Sashe 98
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kuma ta d'ago daga kukan ta kalli Umma tace, "Umma Rahma ta takura min akan naje gidan ta har yanzu Allah bai bani iko ba, bana son zuwa sai naga kamar zuwana gidan ta bazai zama alkhairi ba" ta fad'a muryar ta na rawa sosai. Umma ta zauna a gefen ta ta dafa ta tace, "Me zai hana shi zama Alkhairi Rauda? Daman fa ba kece matar Anas ba duk wannan fad'i tashin da yayi a kanki Rahma ce matar sa bake ba, Allah bai bayyana mana hakan bane sai yanzu da lokacin bayyanar tayi. Ki duba k'addarar farko da ta raba ku sannan ki duba wannan wacce ta sake raba ku in kikayi tunanin nutsuwa zaki tabbatar da daman ba shine mijin ki ba kuma kin sa baka tab'a auren mijin da ba naka ba kamar yadda baza ki shiga kabarin da ba naki ba, shiyasa hausawa suke cewa matar mutum kabarin sa."
Kai ta d'aga ta goge siraran hawayen ta tace, "Haka ne Umma. Amma ina jin kunyar had'a ido dashi ita kuma kar taga kamar da biyu nak'i zuwa gidan." Umma tace, "babu komai ki bari ki samu lafiya sosai sai kije." Rauda tayi shiru kanta a sunkuye Umma tace, "Me kike so kici yanzu? Tun safe baki ci komai ba."
Rauda bakin ta ya fara rawa tana so tayi magana kuma kuka ya hanata fad'a. Umma tace, "Wai sau nawa zaki kuka ne a rana Rauda? Bakya gudun idanun ki su samu matsala sabida zubar da hawaye?. Haba dan Allah ki d'auki k'addara mana kamar yadda muma muka d'auka, mun san kin fimu jin ciwo amma ya za'ayi fad'an da yafi k'arfin ka sai ka mayar dashi wasa, waye ya isa yaja da jarabawar ubangiji a cikin mu?."
Rauda ta goge idon ta tace, "Umma ciki ne fa dani." Umma tayi murmushi tace, "Cikin halak ne ai wanda aka same shi da aure da meyasa kike damuwa aka sa?."
"Bani da tabbacin cikin Asad ne Umma, zuciyata tana fad'a min cikin Aliyu ne bana Asad ba."
"Ni jikina yana bani cikin Asad ne, zuciyata ta gamsu da Asad mijin kine cikin sane a jikin ki bana dan uwan sa ba."
"Ni kuma in na tuna ance bashi da lafiya sai naji jikina yayi sanyi na sake tabbatar da cikin na Aliyu ne Umma, in hakan ta kasance na shiga uku na lalace."
"Kar na sake ji kince kin shiga uku na fad'a miki komai ya faru da bawa daga rabbil alamina ne kema tak'i jarabawar shine ya jarrabo miki in kina furta irin wad'annan kalaman sai kizo ki fad'i, fad'uwar jarabawar ubangiji ba fad'uwar jarabawar duniya bace ba da zaka jure kace ka sake rubutawa, fad'uwa ce ta har abada domin kuwa imanin kine yayi rauni shiyasa kika fad'in."
Rauda tayi shiru ta lumshe idanunta ta buɗe tana kallon bangon d'akin Umma tace, "Me kike so kici?." Rauda ta kalli Umma ta sunkuyar da kanta k'asa tace, "Shinkafa da miyar manja mai kifi." Umma ta mik'e tace, "Yanzu za'a kawo miki" ta fad'a tana fita zuciyar ta cike da tausayin Rauda d'in.
Babu b'ata lokaci Umma ta had'a mata shinkafa da miyar manja kamar yadda tace ai kuwa taci sosai dan ta jima bata ci abinci mai yawan wanda taci ba dan taji dad'in ta musmaman da Umma ce tayi mata da kanta sai take jin wani abun na zuciyar ta na raguwa.
Bayan sallar azahar aka aiko da mota daga gidan sarauta gidan su Rauda dan d'aukar su aje inda mai martaba yake neman su gabad'aya, Umma dak'yar ta lallab'a Rauda Baba ya dawo suka tafi a motar baza ma ka d'auka su bane da glass d'in ta bak'i ne sosai baka ganin na ciki sai dai shi ya ganka.
Can wajen gari suka nufa dan a can ne za'a taru ba cikin gidan sarauta ba sabida abinda za'a tattauna baza'a yishi kowa yaji ba, babban gida ne ginin sarauta mai kyau da tsari tamkar masarauta haka yake sabida kyau da kuma zanen jikin sa. tunda suka doshe shi gaban Rauda yake fad'uwa haka kawai bata san dalilin hakan ba jikinta ya sake jin sanyi fargabar da take ciki ta saka take jin marar ta na ciwo kad'an-kad'an.
A harabar gidan suka ga tarin motoci da alama mutanen da suka danganci taron duk sun hallara aka faka tasu motar drivern ya kalle su yace, "Ranku ya dad'e ciki zaku shiga." Da to suka amsa suka fito Umma ta rik'e hannun Rauda suka nufi inda ya nuna musu dukkan su zuciyar su rawa take.
Duk takun da zasuyi da bugun zuciyar Rauda ake yin sa har suka bud'e wata k'ofar glass suka shiga sai ga mutane a zaune a falon dukkan su a k'asa, kan Rauda yana k'asa tana ji suna gaisawa dasu Baba ita kam bata iya kallon kowa ba kirjin ta bugawa kawai yake yi tashin hankali yayi mata yawa. D'ago ido tayi a hankali idon ta ya fad'a na Jidda da take binta da kallo ta d'auke kai ta kalli gefen ta taga Asad a zaune ya dafe kansa kana kallon sa kaga mara lafiya dan ya rame sosai.
Nan take gabanta ya sake fad'uwa ta mayar da kanta k'asa zuciyar ta na tafiya a guje kamar zata fito sabida tashin hankali. Sallama sukaji dukkan su suka mik'e tsaye ganin hakan Rauda ma ta tashi mai martaba ya shigo yana kallon kowa da murmushi a fuskar sa ya zauna a akan kujera yana bin su dukka da idanun sa kafin ya girgiza kai yace, "muna fatan mun same ku lafiya dukkan ku."
A tare aka had'a baki aka amsa yayi shiru kafin ya kalli Uncle yace, "a bud'e mana taro da addu'a." Uncle kalle su yace, "Salati ga annabi." Aka amsa gabad'aya kowa yayi shiru ana salati kafin Uncle ya kuma cewa, "A karanta suratul iklas k'afa uku da niyar saukar alkur'ani duk abinda muka saka gaba a taron nan Allah ya tabbatar mana dashi, duk sharrin da yake ciki Allah ya watsar dashi a wannan lokacin." Aka amsa nan ma akayi ya kalli mai martaba alamun an kammala.
Mai martaba yace, "Alhamdulillah. Ina godiya ga Allah da ya bani ikon ganin wannan rana mai cike da rud'ani da farin ciki da tashin hankali da bayyanar wasu abubuwa a cikin ta, nasan akwai wanda basu so ganinta ba amma da yake Allah ya k'addara zuwan ta babu abinda mutum ya isa yayi a akan hakan."
"Da yawanku baku san Malam Adam da kuma iyalan sa ba wasun ku suna ta mamakin me ya kawo su taron cikin gida to suma y'an gida ne domin y'ar sa itace tsohuwar matar Asad duk wani abu da za'a tattauna ya shafe ta domin kuwa tana cikin rud'ani itama tana so a warware mata duk abinda yake wakana a cikin tata rayuwar.
Kowa ya d'ago yana kallon su ita dai Rauda bata kalli kowa ba mai martaba ya sake cewa, "Ina so dukkan ku ku kalli Asad da Aliyu ku nuna min waye Sarkin Katagum a cikin su." Mamaki fal zuciyar dukkan su kowa ya kalle su cikin mamakin tambayar mai martaba aka nuna Asad da yake zaune cikin manyan kaya har lokacin hannun sa na dafe da kansa.
Mai martaba ya girgiza kai gani wanda suka nuna yace, "Rauda!." Gabanta ya fad'i ta d'ago kafin tayi magana yace, "Nuna min mijin ki a cikin su." Ta kalle su dukkan su duka babu wanda yake kallon ta a cikin su ta nuna Asad da yake zaune kamar yadda aka nuna shi d'azu.
Mai martaba yayi murmushi ya kalli Mama da take a firgice matuk'a yace, "Rabi'a nuna min d'anki Asad kuma sarkin ku a cikin su." Mama ta firgita dan bata hankalin ta ta fara zare idanu cikin tashin hankali, "baki ji abinda nace ba?" Ya sake maimaitawa sai lokacin ta dawo nutsuwar ta ta nuna Asad da yake zaune kamar yadda kowa ya nuna.
Mai martaba yayi murmushi yana kallon su shima kafin yace, "Duk wanda kuka nuna kunyi daidai shine Asad kamar yadda kuka sani amma fa kamar yadda ake nuna muku." Kowa ya kalli mai martaba alamun karin bayani dan basu fahimci kalmar sa ta k'arshe ba. Ganin hakan ya saka shi ya girgiza kai yace, "Wanda kuka nuna ba shine Asad ba, wanda yake zaune a gefen sa shine Asad duk wanna kuke nunawa yanzu Aliyu ne ba Asad ba!."
[17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*078.*
A tare dukkan su k'irjin su ya buga nan take kowa ya d'ago kai yana kallon mai martaba ana kuma kallon Asad da Aliyu da suke zaune kowa d'auke da zallar mamaki da tsoro a tare dashi. Rauda firgitar da tayi sai da ta bayyana a gangar jikinta tayi baya kamar zata fad'i tayi saurin dafa carpet ta kai kallon ta ga wanda akace shine Asad idon ta ya shiga cikin nasa tayi saurin janye nata ta dafe k'irjin ta da yake bugawa tana raba idanu a kan carpet tsoron ta ya ninka na baya.
Babban tashin hankalin ta da firgicin ta bai wuce da gaske cikin Aliyu ne kenan a jikinta bana Asad ba tunda gashi wanda duk suka nuna ba shine Asad d'in ba Aliyu ne, nan take hawaye suka fara wanke mata fuska jiri yana d'aukar ta tana jin kamar ta zube a wajan duk da a zaune take hakan bai hanata jin kamar iska zata kwashe ta ba, marar ta juyawa take kad'an-kad'an ta runtse tana cije bakin ta hankalin ta ya kai k'arshe wajan tashi.
Babu wanda ya isa yayi magana sai an bashi umarni hakan ya saka kowa yayi shiru idanu a waje yana jiran yaji abinda mai martaba zaice. Mai martaba ganin dukkan su firgici ya bayyana a tare dasu sai ya murmusa yana kallon Asad da Aliyu yace, "Dukkan ku mamaki ya bayyana a tare daku, wataƙila ma wasu suna tunanin Anya abinda na fad'a gaskiya ne?. Abinda kuka ji gaskiya ne wannan shine Asad wannan kuma shine Aliyu" ya sake fad'a yana nuna su da yatsa kamar d'azu.