← Book details Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 131

Sashe 120

Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Alhamdulillah. Daman sanar dake zanyi y'ar wajan kawun ku Lawan ta haihu sai ki kirata kiyi mata barka kafin kije."
Rauda kamar tana gaban ta ta d'aga kai kafin tace, "in sha Allah Umma, Allah ya raya." Umma tace, Amin. Amma akwai abinda yake damun ki fad'a min ina jinki kar kice min babu." Rauda ta fashe da kuka jin hakan sai Umma tayi shiru gabanta yana fad'uwa kafin tace, "Nutsu kiyi min bayani, meya faru?." Rauda murya na rawa tace, "Umma na gaji da gidan nan gabad'aya."

Umma tace, "Meya faru?."
Rauda tace, "Umma baya sona gabad'aya sai a kwana biyu ban ganshi ba shima bai ganni ba kuma hakan bai dame shi ba, yau tafiya yayi zuwa Abuja amma ban sani ba sai a bakin k'annen sa nake ji Umma."

Umma tayi shiru kafin tace, "Tsayar da kukan tukunna." Rauda taja numfashi ta goge idanunta sannan Umma tace, "Shine zai neme ki kenan ba kece zaki neme shi ba ko Rauda? Wato kece mijin shi kuma shine matar ko?." Kafin tayi magana Umma tace, "duk irin qalubalen da ya tsallake da rijiya da ya tsallake da baya duk baki gani ba sai kin sake d'ora masa wata damuwar? Zuwan ki gidan wacce gudunmawa kika bashi wacce zata kore masa damuwar da yake ciki?."

Rauda tayi shiru kafin tace, "Tsakani da Allah Umma ni banyi komai ba, hasalima ni bana zuwa inda yake indai ba abinci zan kai masa ba." Umma tace, "Baki da hankali ashe ban sani ba Rauda?." Rauda tace, "Umma haushin sa nake ji kin sani, ta dalilin sa fa kika......" Umma ta katse ta tace, "Dake da haushin nasa da kike ji kunci uban ku, shi baice yana jin haushin ki ba sai kece zaki ce kina jin haushin sa?. Ki tuna mahaifiyar sa kwanciya rashin lafiya tayi, ya rasa soyayyar y'an uwan sa guda biyu dukkan su suna son ganin bayan sa, ya rasa lafiyar mahaifin sa a baya, ya rasa komai hatta ke ya rasa, a wannan gab'ar yana neman wacce zata share masa hawaye ta yaye masa damuwa ta taushi zuciyar sa ta rarrashe shi kodan ya rage zafin da yake ji a zuciyar sa. Ki tuna Hydar ke kanki da Hydar kika sanshi amma me Hydar yayi masa? Ke wannan an fad'a miki abu ne mai sauk'i? Kin san zafi da k'unar da zaiji a ransa ace k'anin sa uwa d'aya uba daya shine yake neman kashe shi?. Ki tuna yayan sa da suke ciki d'aya shine ya dinga Zina da matar sa har tayi ciki wannan ma ba damuwa bace? Ke wacece da zai saurare ki yana cikin wannan yanayin bayan baki taimake shi wajan ganin an kawar da damuwar ba?."

Yadda Umma take mata fad'a sai taji fad'an yana shiga zuciyar ta abinda take fad'a kuma gaskiya ne sai ta sake nutsuwa taji tana cewa, "Ke kad'ai ce zaki d'auke masa damuwa kuma kin share shi to me kike so yayi miki? Zuwa zaiyi ya durk'usa akan guiwar sa yace miki Rauda ki rarrashe ni?."

Nan ma Rauda tayi shiru Umma tace, "Zaki ragewa kanki matsayi da k'ima a wajan sa, duk soyayyar da yake miki wannan banzar dabi'ar taki zata d'auke ta cillar da ita a gefe domin baki da amfani a wajan sa indai baza ki wanke masa damuwar da take ransa ba. Na tabbata yana buk'atar ki a kusa dashi ko in kula d'in ne da kike nunawa ya saka shima ya watsar dake, to dan yayi tafiya bai fad'a miki ba kuma sai kiji haushi? Naga ke kika zab'arwa kanki hakan ai ko?. Ai sai kije ki tayi Rauda tunda haka kika zab'a Allah ya bada sa'a kina zaune zai k'ara aure daman sarakuna basu zama da mata d'aya" tana fad'ar hakan ta yanke wayar bata jira Rauda tace komai ba.

Rauda tabi wayar da kallo k'irjin ta yana bugawa matuk'a cikin tashin hankali da gano zallar laifinta da kuma wautar da ta tafka a cikin lamarin, babban abinda yafi d'aga mata hankali bai wuce kalmar kishiya da Umma tace ba nan take hankalin ta ya sake tashi matuk'a......
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*090.*

       Da kallo tabi wayar jikinta kamar an zare duk kuzarin jiki ta ajjiye ta a gefen ta ta sauke numfashi ta tallafi hab'ar ta da duka hannayen ta ta lumshe idanu tare da jan numfashi ta sauke sannan ta buɗe idanunta tana jin babu dad'i a zuciyar ta.

Bata kai ga yanke tunanin da zatayi ba wayar ta ta sake yin k'ara ta duba ganin sunan Yaya Ummi ya saka ta d'auka kafin tayi magana ta rufe ta da fad'a ta inda take shiga bata nan take fita ba hakan ya saka ta tayi shiru tana jin me take cewa.

"Wallahi Rauda ban d'auka shirmen ki ya kai haka ba, duk ina jin yadda kukayi da Umma kin bani kunya da mamaki wallahi. Duk abinda yayi miki wannan halin da yake ciki ai yaci ace kin ajjiye naki fushin ki taya shi korar nasa kodan samun sasauci a zuciyar sa. Wa yake dashi da zai rarrashe shi Hydar ne yanzu kuma yana ina?."

Rauda bata iya magana ba Yaya Ummi ta kuma cewa, "Kiyi gaggawar samun sa yanzu in da yadda za'ayi ki bishi inda ya tafi in babu hali kuma ki jira ya dawo ki gyara kuskuren ki in ba haka ba zakiyi dana sani" tana fad'ar hakan ta yanke wayar Rauda ta sake ajjiye wayar tana jin zuciyar ta na rawa sosai.

Duk sai hankalin ta ya tashi ta rasa inda zata saka kanta tunawa fa da duk abinda kace mata gaskiya ne gashi bata san ya zatayi ba,yanke shawarar kiran sa tayi a waya sai kuma ta fasa ta kira number Suhaima. Suhaima tana d'auka tace, "Babar Yayar mu." Rauda tace, "Sister number Suhail zaki tura min." Ta amsa da to ta kashe wayar jim kad'an sai ga number ta shigo ba tare da shawara ba Rauda ta kira number.

Bata jima tana ringing ba aka d'auka tayi sallama ya amsa kafin tace, "Dan Allah Suhail ne?." Ya amsa da fad'in, "Eh shine." Rauda ta sauke ajiyar zuciya tace, "Rauda ce take magana." Jin abinda tace sai yace, "Ranki ya dad'e, da kanki Allah yasa lafiya?." Rauda ta d'anyi shiru kafin tace, "Ina so zaka kai ni inda Sultan yake dan Allah."

Suhail yayi murmushi yace, "Haba ranki ya dad'e umarni kawai zaki bani sai a aiwatar, yanzu zan k'araso in sha Allah."
"Na gode" ta amsa tana yanke wayar kafin ta tashi jikinta duka babu dad'i.

Rasa ma abinda zatayi tayi gabad'aya zuciyar ta babu dad'i ta koma ta zauna tayi tagumi kawai tana tuno fuskar sa a jiya da daddare yadda yake kallon ta da alamun maganar ta ta shige shi sosai. Furzar da iska tayi tana k'arewa d'akin nata kallo cikin rashin sanin abinda zatayi.

Tashi tayi ta shiga band'aki tayi sabon wanka ta canja kaya ta saka dogon wando ta saka vest mai k'aramin hannu ta zuba turare a jikinta kafin ta d'auko abaya cikin kayanta ta saka a jikinta ta nad'a mayafin tayi kyau sosai cikin shigar ta d'auki zoben da ya bata a Cairo ta cire ta saka a daidai lokacin da Suhail ya kira number ta.

D'aukar wayar tayi kafin tayi magana yace, "Ranki ya dad'e na iso, a ina zan same ki?." Rauda ta sauke numfashi tace, "Kazo kawai bakin apartment d'in nan zan fito." Ya amsa ta kashe wayar ta fito falon tare da kulle d'akin ta ta zare key d'in ta fito k'aramin falon ta dukka babu kowa ta fito babban nan taga hadiman ta ganin ta duk suka mik'e tsaye Jakadiyar tana fadin, "Barka da fitowa uwar gida ga mai martaba sarki katagum, takawar ki lafiya mara mai farar aniya, zuciyar ki wankakkiya fuskar ki wankakkiya. Allah yaja zamanin ki ya baki dukkan abinda kike so." Kanta taji ya fashe sosai tana jinjina dad'in mulki domin kuwa ba k'aramin girma taji ta k'ara ba fad'ar wad'annan kalaman da suke yi.

Tace, "Zanyi tafiya zuwa wani waje amma bazan jima ba a kula da komai." Jakadiyar ta tace, "Zamu iya raka mai girma fulani?." Rauda ta girgiza kai tace, "A'a zanje ni kad'ai."
"Allah ya dawo dake lafiya, ya tsare gaban ki da bayan ki, ya kare ki daga mak'iyan ki ya baki nasara da rinjaye akan komai." Amsa tayi ta fita Jakadiyar ta ta kulle b'angaren gabad'aya dukkan su suka fita.

A daidai k'ofar fita daga apartment d'inta ta ga motar kai tsaye Jakadiyar ta da take bayanta ta buɗe mata baya ta shiga Suhail yaja suka fita daga gidan. Sai da suka fita sannan yace, "Barka da safiya ranki ya dad'e." Rauda tace, "an tashi lafiya."
"Lafiya lau Alhamdulillah." Daga nan sukayi shiru yana jan motar duk a tunanin ta garin zasu bari.

Gaban wani gate d'in gida taga yayi slow ya danna horn aka lek'o ganin shine aka buɗe masa ya saka motar a ciki sai da ya faka sannan ya juyo yana kallon ta yace, "Afuwa ranki ya dad'e ban miki bayani ba. Mai martaba yana cikin gidan nan ya sanar dani kar na fad'awa kowa yana garin nan har Abba ya d'auka yana Abuja, na sab'a umarnin sane sabida kece babu yadda zanyi na iya b'oye miki inda yake. Ki rok'a min afuwa a wajan sa nayi laifi."
Chapter 120 · 0% Book details