Sashe 23
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kan table ta kalla taga abincin ta gashi nan sai ta kalli d'akin da yake taga k'ofar a kulle ta zauna ta fara cin abincin da yake a wajan. Taci sosai tana rufe bowl d'in ya shigo falon hannun sa zube a aljihu cikin riga da wando y'an kanti da suka yi masa bala'in kyau kansa da hular sanyi kalar rigar ta lura baya son sanyi sosai. Gaban ta ya fad'i ta d'auke ido daga kansa ya k'araso inda take baiyi magana ba taga ya d'auki wata leda ya ballo magani ya mik'a mata, hannu ta mik'a ta karb'a ya kalli ruwan da tasha ta rage sai itama ta kalla ta d'auka ya juya zai bar wajan amma bata sha ba.
Juyowa yayi ya kalle ta sai ta saka maganungunan a baki ta kora da ruwa sai taga ya juya ya fita daga d'akin gabad'aya ba tare da yace mata k'ala ba. K'irjita dafe domin ba k'aramin bugu yake mata ba ta kalli inda yabi taga baya nan tayi ajiyar zuciya tace, "Allah sarki ni na manta ma da maganin ashe shi bai manta ba jira yake na tashi." Sai kuma ta tab'e baki tace, "To ba dole yaso na warke ba tunda d'an uwan sane silar komai" ta fad'a tana bud'e na shafawar tana shafawa.
Bayan ta gama ta mayar dasu leda ta tashi kenan taji ana buga k'ofar sai tayi jimmm gudun kar ta bud'e a samu matsala jin ana ta bugu ya saka ta nufar wajan ta bud'e k'ofar. Balarabe ta gani sanye da riga fara wando bak'i da broom machine a hannun sa cikin harshen larabci yake mata magana amma bata gane me yake nufi ba. Asad ta gani a bayan sa sai ya juya suna magana da larabci kafin ya kalle ta, irin kallon da yayi mata basai yace mata komai ba ta fahimta tayi baya shi kuma balaraben ya wuce zuwa d'akin ta daman nan ne bai gyara ba.
Asad d'akin sa yayi niyar shiga sai ya kalle ta da hannu yayi mata alama da ta shiga yayi baya ta fara shiga sannan shima ya shiga ya k'arasa inda kayan sa suke yana dube-dube. Rauda sai yanzu ta fahimci wanda suke yin shara tana ta girgiza kai tana jinjina aikin kud'i wato in akan da kud'i komai ma yi maka za'ayi. Asad kuwa yana d'aukar abinda yake nema ya fita dan ta sake bashi haushi bama d'an kad'an ba.
Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta fito ta shiga d'akin ta ganshi tass kamar kar ka daina kallon sa komai yayi kyau ta shiga band'aki nan ka kamar ka zauna kaci abinci sabida yadda yayi kyau. Falon ta fito ta zauna ta rasa me zatayi sai kawai ta fara karatun alkur'ani a fili.
Ta jima tana yi sauk'in karatu ya d'auke tayi da yawa sosai sai da akayi la'asar ta tashi tayi sallah ta dawo ta cigaba da karatun dan bata san abinda zatayi ba.
Tana cikin karatun ya shigo bata ji shigowar sa bama tana ta karatu ya zauna kusa da ita yana saurarar abinda take fad'a yana kallon ta jin yadda take karatun da k'warewa kana ji kasan ba y'ar koyo bace ta iya sosai haddar ta zauna sosai a kanta. Lumshe ido yayi yana jinta tana k'aruwa a zuciyar sa fushin da yake da ita yana raguwa a hankali ya samu kansa da yin murmushi yana kallon ta har lokacin bata san yana nan ba. Sai da taje k'arshen aya sannan ta tsaya ta kalli falon ta ganshi a zaune amma ba ita yake kallo ba.
Tana so tayi masa magana amma tana jin tsoron hakan gudun kar yayi mata banza dan ba son hakan take yi ba sai taja bakin ta tayi shiru amma nasihar da Umma tayi mata ce take mata yawo a kanta. Wayar sace tayi k'ara ya duba ganin sunan mai kiran sai ya share bai d'auka ba ya cigaba da kallo waje d'aya kamar me neman wani abu a bangon da yake kallo. Tashi yayi ya shiga d'aki ba jimawa ya dawo da laptop a hannun sa ya zauna yana dannawa a hankali.
Tasowa tayi cikin dauriya ta dawo kusa dashi kan kujerar da yake ta zauna ta kalle shi taga ba ita yake kallo ba tace, "kayi hak'uri in nayi maka laifi." Cak ya tsaya da danna laptop d'in da yake yi ya juyo ya kalle ta ya d'auke kansa ya cigaba da aikin sa ba tare da yace komai ba, Rauda tace, "Bana so nayi magana ayi min banza Allah ya sani" ta furta cikin nuna rashin jin daɗin ta ga hakan kamar zatayi masa kuka.
Nan ma yayi mata banza bai kula ta ba ta yunk'ura zata tashi ya rik'o hannunta ta tsaya ba tare da ta juyo ba ya dawo da ita ta zauna kusa dashi har lokacin bai cika hannun ta ba, baice komai ba ya cigaba da aikin sa wayar sa ta sake yin k'ara ya kalla yaga number Egypt yaja k'aramin tsaki ya d'auka ya danna a speaker ba tare da yayi magana ba. Daga can b'angaren Muhibba ta sauke ajiyar zuciya tace, "finally u pick my call. Ni ko baza kayi min magana ba indai nasan kana jina hakan yayi min, ina Sister na?."
Gaban Rauda ya fad'i jin abinda take cewa bata san lokacin da ta kashe wayar ba ya kalle ta itama ta kalle shi tace, "Haushin ta nake ji." Sai ya murmusa kad'an baice mata komai ba itama tayi shiru bata ce komai ba. Suna nan zaune hannun ta yana cikin nasa ya rik'e yana murza tafin hannun ta a hankali ba tare da yace mata komai ba. Rauda wani iri take ji a jikin ta taja hannun ta zata kwace ya kuma riƙewa yak'i bata damar hakan sai ta kalle shi tace, "Meyasa baka ce mata ni matar ka bace?."
Bai daina abinda yake yi ba kusan sacan goma da yin maganar tata kana yace, "Meyasa baki ce ba ke?." Mamakin abinda yace tayi ta kalle shi tace, "fad'ar a kanka yake ai bani ba sabida ban santa ba." Murmushi ya kumayi bai ce komai ba itama bata kuma magana ba amma taji dad'i da taga yayi murmushi.
Sallar magariba ce ta tashe shi yaje masallacin hotel d'in yayi sallah bayan ya idar ya dawo yayi wanka ya saka doguwar riga fara sai kyalli take ya d'auko key na mota da wayar sa ya fito falon.
A zaune ya ganta da alama tayi wanka dan yaga ba kayan d'azu ne a jikin ta ba doguwar riga ce mai mayafi a jikin ta ya kalle ta yace, "Let go" abinda yace kenan ya fita ta bishi da kallo tace, "ko ina zamu je oho, bama ku fita d'in ba ya kasa yi maka magana" ta fad'a tana yafa mayafin tabi bayan sa ya kulle k'ofar suka shiga elevator suka sauka.
Basu wuce ko ina ba sai The Egyptian museum Cairo, inda komai na tarihi yake tun daga kan gawar fir'auna har zuwa kayan tarihin da ya faru ka k'asar misra akwai shi a wajan.
Sun sha wayo kasancewar sa babba d'an masu mulki kuma wanda yayi karatu a k'asar labarawa shugaban mai kula da wajan ya san shi har inda gawar fir'auna take ta asali sai da suka je, ba'a nunawa mutane ta asalin sai wacce sukayi creating suka ajjiye manyan mutane ake nunawa ta asalin Asad da Rauda sun shiga cikin su.
Ana ta nuna musu Rauda sai d'aukar hoto take hannun ta yana cikin nasa ya lura da tayi farin cikin zuwa wajan shiyasa shima yaji dad'in zuwan. Rauda mamakin yadda aka sanshi kawai take yi wani b'angaren na zuciyar taji farin cikin hakan wani b'angaren akasin sa.
Bayan sun gama da nan suka wuce shogun Japanese Restaurant baban gidan abinci a k'asar Egypt cikin garin Cairo, suka zauna a teburan da aka tanada har lokacin murmushi take yi ya kalle ta suka had'a ido sai yayi murmushi shima sai ta kulle fuskar ta. Yanayin garin larabawan yana burge Rauda ganin dare yayi amma kamar ba dare ba mutane sai zirga-zirga suke abin su.
Abinda suka yi order aka kawo musu suka fara ci juyawar da Rauda zatayi taga Muhibba a bayan su sai murmushi take musu, k'aramin tsaki taja ta dawo da kallon ta gare shi ya kalle ta alamun meya faru tace, "bakuwar kace."
Muhibba ya gani ta k'araso ta zauna kusa dashi tana kallon sa tace, "banyi niyar zuwa joint d'in nan ba ashe rabon zan ganka ya fito dani." Baice komai ba ta kalli Rauda tace, "Sister ya kike?." A dakike Rauda ta amsa mata ta sake dawo da kallon ta ga Asad tace, "Handsome kayi min magana please." Nan ma baice komai ba hannun sa guda d'aya da yake kan table d'in ta d'ora nata a kai yana kallon ta shi kuma ya tsaya cak da cin abincin.
Kallon hannun nasa yayi ya kalle ta bata d'auke hannun ta sai murmushi da take masa tace, "please talk." Asad ya kalli Rauda yaga itama shi take kallo ya kalli Muhibba ya janye hannun sa kana yace, "Depriving me abeg."
"I can't Handsome, I love you so much, I want to be your wife forever. Please allow me to show u how much I love you abeg."
Yatsun sa ya murza ya nuna Rauda da yatsa yana kallon Muhibba yace, "She's my wife, so respect yourself and stay away from me." A tare k'irjin mata biyu ya buga Muhibba ta kalli Rauda itama Raudan kallon ta take yi kafin Muhibba tayi murmushi tace, "Nooo Handsome you must be joking, nasan baka da aure don kana sona rabu dakai kar kayi min k'arya." Banza yayi mata ya girgiza kansa ta kuka cewa, "ba wasa nake ba ina sonka, ka kalle ni ina da kyau da ilimi zan dace da rayuwar ka. Please and please ka taimake ni."