Sashe 1
Munafukin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Page 1
Ridayya tana durƙoshe dafe da turtsetsen cikinta, kwalbar fiya-fiya ɗin can waje guda wacce ta gama aunawa cikinta ita. Zufa ce take yanko wa ilahirin jikinta, tun gabɓanta na motsi da rawa har ya zamana ya saki bata da kuzari da ƙarfin qiwwar taimakawa kanta.
Idanunta da suke rufe ne hawaye mai zafi ya shiga bin gefensu, wani irin zafi da raɗaɗi take ji a ƙasan zuciyarta wanda sannu a hankali yake mamaye dukkan wata tsoka ta zuciyar, bata taɓa tunanin illar da fiya-fiyar zata yi wa abinda ke cikin cikinta ba, more especially da tun ɗazo ta daina jin motsin halittar ciki.
“Ya Allah!â€
Ta furta a ƙasan maƙoshi daidai lokacin da kumfa ta fara fita daga cikin bakinta, ta ƙara runtse Idanunta, a cikin halin rayuwa ko mutuwa take, amma hakan baya hana mummunan abubuwan data gani a zahiri gilmawa ta cikinsu, abin na zaune daram a zuciyarta wanda ko fiya-fiya ɗin data sha bai kaita zuwa kushewa ba, tabbas abin na iya kaita kabarinta hakan yasa take kokawa da zuciyarta wajan ganin ta daina bugawa da soyayyar mijinta. Ridayya bata san adadin lokacin data ɗauka kwance saman ledar tsakar ɗakinta ba, tana faman jujjuya kanta kafin numfashinta ya tsaya gabaɗaya ta daina jin sautin muryar MEER wacce kullum ta zame mata tamkar busar sarewar Algaita.
"Baby kamar ƙarar ƙofa na ji fa?" Ta faɗa da ƙyar cike da tsoro, domin iya adadin zamanta a gidan Ridayya bata taɓa ganinta ko zaune kujera ɗaya da MEER ba, balle ɗaki ɗaya. Zameer ya yi shiru sai kuma ya miƙe a hankali yana gyara zaman gajeren wandonsa ya nufi ƙofar tare da buɗewa, ganin ba kowa a tsakar gidan sai hasken wutar nepa ya sanya ya zura slipper ɗinsa ya nufi ɗakin Ridayya bata cikin parlon sai ya shige uwar ɗaki kai tsaye, yana shiga ya rusketa kwance a ƙasa ta bawa ƙofa baya, ganin kamar bacci take ya sanya Zameer ɗaga kafaɗusa dukka biyun ba tare da damuwar zuwa dubawa yaga mene ya sanya ta kifa cikinta ba, mene ya sanya ta kwanta a ƙasa ba?
Meer ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya, yana jin fargabar data dirar masa na yayewa da alama motsin da suka ji da ƙarar ƙofar iska ce mai ƙarfi ta kaɗa tunda tsakiyar dare ne.
Yana komawa É—akin ya samu Khairiyya tsaye tana ganinsa ta matsa ta ce "Ita ce ko?"
Ya yi shiru yana kallonta ta sake cewa "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Matarka ta ganmu baby"
"Keee!!" Meer ya faɗa a taƙaice yana ƙanƙantar da idanunsa a kan Khairiyya kafin ya shafa sumar kansa yana yin ciki, Khairiyya ta langwaɓe ta ce
"Baby ina magana kana sharewa? Ina Ridayya take? Ta gan mu tare ko?"
Cikin tsawa cike da masifa ya ce
"Saurara, ni kam ki saurara mini da ihu saman kai na" Ya É—an hargitse mata nan take, Khairiyya ta yi shiru domin ta san halin Meer ciki da waje yanzu zai zama kamar Mahaukaci idan ana masa surutu akan shi.
"Ka buɗe mini ƙofa na fita" Khairiyya
muryarta na É—an rawa ta faÉ—i maganar a lokacin na farko da tsoro haÉ—i da shakkar Ridayya ya saukar mata a zuciya wata matsananciyar kunyar ta, ta dirar mata ainun ba tare data shirya ba. Babu macen da zata jure ganin mijinta wanda ke shirin zama uban abinda zata haifa yana kula wasu Æ´an matan, balle kuma har ta ganshi tare da wata mace a cikin gidansu na sunna, a É—aki É—aya, kwance gado É—aya ko ita da kanta idan bata kashe yarinyar ba, to babu abinda zai hanata sanyata jinya wajan ganin ta illata ta.
"Baby ka buɗe mini ƙofa"
"Shiittt...!" Meer ya ce a kasalance yana ƙara juya mata baya, ya fahimci da gaske Khairiyya bata san tasirin da muryarta keyi a zuciyarsa ba, gashin jikinsa a mimmiƙe gudun bugun zuciyarsa ya ƙaro fiye da kima, bai san meke faruwa da shi ba, ya kuma kasa ganewa, bashi da lokacin zama ya tantance halin da yake, photon Khairiyya ne zane daram a zuciyarsa, surar jikinta ke masa yawo a cikin idanunsa.
"Wallahi ba zan iya kwana gidan nan ba, matarka zata kashe ni, zata kashe ni tana mugun son ka"
Sai a lokacin ya juya ya kalleta yana mata mitsi mitsi da Æ´an iskan idanunsa ya ce
"Tana so na, tana son abinda nake so...," Ya É—an ya yi jim, kafin ya ce
"Ki nemi guri ki kwanta, kina takura ni da ganinki a idanuna kina matsawa zuciyata!" Da rashin fahimta Khairiyya ta kalli Meer domin bata gane ainahin abinda kalaman shi suke nufi ba, ta rasa wajan da zata zuba su da zasu auna zancan ta fahimta.
Kokawa yake da zuciyarsa da gaske wajan ganin ta daina dokawa da tunanin Khairy, da hana kansa juyawa ya sake ganinta a karo na babu adadi, riƙe kansa ya yi da kyau a zuciyarsa yake faɗin
"Ƙarya kike, da gaske ƙarya kike Khairy baki isa na yi tunaninki ba"
Tunaninta ke neman jirkita zuciyarsa dukda kasancewar ɗaki ɗaya suke, da ƙyar ya kauda wannan tare da zaro wayarsa ya shiga Internet, ƴan mata ya fara kalla sai dai yana da a ji ba ko wacce yake dannawa like ba, duk yar da ki ka kai da burge Meer.
Kamar yadda ya saba, kafin sallar subhi ya yi alwala tare da gabatar da raka'atul fjr.
Tana tsaye gaban daƙin tana kiran sunan Ridayya kafin ta ga ji ta ce
"Ikon Allah, duk abinda ya hana Ridayya yin ƴar tsala ba ƙarami bane, Allah ya sa lafiya take"
Ta furta tana riƙe plate ɗin hannunta, har ta juya ta ji hankalinta bai kwanta ba, sunan Ridayya daya gilma ta zuciyarta ya sanyata dokawa da ƙarfi. Da sauri ta shiga bakinta ɗauke da sallama, ta manta Ridayya bata taɓa bari ka shigar mata cikin uwar ɗaka amma ta shure wannan sharaɗin, was the first abinda idanun Zainaba ya gane mata, Ridayya ce yashe a ƙasa bata motsi fatar nan ta jikinta ta ƙara yin baƙiƙƙirin kumfar bakinta har yanzu fita take, a gigice Zainaba ta yar da plate ɗin siyan ƴar tsalar tana faɗin
"Innalillahi, Ridayya mai haƙuri mene ya sameki ƴar nan" Ridayya bata numfashi, gangar jiki baya magana, kunnenta sun jima da ɗaukewa. Ganin da gaske Ridayya ta zama gawa ya sanya Zainaba fita da sauri tana faɗin.
"Bawan Allah, mijin gidan kana ina, na ce kana ina"
Shiru ba amsa! Bata damu ba domin tana da yaƙinin bai san halin da matarsa ke ciki bane, ta nufi ɗakin Zameer kai tsaye tana ɗaga labule ta tsaya ganin mace zaune a tsakiyar katifa daga ita sai short skirt, da riga ba zata huce half-vest ba.
"Khary?" Ta faÉ—a a gigice
domin ba wanda bai san cewa Khairiyya ƙanwar Meer ba ce, Khairiyya ta miƙe jiki na rawa da ɓari da ƙyarma, ta kasa cewa komai sai laɓɓanta da suke kokawa da juna
Zainaba ta ce
"Sannu Khairy"
"Don....don....," Khairiyya ta kasa faÉ—ar abinda take son cewa, domin ta É—auka Zainaba ta fahimci komai, itama Zainaba shiru ta yi, ta yi amfani da tunaninta na mace mai hankali na daidai shekarunta ta gane akwai abinda ke faruwa _something is fishy...!_
Ta gyara tsaiwa ta ce
"Sannu na yi miki, sannun ne bakya so Khairiyya?"
Ta girgiza kai Idanunta cike da hawaye ta ce
"Ridayya ta turo ki yankani ko? Ta gano cewa ni ba ƙanwar mijinta Zameer bace kamar yadda yake faɗa mata kullum? Ta gano bani da haɗi da shi ta ko'ina, ta gano ni bama ƴar asalin garin kano bace balle na zama ƙanwar Meer? Ta gane hakan da gaske ta fahimta!" Zainaba ji ta yi komai na kanta ya tsaya, ƙwaƙwalwarta kamar za ta yi hooking haka take ji,
Kallon Khairiyya kawai take kamar zautacciyya kai ka ce ita akaiwa hakan. Khairy ta ce
"Yanzu yanzu zan bar gidan wallahi don Allah karku mini komai.....,"
Zainaba ta girgiza kai ta ce "Bantan Uba kibar ina? Nan gida? To ai ko za ki fita a raye dole sai dana kasa a jikinki, za ki rasa hannu ko ƙafa" Hawayen takaici ta goge ta ce
"Ke macace, watarana za ki ji baƙin cikin da kika saka Ridayya, ki yi tunani rayuwar da fasiƙa mazinaciyya a gidan aurenka matsayin ƙanwar mijinka ashe duk ƙarya ne, Allah ba zai barku ba daga ke har mijin nata"
Tana faɗin hakan ta jawo ƙofar tare da saka key ta rufe Khairiyya a ciki, da sauri ta juya inda Ridayya take amfani ta yi da wayarta ta shiga ɓangaren kira, last number da aka kira shi ne _RAYUWATA_
Ta yi masa kira biyar ba amsa, daga number sai ta sister Diyya.
Ƙara dubawa ta yi taga an saka Yaya Bilal, Zainaba bata tsaya jinkiri wajan dannawa Yaya Bilal kira ba, kamar wanda yake shirye na tsammanin kiran nata tana shiga ya ɗaga ta cikin wayar ya ce
"Auta kiran safe haka"
Shiru Zainaba ta yi muryar Bilal ta yi zaune daram a zuciyarta, wani dakakken sauti ne dake fita kamar busar Algaita a nutse ba hargowa, jin shiru ya sanya Bilal yin jim da gaske ba Auta ba ce, sam bai ji bugawar da zuciyarsa ke masa ba a duk sanda sukai kusa ko a waya ne, bai ji wannan maganaÉ—isun dake kwasar shi a kullum yana jirkita duniyarsa ba.
Bai ce komai, don baya da zarafin cewa ɗin magana mara dalili bata tsarinsa ko waye ya kira da number Auta dole akwai dalilin kiran, sai dai ya yi imani Zameer ba zai taɓa kiran shi ba.
Zainaba ta sauke ajjiyar zuciyar da take riƙe da ita tun ɗazo, kafin ta ce
"Your... Your.......,"
Bilal ya dakatar da ita da cewa "Riƙe ƙinƙinarki, ina take?" Da ƙyar ta ce
"Babu tabbacin tana raye ko babu, zahirin abinda Idanuna ke ganin Ridayya ta mutu..."