Sashe 42
Kwantan Bauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama tace, "haka yayi ki fad'a masa yadda akayi sai ki sanar dani, a wannan karon kar ya bamu matsala dan Allah."
"Shi d'in banza" ta fad'a tana murmushi. Mama tace, "Ya kamata a fara shiri fa dan nasan bikin nad'in nasa bazai wuce juma'a ba kuma kin san da bikin auren sa za'a had'a a huta, ki fad'a Jidda ta fara shirin zama mata ga sarkin Katagum" ta fad'a tana kallon Mum tana murmushi.
Mum ta sake washe bakin ta tace, "Ai wannan maganar kamar a kunnen ta ranki ya dad'e, za'a sha murna kuwa dan kwana biyu kwana take kuka." Mama tayi dariya kad'an bata ce komai ba Mum tace, "ya tsarin zaman gidan yake a ina zata zauna ranki ya dad'e?." Mama tace, "Zata zauna a apartment d'in kusa dana mai martaba dan aiki ma an gama zance, an gyara inda mai martaba ya tashi itama an gyara mata nata su kawai ake jira su shigo."
Mum tace, "Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Mama tace, "Amin." Daga haka taja bakin ta tayi shiru Mum tayi murmushi a zuciyar ta tana fad'in, _Lokaci yazo Rabi'atu, lokacin da zan kwace duk wata isar da kike ji da ita tazo, lokacin da komai zai dawo hannuna yazo, lokacin da zan zama uwar sarki a madadin ki yazo, lokacin da zan ajjiye ki a gefe ki koma tamkar hoto yazo, lokacin da y'ata zata zamar miki ciwon ido yazo. Asad zai zama tamkar k'aramin yaro ne sai abinda Jidda taso zaiyi, ita zata sarrafa shi yadda take so bazan yi sake ba nafi kowa sanin halin ki sai na tabbatar da y'ata ta zama sama da kowa a masarautar katagum._
Mama ta kalle ta taga tana ta murmushi ita kad'ai tana kuma d'an kad'a kai alamun tunani take yi tace, "tunanin me kike yi?." Ta kalli Mama tace, "tunani nake burin k'awata kuma shugabata ya kusa cika ina tuna irin farin cikin da zakiyi a duk sanda aka d'ora Asad a wannan kujera, tuna zaki farin ciki shine yake bani ninkin farin ciki."
Mama ta murmusa tace, "gab burina yake da cika kam, zan mallaki abinda na jima ina fata, a bayyane Asad zai kasance sarki ne amma a b'oye zan kasance nice nake mulki domin kuwa sai abinda nace yayi sannan zanyi. Lokaci yayi da Rukayya da Sa'adatu zasu san ni ba sa'ar yin su bace."
Kallon ta Mum take yi tana maganar tana bata amsa a zuciyarta tana fad'in, _K'arya kike wallahi kema baya zaki koma duk wannan jin kan naki sai na sauke shi domin komai naki a tafin hannuna yake, sai na nuna miki nima bata wasa bace ba._ A bayyane kuma sai tace, "Haka ne ranki ya dad'e, zamuyi abinda muke za kuma mu bar abinda muke so." Mama tayi dariyar nishad'i tana kallon Mum tana taya ta a zuciyarta tana fad'in, _Anzo wajan Rabi'atu!._
_Fan's nima nace Anzo wajan._👐🏼👨🏻🦯🤐[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*047.*
Takawa take a hankali tana k'arewa gidan kallo ganin harda wajan ajjiye mota guda d'aya, dan kyau gidan yayi kyau ta juya tana zagawa tare da d'aga kai tana kallon gidan. Kai ta girgiza gaban ta na tsananta bugawa a bayyane tace, "Ina amfanin wannan hidimar an wulak'anta maka diya?" Ta fad'a tana jan jakar ta zuwa k'ofar da ta gani tana kallon ta.
K'ofar mai kyau kalar kofi ta tura ta ta shiga a lokacin Sammani yana niyar fitowa, kallon kallo suke yana kallon ta tana kallon sa da murmushi dan taga alamun bai gane ta ba, y'ar dariya tayi cikin k'arfin hali tace, "Sammani ya dai?." Sai kuwa yace, "La wallahi ita, Anty Rauda ta dawo!" Ya koma a guje yana faman kiran Anty Rauda ta dawo. Dariya tayi ta kalli inda ya fito taga tsakar gida ne babba gabad'ayan sa tiles ne a k'asan sa gefe ga matattakalan sama ita duka tiles tabi inda Sammani yabi tana jiyo ihun sa har lokacin.
"Anty Raudaaaaa!" Aka fad'a da k'arfi lokacin da ta shiga babban falo madaidaici mai kyau mai d'auke da kujeru madaidaita da carpet har da tv bango da a.c da fridge. Ummulkhairi ta gani a guje ta rungume ta tana ihu ta rik'e ta itama tana cewa, "Ke zaki yar dani." Ta d'aga ta tana kallon ta tace, "Anty Rauda kinga yadda kika koma kuwa? Kinyi kyau kinyi kib'a gashi kina tafiya." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba ta juya ta kalli Khalil da ya shigo shima ya rik'e ta yana ihu tayi dariya tace, "Ina Rahma take?." Ummulkhairi tace, "tana gidan Yaya Ummi, kinga gidan da muka dawo muma mun zama y'an gayu."
Rauda tace, "Ina Umma da Inna suke kun barni Ina ta zuba ban gansu ba" ta fad'a tana yin gaba suka bita a baya Khalil yana jan jakar ta zasu shiga wajan Umma suna ga Inna ta fito daga wata k'ofa tana fad'in, "Ashe da gaske kece Rauda, Tabd'ijam wannan in a hanya na ganki ai bazan gane ki ba." Rauda tayi dariya suka gaisa cikin farin ciki kafin ta shiga wajan Umma.
Ihun su ne ya tashi Umma daga bacci ta fito daga d'aki tana tambayar lafiya taga Rauda na shigo k'aramin falon Umman ta nufe ta da sauri ta fad'a jikinta tana fad'in, "Nayi kewar ki Ummana." Umma da mamaki da farin ciki tace, "Rauda! Saukar yaushe?" Ta fad'a da mamaki da farin ciki tana kallon ta. Rauda ta d'ago daga jikin ta tace, "Umma wallahi nayi kewar ki sosai." Umma tayi dariya tace, "Muma duka munyi kewar ki. Alhamdulillah lafiya ta samu Rauda kece kike tafiya da k'afafun ki?."
"Anty Rauda ina tsarabar mu?" Khalil ya katse su ta kalle shi Umma ta riga ta magana tace, "Kwa dai barta ta huta dai tukunna kwa tambayi tsarabar." Rauda tabi falon Umman da kallo ganin sa ba kai girman na farko ba amma mai kyau komai akwai a ciki sa kamar waccan Umma ta kalle ta tayi murmushi tace, "Ki huta duka za'a baki labari, shiga ciki kiyi wanka ki samu ki kwanta duk da tafiyar jirgi gani nake ai ba wata wahala sai dai zuwa nan daga bauchi."
"Ummana Ina Baba?." Umma tace, "Ya fita amma nan da anjima zaki ganshi." Rauda ta shiga d'akin Ummulkhairi ta biyo ta da jaka duk suka mara mata baya gabad'aya dok'in ganinta suke yi gani suke kamar an canja ta. D'akin babba mai d'auke da kayan gado komai akwai harda carpet a tsakiya ga band'aki a ciki ta girgiza kai tace, "Lallai da gaske kike Khairi mun koma y'an gayu" ta fad'a tana shiga band'akin zuciyar a cushe.
Wanka tayi da alwala ta fito har lokacin suna nan tayi dariya ita kanta taji dad'in ganin k'annen nata ta kalli Khairi tace, "Ina kayana na wancan gidan?." Khairi ta mik'e ta bud'e mata wardrobe tace, "gasu a ciki." Ta kalle su tace, "to ku bani waje zan shirya." Ba musu duk suka fita tayi dariya ta d'auko riga da zani cikin kayan ta ta saka ta tayar da sallar la'asar da take kanta bayan ta idar Ummulkhairi ta shigo mata da abinci.
Karb'ar abincin tayi taci kad'an bada yawa ba kafin ta ajjiye ta kwanta amma sai ta kasa baccin. Babban tashin hankalin ta abinda zata fad'a musu in suka tambaye ta hakan ya saka ta dinga juyi a haka baccin ya d'auke ta.
Sai magriba ta tashi tunda ta tashi take jin hayaniya ta k'aru bata fita ba sai da tayi sallar magriba sannan ta fito falon sai kuwa akayi ihuu Rahma ta tawo a guje ta rik'e ta tana murnar ganin ta, itama rik'en ta tayi tace, "Nayi kewar ki Rahma."
"Nima haka Anty Rauda, kinyi kyau har fari kinyi ko bleaching kika fara a can?." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba Rahma ta kuma cewa, "Kan uba! Kinji fatar hannun ki laushi kamar audiga." Ita dai bata ce komai ba ta tawo cikin falon dan taga Baba a zaune ta k'arasa ta durk'usa har k'asa tace, "Barka da dare Baba."
Baba ya kasa rufe baki sai dashe hak'ora yake yi yace, "lafiya lau yar albarka. K'afa tayi lafiya ko?."
"Eh Baba."
"Ma sha Allah, haka ake so ai. Kinga gidan mu yadda ya koma ko ta dalilin ki?." Gaban Rauda ya yanke ya fad'i tayi murmushi kawai bata ce komai ba kafin Baba ya kuma cewa, "Tare kuka dawo dashi mijin ki?." Gaban ta ya tsananta bugawa tace, "Eh tare muke."
Baba ya sake washe bakin sa farin ciki yake ji kamar ya goya Rauda sabida alkhairin da ta kawo masa kana yace, "Shi ya kawo ki nan?." Rauda had'd'iye yawu tace, "A'a ya saka a kawo ni ya wuce gida zaizo daga baya yace." Baba ya sake sakin murmushi yace, "Allah sarki d'an albarka." Rauda dai bata iya cewa wani abun ba kuma jikinta yayi sanyi har Umma ta lura da hakan Baba yace, "Bara na fita na samo miki gashashiyar kaza kici dan nasan bakin naki ya saba da cin kazar larabawa" ya fad'a yana fita Umma ta bishi da kallon mamaki.
Gabad'aya Rauda ta bar nutsuwar ta had'a idanun da sukayi da Umma sai ta d'an wayance tayi murmushi tana sosa kai k'annen ta suka fara bata labari wannan yace ga abinda ya faru wannan ma ya fad'a haka suka deb'e mata kewa har akayi sallar i'sha tayi sallah ta shiga d'akin da tayi wanka d'azu.
Umma ce ta biyo bayan ta ta ganta a zaune tayi tagumi fuskar ta gabad'aya ta nuna damuwa k'arara ta zauna kusa da ita tace, "Rauda akwai wani abun ne naga kin canja gabad'aya?." Rauda ta kalli Umman cikin alamu na rashin gaskiya tace, "Babu komai Umma. Nayi mamakin gama gidan nan cikin y'an kwanaki haka Umma, ki duba yadda yayi kyau kamar anyi shekara anayi" ta fad'a dan ta kawar da waccan maganar.