← Book details Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 118

Sashe 9

Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mahaifi da auren ƴarsa ina aka taɓa haka? Asstagafirullah Allah ka ya fewa Abbana" Baba ƙarami ya saki baki kafin ya ce "Zan sassaɓa maka yanzu, idan ranka ya yi dubu to zai ɓaci, ka kuma gaggauta cire abin da ke yawo a zuciyarka ka daina haramtawa kan ka abinda yake halak ne zaka iya jahadi ne" Ustaz ya miƙe tsaye idanunsa jajur ya ce
"Abba kai na ciwo yake nikam ciwo kai na ke mini, Matar auren kake jingina mata auren wani Abba haza haramun Ya Rasulullah Asstagafirullah!" Yana faÉ—in hakan ya fice shi kansa bashi da tabbaci akan maganganun da yake furtawa.

Washegari wajan shi da na safe Baba ƙarami ya saka a haɗa abin karyawa zai kaiwa Ridayya ta sha, ta ci abinci ta ƙara hutawa sai a sauya mata asibiti domin wani abun da yake damun Ridayya hadda sakacin iyaye da rashin kula da al'amarin yaran su. Da sallama ya shiga ɗakin amma shiru ba amsa ya dinga bin ko'ina da kallo ba Ridayya babu mai kama da ita, yana shirin fita idanunsa ya a kan takardar da aka ajjiye saman gado ya saka hannu ya ɗauka, saƙon daya gani ya gigita shi tare da sauya masa lissafi da jin komai zai yi a rayuwa dole ya kashe auren Ridayya Ustaz ya aura, Ubangiji shi ne shaida bai aikata hakan domin ya ci mutuncin wani ba, ko ya lalata mata auren ta ba, zai yi ne domin taimakon rayuwar ƴar ɗan'uwansa. Ya sake ware farar faifa ɗin idanunsa ya sauka a kan rubutun nata.

_Ni na san ban kasance alheri a zuri'armu Abba zan so ka cire hannu a cikin al'amarina kamar yadda Baffana ya cire, na gode da taimako daga yanzu har zuwa ƙarshen rayuwa bana buƙatar ko wanne taimako mijina ya tsaya mini, ya share mini kukana, daman kune baku fahimta ba amma nasan ba wata mace da Zameer ke so kamar mata ni Ridayya, zan yi nisa daku domin na fahimci za ku iya raba aurena, Abba kar ka yi mini kuskuren fahimta Zameer ya zo na bi mijina gidan aurena na sunna ya ce muddin ban bisa ba to zai sake ni, ba zan iya zawarci ba, ba zan iya barin Zameer ya rayu da wata mace bayan ni ba, wallahi ina son mijina shi ne rayuwata_

Murmushin takaici kawai Baba ƙarami ya yi tare da yaga saƙon, ƙiri-ƙiri Ridayya ta watsa masa ƙasa a ido? Allah ya sa banda Bilal babu wanda ya san da zuwanta nan daman mahaifiyarsa Bilal bata nan ɗin. Ya juya yana kiran ɗan'uwansa a waya domin akwai buƙatar ya baro Rano zuwa Kano.

Ustaz a gida ya bar motarsa kasancewar aljihunsa da É—an nauyi tunda an yi albashi ya biya kuÉ—in jirgi daga Kano zuwa Lagos É—in. Suna tafe a mota zuwa airport Junaid na driving Ustaz na zaune idanunsa rufe ya ce "Baku daidaita da Batool ba?"
Damuwar Junaid ta bayyana ya ce "Kowa da ƙaddarar shi, itama Batool an yi Genotype jikinta AS ne dole za mu haƙura da juna ne, idan ban manta ba Batool ita ce mace ta shida"
Ustaz ya ce "Ikon Allah, to Allah ya shiga lamarin"
Junaid ya ce "Amin, yaushe zaka dawo Kano idan ka tafi?" Ustaz ya yi shiru can ya ce "Shekara war haka" Jinjina kai kawai Junaid ya yi domin shi na zai so ace Bilal É—in bai dawo ba balle ya ci-gaba da taimakawa Ridayya.

"Na manta wayata É—an bani a ron wayarka"
Kamar Ustaz ba zai bayar ba sai kuma ya miƙa masa, Junaid ya matsa can gefe ya shiga lalubar number Ridayya da ƙyar ya gano ta yaga an yi saved da _Ustaza_ Number ya saka a black list ya yi blocking gabaɗaya kana ya dawo yana cewa.
"Nama tuna inda na ajjiye wayar tawa, daman ita zan kira na bar ta a parlon Mami wajan Zainura" Bilal bai ce komai ba har aka kira su ya shiga jirgi kana Junaid ya juya zuwa gida zuciyarsa cike da tausayin Ridayya amma dole ta gane kuskurenta yanzu zata fahimci muhimmancin Ustaz a cikin rayuwarta.

Ridayya na kwance tun cikin dare da Zameer ya je ya biya buƙatarsa wanda a lokacin ta ɗauka mutuwa za ta yi saboda wahala amma shi ko a jikinsa, tunda ya fita bai dawo gidan ba har gari ya waye, ko ƙwayar abinci bata kai bakinta ba balle kuma a yi batun maganinta ga ɗinkin da akai mata yana neman farke wa dalilin abinda Zameer ya yi mata a asibiti da kuma gida sai ruwa wajan yake. Kai ta ɗaga ta kalli lokaci ƙarfe 1:56 so take ta tashi ta gabatar da sallar zhur wato azahar amma ta kasa jikinta duka ciwo yake mata jijiyar bayanta ta riƙe sosai, ta ci kuka son ranta har ta ga ji. Khairy ce ta shigo daga ita sai ɗaurin ƙirji da towel ya tsaya iya cinya, kamar daga sama kuma taga Zameer ya shigo shima gajeren wando ne a jikinsa ruwa na zuba alamar wanka ya yi ko kuma sukai tare da Khairy ɗin.
Farar fatar Khairy sai ɗaukan idanu take a barka da kyakkawa kuma mai diri da kyan fuska, hakan ya ƙara sawa Zameer jin komai ya dawo masa sabo fil dan gane da abinda yake ji game da Khairy. Ridayya ta dinga kallon su tana haɗiye yawun daya taro a bakinta ƙirjinta na bugawa numfashinta na ƙoƙarin tsayawa, kallon Khairiyya take kamar bata taɓa ganinta ba tana ƙoƙarin magana Khairy ta saka hannu ta ja gajeren wandon Zameer ta ce

"Kai Yaya tun safe nake nemanka zani wajan Mama yau zuwa dare na dawo" Zameer ya kasa kallon Khairy duk yar da zuciyarsa ke kwaÉ—aituwa da son haka, haka kuma ya kasa kallon Ridayya ganin yar da take binsu da kallo sai kuma ya haÉ—e fuska ya ce
"Ridayya jikin ne ya sa ba ki iya sannu ba? Sai bina kike da idanu da kuma dugun baki?"
A hankali ta ce "Ka yi haƙuri" Niyyar ƙorafi take amma ganin fushinsa ya saka ta haƙura da nata domin ko da wasa bata ƙaunar taka sauyi a fuskarsa. Khairiyya ta ce
"Laa matar taka kake cewa mai dugun baki? Daman gashi duk ta zama tsohuwa" Caraf ya saka hannu da nufin make Khairy sai ya hau yi mata cakulkuli ta shiga dariya tana guduwa yana binta suka shiga tsere a parlon Ridayya suna zagayeta ba kunya da tsoran Allah. Suna cikin gudun towel ɗin Khairy na faɗuwa ƙasa, sarai Khairy ta san towel ɗin ya faɗi ta rufe idanunta tare da juyowa inda Zameer yake tana girgiza ƙirji da banƙaro ƙirji haɗe da faɗin "Hooo bai kamani ba, a yi masa gwalo wulwul bai kamani ba" Ta sake faɗa tana tura ƙirji gashi daman ba komai a jikin nata sai towel kuma ya faɗi.

"Kau!" Ridayya ta ɗauke Khairy da mari tana shirin ƙara mata wani kamar daga sama ta ji an ɗauketa da wasu tawayen maruka wanda sai da taga wuta ta gilma ta tsakanin idanunta, daman ba ƙwari gare ta ta yi bata zata faɗi ta yi Khairy cike da makirci ta tare Ridayya ta ce
"Haba yaya me ya sa zaka mata wannan jahilin marin? Ka manta bata lafiya? Ya kake abu kamar baka damu da matarka ba"
Zameer ya yi mitsi mitsi da Idanu ya ce "Shiru a nan Khairiyya, shiru na ce, ke me kika yi mata da zata saka hannu ta daki lafiyayyiyar farar fuskarki? An faÉ—a mata ko wacce fuska ake mari?" Khairy rai fes ta ce "Babu mamaki tana da hujjar marina ko na yi mata laifi ban sani ba"

Ridayya kishi ya turnuƙe ta kenan suna nufin daga Khairy har Zameer ba wanda ya fahimci me sukai? Idanunta ya rine jiri na ɗaukan ta ga ɗinkin jikinta dake amsawa ta ce "Rayuwata mari na ka yi? Mari har biyu?" Ya juya yana kallonta ya ce "Zan miki mahaukacin duka ba mari ba muddin za ki taɓa jinina bana wasa da ƴan'uwana"
Ta runtse idanunta ta yi tana kiran sunan Allah kafin ta ce "Yanzu ya dace ka dinga bin baligar mace da cakulkuli a gabana Meer? Har towel É—in jikinta na faÉ—uwa kai hakan duk bai dameka ba? Tsaraicinta shi ne abin kallo Meer?"
Zameer ya yi kan Ridayya zai daka Khairy ta yi saurin tare shi tana haÉ—e jikinsu waje guda ta ce
"Haba yaya Anti Ridayya gaskiya ta faɗa ɗan miƙo mini towel ɗin na rufe jikina" Zameer ya juya tare da ficewa yabar wajan, Khairy ta ce
"Ki yi haƙuri ban san towel ɗina ya faɗi ba, bada gangan na yi hakan ba, amma kar ki sake gangancin marina domin amana Mama ta bawa Zameer ni zai iya komai a kaina" Ridayya ta kasa furta komai takaici ya mamaye ta, kenan ita data bar kowa nata saboda miji hankali ne bata da shi kome? Yau Zameer ita ya mara a kan ƙanwarsa? Saboda suna aikata abinda bai dace ba? Ko kuma laifi ne don ta nuna kishi akan abinda take mutuwar so?.
Kuka ta dinga yi ita kaɗai domin hakan sabon abu ne a wajanta, ga yunwa ga ciwo ga takaicin da miji ya ƙunsa mata, ga matsalar ciwon zuciyarta na soyayyar Zameer.

Da ƙyar ta miƙe ta gabatar da sallah ta haɗa azahar da la'asar, Zameer na fita ya shige ɗaki Khairy ta bi bayansa suka kulle ƙofa bata tare da yin shiru. Ridayya bata san meke faruwa sai jin sautin waƙa ta ji yana tashi daga ɗakin Zameer ta rufe ido tana jiran taga ta ina mala'ika azara'ilu zai fito? Domin mutuwa ita ce abar da take fata ta risketa. Sallamar Zainaba da yar da take bubbuga kafaɗar Ridayya ya fahimtar da ita ce ita da rayuwa sun ƙalla aminci ne, haƙarta sam bata cimma ruwa ba, ta bi Zainaba da jimammen idanunta ta kasa cewa komai.
Chapter 9 · 0% Book details