← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 118

Sashe 43

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kuka? Duk kukan da na yi a rayuwa? Bari ki ji Abbiey ba irin mutanen ne ba daban Allah ya yi mini Abbiey na, kuma da na ke cewa ki aure shi wasa nake miki shi ba zai yi aure ba ai faɗa mini, kuma uba ne a wajena har abada ba kuma yadda za a yi ya sauya mini ba zai taɓa barina na yi kuka kuma ni ma bana son damuwarsa, ni kawai bana son shi kuma shi ma bai taɓa cewa yana so ba idan kina tunanin na yi ba daidai ba don Allah watarana na ji labarin aurenku ke da shi" Tana faɗin hakan ta ɗauki jakarta ta bar wajan. Mardiyya ta bi Ridayya da kallo tunda suke yau ta taɓa jin Ridayya ɗin ta yi magana mai tsayi dukda faɗa take amma sanyi ne a muryarta sosai idanunta da maganganunta na ƙarshe sun nuna zallar kishin Abbiey. Idan ta fahimta SO shi Ridayya ta ke wa Abbiey, BURGEWAR da Zameer ke yi mata ya danna son take ganin kamar shi zuciyarta ke buƙata da yawan lokaci ganganci da mata ke yi kenan da zarar anga farin namiji yana murza shadda za a ɗauki soyayya a aza masa.

Ridayya ta sake kiran number Ustaz cikin sa a ta shiga kuma aka ɗaga sai dai ba magana. Shirun Abbiey na taɓa zuciyarta ainun muryarta na rawa ta ce "Abbieyna don Allah kar ka yi fushi dani ka taimaka ka saka baki su Abba su amin na yi auren nan" Ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ta ce "Baka da lafiya? Please kar ka yi ciwo ka taimaka mini"

"Shalale just think about me, kar ki cutar dani please"

"Abbiey wallahi bana son ka wallahi baka taɓa burgeni ba ka tausaya mini" Ba zata tantance yanayinsa ba sun jima kafin ya ce "Ki yi tunani iya yau, a yanzu ba ruwana Ustaza" Ya kashe wayar. Ta yi ta kuka ta dinga neman Zameer da ƙyar ta same shi cikin tawagar su.

"Meer ga mayyarka can" In ji Moo ya ce "Wallahi duk ta daman gashi bana son Khairy ta fahimci da ita, kasan halinta amma yau zan kawo ƙarshen komai" Ta tsaya daga nesa da tunanin zai zo amma ya yi burus ya haɗe fuska ta ƙarasa kan ta a ƙasa ba wanda ta kuma sai shi ta ce "Ina son magana da kai"

Suka matsa ya haÉ—e fuska ya ce "Ki rabu dani kawai tunda bakya tausayina ba ki damu dani ba, kina kallo za a rabani da ke" Ta girgiza kai ta ce "Ba zan bari ba"

"Me za ki? Ai wannan Abbiey É—in baya son farin cikin ki daya bari mun yi aure amma zan nemi wata kawai" Jikinta na rawa ta ce "A'a don Allah idan ka bar ni ba zan samu wani mijin ba"

"Kina so na?" Ya tambaya idanunsa cikin nata, ita ma cikin idanunsa take kallo kamar yadda yake kallon nata. "Ina son ka"

"Ki tabbatar mini da wannan son Ridayya ki bani dama mu raya yau, muddin na same ki yau babu wani abu da zai yi mana shamaki da aure, ki mallaka mini kan ki budurcinki yau É—in nan idan ba haka ba kawai zan rabu da ke"

"Kana nufin mu yi iskanci?" Ya ce "Oh C'mn auren ki zan yi so babu wani batun kalma mai kama da iskanci, amince mini shi zai tabbatar da kina so na za ki iya yin komai domin ni, kamar yadda ni ma zan iya ka kalli yadda na rame ki duba ko abinci bana ci saboda tunaninki, idan na bar ki ba za ki samu mijin aure ba" Ridayya ta fara tunani da gaske idan Zameer ya rabu da ita babu wani da zai zo mata da kalmar Soyayya balle aure, domin har yanzu kalaman Burhan yana zaune a zuciyarta.

"Idan ban amince ba wata zaka aura?" Ya kashe ido yana kwantar da kai ya ce "Bisa dole, domin tun yanzu zan fahimci ba za ki iya sadaukar da abi domin ni ba, kuma ai daman haka ake soyayyar yanzu don dai ba ki taɓa yi ba, ni kam idan ba ki amince ba daga yau babu ni ba ke"

"Na amince" Ta faÉ—a ba tare da tunanin komai ba. Zameer ya zage ya dinga mata kalamai masu daÉ—i da sanyaya zuciya ya tabbatar mata ita da shi mutukaraba takalmin kaza. Haka ya É—auketa zuwa hotel ta na ji tana gani ya yi fatali da budurcinta ya mayar da ita cikakkiyar mace a waje tun kafin ta je gidansa, ba tare data sani ba duk abubuwan da suka wakana a lokacin Zameer yana yin vedion komai a wayarsa tun daga zuwansu hotel É—in har sanda ya rabata da budurcinta....

Ku jira ni zuwa dare idan naga comment.

Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv
08164069385
*✿ MUNAFUKIN MIJI 22 ✿*
Mikiya Writers Ass.....

BRIGHT PENS🤙🏼 free batch
Nimcyluv

Ya juya ya kalleta jin yadda take ta kuka, zuciyarsa fes ya samu miliyan goma a caca ta sanadin yarjejeniyar soyayya ta samu budurcin Ridayya. "Kukan na mene kuma? Bafa dole na yi miki ba"

Kukan da bata san dalilin yin sa ba shi take a lokacin da ƙaddara ta yi fatali da dukkan wata kima da darajarta na ɗiya mace saboda ƊA NAMIJI, da soyayyar da bata tabbacin zahirin ta a cikin zuciyarta, ta wofintar da duk wata kulawa tarbiyar da Abbiey ya bata sun zama tarihi a yanzu. Shigowar Zameer cikin rayuwarta tsakanin wasu ƴan watanni ya rusa tarbiyyar shekara goma sha shida da watanni.

"Haba Pretty idan kina kukan nan ina jin kamar ban dace da ki mallaka mini komai a matsayina na wanda kike so kuma kike shirin aure ba"

Ta kasa magana sai sautin kukan dake tashi a hankali tana naÉ—e jikinta a bargo, haka kawai fargabar Abbiey ya san wannan abin mai shirin tarwatsa zuciya ya rusketa. Ta tsinkayi muryar Zameer dab da kunnenta yana kama hannunta da yanzu bashi da shamaki da shi ya ce

"Look into my eyes Ridayya, na yi miki dole? Ita fa soyayyar zamani haka take kina so na yi believing da haka, kuma wannan abin daya faruwa babu komai sai ƙauna kin bani kyauta mai muhimmanci wacce ba zan mance da ita ba, zan dinga tunawa a kullum, kin bani budurcinki na ba ki nawa kinga 50/50 kenan ko?"

"Idan har zaka aure ni shikenan hakan shi ne muradi na, i know nothing about the love.....,"

"Shi ya sa na fara nuna miki yadda soyayyar take yanzu ai, cikakken masoyi shi ne mai yin haka idan ban yarda da ke babu ta yadda za a yi na yi tarayya dake Ridayya" Ta jinjina kai a hankali ba tare da ta ce komai ba a hankali maganganun Zameer na yaudara ke ratsa zuciyarta ya ce

"Ki yi wanka na yi dropping naki gida baby" Da ƙyar ta ja ƙafafuwanta tana rufe Idanu saboda tsananin azabar dake ratsa gaɓoɓin jikinta yana kai wa zuwa jijiyar dake sadar da yanayin mutum a kwakwalwa.

Yana tsaye ya sauya kaya zuwa wani milk É—in voyel mai manyan zane iya kyau da É—aukar hankali Zameer ya yi, ya taje sumar kan da comb sai É—aukar ido take komai nasa dabanne a idanun Ridayya ta yi tsaye tare da shagala da kallon shi.

"Ya dai? Wannan kallon fa Mai so na?" Ta É—auke idanu sanyaye ta ce

"Ka iya kwalliya ko wanne kaya na yi maka kyau ina son yadda kake dressing" Ya ɗan taɓe fuska yana lumshe idanunsa can ya riƙe ƙugu ya ce

"Oh hello na fahimci ke kalmar _I love you_ wahala yake miki ban taɓa ji kin ce Zameer i love You ba, sai dai a ce na yi kyau? To ki riƙe yabon nikam yau kalmar soyayya nake buƙata wajan ki" Cikin yanayin da ya zame mata ɗabi'a ma rashin son magana da sanyin jiki ta ce

"To ai ban san me zan ce ba, Abbiey kawai nake iya cewa ina son shi" Ya watsa idanunsa cikin nata can ya ce "Say something different....,"

"Rayuwata"

Ya juya da sauri jin sunan da ta ce ya dinga binta da wani irin kallo can ya saka hannu ya cira ta sama yana zagaye da ita ya ce "Oh wow gaskiya I'm lucky person, irin wannan suna haka say it again"

"Rayuwata"

"Mai sona" Ya faɗa yana kallon idanunta da suke a lumshe komai nata a nutse yake hatta muryarta golden voice Ubangiji ya bata, idanunta sexcy eyes ne irin nasu kyau da tsari shi sam har lokacin a gigice yake da lamarin Ubangiji, yadda take da muni daban yadda Allah ya sanya ni'ima da baiwa a jikinta daban, ya kasa mance irin tagoma shin lagwadar daɗin daya kwasa, sanda ya fara kai hannunsa zuwa jikinta ya girgiza the real definition na jin daɗi fata mai kyau ita ce Ridayya's skin bashi da ƙarfin qiwwar faɗar taushi da laushi fatar ta, ko'ina ya taɓa lutsum yake nutsa hannunsa babu rama ko misƙata zarratan a jikinta. Lafiyayyen diri mai ɗaukan hankalin namiji gata a sangarce take komai kuka Abbiey ya riga daya lalata Ridayya a ɓangaren shagwaɓa ko tari baya so da ƙaunar yaga tayi hakan bai rufe masa ido wajan tsawatar mata ba idan ta kuskure.

Da ƙyar take jan ƙafar tana tafiya a hankali cikin ikon Allah ta shige bedroom ɗinta, tare da faɗawa kan gado ta kwanta idanunta lumshe, abinda ya faru tsakaninta da Zameer ba komai bane sai soyayya kuma zai tabbatar zata iya komai domin shi. Amma ta sha jin ana cewa cikar kima da darajar mace shi ne ta kai budurcinta gidan miji? Mene bambancin wacce ta bawa saurayi a waje da nufin nuna masa soyayya da wacce takai gidan miji? Ta mirgina wani irin zafi ƙafafuwanta ke mata wa zata faɗawa? Me zata saka ta daina jin zafin? Nan da nan zazzaɓi kuma ya rufe ta ta rufe jikinta sai rawar san yi take hawayen da bata da masaniyyar dalilin taruwar su suka shiga wanke mata fuska.
Chapter 43 · 0% Book details