← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 131

Sashe 90

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma tayi shiru na wani lokaci kafin tace, "Lamarin akwai d'aure kai Rauda." Rauda tace, "Na fad'a masa ya fita daga rayuwa ta wallahi bana son ganin sa ko kad'an na tsane shi na tsani ahlin su gabad'aya, yaje can ya k'arata kuma wallahi sai na zubar da cikin....." kallon da Umma tayi mata ya saka bata k'arasa ba ta sauke ido k'asa ta fashe da kuka tana fad'in, "Umma na tsani kaina bana son rayuwata, ta silar Asad kika ce min baki yafe min ba Umma, ina zan saka kaina naji dad'i bayan wannan furucin da kika yi a kaina?. Kallon fasiqa kike min Umma kuma wallahi ban tab'a zina sai a lokacin shima kuma fyad'e zan kira shi Umma. Ta silar sa Baba ya d'aga bulala ya dake ni har aka fasa min jiki, Umma ciki ne fa a jikina, ciki na haihuwa ba tare da aure ba. Bazan yafe masa ba Allah ya isa tsakanina dashi" ta fad'a tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya.

Umma tayi shiru na wani lokaci kafin tace, "Allah kad'ai yasan abinda ya b'oye amma har zuciyata na amince dashi, badan yana sarki ko yana mai kud'i ba ke kin san halina ni ba irin mahaifin ki bace, dan haka na amince da cikin jikin ki na sunna ne bana shege ba. Zaki raine shi kamar yadda ko wacce uwa take rainon cikin y'ay'anta ki haife shi kamar kowa, kar na sake jin maganar zubar dashi a bakin ki balle ma ki aikata kona shege ne baza'a zubar dashi ba balle cikin sunna ne. Indai kina son farin cikina kar ki aikata makamancin hakan."

Rauda bata daina kuka ba maganar Umma jinta take wani iri, wai ya zasu had'e mata kai kowa ya yadda cikin sunna ne bayan ita tasan ya sake ta? Meyasa suke mantawa da ita tasan shi tasan yanayin maganar sa ba Aliyu bane shine.

Umma tace, "Bana son wannan koke-koken komai ya wuce, na yafe miki har zuciyata ki kuma yi hak'uri zargin ki da mukayi dukkan mu. Shi kuma Anas mahaifin ki zai sanar dashi komai dan ko babu aure tsakanin ki da Asad dole a dakatar da batun auren ki a yanzu."

Kai take girgizawa ta d'ago tana fad'in, "Haba Umma ya zan yiwa Anas haka? Bayan dogon jiran da yayi a kaina tun ba yanzu ba yana gab da samuna kuma ace ya rasa ni?. Umma ke kike cemin daman kinfi sonsa da Asad sabida yana sona sosai ki tuna lokacin da na samu matsala a k'afata bai guje ni ba ya nuna zai aure ni a yadda nake. Umma bazan so na rasa Anas matsayin miji ba sabida k'aunar da yake min dan Allah kar kuyi min haka" ta fad'a tana sake fashewa da kuka.

Umma tace, "Dukkan mu babu wanda ya isa ya canja k'addara sai dai mu zubawa sarautar Allah ido daga nan har zuwa lokacin da zaiyi ikon sa akan dukkan mu. Bai rubuta Anas zai zama mijin ki ba tun farko shiyasa ake ta samun matsala akan auren ku, inda mijin kine babu abinda zai hana baki aure shi ba. Mu d'auka babu auren Asad a kanki amma akwai cikin sa a jikin ki kinfi kowa sanin ba'a aure da ciki kinga kenan auren ki da Anas ba abu ne mai yuwa ba."

Zatayi magana Umma tace, "Ki daina wannan koke-koken ki kwanta babu abinda kuka zai k'ara miki sai ciwo" tana fad'a ta tashi ta bata waje ta fita daga d'akin. Hannu Rauda ta dunqule ta fara dukan cikin ta a zafefe cikin k'unar rai tana yi tana kuka sai kuma ta daina ta sake fashewa da sabon kuka.

Ta jima a haka kafin kukan nata ya tsaya sai kuma ta zubawa waje d'aya idanu kalaman sa suna dawo mata cikin kanta sai taja tsaki ta toshe kunnen ta da duka hannayen ta biyu ta kwanta lamo a kan gadon.
Bata san iya adadin lokacin da ta d'auka a haka ba maganin da tasha ya fara bin jikinta bacci ya d'auke ta.

Umma data fita daga baya ta dawo ta tarar tayi bacci sai hankalin ta ya kwanta ta tafi wajan Baba dan su sake tattauna maganar nan, a zaune ta same shi shima da alama tunanin da yake yi kenan tayi sallama ta zauna tace, "Malam nifa gaskiya yanzu ina tantama, Rauda tace akwai abubuwa da dama wanda suka tattauna ita da Asad d'in kuma lokacin da yazo sakin ta ya maimaita mata su, in bashi bane ba taya Aliyun yasan dasu?."

Baba ya sauke numfashi yace, "Wannan kuma duka zai bayyana tunda wannan d'in ya bayyana a yanzu. Abinda nake so ki fahimta a matsayin Asad bance bazai yi k'arya ba amma bazai yi k'arya irin wannan ba duba da yana da ilimin addini sosai yasan illar da take cikin zaman haramci."

Umma tace, "Ni zuciyata tafi karkata akan shine ya sake ta d'in kawai lokacin baya cikin tunanin sane, ka tuna lokacin da kaje wajan sama mana akan rushe gidan nan ya kuka yi dashi? Ai bai nuna maka ya sanka bama gabad'aya."

Baba ya girgiza kai yace, "Haka ne. Koda shi d'in ne yayi sakin tunda har baya cikin hankalin sa bata saku ba har yanzu matar sace." Umma tace, "ta ya ta zama matar sa bayan shi da kansa yazo gidan nan?, indai har baya cikin hankalin sa ya akayi ya kawo kansa gidan nan? Indai baya cikin hankalin sa ya akayi ya tuna da akwai matar sa a gidan nan? Indai baya cikin hankalin sa ya akayi yasan ya sake ta saki d'aya a baya yazo ya k'arashe ragowar?."

Baba yace, "Ke baki san aikin sihiri babu abinda baya sakawa ba? Abinda nake so ki gane a nan Asad bazai mana rantsuwa a kan k'arya ba, ki tuna waye shi mana a garin nan." Umma tace, "Zai iya malam, zai iya kodan ya d'auke hankalin mu daga cikin jikin ta mu koma yi masa kallon cikin sunnah mu daina masa kallon cikin shege."

Baba ya kalle ta yace, "Kina da matsala Binta, Rauda fa matar sace babu ta inda hakan zata kasance ba tare da aure a tsakanin su ba, yafa karantu yasan daidai da wanda ba daidai ba." Umma ta tab'e baki tace, "sai naga shaidan yana nasara akan kowa mai ilimi dama wanda bamai ilimi ba ya kamata ka tuna."

Baba yace, "to nidai na amince da abinda yace, har yanzu Rauda matar sace ko yau yace zai tafi da matar sa zan bashi ita taje gidan sarauta a dama da ita. Anas kuma na kira shi da safe zai zo ya same ni muyi magana." Umma ta girgiza kai tace, "ya dai kamata a duba lamarin, komai ya faru da Rauda damu ya faru kuma hakkin ta yana wuyan mu dukkan mu sai Allah yayi mana hisabi da ita matuk'ar muka tura ta wajan sa ba tare da munyi bincike ba kamar mun tura ta taje tayi zina ne" ta fad'a tana mik'e ta fita ta bar Baba a zaune dan shi kam baiga abinda zai hana Rauda zama fulani matar sarki ba.

Washe gari.
*11:00 am.*

Baba ne da Anas ne a zaune bayan sun gaisa Baba yayi shiru baice komai ba domin har ga Allah yana jin nauyin Anas d'in da babu yadda zai iya ne. Anas kam tunda yaji kiran jiya haka nan gaban sa yake fad'uwa dalilin da ya saka shi bai k'asa a guiwa ba ya tawo da safe dan yaji me yake faruwa ko hankalin sa zai kwanta.

Baba ya numfasa yace, "Anas nasan zakayi mamakin kiran da nayi maka zuciyar ka zata dinga fad'a maka abubuwa da yawa akan kiran, ina so ka bani hankalin ka ka kuma saurari abinda zan fad'a maka dakyau."

Anas ya gyara zaman sa yace, "to Baba." Baba yace, "Wato Anas akwai k'addarar da zaka ga ta gifta in Allah bai rubuta abu naka bane sai ya kubce ta silar wannan k'addarar da ta kusto kai. In hakan ya faru mukan d'auka daman ba rabon mu bane abinda muka rasa d'in tunda shi rabo hausawa sukace ko kana cikin mahaifiyar kane indai naka ne sai ya same ka."

Baba ya sake d'aure Anas da jijiyoyin jikin sa jikin sa ya sake yin sanyi ya kalli Baba yace, "Baba ban fahimta ba."
"Zaka fahimta yanzu Anas. Wato kamar yadda k'addarar auren ka ta raba ka da Rauda a wannan karon kuma k'addarar auren ta zata sake raba ku Anas." A firgice ya kalli Baba idanun sa a waje yana kallon Baba cikin tashin hankali, ganin hakan sai Baba yace, "Kwantar da hankalin ka Anas kaji bayanin da zan maka. Wato a kwanakin baya duka mun d'auka auren Rauda ya mutu har kai na sanarwa ka kuma nemi sake neman auren ta a karo na biyu har muka zo yau da auren ku bai wuce kwanaki goma ya rage ba. A cikin kwanakin nan abubuwa da yawa sun faru Anas ciki harda bayyanar mijin ta inda ya tabbatar mana da har gobe akwai auren sa akan Rauda bai sake ta ba."

Baba ya kuma cewa, "Bayanan da yayi mana mun gamsu sosai dasu ita kanta Raudan ta tabbatar mana da ya mayar da auren ta bayan ya sake ta,  jin hakan ya saka na neme ka dan nasan kasan a yanzu auren ka da Rauda babu shi Anas!" Baba ya fad'a a tausashe yana kallon Anas da tashin hankali ya bayyana k'arara a kan fuskar sa gumi yana keto masa daga ko wanne kafofi na jikin sa cikin tashin hankali da bugar zuciya.
[17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: *Arewabooks@ nanahaleema11*
*074*

           Hankalin Mum ya tashi sai zagaye take a falon tana dukan hannayen ta tana yi tana kallon Jidda da take zaune tana kuka sosai sai ta d'auke kanta ta cigaba da tafiya tana kallon sama zuciyar ta cike da tunanin mafita. Zama tayi ta kalli Jidda tace, "Jidda sanar dani abinda kika yiwa Aliyu, in baki fad'a min ba bazan taimake ki ba."
Chapter 90 · 0% Book details