Sashe 57
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mahmah ina Little ne?" Ta ce "Ai zazzaɓi yake fama da shi ya mannewa Mimi sai rigima yake" Ya zaro waya a Aljihu ya bawa Mahmah ya ce
"Ki bata an saka mata sim da komai idan da matsala tana iya kira a gaida Junior"
"To an gode Allah ya saka da alheri Tajuddeen"
"Daddy zani" Ya kalli Nadra ya ce "Maza jeki ɗakko mini Junior ku zo kin ji" Ta tafi bedroom ɗin da gudu ba jimawa sai gata ɗauke da Bilal tana ta nishi domin ya fi ƙarfinta a haka ya ɗauke su pictures akan ya ajjiye Little Bilal ya dinga masa vedio yana ƙaunar yaron yana gama yi masa ya ɗora a status ya sa
"Tubarkalla ahhasanulkaliƙin" Ya sanya emojin na crush da love kana ya sauka daga internet.
Tun bayan wayar da Ustaz ya yi da Tajj da kuma sake kiran da ya yi a karo na biyu aka ɗakka babu magana sautin da zuciyarsa ta buga a lokacin ya bambanta da irin bugawar da take masa a kullum a kodayaushe. Baya son ya gasgata abinda zuciyarsa ke faɗa masa, domin babu shakka ko tantama dokawar da zuciyarsa ta yi irin bugawar da zuciyarsa ke masa ne a duk sanda ya yi Ustaza irin abinda yake ji kenan shi kuma ya ji a lokacin, ya yi shiru ne da zaton za a amsa a yi magana sautin numfashinta da ya ji ta cikin wayar ya sanya dukkan wata suma da take jikinsa ta mimmiƙe irin miƙewar da sai Ustaz ta raɓe shi yake jin haka, miƙewar data tuna masa har yanzu yana da sauran cikakkiyar lafiya irin ta ɗa namiji.
A hankali ya mirignawa gefe idanunsa rufe a kan bed a hankali ya buɗe ido yana mai sake ɗauke zancen a ransa yana cewa “Asstaafirulla" domin azuminsa neman lalacewa yake haka kurum. "Ba ki mana adalci ba Ustaza"
Knocking ake a bakin ƙofar bedroom ɗinsa tun ɗazo amma ya kasa tashi ya buɗe ƙofar can ya ji an daina babu jimawa kuma aka buɗe ƙofar aka shigo. Ya juya yaga Hajiya bisa dole ya haɗiye abinda ya yi niyyar domin ɗakinsa tsaraicinsa ne ko boxer ɗinsa aka gani ai kamar shi aka gani haka yake ji a ransa ta lalle shi sosai ta ce
"Babban mutum na aiko Bintalo ta kira ka kaƙi buɗe ƙofa kuma kai kace a daina shigo maka kai tsaye gaba-gaɗi"
Ya dai kalleta bai ce komai ba ta É—ora da "To wai wannan zufar ta magani da mece?"
"Ta magani da kece mana" Ya faɗa yana haɗe fuska tsohuwar rikici da neman magana ya yi mata yawa ta ce "Ka yi baƙuwa ne, ka fito idan ba haka ba na shigo da sanda ya kura ka"
Ta yi waje tana ƙoƙarin fita ya ce "Black tea da lemon please" Ta juya ta ce "Kamarya azumin fa?"
Ya juya mata baya abinsa yana jin yadda zufa ke ƙara wanke masa kyakkawan jikinsa kamar mai shirin yin zazzaɓi. Ya ɗauki wayarsa da tun safe bai duba ba, dake akwai WiFi a gidan kai tsaye WhatsApp ya shiga yaga status ɗin Tajj yana shiga ya ci karo da video Little da ya yi murmushi dimples ɗinsa sun lotsa ya lumshe idanunsa irin na Ridayya ya ɗan shagwaɓe fuska a hankali Ustaz yanayinsa na sauka damuwar daya tashi da ita yau ta fara yayewa ya jima yana ta kallon yaron kana ya yi saving a wayarsa ya sauka.
Sun fitar da rai ta fitowarsa sai ya fito ta ɗaga kai ta kalle shi hannunsa goye a bayansa yana juya idanunsa ash ɗin jallabiyya ce a jikinsa mai gajeren hannu, ita idan aka ce mata Ustaz ya haɗa jini da Larabawa wallahi ba za ta yi musu ba musamman yanzu daya ƙara girma shekaru suka ƙaru hutu da jin daɗi da kuɗi suka ɓoye shekarunsa gashi baya barin duk wani abu da zai nuna ya mayyanta ko'ina na jikinsa luff yake da gargasa ga yatsunsa dugwaye.
Ganin wacce ke zaune ya sanya Ustaz haɗe fuska sai kuma ya ɗan zaƙu da son jin me yake tafe da ita ya akai ta san gidansa dake Lages ɗin? Ya nemi waje saman kujera ya zauna yana harɗe ƙafa idanunsa zube a kan plasma
"Ina yini Abbiey?"
Bai kalleta ba bai kuma amsa ba t.v kawai yake kallo sun fi seconds a haka kafin ya ce
"Mardiyya ko? Kar na sake jin Abbiey a bakinki kin san sunana ai"
"In sha Allah Yaa Bilal" ta faɗa da ƙyar saboda masifar kwarjinin da ya yi mata ta buɗe jakarta ta ɗakko wasu takardu ta tsuguna har ƙasa ta ce
"Gashi kafin a yi auren Ridayya ta bani ajjiyar takardun nan ta ce ranar za a kaita zata amsa, ni kuma ba tare da saninta ba na yi photocopy dana bashi bata sai na bata photocopy ɗin na riƙe original ɗin, ganin yadda ta mini da yadda ta wulaƙanta ni bata buƙatar ganina har tana iƙirarin na auri mijinta ya sanya na rabu da ita, kullum ina addu'ar Allah ya haɗani da wani nata na bashi cikin saa kuma mun zo Lages ɗin shi ne nake tambayar inda kake ta hanyar zuwa bankinka"
Jin ya yi shiru ya saka Mardiyya ta ɗago kai taga gabaɗaya ba ita yake kallo ba t.v yake kallo ba zaka taɓa ɗauka ma da shi take ba.
"Babban mutum ana magana" cewar Hajiya ya nuna mata ƙasan carpet alamar ta ajjiye a nan ta ajjiye zuciyarta babu daɗi ganin yadda ya nuna kamar bai santa ba, ta miƙe ta ce "Hajiya bari na shige" Da sauri Hajiya ta miƙe da yake tana da ɗan raguwar ƙarfinta ta ce
"Bari na saka driver ya kai ki can unguwar da kuka sauka ko?" Suna fita Hajiya ta ɗauki card ɗin Ustaz ta bawa Mardiyya ta ce "Riƙe wannan kina kiran shi kullum kila shi ne rabonki tunda kinga ba ki yi auren ba"
"Hajiya ba za a yi haka ba ni daban wacce yake buƙata daban"
"Ni dai ke kika kwanta mini ba zan je rashin aure ya haukata mana shi ba, shi ne kawai ya yi mini saura ina tsoran matan zamani kar su lalata mini jika"
Tsoro da fargaba suka wanzu a zuciyar Mardiyya lokaci guda kuma kwaÉ—ayin auren Ustaz ya É—arsu a zuciyarta amma tana ganin kamar abu ne mai wahalar gaske tunda ta san waye Ustaz É—in baya É—aukan wasa da kuma raini a rayuwarsa. "Amma Hajiya ba lallai ya amince ba"
Hajiya ta ce "Kin jiki kuma kamar ba mace ba? Ai salo za ki zo da shi da kissa ki siye zuciyarsa kuma nima zan tursashi na nuna masa ni nake buƙatar hakan kuma alfarma na nema wajanki"
Farin ciki ya cika zuciyar Mardiyya idan ta samu miji kamar Ustaz to babu wata ƴa mace da zata iya barinsa ya kalla duk wannan samartakar da tuzuruntakar ta ji ta gani zata iya ɗaukarsu, wani irin so na ban mamaki ya wanzu tare da mamaye zuciyarta nan take ta nufi gida da buri da kuma ƙudiri na samun Muhammad-Bilal Tahir Rano a matsayin mijinta.
Wajan sati guda kullum sai Mardiyya ta kira Ustaz da ya ji muryarta yake kashe kiran. Yau sai issha ya shigo a gajiye yake sosai tun kafin ya shige part ɗinsa Hajiya ta tsayar da shi, Mai ran ƙarfe kowa baya ce mata komai ya nemi waje ya zauna ta ce
"Babban mutum a ranka za ka ji kamar ina takura maka wallahi ba haka bane kwaɗayin ganinka cikin fari da kuma kwaɗayin samun wata zuri'ar da muka rasa sune suke jana zuwa hakan, ka ɗauki hakan matsayin ƙaddara wacce ta ruga fata, rabonka baya taɓa huce ka. Ka ɗauki hakan matsayin wani sabon babi na lissafin zanen ƙaddararka ka ɗauka Mardiyya ita ce matar da Ubangiji ya ƙaddara zaka aura wallahi idan da aure tsakaninku ka bijire to wannan rabon ko a titi ne sai an same shi, Asstagafirullah! Kuma bama fatan hakan don Allah don Annabi ka duba girman Allah ka amince"
Ustaz jikinsa ya yi sanyi ya rufe idanunsa ya buɗe baya son ana gama shi da girman Allah ita kanta Hajiya ta sani. "Zan durƙusa a saman ƙafafuwana idan hakan zai saka ka amince da auren Mardiyya bana son a dinga maka kallon tuzuru shekaru wajan na 41 kake fa?"
Ya numfashi ya kalli Hajiya ya ce "Idan na faÉ—a miki gaskiya za ki aminta?" Ta ce
"Sosai ma ko shakka babu"
Ya cije baki kana ya yi miskilin murmushi ya ce "Wannan jikokin da kike kwaÉ—ayi ba za ki same su ba ko na auri Mar"
"Assha saboda me Babban mutum? Haihuwar ce baka so?"
Ya miƙe tsaye yana juya baya ya ce "Saboda bani da lafiya tarayya da ko wacce mace sai......,"
Ya fasa faÉ—ar abinda ya yi niyya ya sauke numfashi ya ce "Ni nakasashe ne"
Duk sati sai Sadauki ya je gidan Mahmah magana bai taɓa haɗa shi da Ridayya ba, idan Allah ya yi sun haɗu ta gaishe shi wani lokacin ya amsa wani lokacin ya share. Gefe guda kuma kullum cikin bawa mother labarinta yake haka karum cikin dare zai tashi mother ya ce ta yi masa addu'a dole ta miƙe ta yi sallah ya dinga masa addu'a. Prof ma abin har mamaki yake bashi zai wahala kaga ya yi kwana uku cikakke a gida kullum yana da meeting da ma'aikata ko marketing manager ko secretary bashi da aiki sai danna waya da duba pictures ana magana ya ce wani aikin kwangila yake gani.
Mother na zaune taga Sadauki ya fito sai kallonsa take tana murmushi ganin inda ya yi wani irin kyau ya nutsu sosai ya sanya shadda shampoo sky blue bai saka hula ba ya taje gashin kansa ya sanya baƙin glasses a Idanunsa sai baza ƙamshi yake ya ƙarasa ya durƙusa kusa da mother ya ce
"A sanya mini albarka zan je neman matar aure" Hajja Azizat ta yi murmushi ta ce
"Ma sha Allah Ubangiji ya yi maka albarka ya baka sa a, ya É—ora ka a kanta lokaci guda ta amince" Ya lumshe idanu ya ce
"Amin love" Ya yi shiru can ya ce "Zuciyata bugawa take sosai"
"Tsoro mace kake Sadauki?"