← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 131

Sashe 20

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama ta sauke ajiyar zuciya ta dafe kai maganar mai martaba ta fad'o ta kalle shi tace, "Kafin wannan a duba min aga akwai wata alaqa da ta had'a su da yarinyar, ina nufin auratayya ta had'a su ko a'a?." Malamin ya sake cigaba da duba mata kafin yace, "A dai yadda na gani babu abinda ya had'a su sai dai kin san ana samun tangard'a wani lokacin Allah yana yi mana hijjabi da ganin wasu abubuwan, sai mu gani muce anyi kuma ba'ayi ba, ko mu gani munce ba'ayi ba kuma anyi d'in."
"Muje a bai had'a su d'in ba daman bana fatan hakan. Abinda nake so dakai ina so a yiwa Asad aiki a lalata masa mazantakar sa, ina nufin yadda bazai iya kusantar ko wacce y'a mace ba a wannan lokacin sai da nayi niyar hakan!" Ta fad'a tana kallon sa shima ita yake kallo da d'unbin mamaki.......
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*036.*

Mamaki ya kama shi jin abinda ta furta ya girgiza kai yana jinjina tsantsar mugunta da rashin son yarinyar da take yi ya gyara zaman sa yace, "Ranki ya dad'e Asad d'in za'a yiwa aiki?." Ta kalle shi tace, "ashe kaji me nace."
"Abin ne ya bani mamaki ranki ya dad'e, keda bakya so a yiwa Asad aiki da naji kince ayi miki shine nayi mamaki sosai."

"Yanzu tunda kaji sai kayi abinda nace." Malamin yace, "yanzu ranki ya dad'e bakya hango matsala a cikin wannan lamarin? Ayi masa aiki a yanzu nan gaba in ya auri wacce kike so kuma fa?." Mama tace, "Sai a warware shi, kayi masa abinda bazai wahalar warwarewa ba amma bana k'aunar wani abun ya shiga tsakanin sa da yarinyar nan ko meye shi koda hannun ta bana so ya rik'e." Malamin ya girgiza kai yace, "wannan ba damuwa bane ba ranki ya dad'e, za'a yi kamar yadda kika ce."
"Yau nake so ayi ba sai gobe ba."
"Babu damuwa ranki ya dad'e."

Ta d'an yi jimm kafin ta kuma cewa, "sannan ayi dai wani abun da za'a raba su bana son zaman nan nasu tare." Malamin yace, "babu damuwa ranki ya dad'e za'a yi." Bata ce komai ba ta mik'e ta fita ya bita da kallon mamaki kafin ya girgiza kai ya cigaba da abinda yake yi.

Mota ta shiga Suhaima taja suka nufi gida jikin ta duk a gajiye yake sabida dogon tuk'in da tayi. Ta inda Maman ta fita tana nan ta shiga ta wuce b'angaren ta Suhaima ta ajjiye motar ta nufi zuwa ciki. A hanya suka had'u da jakadiya Babba tana ganin Suhaima tace, "Ranki ya dad'e barka da dawowa." Suhaima tace, "barkan ki." Har zata gota tace, "Mai martaba yana kira." Gaban Suhaima ya fad'i amma bata nuna hakan ba ta juya akalar tafiyar ta zuwa b'angaren mai martaba jikin ta a salub'e.

Yana zaune shida Wambai kamar koda yaushe aka yi mata iso ta shiga da sallama ta tsuguna a k'asa tace, "barka da safiya Takawa, ina fatan an tashi lafiya." Mai martaba ya amsa kana yace, "Ina kika je naga kin fita da mota d'azu?." Shiru tayi kafin tace, "Na kai Mama unguwa." Mai martaba jin mai tace ya saka yace, "Shikenan jeki."
"A tashi lafiya" ta fad'a da girmamawa ta fita a sanyaye.

Mama kuwa tana shiga ta tarar da Mum a zaune tana jiran ta tayi tsaki tace, "Dake da Jidda wayoyin ku duka basu da amfani." Mum ta mik'e tsaye tana kallon ta cikin mamaki ganin yadda ta koma kamar ba ita ba tace, "Ranki ya dad'e lafiya na ganki haka?." Mama ta zauna tana zare hijjabin jikin ta tace, "a ko wanne yanayi ma ganina zakiyi indai a wannan lokacin ne, zauna." Ba musu ta zauna tace, "Me yake faruwa? Sarautar Kano aka bawa wani wanda ba namu ba?."

Mama taja tsaki tace, "Inda sarautar Kano aka bayar d'in ma da naji dad'i domin yafi min sauk'i a kan abinda yake faruwa yanzu."
"Me yake faruwa?."
"Mai martaba ya aurawa Asad yarinyar nan yanzu haka suna Egypt." Firgici, tsoro, tashin hankali, mamaki, rud'ani, gigita duka suka had'arwa Mum a lokaci guda ta mik'e tsaye ba tare da tasan tayi hakan ba idanun ta a waje hannun ta dafe da k'irjin ta tace, "What!." Mama da take kallon ta tace, "abinda kika ji shi nace."

Mum ta zauna tana kallon Mama tace, "Nasan dai baza ki min wasa da wannan maganar ba shiyasa na gigice." Mama tace, "na gigice ninkin wacce kika yi sau goma kiris ya rage na rasa hankalina, a fuskar ta kinga hakan ya bayyana." Mum ta sake rud'ewa tace, "Ta yaya?."
"Ina can Kano."
"To Asad ba anyi dashi ya hak'ura ba ya akayi maganar ta dawo?."
"Mahaifin sa shine yayi komai, na tabbata Asad bazai aikata hakan ba tunda yasan bana so."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Fulani kice babban masifa ce ta kawo mana kai" Mum ta fad'a a rud'e tana kallon ta. Mama bata iya cewa komai ba Mum tace, "yanzu ya za'ayi kenan?." Mama ta bud'e hannun ta alamun bata sani ba Mum tace, "kuma kinyi magana dashi?."
"Bana samun sa a waya kwata-kwata."
"Shikenan! Har sun raba mu dashi, mun shiga uku" Mum ta fad'a cikin rud'ani da ya bayyana a tare da ita.

Ba zato Mama taji tana hawaye tace, "Ban san me zanyi ba Sadiya bana son zaman su tare gashi mahaifin sa yace matuk'ar yana da rai da lafiya Asad bazai rabu da ita ba, nasan halin sa zai toshe duk wata hanya da yasan zamu yi magana da Asad, duk kuma abinda na saka a yiwa Asad ko ita yarinyar akan a raba su sai ya lalata shi. Kaina ya kulle Sadiya ya kuma ce in na sake na tafi Cairo raina sai ya b'aci" ta fad'a tana dafe kanta da hannun ta har lokacin hawaye take.

Mum ta dawo kusa da ita ta zauna tace, "dole mu san abinyi in ba haka ba burin mu bazai cika ba." Mama ta d'ago ta goge idanun ta tace, "wannan a rubuce yake dole ne na d'auki mataki na gaggawa kafin a kassara ni. Yanzu daga wajan Malam nake na bashi aiki ayi min za kuma ayi amma kafin lokacin ina so nayi wani abun da zan d'auke hankalin mai martaba daga kaina gabad'aya." Mum tace, "ya kamata kuwa in ba haka ba wallahi zasu cinye mana kurwar yaro, dan nidai nasan wannan ba aikin sa bane wallahi aikin asiri ne bata da abinda namiji zai sota dashi, sunyi nasarar asirce mana shi Fulani."

"Zan warware shi Sadiya, ke kin san zan iya. Dan na aikata komai a duniyar nan wajan ganin d'ana ya dawo abu ne mai sauk'i, zan iya salwantar da komai dan ganin Asad ya dawo gare ni ya cika min burina." Mum tace, "haka ne ranki ya dad'e. Amma iyayen ta sun cuce mu iya cuta, tsakanin mu dasu sai Allah ya isa."
"Hmmm" Mama ta fad'a dan maganar ma tak'i zuwa harshen ta.
"Bakya ganin muje gidan su ayi yiwa iyayen ta barazana da kurari ko zasu ji tsoro suce ya dawo musu da y'ar su?."

Mama tace, "ba aikin da hakan zaiyi mana, a baya munje ai me yayi?." Mum ta girgiza kai tayi shiru cikin tunanin mafita domin a ganin ta tafi Mama shiga tashin hankali.

Mum tayi tagumi kana tace, "ni Jidda ma nake tausayi in taji labarin nan bana tunanin zata iya bacci yau." Mama ta kalle ta tace, "ya zama dole ta sani kodan ta taya mu da wani abun ta dage ta kwato mijin ta." Mum tace, "wannan abu dai sam baiyi dad'i ba ji nake kamar na fashe da kuka. In na tuna irin kalaman yarinyar nan a kan mu sai naga kenan itace tayi nasara a kanmu abinda ta fad'a yana neman tabbata."
"Ki kwantar da hankalin ki Sadiya wallahi sai sun rabu."
"Ba rabuwar ba ranki ya dad'e kar muje wani abun fa ya gifta tsakanin su, hakan tana faruwa wallahi mun cutu har abada. Koda basu had'a jini ba ta shiga jirin matan da zasu yi iddar auren Asad."
"Nayi maganin wannan matsalar hakan bazai faru ba har a tashi duniya."

Mum tayi ajiyar zuciya tace, "Allah ya tabbatar" ta fad'a tana goge idanun ta kamar wacce take kuka. Mama tace, "matakina farko akan mai martaba zan d'auke shi domin shine babbar matsalata a yanzu." Mum tace, "Shine abinda ya kamata ayi ranki ya dad'e, amma me za'ayi?." Mama ta kalle ta kamar zatayi magana sai kuma ta fasa tace, "zan aiwatar dashi kowa kuma zai gani lokacin da zan dawo da Asad bai ma san nayi ba. Babban abinda yake gabana a yanzu na samu nayi magana da Asad gashi nasan ko da wasa bazai bari naje Egypt d'in ba."

"Hydar bakin su d'aya a gani na shi ya kamata ki kira ya had'a ku a waya." Shiru Mama tayi kafin Mum tace, "Kenan dana gansu a airport daman shine ba Aliyu ba?" Ta d'aki kujera tace, "wallahi naji hakan a jikina amma kalaman ki ya saka na manta da maganar ashe sune da yanzu mun d'auki mataki." Mama taja tsaki ta furzar da iska ta tab'a wuyan ta tace, "Zazzab'i ne a jikina Sadiya." Mum tace, "dole kiyi Zazzab'i fulani, bara na kira Suhaima ta kawo miki magani" ta fad'a tana tashi ta shiga ciki wajan Suhaima Mama ta sauke ajiyar zuciya tana jin zuciyar ta nayi mata zafi da rad'ad'i.

*☆☆☆*

"Ki taka slowly" ya furta mata daidai kunnen ta yana rik'e da ita hannun sa na zagaye akan shafaffen cikin ta domin ya karb'i sandar yace ta taka a haka. Gabad'aya ta kasa sakewa sabida hannun sa da yake zagaye da ita ga khamshin turaren sa da yake sanya mata kasala kanta na daf da kafad'ar sa hannun sa d'aya yana rik'e da hannun ta guda d'aya suna takawa a cikin asibitin a hankalin.
Chapter 20 · 0% Book details