← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 118

Sashe 72

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har aka fita da Sadauki idanunsa yana kan Ridayya yana jin kamar yanzu ne ma ya santa kuma ya fara sonta a cikin zuciyarsa. Jansa Æ´an'sandan suke yana ji kamar ana saka abu ana cakar masa zuciyar gabaÉ—aya ji ya yi he just left himself wajan Ridayya there are millions of people in this dunia but all what he see is RIDAYYA no one can make him feel like her, and he will do anything to keep this feeling safe dole zai dawo kuma da iyayensa.

Sadauki na kallonta ita tana kallon Ustaz shi kuma Ustaz na kallon ƙasa Tajj kuma yana wayar a gaggauce. "Abbiey jini a jikinka mu je hospital ka ji kar ka yi ciwo"

Kallonta ya yi, wanda sai da hantar cikinta ta juya sai da ta yi ƙarfin hali wajan sake kallon cikin idanunsa amma abinda ta gani ya nemi ɗauke numfashinta, jinta ganinta murmushi taga ya yi tare da yi mata nuni da ta zo. Jikinta na ɓari ta ƙarasa ya yi saurin dakatar da ita ɗan nesa da shi ya ƙarasa miƙewa tsaye daman yana ɗan durƙushe ne gudun kar ya faɗi. A daidai inda take ya tsaya ya dinga murmushi sai kuma ya haɗe fuska ta ji muryarsa a saman kanta na faɗin.

"I don't hate you for not loving me anymore, but I hate myself for still loving you." Ya sake yin murmushi idanunsa jajur komai na zuciyarsa na buÉ—ewa dukda ta gama yin rauni ya kuma sare da al'amarin bata isa ya mutu saboda ita ba "Abbiey don....,"

"Shhhh!" Ya faÉ—a yana É—ora yatsarsa a bakinta yana jin dukkan wasu feelings and emotions É—in zuciyarsa suna tattarewa zuwa wuya ya ce "I've lived all this while for your happiness, but now, it is time I'll have to live for my own. I hope someday karma makes you suffer very much for betraying my trust. I hate you."

Komai na kan Ridayya ya zama fresh kuma new kamar an yi updating ɗinta da kwakwalwarta da tunaninta to the latest version ba a taɓa furta mata kalma mai zafi da ɗacin wannan ba, har maƙogaronta take jin ɗacin maganar ta dinga girgiza kai ina ma zata iya faɗa masa gaskiyar abinda take tsoro kuma take shakkarsa? Me ya sa rayuwarta take zuwa a haka ne ta ji dama bata zo duniya ba.

"I just hate you Ustaza"

Fitowar Mardiyya ya saka kai tsaye Ustaz ya nufi wajanta da yana da iyaye babu shakka wajansu za shi ko ya samu sauƙi yana ƙoƙarin ƙarasawa inda take ya yanke jiki ya faɗi ga wani dutse a wajan kai tsaye kuma mararsa ta sauka a kan dutsen.

"Abbiey!!!" Ridayyerh ta faÉ—a shout and soundly daidai nan itama ta yanke jiki ta faÉ—i a sume kafin Tajj ya motsa motoci wajan guda uku suka shigo.
Da sauri Alhji Mansur ya fito bayan Junaid ya yi parking suka, daga nan kowa ya fito hadda Barrister jikin Mami na rawa ta nufi wajan Ustaz Ammi kuma ta tsaya tana addu'ar Allah ya sa Ridayya mutuwa ta yi uban kowa ya huta don kar a ganota ta yi saurin nufar wajan Ridayya Baba ƙarami kallon tilon yaronsa ɗaya tal a duniya yake zuciyarsa na tsinkewa bai yi zaton a haka za su ruski yaran nasu ba. Tsoron rasa Muhammmmd ya saka shi rikicewa dukda kawaicinsa a kan Ustaz ɗin. Umma ta rushe da wani irin kuka tana cewa

"Shikenan ta kashe mini yaro ta kashe shi wallahi idan Muhammmmd ya rasu a kan ta ba zan yarda ba itama sai an kashe ta innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Babana baban mutum" kuka take tana jijjiga shi hankali tashe.

Barrister ne ya yi ƙoƙarin cewa "Asibiti ya kamata mu tafi da su ba mu tsaya kallon su ba"

Alhaji Mansur ya ce "Tajuddeen Junaid ku saka Babban mutum a mota" Suka kama Ustaz tare da sa shi a mota Baffa da kansa ya ɗauki Ridayya da hannunsa abinda bai taɓa yi ba tunda aka haifeta yana jin wani danshi na bin fuskarsa ya saka ta a mota, gabaɗaya basu lura da Mardiyya dake ta kuka kamar ranta zai fita ba.

Ta ƙasan Idanu yake kallon tafin ƙafarta da sukai fari tas ga dugwayen yatsunta gwanin sha'awa yadda aka gigice a kanta abin har mamaki yake bashi. Ya taɓe bakinsa tare da ɗaga kafaɗunsa cikin ko in kula ya zaro mandula yana murzawa tare da kunnawa ya shiga bata hayaƙi. Ammi data lura ta yi saurin dawowa baya ta ce "What rubbish? Mene haka shaye-shaye za ka yi anan wajan?"

"And so what? Ni fa gaskiya ba zaki kawo ni nan kuma ki takura ni ba"

"Amma Burhan kasan plan ɗinmu ko? Kai gabaɗaya kwakwalwarka bata faɗa maka gaskiya haka fa jiya na ji ance kun yi faɗa da wani ka saka wuƙa ka yayyanka shi yana asibiti da ban zo da kai nan ba da tuni police sun kama ka"

"Uhm" kawai ya ce yana girgiza kansa yana jin hayaƙin mandulan har tsakiyar kansa ga wani lafcecen yanka a ƙasan wuyansa.

"Ina magana kana sake hura mini hayaƙi bana son warin abar nan" zuƙar ƙarshe ya yi mata ya cillar a ƙasa ya saka ƙafa ya take sai yanzu yake ganin mutane tarr kuma daidai.

"Muje asibitin" Burhan ya girgiza kai ya ce "Kuje kawai" ya nemi waje can kusa da Maigadi ya zauna Maigadin duk a tsorace yake da Burhan.

Emergency a nan aka amshi Ustaz shi da Ridayya aka sanya su a ɗaki ko wanne daban nan da nan aka shiga kulawa da su har yanzu Umma kuka take Mami ta kasa cewa komai kasancewarta mace jaruma mai shanye abubuwa da yawa. Alhaji Mansur ya ce "Ban yi tsammanin ganin hakan ba, na ɗauka zanga Muhammmmd da Ridayya cikin farinciki suna tare ina jin kamar na yi kuskure wajan ɓoye gaskiyar komai akan cewa mun mutu, ban kyautawa kaina na ji ban cancanci zama uba a wajan Ridayya ba, na wulaƙanta ta na aibata ta, ta nuna wa duniya bata da wata daraja irin ta ɗa, ina tsoro kar ta mutu ban kyautatawa rayuwarta ba tunda aka haifeta bata yi farinciki ba...," Barrister ya riƙe hannun Baffa ya ce

"Alhaji Mansur mu bar maganar nan, fatanmu Allah ya basu lafiya bakiÉ—aya. Za su yi farinciki in sha Allah za a zama one big family"

"Na rasa wake da saka hannu wajan rusa farincikin iyalina, dole akwai dalili wannan dalilin bai shige ni ba"

"Kai Munafikin miji ba, daka fifita yarinya tun tana ciki ka nuna kamar ba a taɓa yi maka haihuwa ba, munafurcinka ya ja komai"

Cewa akai duk su tafi gida har zuwa sanda wani daga ciki zai farfaɗo Junaid ya kasa tafiya yana masifar ƙaunar Yaa Bilal kamar rai yana tausayin ƙaddararsa kamar yadda yake tausayin nasa ƙaddarar wacce har yanzu ta hana shi aure. Suka koma gidan Ustaz aka bar Junaid da Tajj da kuma Yaya Balkisu. A can suka samu Mardiyya mamakin ganinta ya cika masu rai, Hajiya tana ta kuka itama Mardiyya haka.

Farincikin ganin Alhalin Mai ran ƙarfe ya saka Hajiya da Mai ran ƙarfe yin kukan da basu taɓa yi ba, daman komai cuɗe musu sun kasa aiwatar da abinda ya dace, sun yi kuka har sun gaji bayan Baffa ya basu labarin komai.

Ammi ta juya ta kalli Mardiyya ta ce "Mardiyya tare kuka dawo da Ridayya ne domin idan anga zara za a ga wata, to ai ba kuka ya dace ki yi mata ba addu'a ya kamata ki yi ko?"

Hawayenta yaƙi tsayawa ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta wajan Ustaz. Hajiya ta ce "A'a ai matar Ustaz"

Da wani irin shock Baffa da Baba ƙarami suka kalli juna hatta Barrister ya razana da jin furucin na Hajiya Yaya Zuhura ta ce "Matarwa kika ce Hajiya?"

"Matar Muhammad-Bilal matarsa ta sunna"

"TamÉ—ijam! Kuma ya san an yi auren shi ya ce yana sonta wannan dai haÉ—inki ne"

A fusace Hajiya ta ce "Dam ƙundun ubanki haɗin nawa ne, ba zuba idanu ya tsofe babu aure ba masifa ta ci ta cinye shi"

Yaya Zuhura ta ce "To a gaskiya ba ki kyauta ba, ita kuma ya yarda ta aure shi har da shimfiɗe ƙafafuwa?"

Baffa dai ya kasa magana ba'a rabu da Bukar ba an haifi Habu rikici kan rikici Allah ne kaɗai ya san manufar faruwar hakan. "To yana can Kano aka yi komai, kuma Allahamdulillah ya aminci bai bani kunya ba dukda har cewa ya yi bashi da lafiyar zama da mace wai nakasashe shi, bayan nasan ƙarya yake ni zai mayar karfa kullum yana cikin azumi ai tarr nake kallonsa lafiya lou yake itama yarinyar na faɗa mata ta kwantar da hankalinta"

Wani sanyi Mardiyya ta ji at the end zata san mijinta, za su yi tarayya matsayin miji da mata hope ɗinsa a kanta ya ƙaru tare da wata kalar soyayya mai zafi dole ita kaɗai zata kasance da shi babu wata ƴar mace da zata yi musu shamaki ko ta zama labule tsakaninsu.

"Alhaji Mansur mun makara" Baffa ya girgiza kai ya ce "Ya ce haba kafi kowa sanin komai"

"Ma sha Allah, na ji daÉ—i Allah ya sanya albarka ya basu zama lafiya daman Babban mutum mace É—aya yake da muradi a rayuwarsa tunda an masa aure da Mardiyya magana ya shige su zauna lafiya su biyu abinsu ni kam Hajiya kin kyauta mini sosai"

Daga Baffa har Mai ran ƙarfe sun gane manufar Umma suka share. Ammi hamdala ta yi tunda Ustaz ya yi aure yanzu dole Burhan ya zama zaɓin Ridayya. Mami bata cewa komai tana jin zafin yadda Umma take nuna tsanar Ridayya idanu biyu Zainura ta yi shiru.

Can dare aka kira su Ustaz ya farka kuma Allahamdulillah da sauƙi amma akwai matsala zuwa safe suna iya zuwa a yi musu bayani. Har kuma gari ya waye Ridayya ko motsi ba ta yi suka fara shiga fargaba har likitoci har kawo lokacin Ustaz bai san su waye suke tare da Tajj ba.

Kokawa suke sosai shi da Hanne yana haki tana haki ta ce "Ba jaka bace ni da zaka dinga faÉ—o mini kamar dabba ko dabba ta san soyayya"
Chapter 72 · 0% Book details