← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 131

Sashe 126

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanun take gogewa ta matsa kusa dashi ta kwanta akan cinyar sa bai hanata ba ya fara karatun alkur'ani a bayyane ba tare da alkur'anin ba. Nan da nan ta d'auka itama suna yi tare a hankali duk da kira'ar ba iri d'aya sukeyi ba amma yana k'ok'arin yin irin tata suna tafiya a hankali. Sunyi sama da izu biyu a haka sai da yaji muryar ta tana rawa zatayi masa kuka ya saka shi ya dakata yace, "Haddar ki ta zauna sosai, kina ganin zaki iya national world Quran competition?."

Da sauri ta tashi daga kan cinyaar sa tana kallon sa tace, "Zan iya Sultan, shine burina ina so nayi koda bazan ci ba ace na shiga shima nasara ne." Ya girgiza kai alamun gamsuwa ya dawo da ita jikin sa ta jingina da kafad'ar sa yace, "Zakiyi."

"Thanks you Sultan. Allah ya kare min kai a duk inda kake, ya yaye maka dukkan damuwar da take zuciyar ka, ya saka maka da gidan aljanna yasa mu rayu tare nida kai a can. Ina sonka Sultan" ta fad'a tana jikin sa baice komai ba sai sake rik'e ta da yayi.

Itama shiru tayi bata ce komai ba sun d'auki lokaci a haka akwai hango en gidan su a Saudia take yi taji yace, "Naso na had'a dake ku tafi gabad'aya sai na fasa" ya kalle ta yace, "Maje tare dake ko?." Ta girgiza kai tana murmushi shima murmushin yayi domin farin ciki ne kwance a kan fuskar ta daka gani zaka gane basai ka fad'a ba.

Shiru tayi tana murmushi ita kad'ai ganin ta a farin ciki saka shi farin ciki yake sai yaji dukkan damuwar sa tana yayewa kamar bashi ne wanda yake da damuwa a kwanakin baya ba.  Sun jima suna a haka babu mai magana a cikin su ko wayar sa baya d'auka in an kira sunyi shiru basa magana.

Cikin ta taji yana shafawa ya kalle ta sai ta mik'e ta jawo abincin tace, "Tunda kaci dan kad'an banga ka kuma ci ba" ta fad'a tana buɗewa takai bakin sa tace, "Kaci abinci." Bai mata musu ba yaci tana yi tana d'auke kanta daga kan abincin dan bata son khamshin hakan ya saka ta tashi ta d'auki ledar kayan ta shiga d'aki.

Bayan sallar i'sha tayi wanka ta saka riga da wando na bacci wanda ya siyo mata a cikin kayan ta saka hula sunyi mata kyau shima ya saka nasa riga da wandon suka fito suna zaga cikin gidan hannun sa na sark'e da juna. Kallon gidan take tana girgiza kai tace, "Sultan!."
"Sultana" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba tace, "Ban tab'a ganin gida irin wannan ba tunda nake."

Yayi murmushi suka tafiya yace, "Badan Abba ya d'ora min nauyi ba da a nan gidan zamu zauna."
"Tsarin ginin gidan larabawa akayi gabad'aya." Baice komai ba suna cigaba da tafiya tace, "Wai kuna waya da Dr Khalifa kuwa?."

Cak taga ya tsaya ta kalle shi sai taga ya canja gabad'aya kamar ba shine yake murmushi ba sai jikin ta yayi sanyi tace, "I'm sorry." Tafiya suka cigaba da yi bata ce komai ba shima baice ba. Kallon sa tayi taga har lokacin fuskar a d'aure take sai tace, "Sultan yaushe zan fara makaranta? Ina son zama y'ar jarida."

Banza yayi mata kamar baiji ba suna tafiya har ta fitar da rai zai amsa sama da mintina goma kafin taji yace, "Ki haƙura." Ta kalle shi jin abinda yace sai ta sauke kai k'asa bata sake cewa komai ba. Gama zagayen sukayi suka zo zasu koma ta tsaya yana kifta masa ido ya kalle ta tace, "Na gaji, ka goya ni."

Cikin ta ya kalla itama sai ta kalla sai tace, "Bafa abinda cikina zaiyi." Yak'i magana ta fara bubbga k'afa tana cewa, "Nidai na gaji ka d'auke ni bazan iya tafiya ba." Hard'e hannu yayi a k'irji yana kallon ta kamar bazai saurare ta ba sai kuma ya sunkuya ya d'auke ta suka cigaba ciki.

Har cikin d'akin ya ajjiye ta baiyi magana bai kuma yi murmushi ba ya juya ya fita, biyo bayan shi yayi ta same shi a zaune yana danna waya da alama aiki yake yi ta k'arasa inda yake ta wara hannayen sa ta shiga ciki ta mayar ta rufe ta kwanta a jikin sa.

Baice mata kanzil ba ya cigaba da danna wayar sa dan yasan ba yunwa take ji ba taci abincin da Suhail ya kuma kawo musu, "Sultan!" Ta furta a hankali tana kallon sa. Bai kalle ta ba ta kuma cewa, "Sultan nayi maka laifi?."
Nan ma baice komai ba ta sauke numfashi tace, "Kayi haƙuri."

"Kar kiyi min kuka" ya fad'a bai kalle ta ba jin muryar ta fara rawa ta mayar da hawayen ya cigaba da abinda yake yi. Sun jima a haka kafin yace, "Nasan kin san Khalifa har kina da number sa meye naki da zaki tambaye ni? Tare kika ganmu ko?." Ta d'ago ta kalle shi tace, "Kayi haƙuri ban fad'a da wata manufa ba, Khalifa ya taimake ni kuma muna zumunci da matar sa. In baka son hakan zan daina."

K'aramin tsaki yayi baice komai ba ganin hakan duk sai jikin ta yayi sanyi tace, "Kayi haƙuri dan Allah bazan sake yin maganar sa ba." Nan ma bai kulata ba tayi shiru bata ce komai ba shima kuma baice ba.

Sun jima a haka babu wanda yake magana sai danna waya da yake yi ita kuma tana kwance a jikin sa. Wayar tace tayi k'ara ta d'auka ba tare da ta bar jikin sa ba ganin Rahma ce take waya tace, "Hajiya Rahma." Rahma tace, "Anty Rauda nida wallahi fushi nake dake har yanzu baki zo ba gashi su Umma sunyi tafiya sai ni kad'ai."

Rauda tayi dariya tace, "Kiyi hak'uri ki daina fushi in sha Allah zanzo gidan, bazata zan miki sai dai kawai ki ganni." Rahma tace, "Allah ya kawo ki. Shima jiya yake cewa kink'i kizo mana ko sau d'aya nace nasan kina hanya yace shi ai yayi fushi." Ta sake yin murmushi  tace, "Ki basa haƙuri zaku ganni in sha Allah in nazo sai kun kore ni."
"To Anty Allah ya kawo ki. An yiwa su Umma da Inna abin alkhairi fa Allah ya biya mai martaba ya saka masa da gidan aljanna. Kinga yadda y'an uwa suke murna da wannan abun da ya faru kuwa? Ai Anty Rauda addu'ar da kika sha dake dashi ba y'ar kad'an bace."

Rauda tace, "Amin Rahma. Ban ma sani bafa ni sai yanzu da Yaya Ummi take sanar dani, ashe har sun kwanaa d'aya."
"Wallahi kuwa Anty, abu ai yayi mugun dad'i. Harda Baba malam fa." Rauda tace, "Au harda shi? Ni da yake ban ma gama jin labarin ba na kashe."

"Wallahi harda shi." Rauda tayi murmushi tace, "sun tafi sun bar mu daga ni sai ke." Rahma tace, "Lahh nima passport dina ne bai fito ba da ya fito zamu tafi nida shi." Rauda tace, "Ma sha Allah. Ina taya ki murna."
"Na gode Antyna." Daga nan sukayi sallama ta yanke wayar tana fad'in, "Nidai naga ranar da zanje gidan ki Rahma, in sha Allah zanje ko zan huta da gorin nan da ake min."

Gaban ta ya fad'i ganin kallon da yake mata ta had'd'iye yawu tana kallon sa yace, "D'aga ni." Jin yadda yayi maganar ya saka ta mik'ewa ya tashi ya shiga d'aki ta bishi da kallon mamaki ganin ya sake birkicewa. Sai da ta bari ya d'an jima da shiga sannan ta tashi tabi bayan sa ta ganshi a zaune yayi shiru ba tare da  yana wani abun ba.

Ta zauna kusa dashi tana kallon sa tace, "Sultan kayi haƙuri naga ranka ya b'aci." A fusace ya kalle ta yace, "Waye shi d'inki da zaki je gidan shi? Waye a wajan ki da zaiyi fushi dan baki je gidan sa ba?. Har abada baza kije ba!" Ya fad'a yana tashi tsaye ya juya mata baya ba tare da yace komai ba.

Yanzu ta gano laifin ta wato maganar gidan Anas da maganar Khalifa itace laifin da tayi masa sai ta tashi ya isa inda yake ta rugume shi ta baya ta kwanta akan bayan sa tace, "I'm sorry Sultan bazan sake ba in sha Allah. Rahma k'anwata ce dan naje gidan ta a ganina ba wani abun bane dan ita naje badan mijin ta ba amma tunda baka so bazan je ba, kayi haƙuri dan Allah."

Shiru yayi bai amsa ba yana jin zafin kishi yana taso masa daga cikin zuciyar sa yana sauke numfashi ta dawo ta gaban sa tace, "Dan Allah kayi haƙuri Sultan, bana so kana fushi dani hankalina yana tashi. In baka so zan daina kula Khalifa ko gaisawa zamu daina." Ya sauke numfashi yana kallon ta in ya tuna yadda ya rik'e ta a Cairo sai yaji haushin sa yake ji gabad'aya shiyasa wani lokacin ko wayar sa baya d'auka sabida haushin hakan.

Amma kuma ya taimake ta haka kuma Rahma k'anwar tace bazai raba su ba amma baya so yaga ta rab'i Anas balle taje gidan sa dan yasan tabbas zasu had'u shi kuma baya son hakan ko kusa. Jin ta fara yi masa kuka ya saka ya kalle ta tana jikin sa yace, "Shikenan ki bar kuka."

"Ka yafe min?." Kallon sa tayi shima ya kalle ta ya rik'e hannun ta ya d'ora a saitin zuciyar sa yace, "Bana son naji kina maganar wani Muwaddaty, ina ji kamar zuciyata zata fashe."
"Bazan sake ba in sha Allah, kayi haƙuri ka yafe min dan Allah bazan kuma ba." Rarrashin ta yake yana bubbuga bayanta ba tare da yayi magana ba.

"Ina sonki Muwaddaty! Sonki a jinina yake, na fara sonki tun a mafarki" ya furta yana sauke numfashi ya rik'e ta sosai a jikin sa. D'agowa tayi tace, "Mafarki?." Ya d'aga mata kai alamun eh tace, "Ka bani labari." Murmushi yayi ya girgiza kai alamun a'a ya jata kan gado suka zauna ya kashe hasken d'akin ya jata suka kwanta zata sake magana ya fara kissing d'inta dole taja bakin ta tayi shiru ta fara taya shi a karo na farko.

Bayan kwana biyu.
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*092.*
Chapter 126 · 0% Book details