yi saurin sakinsa wani irin kallo mai kama da “Last warning”

Bayan ya gama shiryawa tsaf ya nufi bedroom ɗin Ridayya da niyyar tambayarta abubuwan da suka faru da yadda akai ta haɗu da Tajj. Yana shiga ya ganta tamkar mahaukaciya tana zaune a saman gado gashinta ya sauka har baya ta ci kuka son ranta ga Little nata kuka taƙi kula shi.

Ya kasa magana sai tsayawa da ya yi kawai a kanta ƙamshinsa da ta ji ya saka ta ɗago idanunta, ganinsa ya saka ta ji wani irin abu yarr a jikinta ta miƙe tsaye zata shige parlour ya ɗan sha gabanta

"Ina kwana?"

Bai amsa ba ya saka hannu ya tallafo haɓarta yana ƙare mata kallo sosai kafin ya ce "Kukan na mene?" Ta kasa magana sai kawai ta rushe da raunataccen kuka gabaɗaya ta nufi kan Ustaz shi kuma ya ɗan yi baya tana zuwa ta faɗa jikinsa kamar yadda ta saba a baya ta ƙanƙame shi tana wani irin kuka kamar ranta zai fita kuka take da dukkan zuciyarta da ƙarfinta wani irin kuka take wanda bata taɓa yinsa ba a rayuwarta, kuka take wanda ko sanda aka ce su Baffa sun mutu ba ta yi irinsa ba, har wani irin shiɗewa take jikinta na rawa da karkarwa babban tashin hankalinta bai shige zunubin data aikata ba ko rufe Idanu ta yi tana hango ranar data bawa Zameer kanta.

"Abbi..... Abbiey" Ta kasa magana tana neman zubewa a ƙasa saboda yadda jikinta ke rawa magana take son yi ta kasa ta haɗa zufa shi kansa Ustaz sai da ya ji tausayinta.

"Ka yafe mini Abbiey don girman Allah ka ya....," Maganar ta tsaya sanda ta sake fashewa da kuka gabaɗaya ta ɓata masa farar shaddarsa he could feel yadda hawayenta ke sauka a jikinsa.
Ya riƙe ta da kyau bashi da wani zaɓi dole ya bata damar kukan ko hakan zai sanya ta ji sauƙi

"Abbiey an ce ni mayya ce an ce bani da gata" Ustaz bai san lokacin daya rungumeta a jikinsa ba idanunsa ya yi wata kala ƙirjinsa na buga ta yi luff tana kuka sosai "Da gaske mayya ce ni Abbiey?"

"Shhhh" ya faɗa daidai kunnenta yana ɗan bubbuga bayanta, Ridayya ta juya fuskarta tsakiyar ƙirjinsa da sauri Ustaz ya ce "Ya Rasulullahi Manzon Allah.....

Karku yanke hukunci sai an sauke littafi
*MUNAFUKIN MIJI 32*
Mikiya Writers Ass..

Bright pens free batch
Nimcyluv

Ustaz ya girgiza kai ya kama hannunta suka zauna bakin gado, har lokacin kuka take ta ɗora kanta a ƙafarsa tare da zamewa zuwa ƙasan carpet, sosai take kukan ta riƙe ƙafafuwansa gani take kamar zai gudu ya sake barinta rashin gatan ya tabbata a gare ta.

Sai da ta yi mai isarta ta fara sauke ajjiyar zuciya nan da nan kanta ya fara ciwo ta É—aga kai ta kalli Ustaz shi ma ita yake kawai yake kallo.

"Kin gama?"

"E, ina jin kamar na yi ta kuka" ya miƙe tsaye ya nufi wajan fridge ruwa mai sanyi ya ɗakko ya ɓalle murfin gorar ya dawo ya miƙa mata yana mai sake zama inda ya tashi.

Ta tsare shi da idanu dukda gefen fuskarsa kawai take kallo. Ruwan ta sha sosai kana ta ajjiye tana sauke ajjiyar zuciya mai nauyi.

"Ki kwanta, bacci ko za ki ji daidai"

Ta girgiza kai tana ƙoƙarin sake ɗora kanta a ƙafarsa ya zame yana kame fuska ya san tuni ta saba, ko bacci wani lokacin a kan ƙafafuwansa take yi, ta ɗauke shi uba, aboki, uwa, amini bata shakkar faɗa masa komai da zama a duk yadda ta so idan yana wajan.

"Abbiey magana zan yi maka"

"Ki kwanta"

"Ko na kwanta ba zan iya bacci ba, ka bari na faɗa maka ka ji" ta ƙare maganar tana marairaice fuska ta ɗan tura bakinta gaba. Jinjina mata kai ya yi ta sauke kan ta a ƙasa

"Abbiey don Allah yau ɗaya ka faɗa mini me ya sa Baffa da Mami basa so na? Me ya sa Mami take son Zainura ni bata so na, me ya sa Baffa yake son kowa ni ban dani, me ya sa nake amfani da sunanka a makaranta maimakon na Baffa? Me ya sa kuma kowa na gidanmu fari ne ni kuma baƙa mummuna? Me ya sa ko a makaranta kowa ke guduna? Me ya sa mutane suke cewa ba zan taɓa samun mijin aure ba saboda ni mummuna ce ina da manyan idanu, da babban leɓe kuma ina da jiki da gashi me ya sa fatata take maiƙo kamar an shafa mai? Me ya sa kowa baya sona kowa yake guduna kai kuma kake so na Abbiey?"

Ustaz ya yi shiru ta ce "Ka faÉ—a mini mana kamar na so na gane"

"Ustaza ba za ki gane bane, ki na ta harbo tambayoyi"

Ya miƙe ya nufi gaban madubin ɗakin da hannu ya nuna mata ta zo, tana zuwa ta yi ƙoƙarin jingina da jikinsa ya yi saurin zamewa kan hakan ya faru ya yi baya ya nuna ta tsaya gaban madubin a hankali ya saka hannu ya yaye labulen gabaɗaya suka fito a cikin madubin tana gaba yana baya da ta zara

"Bani za ki kalla ba, dubi kan ki sosai"

Ta ƙura wa kanta Idanu dan baƙi da gaske ita ɗin asalin baƙar fata ce, asalin Bahaushiya ƴar'hausawa cikakkiya kuma. Idanunta farare tas sai dugwayen gashin Idanu har kwanciya suke, girarta a haɗe suke sai yalwar gashi gaban goshinta ma haka, lips ɗinta su ba jaa ba kuma ba pink ba sun yi wani colour yirrr da su ɗaya ƙarami ɗaya mai ɗan faɗi ya bada wani shap tana da Oval face kawai tsananin baƙi da duhun fatarta ya saka ake ganin muninta.

Ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Na gani ni dai ban gane ba"

"Ki gode Allah ki gode Annabi irin ku, ku ne ya yi yin zamani. Farin mutum har abada ba zai iya komawa kalar fatarki ba, ke kuma kina iya komawa fara idan ba ki gode Allah da irin zubin halittar da ya yi miki ba...," Ya sauke numfashi yana É—an hutawa.
Chapter 68 · 0% Book details